(Redirected from GLOSS/403)
Kurkunu | <> | The Guinea Worm |
Jama’a barkanmu da war haka. Ni ne Janar Yakubu Gowon. | <> | Greetings to all of you. This is General Yakubu Gowon. |
Ina kira ga kowa da kowa domin mu yi himmar kawar da wannan mugun cutar kurkunu. | <> | I am calling on everyone to put forth a real effort to eradicate the horrible Guinea worm disease. |
Ina kiranku da ku taka taku rawar domin kawar da wannan cutar ɗungum daga ƙasarmu. Ku bada taku gudumawar wajen hana duk mai ciwon kurkunu shiga wata ƙofar samu ruwan sha. Ku bada taku gudumawar ta hanyar tsabtacce ko tace ruwa da za a sha. Ku bada taku gudumawar ta kai da rahoton ɓullar cutar kurkunu ga ma’aikatar kiwon lafiya mafi kusa. | <> | I am calling on you to do your part to eradicate this disease completely from our country. Make your contribution by preventing anyone who is suffering with Guinea worm from entering a source of drinking water. Make your contribution by purifying or filtering drinking water. Make your contribution by reporting any outbreak of Guinea worm to the nearest Health Ministry office. |
Taka taku rawar a koyaushe domin tsayar da cutar kurkunu yanzu. Domin tabbatar da ci-gaban tattalin arzikinku, da tabbatar da lafiyarku. Ku bada taku gudumawar domin kawar da wannan cutar kurkunu a yanzu. | <> | Do your part all of the time to stop Guinea worm now, to ensure your economic future and to protect your health. Make your contribution to eradicate Guinea worm now. |
Duniya tana gab da kawar da wannan mummunar cuta. Saboda wannan, to sa dole ne mu haɗa hannu da ƙarfi wajen yaƙi da wannan cutar kurkunu. | <> | The world is on the verge of eradicating this horrible disease. Because of that, it is necessary that we work together to fight Guinea worm disease. |
Kowa yana da muhimmin matsayi. A tuna, a koyaushe, hana ta, guje mata, tace ta, kai labarin ɓullarta. | <> | Everyone has an important role. Always remember: prevent it, avoid it, filter it, and report it. |