https://gloss.dliflc.edu/products/gloss/hua_soc417/hua_soc417_source.html
Ilimin Mata | Girls' Education | |
Mohamed: Barka Aisha.
Aisha: Ina gajiya Malam Mohamed? Mohamed: Babu gajiya Aisha. Kin ji sabon albishir? Aisha: A’a, albishir a ina? |
Mohamed: Hello, Aisha.
Aisha: How are you, Mr. Mohamed? Mohamed: I am well, Aisha. Did you hear the good news? Aisha: No. Good news? What good news? | |
Mohamed: Gwamnati da kamfanoni za su taimaki mata.
Aisha: Yaya za su taimaki mata? Mohamed: Gwamnati za ta buɗe makarantun mata cikin garin Kaduna da wasu ƙauyuka. Aisha: Makarantun mata? |
Mohamed: The government and some companies are going to help young girls.
Aisha: How are they going to help girls? Mohamed: The government is going to open girls' schools in Kaduna City and some villages. Aisha: Girls' schools? | |
Mohamed: E, makarantu don ƙara ma mata ilimi.
Aisha: Nawa ne kuɗin makarantar? Mohamed: Makarantun kyauta ne. Sabbin makarantun gwamnati ne. Za’a koya ma mata karatu da rubutu. Aisha: Yaya ake iya shiga wannan makarantar? |
Mohamed: Yes, schools to increase the level of girls' educations.
Aisha: How much is the school tuition? Mohamed: The schools are free of charge. They are new government schools. Girls will be taught how to read and write. Aisha: How can one enroll in this type of school? | |
Mohamed: Ke da abokanki sai ku je babban ofishin gwamnati kusan kasuwa
babba a rubuta sunayenku. Aisha: Ana koya ɗinki a makarantun? Mohamed: E. Za'a koya aikin hannu kamar ɗinki da rini da saƙa, da sana’a. Aisha: Wallahi ina son ɗinki. Wannan makaranta tana da kyau. Makarantun za su taimaki mata sosai. |
Mohamed: You and your friends should go to the government's head office close to central market to get signed up.
Aisha: Do they teach how to sew in these schools? Mohamed: Yes, they teach handicrafts, such as sewing, dyeing, weaving, and trade. Aisha: I really like sewing. This school is good and it will help a lot. | |
Mohamed: E, mata za su iya samun aiki ko ba su yi dogon karatu ba saboda akwai
aikin hannu da sana’a. Aisha: To bayan wannan karatu ina iya ci gaba ko shikenan? Mohamed: Sosai Aisha, kina iya ci gaba da makarantar boko har zuwa jami’a. Aisha: Madalla, na ji daɗi sossai saboda ina son karatu amma iyayena ba su da kuɗi. Mohamed: Yanzu za ki je makaranta kyauta. Aisha: Na gode Mohamed, zan je in ba abokaina da iyayena labari. Sai an jima. Mohamed: To Aisha, sai anjima. |
Mohamed: Yes, girls will be able to obtain jobs, even without furthering their education. There are handicrafts and trade.
Aisha: Okay, after this study, am I able to continue or that is it? Mohamed: Very good, Aisha. You can continue with your studies up to university level. Aisha: Great, I am very happy because I like to study, but my parents do not have the money. Mohamed: You can now go to school free of charge. Aisha: Thank you, Mohamed. Let me go and tell my friends and family about it. See you later. Mohamed: Okay, Aisha. See you later. |