Toggle menu
24K
664
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

GLOSS/401soc Haifuwa a Nijeriya (Childbirth in Nigeria)

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from GLOSS/408)
Haifuwa a Nijeriya <>

Childbirth in Nigeria

Haihuwa na dai daga cikin burin akasarin ma'aurata, a rayuwarsu ta aure a Nijeriya. To, sai dai ba dukkan ma'aurata ke cika wannan babban burin nasu ba saboda wasu matsaloli waɗanda ana iya rigakafinsu a yayin da abokiyar zama ko kuma in ce uwa ta zo haifuwa. Ko kuma jim kaɗan bayan haihuwar. <> Having children during their married life is one of the goals of most couples in Nigeria. However, not all couples are able to reach this goal because of preventable problems when giving birth or shortly after the birth.
Shekaru da dama da suka wuce, Nijeriya ke fama da matsala ta mata masu juna biyu da ke mutuwa. Ko dai a yayin da suke goyon cikin, ko kuma lokacin da suka zo naƙuda, ko kuma bayan haifuwa. <> For a number of years, Nigeria has been struggling with pregnant women dying, either during pregnancy, in labor, or after childbirth.
Wannan matsala ta kai wa inda Nijeriya ke matsayi na biyu a duniya baki ɗaya kan mace-macen mata masu juna biyu, kamar dai da rahoton haɗin gwiwa na hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya guda uku na shekara dubu biyu da biyar ta nuna. <> According to the joint report issued by three United Nations agencies in 2005, this problem has reached the point where Nigeria has the status of being number two worldwide in the number of pregnant women dying.
Daga lokacin samun ciki har zuwa lokacin haifuwa da ma bayan haifuwar, uwa na bukatar kulawar jami'a lafiya, ko da wata matsala na iya bijirowa. Ko dai ga ita kanta ko kuma ga ɗanta da ke cikin, don a yi saurin magance wannan matsalar. <> From conception to birth, and even after the birth, a mother needs the care of health workers in order to quickly attend to any problem that might get out of hand and pose a danger, either to her or to her child. .
Nijeriya dai, ta hasara rayukan mata har dubu hamsin da tara sanadin matsalar haifuwa a shekara ta 2005. Wannan adadi dai bai haɗa da na matan da ajalin nasu ya riskesu a gidajensu ba, musamman ma dai matan da ke yankunan karkara. <> Nigeria lost 59,000 women as a result of childbirth in 2005. This number, however, does not include the women who lost their lives in their homes, especially those in the rural areas.
Sakamakon wani taro kan lafiyar mata da wannan matsala ta mace-macensu da ya gudana a Landan watannin baya da suke wuce, ƙungiyoyi da gwamnatocin ƙasashe sun himmatu wajen shawo kan wannan gagaruman matsala. <> As a result of a conference that took place in London a few months ago on women's health and the problem of women dying during childbirth, organizations and national governments have made an effort to find a solution to this enormous problem.
Abdurahaman Kabir, Sashen Hausa na DW, daga Kano. <> Abdurahaman Kabir, Hausa Section of Deutsche Welle, from Kano.