Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/402 Noman Makamashi a Nijeriya (Growing Fuel in Nigeria)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/402)
Noman Makamashi a Nijeriya <>
Growing Fuel in Nigeria
Mar Karanta Labari: Hukumar Makamashi ta ƙasar Nijeriya ta haɗa gwiwa da gwamnatin jihar Kano da kuma wasu kamfanoni sun shirya wan taron bita na kwanaki uku domin faɗakar da manoma a kan noman itacen Bini-da-zugu, ko Bindargu, wanda ke samar da makamashi. Daga Kanon Dabo ga Muhammad Salisu Rabi’u da ci-gaban labarin. <> Announcer: The Nigerian National Energy Commission is collaborating with the Kano State government and several companies to hold a three-day workshop to educate farmers on growing jatropha, which is used to create fuel. From Kano, here is Muhammad Salisu Rabi’u with the continuation of the story.
Muhammad Salisu Rabi’u: Da nake yi tattanawa da shi bayan buɗe bitar shugaban Hukumar Makamashi ta ƙasa farfasa Abubakar Sani Sambo, ya ce in har manoma suka karɓi noman Bini-da-zugu hannu bibbiyu, to, babu shakka za su sami riba mai tarin yawa. <> Muhammad Salisu Rabi’u: When I was speaking with him after the opening of the workshop, the director general of the National Energy Commission, Professor Abubakar Sani Sambo, said that if the farmers really do adopt the cultivation of jatropha for energy production, there is no doubt that they will see a lot of profit.
Abubakar Sani Sambo: Riban da yake da shi suna dayawa ƙwarai. Na farko idan suka ci gaba da shuka abin da suka saba kama a ce gero ko masara haka suna iya sake tsakankani. Shi kuma wanda ya cire shi daga baya, sayar da shi, duk nan gaba kaɗan za a ga za a fara nema irin. Duk irin ne za a tace a samu mai. Saboda haka yana da alfanu ƙwarai da gaske. Zai taimaki manoma don daɗa samun kuɗi, wanda zai taimaki harkokin nomansu. <> Abubakar Sani Sambo: There are many benefits in this. First of all, if they continue to plant what they usually plant, like millet or corn, they can plant this in between. Then afterwards, it can be cut down and sold. Soon, these seeds will be in demand. It is these seeds that will be turned into fuel. Because of that, it has a huge value. This will help farmers add to their earnings, which helps the farming business.
Muhammad Salisu Rabi’u: A baya gwamnatoci sun sha fito da irin wannan tsari, amma manoma in sun noma ana barinshi da shi. Ko wane ƙuduri kuke da shi na ganin lalle ba a bar manoma da wannan abin da za su noma ba? <> Muhammad Salisu Rabi’u: Governments have often created this kind of program in the past, but after the farmers grew it they were left with it. What sort of plan do you have to make sure that the farmers will not be left holding what they grow?
Abubakar Sani Sambo: Abin dai waɗancan na baya da wul ga an fetsar an watsar, watau ba a tsara da kyau ba. A taƙaice zan ce maka shi wannan Bini-da-zugu ba zai kawo matsala ba irin na waɗancan. Idan aka fara ba yadda za a yi watsa da shi. <> Abubakar Sani Sambo: The thing with those programs that were so quickly abandoned in the past is that they were not well planned. In short, I can tell you that this jatropha will not present that kind of problem. If this gets started, there is no way that it will be abandoned.
Muhammad Salisu Rabi’u: Farfasa Abubukar Sani Samba kenan. A ɓangarensa, shugaban Kwamitin Makamashi na gwamnatin Kano, farfasa Abdu Salihi ya bayyana dalilin da ya sa suka haɗa gwiwa da Hukumar Makamashi ta ƙasa don gudana da bita a jihar Kano. <> Muhammad Salisu Rabi’u: That was Professor Abubakar Sani Sambo. For his part, the director of the Kano State Power Committee, Professor Abdu Salihi, explained the reason why they collaborated with the National Energy Commission to hold this workshop in Kano State.
Abdu Salihi: Na farko abu ne wanda yake na alheri. Muka ga yana ci gaba a duniya baki ɗaya koma ga cewan a Kano muna da wannan abu a banza a zube tun ma muna yara. Saboda haka muka ga dama ce da manomanmu za su samu su ma su shiga wannan harka ta noman Bini-da-zugu. Kuma, da sai lokaci guda mu samu dizal din da idan babban manomi ne kai za ka iya sawa a tantan dinka misali ka kyautata nomanka. Idan ƙaramin manomi ne za ka iya sayarwa ka samu kuɗi. <> Abdu Salihi: First of all, it is something that is beneficial. We saw it spreading around the world, and in Kano, we saw it going to waste all around us since our childhood. Because of this, we saw that there was an opportunity for the farmers to get into this business of cultivating jatropha. And, at the same time, we get this diesel, which, if you are a large-scale farmer, you can use it in your tractors to improve your farming, and if you are a small-scale farmer, you can sell it for cash.
