(Redirected from GLOSS/405soc)
See also: UMD_NFLC_Hausa_Lessons/17_An_Esteemed_Media_Veteran_Retires
Steve Lucas Ya Yi Ban Kwana | <> | Steve Lucas Says Goodbye |
Ibrahim Alfa Ahmed: To, mun tattanawa, kamar yadda na ce, da shi Steve Lucas tare da mai ɗakinsa Fatima. Kuma na fara da tambayarshi Steve ko mi ya sa ya yi niyya, ko kuma ya yanke shawara cewa zai yi ritaya a wannan lokaci. Sai ya bada amsa yana cewa: | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: Well, we spoke, as I said, with Steve Lucas, along with his wife Fatima. And, I started by asking Steve why he intends, or rather, why he made the decision to retire now. He answered by saying the following: |
Steve Lucas: To, babban dalili shi ne na yi na share kusan shekara ashirin da biyar, ashirin da huɗu daidai ne. To, kuma, ah, muna da gida a can Niamey. Na ce hakan ya isa. Ah, ɗiyata, yanzu ta kai shekara ukku. Ina so ta girma a Niger, ta koyi, ta ɗauki halayen mutane can. Ah, ka san Amurka, yara in suna tashi, suna, ah, ana sakaci da yadda suke, suke girma. Ba ni so wannan ya faru da ita. Ah, shi ne babban dalili. | <> | Steve Lucas: Well, the main reason is that I have done, or I have worked for nearly 25 years, 24 to be precise. And, well, we have a house over in Niamey. I decided that it was enough. Um, my daughter is three years old now. I want her to grow up in Niger so that she will learn to adopt the ways of the people there. Um, you know, in America, as children grow up, um, people become careless with how, um, how children grow up. I don’t want that to happen with her. So, that is the main reason. |
Ibrahim Alfa Ahmed: Fatima, kin goyi bayan wannan shawara da ya yanke ta cewa zai yi ritaya a wannan lokaci, ku koma baki ɗaya ku zauna a Nijar? | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: Fatima, do you support this decision he made to retire now, so that you can return to Niger to live there? |
Fatima: To, E, na, na goyi bayanshi gaskiya, don bayan shekara ashirin da huɗu na aiki, to, ya kai lokacin da zai yi, ya ɗauki retirement kin shi, ya je ya huta. Ya huta, kuma mu zamna a gida da … ai ni ma ina jin daɗin komawa a Nijar. | <> | Fatima: Well, yes, I, I really do support him because after 24 years of working, well, it is time for him to take his retirement and rest. He can rest, and we can live at home, and I’m also glad to be returning to Niger. |
Ibrahim Alfa Ahmed: Steve, ah, zan jefa wannan tambaya da dukanku za ku iya amsawa. Wane abu ne kuka yi la’akari da shi a kan cewa idan ka yi ritaya ba za ku zauna a nan Amurka? Na san ka yi batun tarbiyyan yara, kuma kana so ɗiyarka ta tashi a can. Amma kamar wasu abubuwa ne ka duba kafin kun yanki shawara cewa za ku koma Nijar baki daya da zama? | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: Steve, um, I’m going to throw this question out there, and both of you can answer it. What did you take into consideration when you decided that when you retire, you would not live here in America? I know you mentioned your concern for children to have a proper upbringing and that you want your daughter to grow up there, but what other things did you look at before making the decision to move to Niger for good? |
Steve Lucas: Ai, to, dalilai suna dayawa. Kuma da wuya a tsaya ana tattauna kowanensu. A ƙarshen gaskiya, ah, zama a Nijar ya fi sauƙi ga lafiyar jiki. Babu hauhawan jini. Babu irin hayaniya irin da ake samu a wurin aiki. Saboda haka, yadda ta Fati ta ce, zan iya in dan huta can cikin salin-alin. | <> | Steve Lucas: Oh, you know, there are so many reasons. It would be hard to explain all of them right now. What it comes down to is that, um, living in Niger is easier on a person in terms of health. There is no stress, none of the hubbub that one finds in the workplace. That’s why, like Fati said, I will be able to rest and get some peace. |
