Toggle menu
25K
777
183
165.6K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:statement

Discussion page of statement

Glosbe's example sentences of statement [1]

  1. Misalin kalmar da jimlolin turanci da Hausa na kalmar statement:
    1. Because the psalmist’s statement has a broader significance.
      Domin wannan kalamin marubucin zabura yana da wata ma’ana dabam. [2]

    2. Moses declared in connection with the deliverance of Israel from slavery in Egypt: “It was because of Jehovah’s loving you, and because of his keeping the sworn statement that he had sworn to your forefathers, that Jehovah brought you out with a strong hand.” —Deuteronomy 7:8.
      Musa ya sanar haka game da ceton Isra’ila daga bauta a Masar: “Domin Ubangiji yana ƙaunarku yana kuwa da nufin ya tsayadda rantsuwa wadda ya rantse ma ubanninku, domin wannan Ubangiji ya fishe ku da hannu mai-ƙarfi.”—Kubawar Shari’a 7:8. [3]

    3. His statement has often been repeated, perhaps because so many people see it as undeniably true.
      Wannan furcin nasa an maimaita shi sau da yawa, watakila domin mutane da yawa suna ganin gaskiya ce da ba za a yi jayayya da ita ba. [4]

    4. (b) What did Martha’s important statement show about her?
      (b) Mene ne kalamin Martha ya nuna game da ita? [5]

    5. In the centuries since, much has been said and written about that simple statement.
      A cikin ƙarnuka bayan haka, an yi magana ƙwarai kuma an yi rubutu sosai bisa wannan kalami mai sauƙi. [6]

    6. Explain the meaning of Jesus’ unforgettable statement recorded at John 11:25-27 and of Martha’s reply.
      Mene ne kalamin Yesu da ke cikin littafin Yohanna 11:25-27 yake nufi kuma mene ne amsar da Martha ta bayar take nufi? [7]

    7. (Genesis 3:15) By that prophetic statement, a ray of hope burst forth for all who would put faith in that promise.
      (Farawa 3:15) Ta wannan furci na annabci, duk waɗanda suka ba da gaskiya cikin wannan alkawari sun sami bege. [8]

    8. Getting back to Paul’s statement in Hebrews, we note that he pointed out that “there remains a sabbath resting for the people of God,” and he urged his fellow Christians to do their utmost “to enter into that rest.”
      Idan muka koma ga maganar Bulus a Ibraniyawa, za mu lura ya ambaci cewa “akwai fa hutun asabaci ajiyayye domin jama’ar Allah,” sai ya aririci ’yan’uwansa Kirista su yi iyakacin ƙoƙarinsu su “shiga cikin wannan hutu.” [9]

    9. 6 If we love Jehovah and loyally stick with his people, we can draw comfort from the statement at 1 Samuel 12:22: “Jehovah will not desert his people for the sake of his great name.”
      6 Idan muna ƙaunar Jehovah kuma cikin aminci muka manne wa mutanensa, za mu samu ƙarfafa daga furcin da yake cikin 1 Samuila 12:22: “Ubangiji ba za ya yarda jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.” [10]

    10. Continuing, the speaker made this very significant statement: “The governing body does not have officers such as the Society’s Board of Directors has, namely, president, vice president, secretary-treasurer and assistant secretary-treasurer.
      Da yake ci gaba, mai jawabin ya yi wannan furci mai muhimmanci: “Hukumar mulkin ba ta da hafsoshi irin waɗanda Rukunin Darektoci na Society suke da shi, wato, shugaba, mataimakin shugaba, ma’ajin sakatare da mataimakin ma’ajin sakatare. [11]

    11. 8 In this statement Satan implied not only that Jehovah had withheld crucial information from Eve but also that He had lied to her.
      8 Wannan furcin Shaidan yana nufin ba kawai cewa Jehovah ya hana Hauwa’u sani da ya wajaba ba ne amma cewa Ya yi mata karya. [12]

