Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/401 Albishiri ga Afirka (Good News for Africa)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/401)
Albishiri ga Afirka Good News for Africa
Masauraro, albishirinku! Ƙungiyar Lafiya ta Duniya ta bada labarin cewa akwai yiwuwar kafin ƙarshen shekara ta dubu biyu da tara za a samu sabon allurar rigakafin Sanƙarau mara tsada. <> Listeners, here’s some good news for you! The World Health Organization has announced that it is possible that by the end of the year 2009 there will be a new inexpensive meningitis immunization injection.
A yayin da yanzu sauran kimanin watani uku kamin a fita daga lokacin da aka fi ganin annobar ciwon sanƙarau, bala’in annonba ta ƙasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kashe daruruwan mutane. <> With about three more months remaining before the end of the season in which meningitis is most prevalent, this epidemic has killed hundreds in Burkina Faso and in the Central African Republic.
Ƙasashen Afirka da suka kama daga Senegal zuwa Ethiopia nan ne aka fi fama da matsalar annobar sankarau. Fiye da kashi biyu daga cikin uku na waɗanda ke kamuwa da ciwon a duk faɗin duniya, suna a wannan yankin. A bana kawai kimanin mutane ɗari uku da hamsin suka mutu a kasar Burkina Faso, a saboda sanƙarau. <> The African countries that stretch from Senegal to Ethiopia comprise the area that suffers the most from the meningitis epidemic. More than two-thirds of the world's cases of this disease occur in this region. This year alone, about 350 people died from meningitis in Burkina Faso.
Ƙwayar cutar wannan ciwo kan kai wa wani layi da ke kewaye da ƙwaƙwalwa da kuma ƙashin baya hari. Ko da an yi jinya ma, an bayyana cewa kimanin kashi goma daga cikin dari na waɗanda suka kamu da ciwon suka mutu. <> The bacteria that cause this disease attack the lining around the brain and spinal cord. Even with treatment, it is said that about 10 percent of meningitis patients die.
An kuma fi ganin annobar sanƙarau ne a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yuni. <> Most meningitis cases occur between January and June.