Muhammad Salisu Rabi’u: Wane hanyoyi za ku amfani da shi wajen ilimintar da mutane domin su amshi noman wannan Bini-da-zugu? <> Muhammad Salisu Rabi’u: What methods are you using to educate people so that they accept this jatropha?
Abdu Salihi: To, hanya ta farko dai shi ne kamar yanda an gani a wannan taron da muka shirya. Mutane sun sani, kuma ko da an gama muna fatan ku ‘yan jaridu za ku aiki tare da mu wajen ci gaba da nanatawa da maimaita musu. Mu kuma kama yanda na ce za mu je wurin gwamnatin jiha, domin ta ɗau nauyin samo iri wanda za mu rarraba wa manoma domin su shuka cikin damana nan in sha Allahu. <> Abdu Salihi: Well, the first method is just what is occurring at this conference that we are holding. People are learning about it. And, even after the conference ends, we hope that you journalists will work with us to continue to remind the farmers and to reinforce it. As for us, as I said, we will ask the state government to take responsibility for procuring the seeds, which we will distribute to the farmers to plant this rainy season, Lord willing.
Muhammad Salisu Rabi’u: Wane mataki za ku ɗauka a wannan karon don ganin in manomi ya noma yana da wurin da zai sayar? <> Muhammad Salisu Rabi’u: What steps will you take this time to ensure that if a farmer grows it he will have a market for it?
Abdu Salihi: Ai, na baya watakila za a ga abu ne wanda yake shi manomin ba zai iya amfani da shi ba. In ba a samu mai sayar ba, sai ya zama asara. Wannan, ai abu ne wanda kama idan ka ji za ka iya amfani da shi a janaratorka zaka amfani da shi a tantan ɗinka zaka iya amfani da shi motar da ake zuba wa dizal din. Shi kansa za ka iya ma amfani da shi wajen kunna fitila. Zamu koyar da kowa yanda ake tacen man nan, kuma muna da injunan tacen mai dayawa dama a jihar Kano, saboda haka ba matsala ba ce in sha Allahu. <> Abdu Salihi: Well, in past programs, you see, it was something that the farmer had no use for. If there were no buyers, it was a loss. This, um, is something that, you see, you will be able to use in your generator, in your tractor, and in a diesel car. This same thing can be used in your lantern. We will teach everyone how it is refined, and we already have a lot of oil refining machines in Kano. Because of that, it won’t be a problem, Lord willing.
Muhammad Salisu Rabi’u: Farfesa Abdu Salihi kenan. Da yake jawabi, mataimakin gwamnan Kano Injinya Abdulahi Tijani Gwarzo ya ce samo wannan dabara ta noman Bini-da-zugu don samar da mai zai taimaka wajen magance matsalar makamashi. Don haka ya jadada ƙudurin gwamnatin jiha na tallafa wa manoma domin su noma Bini-da-zugun ka’in da na’in. <> Muhammad Salisu Rabi’u: That was Professor Abdu Salihi. In his speech, the deputy governor of Kano and engineer, Abdulahi Tijani Gwarzo, said that this idea of farming jatropha for fuel will help to address the energy problem. Because of that, he re-emphasized the resolution of the state government to aid farmers in cultivating jatropha on a large scale.
Abdulahi Gwarzo: Gwamnati na goyon bayan wannan tsari. Za kuma ta tsaya domin a taimaki manoma su noma. Zai taimaka wajen ƙara tattalin arziki ga mutanenmu. Za a samu abin yi, za a kuma samu abin da za su saya su samu abin yau da kullum. <> Abdulahi Gwarzo: The government supports this plan. It will stand behind it in order to help farmers in their farming. This will help our people economically. It will provide work, and it will provide something to sell so as to provide for their daily needs.
Muhammad Salisu Rabi’u: Injinya Abdulahi Gwarzo kenan. Masana dai sun yi bayyanin cewa bayan man dizal da ake samu a jikin ‘ya’yan Bini-da-zugu, akan kuma samu sinadaran da kamfanonin harhaɗa magunguna da na yin takin zamani ke yin amfani da su. Muhammad Salisu Rabi’u, Muryar Amurka, daga kano Nijeriya. <> Muhammad Salisu Rabi’u: That was Injinya Abdulahi Gwarzo. Experts say that in addition to the diesel that can be obtained from jatropha seeds, it is also possible to obtain chemicals that pharmaceutical companies and fertilizer companies use. This is Muhammad Salisu Rabi’u, Voice of America, from Kano, Nigeria.