Overview
- Lesson Title: Presidential Candidates
- This interview with the media consultant for Nigeria's Vice President discusses the Nigerian political parties and how the Vice President stands as a presidential candidate.
- Language: Hausa
- Topic: Economics/Politics
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
- This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Listening
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2007
- ObjectID: HAUS_11912
Transcript
Original | Translation |
---|---|
Presidential Candidate A: Watau dai, abin nan da zan ce akan wannan, shi ne: ai, za ɓi da yake dashi shi mataimakin shugaban Ƙasa, suna da dama kwarai da gaske. Ai, kada a manta cewan, shi ɗin nan fa, akwai jam’iyyu bama ɗ aya ba da suke mar tayin cewa, suna gayyatarsa da yazo, za su ba shi tikitin su na ɗan takarar shugaban Ƙasa, idon har yana da buƘ atar ya yi hakan. Kuma kana sane da cewa satin nan da ya wuce ne , kotu a nan Abuja ta yanke hukuncin cewa dakatar da shi da akayi a.. jamiyyar PDP da kwace masa dama da kuma … haƘƘoƘinsa duk baibi ka’ida ba bai dace a tsarin mulki ba.Saboda haka, a maida masa komi. Kuma kamar yadda muka zato din, ita kamar da ma jam’iyyar PDP Ai, ita da ma da ita da shari’a sun riga sun raba gari. Sun rigaya su raba hanya domin ba jamiyya ce dake sha’awar bin doka ba. Don ta yi karfi, ta cika, tayi bugu da giyar mulki. B: Mmm… A: Da haka, ba su da wani haufi dangane da…watau..takaran tsaye . Saboda haka, har yanzu wancen ba su nemi mataimakin shugaban kasa akan wannan hukuncin da kotu ta yanke ba. Saboda haka, mu dai munsa idanu -- B: Mmm … A: -- amma dai ba’a…ai.. cikin ubangiji , akwai matakai da mataimakin shugaban Ƙasa zai dauka wanda yake cikin nan da sati guda za’a ji su. B: To, Alhaji Garba Shehu, akwai raɗe raɗin cewa tuni har shi shugaba Obasanjo da kuma manyan jam’iyyar PDP sun yanke sha’awar cewa, za su tsaida gwamnan Katsina Umar Musa Yar’adua ya yi takara. Akwai kuma waɗ anda ke cewa, idan haka ne, wani mataki ne na karya irin tasirin da shi mataimakin shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubukar yake da shi a ɓangaren jam’iyyar PDP da ake kira PDM, watau ɗaya da cikin ɓangarorin da suka haɗu suka kafa a jam’iyyar PDP ɗin tun da fari. Ina … ah … ra’ayinka game da wannan ikirari da jama’a suke yi? A: To, na farko dai, shi ne: shi kansa gwamnan Katsina … ah … mai girma Umaru Yar’adua, ya faɗ a da bakinsa cewa shi ba ya cikin wannan ɓangare na PDM da ke PDP, ya ce shi baya yin PDM. To, saboda haka, ka ga, don an zaro shi an ce za’a ba shi takara ko Ƙ anƘane, mataimakin shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ba zai yi wani ciwon kai ba. Ba zai rage mu da kome ba. Sannan, na biyu, shi ne: Allah ya bawa PDP sa’a. In dai wannan shi ne gwaninsu da zasu fito dashi, to wallahi tallahi, mu ma muna taya su murna. B: Ahaji Garba Shehu a gurguje jam’iyyar ANPP da kuma jam’iyyar AC, sun Ƙ ulla Ƙ awance akan cewa za su tsayar da dan takarar shugaban Ƙasa guda ne. Kuma akwai raɗ e-raɗin cewa shi mataimakin shugaba Atiku Abubakar yana da niyyar shiga jam’iyyar AC ne domin ya yi takara ƘarƘashin ta. A wannan Ƙawance da aka kulla tsakanin AC da kuma ANPP, ta yaya zai shafi ɗan takara naku? A: To, ni, ina ganin ana neman a yi taron gaba. Wannan … yarje-jeniya da aka sa hannu akanta, ai tabbas akwai bukatar a tsaida ɗ an takara daya a jeha, da Ƙananan hukumomi hatta kansila tsakanin wadannan jam’iyyu biyu guda biyu. Zancen maganar shugaban kasa, akwai sauran aiki a gaba, wataƘila sai lokacin da Allah yakai mu, lokacin da za’a yi wannan abu sannan za’a tattauna akai. Amma, ina da kyakkwawan zato cewar wadannan jam’iyyu guda biyu ba za su gagara, cimma yarje-janiya akan matsayi daya, akan wannan ɗ an takara na shugaban Ƙasa ba. B: Ai … A: Abinda dai nake so in ce, shi ne: Awkai ɗ an sauran aiki a gaba, kuma muna fata nan da ɗ an kankanan lokaci. B: Mmm … A: Za’a samu daidaito, kuma za’a ji maganar ɗ aya ta fito daga waɗannan jam’iyyu. |
