Overview
Lesson Title: The People of Kano Have Played Their Part, It Is Now Malam Shekarau's Turn. This editorial discusses the experience of the people in Kano State in ensuring a fair gubernatorial election.
- Language: Hausa
- Topic: Economics/Politics
- ILR Level: 2+/3
- ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High
- This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
- Modality: Reading
- Learning Objective: Maintenance & Improvement
- Subject Area: Language
- Material Type: LO
- Publication Year: 2007
- ObjectID: HAUS_12120
Transcript
Original | Translation |
---|---|
The People of Kano Have Played Their Part, It Is Now Malam Shekarau's Turn 2007: Kanawa sun yi nasu saura Malam Shekarau NOTE: ”Q” represents the Hausa hooked ”K” “X” represents the Hausa hooked “D” “V” represents the Hausa hooked “B” Ga dukkanin alamu kiran nan da xan takarar Shugabancin qasar nan a qarqashin Jam’iyyar ANPP wato Janara Muhammadu Buhari ya yi wa ‘Yan Nijeriya kan cewa su Kasa, su tsare quri’unsu, a lokacin zavuvvukan da suka gabata, ya yi tasiri a wasu daga cikin Jihohin qasar nan. Aminiya ta gano haka ne a lokacin da ta yi nazari a kan zavuvvukan da suka gabata a Jihar Kano a inda ta lura da kyau cewa talakawan a Kano sun bi huxubar ta Janar Buhari, domin a lokutan zavuvvukan sun yi fitar xango zuwa wajen zaven, bayan sun kaxa quri’unsu sai suka tsare su daga magauta a qarshen zave kuma suka raka quri’unsu zuwa Babban ofishin hukumar zave na Jihar sannan kuma suka jira har sai da aka bayyana sakamakon zave. Duk wannan gwagwarmayar da Talakawan suka yi sun yi ta ne a wani irin yanayi na ban tsoro da firgici, domin a lokutan zavuvvukan an yi amfani da dukkanin jami’an tsaro har da sojoji waxanda aka tungace su a wuraren shige da ficen al’umma a faxin Jihar ta Kano. Amma duk wannan bai hana talakawan sun tabbatar da bin hakkinsu a siyasance ba, domin sun nuna wa duniya cewa a shirye suke da su tabbatar da ’yancinsu na dimokuraxiyya komai wuya komai matsin lamba. Wannan jajurcewa ce da talakawan na Kano suka yi ta ba wa sauran Jihohin qasar nan qwarin guiwar cewa idan da duk sauran jihohin qasar nan za su bi sahun Kano to da haqiqa ximokaraxiyya ta sami wani babban tagomashi a Nijeriya. Idan Mai-Karatu zai iya tunawa a zavuvvukan shekara ta 2003 Al’ummar ta Kano irin wannan tsari ne suka bi suka karve mulki a hannun Gwannatin PDP a qarqashin jagorancin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso” kuma sai ga shi a Shekara ta 2007 ma tarihi ya maimaita kansa. A lokacin waxannan zavuvvuka da aka gudanar a wannan Shekara ta 2007 talakawan na Kano sun ga uquba iri-iri a hannun ‘yan’adawa da jamai’an tsaro, amma duk da haka suka kasa, suka tsare, suka raka kuma suka jira har sai da sakamakon abin da suka zava ya tabbata. Kamar yadda kowa ya gani ko yaji ko kuma ya sani, an gudanar da zavuvvukan na bana ne cikin ruxani, domin tun a farkon al’amari an sami tsaikon isowar kayan aiki wajen zave a inda talakawa suka wahala suna jiran Jami’an Hukumar ta zave (INEC) ta kawo kayan aiki amma ba a kawo ba har sai da aka galabaita, wasu ma musamman mata har sun fara komawa gidajensu. Duk da wannan tsaiko wasu suka yi qememe suka kasa suka tsare, har sai da aka kawo kayan zaven sannan suka kaxa quri’unsu kuma suka qi tafiya har sai da sakamakon ya bayyana sa’ilin nan kowa ya kama gabansa bayan da aka wakilta masu raka akwatunan zave zuwa Ofishin Hukumar Zave ta Jiha. Wasu daga cikin talakawan sun fuskancin fushin ’yan’adawa wanda a sakamakon haka suka sha duka da sara da adduna da wuqaqe da barandami da dai sauran manyan makamai a lokutan da suke raka akwatunana zaven Ofishin Hukumar ta zave. Alal misali talakawan da suka rako akwatunan zave daga Qaramar Hukumar Makoxa ba su sha ta daxi ba a lokacin da wasu ‘yan’adawa suka yi masu wanton Vauna a Hanyar Makoxa Zuwa Kano, kuma suka far masu da duka da sara, amma duk da haka sai da suka cika burinsu na ganin cewa akwatunan zaven sun isa Ofishin na INEC lafiya. Haka ma al’amarin ya kasance da masu rakiyar akwatunan zaven Qaramar Hukumar Madobi da Tudun-Wada da Tsanyawa ba ya ga firgitarwa da aka yi ta yiwa talakawa a lokacin zavuvvukan. Idan Mai-Karatu zai tuna a ranar da aka kammala zaven na Gwamna, wato 12 ga Watan Afrilu sakamakon zaven bai samu ba a wannan ranar sai washegari, a sakamakon haka ne kamar yadda binkice ya nuna wasu samari suka kasa suka tsare a wani makeken fili dake daura da inda Ofishin Hukumar zaven yake, wanda ake kira Filin Polo har sai da gari ya waya aka bayyan sakamakon zaven sannan suka bazama cikin gari don nuna murnarsu da sakamakon zaven. A dalilin samun wanna nasar ce Aminiya ta tattauna da wasu Kanawa dangane da fatansu ga sabuwar gwamnatin