Fatima: Kuma tun bayan mun yi aure, ni na fita daga Nijar. Ai mun yi garuruwa dayawa. So yanzu, ina so in koma Nijar in zamna tare da iyali da komi mu ji daɗi … | <> | Fatima: Also, after we got married, I left Niger, and we have lived in a lot of towns. So, now I want to return to Niger to live together with my family and everything else and enjoy… |
Ibrahim Alfa Ahmed: Watau dai, keywayar Nijar ce ah babban dalilin ke a ɓangarenki, ah dalilin komawa can Nijar. | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: So then, for you, going back to Niger is the main reason for moving to Niger? |
Fatima: E gaskiya. E gaskiya. | <> | Fatima: Yeah, absolutely, absolutely. |
Ibrahim Alfa Ahmed: To, mi ya sa ba ku yanke shawara cewa alal ga misali za ku koma Nijeriya da zama ba? | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: So, why didn’t you decide, for example, that you would move to Nigeria? |
Fatima: E, Nijar da Nijeriya duk guda ne, amma na tashi a Nijar. Na girma a Nijar. Na san mutane da yanzu ina tunaninsu ina so kullum in koma in ganesu. | <> | Fatima: Oh, Nigeria and Niger are both fine, but I grew up in Niger. I spent my childhood there. I know a lot of people there who I constantly miss, and I want to go back and see them. |
Steve Lucas: Kai kuma Ibrahim, ka san dai ba zan zamna a Nijar kaɗai ba. Zan rinka kewayawa. Bauci zai sha ganina. | <> | Steve Lucas: And, Ibrahim, you know, I am not going to just stay in Niger. I am going to keep traveling. Bauchi is going to see plenty of me. |
Ibrahim Alfa Ahmed: Haka yake. Ah, Steve, kamar idan yanzu, ah, kuka koma Nijar ɗin nan, ta yaya za ka yi? Kamar ka saba cewa shekaru aru-aru ɗin nan da suka shige, kullum kana zuwa aiki da sauransu haka. Ta yaya za ka ji? Ba za ka ji kamar wani dabam ba haka yanzu cewa ba za ka tashe cewa kullum karfe takwas kana hanyan ofis, karfe huɗu kuma kana kokowan shiga jirgi koma gida ba? | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: There you go. Um, Steve, when, um, you move to Niger, what are you going to do? You have gotten accustomed to going to work and such for all these years, so what are you going to do? Won’t you feel strange now that you won’t be getting up and heading off to the office at eight and then fighting your way to get on the train to go home at four? |
Steve Lucas: Ban tsamani wannan zai faru ba, saboda lokacin da muka je can hutu, ah, a watan Febrairu da kuma Maris, na gaya wa matata cewa bari in rubuta musu, kawai, su sa takarduna na ritaya. To, wannan ba zai zama wata wahala a gareni ba. | <> | Steve Lucas: I don’t think that will happen because when we went there for vacation in February and March, I said to my wife, “Why don’t I just submit my letter of resignation and take my retirement.” So, I don’t think that this will be a problem for me. |
Ibrahim Alfa Ahmed: To, haka. Ai. To, kamar yanzu idan kun koma, wasu abubuwa ne za ku yi? | <> | Ibrahim Alfa Ahmed: Well, great. Um, so now, when you move, what are you going to do? |
Steve Lucas: Ai, to, wannan, alhalin, a yanda abubuwa ke ɓullo mana, za mu dan gwada. Ba zan ce "ga takamaiman abin da za a yi" ba, saboda Allah kaɗai ya san gobe. Mu kuma za mu, za mu dan huta da, ah, da farko. Sa’anan mu ji yanda za mu yi. | <> | Steve Lucas: Well, as for that, certainly as things come up, we will take a look. I am not going to say “here is what is precisely going to happen,” because only God knows what will happen tomorrow. We are going to rest a bit at first, and then we will see what happens. |