Presidential Candidate A: In other words, what I should say about this is: in the election for Vice-President, he has a real opportunity. You know, don’t forget this: there is one political party that is inviting him to come, and they will give him their ticket for the presidential candidate, if he needs to do it this way. You are aware that this past week, the court here in Abuja ruled that his dismissal from the PDP [People’s Democratic Party], snatching away his opportunity and his rights, was both illegal and unconstitutional. Because of this, everything was restored to him. And as we expected, the PDP and the law have been known to have taken separate paths in the past. They have previously parted ways because it’s not a party that’s interested in following the law. It’s fully intoxicated by power on account of its strength. B: Mmm… A: Thus, they have no doubt regarding … ah … the standing competition. So until now they hadn’t sought the Vice-President on this judgment that the court handed down. Because of this, we are merely watching events unfold -- B: Mmm … A: -- but they didn’t … well … God knows, there are steps that the Vice-President would take which we will hear about within a week. B: So, Alhaji Garba Shehu, there are rumors that President Obasanjo and the PDP bigwigs reached an agreement some time ago that they would pick Governor of Katsina Umaru Musa Yar’Adua as their candidate. There are those who say that, if this is so, this step defeats the influence that Vice-President Alhaji Atiku Abubakar had on the PDP faction known as the PDM [People’s Democratic Movement] from the outset. What is … ah … your opinion about this claim that the public is making? A: Well, the first thing is this: the Governor of Katsina himself … ah … Honorable Umaru Yar’Adua, claims that he isn’t in this PDM faction of PDP, he says it does not belong to the PDM. Because of this, you see, since he’s been taken out, he’ll probably have a little competition, and Vice-President Atiku Abubakar won’t get a headache as a result. It will not affect us in any way. Then, secondly, is this: God has granted good fortune to the PDP. If this is their candidate that they will come out with, then by God, we’re glad for them. B: Alhaji Garba Shehu, regarding the ANPP [All Nigeria People’s Party] and the AC [Action Congress]: they have made a pact to set up a single presidential candidate. And there are rumors that Vice-President Atiku Abubakar intends to join the AC to be their candidate. How will this arrangement that is being planned between the AC and the ANPP affect your candidate? A: Well, I think they’re seeking to have a meeting soon. This … agreement that they have signed, surely there is a need to set up one candidate in each state, when the local authorities share a counselor between these two parties. On the matter of the presidency, there is more work ahead, and perhaps when God brings us together again, when we’ve done this thing, then we can talk about it. But I have a positive expectation that it will not be impossible for these two parties to reach an agreement on the one position, on the presidential candidate. B: Ai … A: What I want to say is this: there’s a bit more work ahead, and we’re hoping for a little more time. B: Mmm … A: We’ll achieve a balance, and we’ll hear one voice coming from these parties. |
Glossary
Hausa | Explanations |
---|---|
tikitinsu | Wannan kalmar hausa ce da aka aro daga turanci 'ticket' kuma a nan tana nufin wurinsu ko kujerasu. |
Sun raba gari | Wannan na bayyana kowa na gefenshi. |
Sun raba hanya | Ba su tare. |
Ta bugu da giyar mulki | Wannan karin magana ce mai nufin ta yi nisa cikin mulki don haka ba ta ji ba ta gani. |
Nan da ɗan ƙanƙanan lokaci | Nan da lokaci kaɗan |
Note
Hausa Note | English Note |
---|---|
A matsayin ƙasa mafi yawancin jama'a a Afrika, Nijeriya na kuma ɗaya daga cikin ƙasashen duniya masu yawan ayyukan rashawa musanman wajen siyasa da zaɓe. Nijeriya kuma sanannar ƙasa ce wajen tashe-tashen hankali da ɓata lokaci wajen zaɓe. Hukumar EFCC na cikin matakan da aka ɗauka don yaƙi da rashawa koda yake jama'a na faɗan cewa suna aiki ne masanman don huƙunta masu adawa da shugaban ƙasa.Yawancin lokaci, ba'a iya komi idan manyan ƴan siyasa suka zaɓi wanda suke so ya zama shugaban ƙasa saboda dokar ƙasa na kare su daga huƙuncin rashin bin tsarin mulki. A matsayin ɗan jam'iyya PDP Obasanjo ya maida ta jam'iyya da bata taɓuwa ga kowa kuma koda yake akwai ƴan takara kamar mataimakin shugaban ƙasa wanda aka maida cikin sunayen ƴan takara, duk da haka Ƴan Nijeriya sun riga sun sa zaton cewa PDP za ta yi anfani da ƙarfinta wajen tabbatar da cin nasarar zaɓen. voanews.com/eng/2007-04-21-voa3 news.bbc.co.uk/2/ni/africa/5339030.stm |
