(Redirected from GLOSS/405)
Ku Bar Shan Taba! | <> | Quit Smoking! |
Jama’a salama alaikum. Ya kamata kowane mai shan taba sigari ya zo kusa ya saurara. | <> | Greetings everyone. Every smoker should listen carefully. |
Muna da sabon shirin da muka kafa a asibitin Murtala. Wannan shiri zai taimaki duk wanda yake so ya bar shan taba. Ya kamata masu shan taba su zo su samu taimako. | <> | We have created a new program at the Murtala Hospital. This is a program that will help anyone who wants to quit smoking. Smokers should come and get help. |
Ku tuna fa: | <> | Remember: |
|
<> |
|
Amma mun san da cewa barin shan taba na da wuya. Saboda haka za mu bada taimako ga duk wanda yake so ya bar shan taba. Ku zo asibitin Murtala. Ku nemi dokta Ali Laminu. Shi ne ke jagorancin wannan shiri. | <> | However, we also understand that quitting is difficult. That is why we are offering help to anyone who smokes. Come to the Murtala Hospital. Ask for Doctor Ali Laminu. He is the director of this program. |
Ga wasu bayanai game da shan taba sigari: | <> | Here are some facts about smoking: |
|
<> |
|
A tuna, shan taba na kawo illoli daban daban. Haka kuma shan taba yana zama wa mutum jaraba. Watau, yana kama mutum. Saboda haka ku zo ku samu taimako. Za ku iya daina shan taba. | <> | Remember, smoking has numerous ill effects. Also, smoking is addictive. It catches hold of a person. So come and get help. You can quit smoking. |
Ku zo asibitin Murtala. Ku tuntuɓi dokta Ali Laminu. Za ku samu taimako. | <> | Come to the Murtala Hospital. Talk to doctor Ali Laminu; you will get help. |
Allah ya bada lafiya. | <> | May God give you health. |