    12. (Proverbs 14:15) Still, loyal Christians refuse to believe just any statement made about their brothers, and they certainly do not allow bad publicity to cause them to miss Christian meetings, to slow down in the field ministry, or to waver in their faith.
      (Misalai 14:15) Har ila, Kiristoci na gaskiya suna ƙin gaskata kowanne furci da ake yi game da ’yan’uwansu, kuma ba sa ƙyale yaɗuwar irin wannan ƙaryar ta sa su ƙi halartar taron Kirista, ta rage himmarsu a hidimar fage, ko kuma su raunana a bangaskiyarsu. [13]

    13. Can you really benefit from the very well-known statement:
      Za ka iya amfana daga furucin nan: [14]

    14. The description of a good wife ends with the statement: “Give her of the fruitage of her hands, and let her works praise her.” —Proverbs 31:31.
      Ya kammala kwatanta matar kirki da wannan furcin: “A ba ta daga cikin amfanin hannuwanta: bari kuma ayyukanta su yabe ta.”—Misalai 31:31. [15]

    15. 15 Hence, when you consider whether you should choose a certain individual as a close friend or not, it would be wise to keep Jesus’ statement in mind.
      15 Saboda haka, kafin ka zaɓi wani ya zama abokinka na kud da kud, zai dace ka tuna da abin da Yesu ya ce. [16]

    16. Notice this profound statement of Jesus.
      Ka lura da wani shawarar da Yesu ya bayar a nan. [17]

    17. This subtle chain of events confirms the truthfulness of the Bible’s statement: “Each one is tried by being drawn out and enticed by his own desire.” —James 1:14.
      Waɗannan abubuwa da suka faru bi da bi suna nuna gaskiyar abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowanne mutum ya jarabtu, sa’anda sha’awatasa ta janye shi, ta yi masa tarko.”—Yaƙub 1:14. [18]

    18. Arthur Willis, in paraphrasing a statement once made in The Golden Age magazine, later declared: “No road too rough or too long for His witnesses.”
      A lokacin da Arthur Willis yake maimaita wani furuci da aka yi a cikin mujallar The Golden Age wato Awake!, ya ce: “Ba abin da zai iya hana Shaidunsa yin wa’azi.” [19]

    19. That text is more than a statement about God’s personality; it is a guiding principle for life.
      Wannan furcin ba kwatanta halayen Allah kawai yake yi ba; amma mizani ne na ja-gora a rayuwa. [20]

    20. 3, 4. (a) What led up to Paul’s statement found at 2 Corinthians 3:17?
      3, 4. (a) Me ya sa Bulus ya yi furucin da ke 2 Korintiyawa 3:17? [21]

    21. Still, Paul’s statement that ‘all Israel would be saved’ was true.
      Duk da haka, kalamin da Bulus ya yi cewa “dukan Isra’ila za su tsira” gaskiya ne. [22]

    22. In fact, when speaking about a person who pays attention to what God says, the Bible makes the bold statement: “Everything he does will succeed.” —Psalm 1:3.
      Hakika, sa’ad da yake magana game da mutumin da ya mai da hankali ga abin da Allah ya ce, Littafi Mai Tsarki ya ce da babbar murya: “Iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka.”—Zabura 1:3. [23]

    23. If his statement is true, the supervisor has wisely displayed an awareness of his limitations.
      Idan kalamansa gaskiya ne, mai kula da aikin ya nuna cewa ba shi da cikakken iko. [24]

    24. I handed the man a written statement, saying, “I only want to be a soldier of Christ.”
      Kuma na miƙa masa takardar da na rubuta cewa, “Ni sojan Kristi kaɗai nake so in zama.” [25]

    25. How should women view this inspired statement?
      Yaya mata za su ɗauki wannan hurarren furci? [26]


Retrieved September 16, 2020, 12:22 pm via glosbe (pid: 3104)