As the most populous country in Africa, Nigeria is also one of the most corrupt countries in the world and this has been most damaging in terms of politics and elections. The country is also known for violence, and in most of its elections there have been issues of delays in ballots. Politicians especially at the highest position are mostly corrupt, making fortunes out of the country's resources. Among attempts in trying to fight corruption is the creation of the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), a commission which the Nigerian public claims only works to the advantage of the president-convicting mainly his political opponents. Usually there is little or nothing that can be done when powerful politicians decide on who would be elected president, because the law makes them immune from being prosecuted. President Obasanjo being a member of the PDP makes it an untouchable party and although there are other candidates like Vice President Atiku Abubakar, who was put back in the list of candidates about 7 days before elections, yet there is little suspense among Nigerians who expect PDP to use its incumbent powers to ensure victory. voanews.com/eng/2007-04-21-voa3 news.bbc.co.uk/2/ni/africa/5339030.stm |
XML
<activity>
<problemset>
<problem correctindex="0">
<choices>
<opt>
<eng-response>This is an interview about presidential candidates in Nigeria, mainly discussing the Vice-President as a potential candidate. Some parties are willing to accept the Vice-President as their presidential candidate if he needs the seat, but according to Shehu Garba there are issues to resolve before getting to that stage. Some of the issues included two parties, AC and ANPP coming together as one and deciding on one presidential candidate. The court also overruled the PDP's actions against the Vice-President, disqualifying him from the race and his rights as a party member. He also described the PDP as a strong party with influence and no respect for the law and concluded that the Vice-President is taking steps against the party for not considering approaching him or responding to the court's decision.</eng-response>
<eng-fdbk>Correct! The interview talks about the Vice-President as a presidential candidate and the support he is getting from different parties.</eng-fdbk>
<response>Wannan ganawa ce akan ƴan takara shugaban ƙasa a Nijeriya kuma ana magana masanman bisa mataimakin shugaban ƙasa a matsayin ɗan takara.Wasu jam'iyyu suna shirye da mataimakin shugaban ƙasa ya zama ɗan takarasu idan yana buƙata kujarar amma Shehu Garba ya bayyana cewa akwai abubuwan da ya kamata a yi maganinsu kafin a kai ga matsayin takarar.Wasu daga cikin matsalolin sun haɗa da ƙulla ƙawancin jam'iyar AC da ANPP kuma su zaɓi ɗan takara ɗaya.Kotu kuma ta yanke huƙunci cewa dakatar da aka yi da shi da PDP ta yi da kuma hana mishi ƴanci shi a matsayin ɗan jam'iyya bai cancanta ba. Ya kuma bayyana cewa jam'iyyar PDP jam'iyya ce mai ƙarfi da iko kuma bata biyyaya ga dokar ƙasa. Ya kuma kammala da cewa mataimakin shugaban ƙasa ya ɗauki matakai bisa huƙuncin da PDP ta yi mishi kuma bata neme shi ba bayan shawara da kotu ta ɗauka.</response>
<fdbk>Wannan daidai ne! Ganawa na bayyani ne akan mataimakin shugaban ƙasa da goyon bayan da yake samu daga jam'iyyu daban daban.</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>A media consultant to the Vice-President of Nigeria stated in an interview the situation of the presidential candidates. According to him, there are several political parties willing and ready to give the Vice-President their seat as a presidential candidate because his former party, the PDP, treated him unfairly and deprived him of his rights and opportunities as a member of the party. Garba Shehu also described the PDP as a strong and influential party with Obasanjo and other members trying to discredit the Vice-President's capabilities and power by electing the governor of Katsina state as their presidential candidate. Garba Shehu concluded that the public is comfortable and in support of whoever wins between the Vice-President and the Governor because PDM founded what is now a strong party called PDP, and they more or less share the same values.</eng-response>
