Toggle menu
25K
777
183
165.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:fuskanta

Discussion page of fuskanta

(1 Tassalunikawa 5:14) Wataƙila “masu-raunanan zukata” sun ga cewa ba su da gaba gaɗi da za su ci gaba ba kuma suna jin suna bukatar taimako domin cikas da suke fuskanta.

(1 Thessalonians 5:14) Perhaps those “depressed souls” find that their courage is giving out and that they cannot surmount the obstacles facing them without a helping hand.



Matta 10:16-22, 28-31 Wace hamayya za mu fuskanta, amma me ya sa bai kamata mu tsoraci ’yan adawa ba?

Matthew 10:16-22, 28-31 What opposition can we expect, but why should we not fear opposers?



Waɗanne matsaloli wata uwa gwauruwa ta fuskanta, ta yaya za mu aza mutane kamarta?

What challenges does one single mother face, and how do we view people like her?



Waɗanne canje-canje Dauda ya fuskanta a rayuwarsa?

How did David’s life undergo change?



zuwa babi na 1 kuma ya karanta sakin layi na 11 da babban murya, a ƙarƙashin ƙaramin jigo “Yaya Allah Yake Ji Game da Rashin Gaskiya da Muke Fuskanta?”

The pioneer opened the Bible Teach book to chapter 1 and read aloud paragraph 11, under the subhead “How Does God Feel About Injustices We Face?”



(2 Timothawus 3:1, 13) Maimakon fid da rai, mu fahimci cewa matsin da muke fuskanta tana ba da tabbaci ne cewa ƙarshen mugun tsarin Shaiɗan ya kusa.

(2 Timothy 3:1, 13) Instead of giving in to despair, realize that the pressures we face give evidence that the end of Satan’s wicked system is near.



(Ayukan Manzanni 16:16-24) Ta yaya wannan abin da suka fuskanta ya taɓa Bulus?

(Acts 16:16-24) How did that painful experience affect Paul?



Wasu daga cikin ƙalubalen da za mu iya fuskanta su ne yin tafiya mai nisa, go-sulo, da kuma ayyuka masu yawa.

Among the challenges that we may have to overcome are long travel distances, heavy traffic, and busy schedules.



Babu shakka, da yake Jehobah ne ya yi rana haka, zai iya ƙarfafa mu mu jimre da duk wata matsalar da muke fuskanta.

Can anyone doubt that the One who “fuels” the sun can give us the strength we need to cope with any problem?



Ko da wace irin matsala ce muke fuskanta, muna bukatar mu bi shawarar marubucin wannan zaburar da ke cikin nassin yini na yau. w17.03 4:6

Whatever the problem may be, we do well to heed the words of the psalmist who said the words of today’s text. w17.03 4:6



7. (a) Saboda kasancewarsu ba na duniya ba, menene almajirai na farko suka fuskanta?

7. (a) Because of being no part of the world, what did the early disciples experience?



Idan haka ne, za ka fahimci irin wahalar da Maryamu ta fuskanta a ƙasar Masar.

If so, you can well understand some of the hardships that Mary may have faced in Egypt.



Waɗanne matsaloli ne mutane ke fuskanta a yau?

What are some problems facing people today?



Wane ƙalubale ne waɗanda suke bauta wa Jehobah suke fuskanta daga danginsu da ba sa bauta wa Jehobah, kuma a ina ne za su samu taimako?

What challenge do believers in divided households often face, and what help is available?



Bari mu tattauna game da inda ka faɗi mu ga yadda za mu magance dukan wata matsala da ka ke fuskanta.”

So let’s talk about this class and find a way to overcome any problems you might be facing.”



4 Ƙalubalen da matasa Kiristoci suke fuskanta a waɗannan kwanaki na ƙarshe yana daɗa kasancewa da “wuya ƙwarai.”

4 The challenges Christian youths must face during these last days are increasingly “hard to deal with.”



Saboda haka, makiyayin ya sunkuya, ya ɗauki tunkiyar a hankali, ya ɗauke ta ya mai da ita garke duk da cikas da ta fuskanta.

Therefore, the shepherd bends down, gently lifts up the sheep, and carries it across all obstacles back to the flock.



Littafi Mai-Tsarki ya tanadar da ƙa’idodi masu yawa da ke da alaƙa da matsaloli da yara suke fuskanta.

The Bible provides an abundance of valuable principles relating to problems faced by children.



Waɗanne matsaloli ne ’yan gudun hijira suke fuskanta (a) sa’ad da suke gudu?

What dangers exist when refugees (a) are fleeing?



Waɗanne matsaloli ne ’yan’uwa Sicurella da Thlimmenos suka fuskanta, amma wane sakamako aka samu?

What issues did Brothers Sicurella and Thlimmenos face, and what was the outcome?



Ku san gwajin da suke fuskanta kuma ku taimaka musu su yi tsayayya da hakan.

Try to be aware of any tests to their faith, and help them to deal with these.



(b) Waɗanne abubuwa ne iyalai ke fuskanta don su je taro da wuri?

(b) What are some challenges that families face in order to get to meetings on time?



Waɗanne jarrabobi ne Ayuba ya fuskanta, kuma mene ne ya nuna ta jimrewarsa cikin aminci?

What trials did Job have to deal with, and what did he show by his faithful endurance?



Waɗanne ƙalubale ne waɗannan suke hidima a inda ake da bukata suka fuskanta?

What challenges have some “need greaters” faced?



Ko da yake Mahaliccinmu ya yi wa Ayuba ne waɗannan tambayoyi, babu shakka sun shafe halinmu, wanzuwarmu, da kuma abin da za mu fuskanta a nan gaba.

Though our Creator directed these questions to Job, they clearly have a bearing on our attitude, our existence, and our future.