<eng-fdbk>This is incorrect! The interviewee did not discuss the public opinion about Atiku and Umaru Yar'adua. Think of a response choice that better captures the PDP's decision on its candidate.</eng-fdbk>
<response>Ɗan jaridar ɓangaren mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana halin da ƴan takara shugaban ƙasa ke ciki.Ya bayyana cewa akwai jam'iyyu da yawa da ke shirye su ba mataimakin shugaban ƙasa kujerarsu ta ɗan takarar shugaban ƙasa saboda jam'iyyar shi watau PDP bata mutuntashi ba kuma ta hana mishi ƴancin shi na ɗan ƙungiya. Garba Shehu ya kwatanta PDP da jam'iyya mai iko da shugabanni kamar su Obasanjo wanda suka zaɓi gwamnan katsina a matsayin ɗan takarasu don ƙokarin ɓata suna da iya aikin mataimakin shugaban ƙasa.Garba Shehu ya kamala da cewa jama' a ta goyi bayan wanda ya ci zaɓen tsakanin mataimakin shugaban ƙasa da gwamna saboda PDM ce asalin PDP kuma su duka matsayinsu ɗaya.</response>
<fdbk>Wannan ba daidai ba ne! Saboda mai bayyanin bai yi magana ba akan ra'ayin jama'a game da Atiku ko da Ƴar'adua ba. Yi tunanin amsa da ta bayyana shawarar PDP bisa ɗan takararsu.</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>According to the interviewee, the PDP is a strong political party in Nigeria with the power to influence the public and disobey the law without penalties from the federal government. The Nigerian Vice President was a member of the party until he decided to run for president. Obasanjo opposed the Vice-President's intentions and elected Omar Musa Yar'adua as the party's candidate. However, the media consultant stated that other parties are willing to accept Atiku as their presidential candidate and the public will support the Governor of Katsina state if he wins since he is not a member of PDM. The Vice-President also plans to join a new party called AC, which is also in the process of coming together with another party, ANPP and Garba Shehu is confident that the two parties will unite and support Atiku Abubakar as their candidate.</eng-response>
<eng-fdbk>This is incorrect! Garba Shehu is not sure of Atiku's fate when AC and ANPP come together as one. Please listen to the interviewee's comments about Obasanjo's party and influence.</eng-fdbk>
<response>Mai amsa tambayoyi ya bayyana cewa PDP jam'iyya ce mai ikon faɗi a yi gaban jama'a kuma tana iya ƙin bin dokar ƙasa ba tare da gwamnatin tarayya ta yi mata huƙunci ba. Mataimakin shugaban ƙasa ya yi zama ɗan jam'iyya PDP kamin ya ɗauki shawarar zama ɗan takara shugaban ƙasa. Bayan haka sai Obasanjo ya zaɓi Umar Musa Yar'adua ya zama ɗan takara PDP saboda bai goyon bayan mataimakinshi. Ɗan jarida mataimakin shugaban ƙasa ya ci gaba da bayanin cewa sauran jam'iyyu na shirye su ba Atiku kujerar takarar shugaban ƙasa, kuma jama'a za su goyi bayan gwamnan Katsina idan ya ci nasara tunda shi ba ɗan jam'iyyar PDM ba ne. Mataimakin shugaban ƙasa na da niyar shiga wata sabuwar ƙungiya mai suna AC wadda za ta haɗa ƙawantaka da ANPP kuma Garba Shehu ya tabbatar da cewa jam'iyyun biyu za su haɗa kai su zaɓi Atiku Abubakar ya zama ɗan takarasu kuma suma goyi bayanshi.</response>
<fdbk>Wannan ba daidai bane! Saboda Garba Shehu bai tabbatar ba da abun da zai faru da Atiku idan AC da ANPP suka haɗa kai. Ƙara sauraren bayyani bisa jam'iyya Obasanjo da tasirin ta.</fdbk>
</opt>
</choices>
</problem>
</problemset>
<instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
<instr type="target">Umurni:
Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
<finish>How do you think the Nigerian political parties relate with each other?</finish>
<finish>What do you think constitutes a good presidential candidate in Nigeria?</finish>
<finish>What is the main objective of presidential candidates in Nigeria?</finish>
<finishtl>A ganinku yaya jam'iyyun siyasa a Nijeriya ke hulɗa da juna?</finishtl>
<finishtl>A gininku wane irin ɗan takara siyasa ne na ƙwarai a Nijeriya?</finishtl>
<finishtl>Minene maƙasudin ƴan takarar shugaban ƙasa a Nijeriya?</finishtl>
</activity>