ta Mallam Ibrahim Shekarau, a inda suke bayyana fatansu da cewa Malamin ya zage damtse ya kwarara wa Kanawa aikin ci gaba da buqasar arziki a Jihar. Malam Yahaya Bello wani Mai-Tallar Qaro da Tawada ya yi kira na musamman ga Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da ya canza tsarin tafiyar da gwamnatinsa ta yadda talakawa da ke qasa za su sami alfanu mai yawa a gwamnatin tasa, domin a cewarsa sune suka yi uwa suka kuma yi makarviya a lokacin zaven gwamnana a karo na biyu. Ya shaida wa Aminiya cewa idan dai har Malam Shekarau ya daure ya kammala aikin ruwan Tamburawa kuma ya tabbatar da kafuwar Cibiyar samar da wutar lantarki ta Jiha Mai-zaman Kanta kamar yadda ya yi alqawari a baya to hakika kwalliya za ta biya kudin Sabulu ta vangaren talakawa. Shi ma da yake tattaunawa da Wakilinmu a Shagonsa na Xinki, Wani Tela Mai Suna Malam Isma’il Ibrahim cewa ya yi shi kam ba ya wata tantama cewa talakawa za su dara a wannan sabuwar gwamnatin ta Malam Ibrahim Shekarau. “Tun a farkon al’amari mun fara jin cewa zai rushe Muqarrabensa, wato Kwamishinoni waxanda dama can sune ake ganin ba sa taimaka masa kamar yadda ya kamata, duk da cewa ya ba su wuqa ya kuma ba su nama dangane da harkokin gudanar da aikace aikacen su.” In ji Isma’il Tela. Don haka sai ya ce “babban abin da za mu yi wa Malam shi ne mu taya shi da addu’a domin samun Mataimaka na gari da za su taimaka masa wajen fita kunyar Talakawan da suka dage sai dai ya jagorancesu a karo na biyu a Jihar.” Ita ma wata Mata, Malama Hanne wadda ke sana’ar sayar da qosai a Kan titin nan da ake kira Sultan “Road” a turance dake cikin unguwar Nasarawa a Qaramar Hukumar Nassarawa dake Jihar ta Kano ta roqi gwamnan ne da ya yi la’akari da irin wahalar da talakawa suka shiga a lokutan zavensa kuma ya saka masu da abin da ya dace. “Musamman mu ’ya’ya mata wasunmu ba su da aure, wasu mazajensu sun mutu sun barsu da yara, wasu suna da auren amma mazajen ba su da aikin yi, wasu kuma mazajenma sun gudu sun bar matan da yara, don haka Malam Shekarau ya kamata a wannan sabuwar gwamnatin ya yi wani shiri na musamman domin magance irin waxannan matsaloli a tsakanin mata a Kano, duk da cewa a baya ma ya yi amma dai ya qara, tunda talakawan sun ce sai shi.” Wata majiya mai-qarfi ta Aminiya wadda kuma ke kusa da Gwamnatin Jiha ta Shaida wa Wakilinmu cewa Gwamnan ya yi alqawarin saka wa Kanawa da abin alheri fiye da abin da ya yi masu a Shekaru Hudun da yayi a karagar mulkin Jihar a baya. “A yanzu haka gwamna ya yanke shawarar canza duk Kwamishinoninsa kuma har ma ya kafa Kwamitin da zai shirya masa tsarin tafiyar da mulkinsa a karo na biyu tare da irin ayyukan da zai gudanar a kowace shekara don amfanin Talakawa.” In ji Majiyar ta Aminiya. Ko ma dai me ake ciki, lokaci ne kaxai zai nuna. Ko dai Malamin zai saka wa talakawan da suka fito zave suka kaxa quri’unsu, suka tsare quri’unsu kuma suka jira har sai da aka bayyana sakamakon zaven a Jihar ta Kano, ko kuma a’a. |
The People of Kano Have Played Their Part, It Is Now Malam Shekarau's Turn By all accounts, the call to Nigerians made by the ANPP [All Nigeria Peoples Party] presidential candidate, General Muhammadu Buhari, during the recent elections, that they should vote en masse and protect their votes during elections, had an effect on some states in this country. Aminiya discovered that this was true when it studied the elections that recently took place in the State of Kano, where it clearly appeared that the populace of Kano had followed General Buhari’s advice, because during the elections they appeared in great numbers at the polling place and, after they cast their ballots, they protected them from their enemies until the end of the election, and escorted their ballots to the main office of the state election authority, and waited until the election results were announced. They made all these efforts under tense and stressful circumstances, because during the elections a large array of security officials and even soldiers were sent to guard all public exits into and out of the cities throughout the State of Kano. But all this did not prevent the voters from defending their political rights, because they showed the world that they were prepared to use their democratic freedom, no matter the difficulty or harassment involved. The perseverance that the people of Kano showed encouraged other states in the country to believe that all Nigerians could apply the same rules, and ensured that Nigeria’s democracy could become firmly established. If the reader would please recall the 2003 elections, the Kano community was organized in this way, and that’s how they were able to wrest power from the PDP government under the leadership of Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, and look at them now in 2007, as history repeats itself. During the elections that took place in 2007, the people of Kano endured all sorts of abuse at the hands of opponents and security officials, but nevertheless they came out and submitted their ballots, accompanied them, and waited until the results of the voting were given to them. As everyone knows, last year’s elections took place amidst confusion, because from the start, there were delays in the arrival of election materials at the polling station. People waited a long time for officials of the election commission (INEC) to bring the materials, but when they finally wandered in, some people, especially women, had already begun to return to their homes. In spite of this delay, many voters resolutely stood their ground until the election materials arrived, then they cast their ballots and refused to leave until the results were revealed, when everyone went his own way after they appointed representatives to accompany the ballot boxes to the office of the state election authority. Some of the people faced the anger of opponents and, as a result, they were attacked with fists, insults, machetes, knives, hatchets and by other means while they were accompanying the ballot boxes to the office of the election authority. For example, the people who accompanied the ballot boxes from Makoɗa Local Government Area didn’t fare well when some opponents cornered them on Makoɗa-Kano Road and attacked them with punches and insults, but nevertheless the resolute Makoɗa voters reached their goal of seeing to it that the ballot boxes reached the INEC office safely. This was also how things were for those accompanying the ballot boxes from Madobi, Tudun-Wada and Tsanyawa Local Government Areas, who also faced the same violence that was unleashed upon the people during the elections. If the reader will recall the day that the gubernatorial election was held, on 12 April, the election results were not received that day but rather on the following day and; as a result, research indicates that several young men stood their ground in a vast field right beside the office of the election authority, which is called the Polo Grounds, until the election results were announced at dawn. They then ran off into the town to express their delight at the outcome of the election. In light of this victory, Aminiya interviewed several Kano residents about their hopes for the new government of Malam Ibrahim Shekarau. They explained their hopes by saying that he would work diligently for the people of Kano to increase the state’s great wealth. Malam Yahaya Bello, a seller of gum and ink, made a special appeal to Governor Malam Ibrahim Shekarau to change the arrangement for administering his government so that people in the region could benefit, since in his opinion, “it was they who nurtured him and shared the burden during the gubernatorial election.” He informed Aminiya that if only Malam Shekarau would endeavor to finish the Tamburawa water works and ensure the establishment of an independent facility for supplying electricity to the state as he had promised before, it would bring much needed development to the public sector. Another person chatting with our representative at his sewing shop was a tailor named Malam Isma’il Ibrahim, who said that, in his opinion, there was no doubt that the people would enjoy tremendous support under this new government of Malam Ibrahim Shekarau. “Since the outset of the matter, we began to feel that he would do away with his cronies, that is, the commissioners who are so numerous there, that we think they won’t help him as is necessary, even though he has provided them everything [“given them both a knife and some meat”] relating to the administration of their work,” explained Isma’il the tailor. “Because of this,” he continued, “the main thing we will do for Malam is help him with our prayers to find local deputies who will assist him, to encourage the people to strive so that he can guide them in his second term.” A woman named Malama Hanne, who is in the business of selling fried bean cakes on a street here, called Sultan Road in English, in the Nassarawa neighborhood of Nassarawa Local Government Area in the State of Kano, begged the governor to consider the enormous difficulties folks suffered to ensure his election and that he should compensate them accordingly. “Especially we young women, some of us aren’t married, others’ husbands have died and left them with children, others are married but their husbands are out of work, and still others’ husbands have run off and abandoned their wives and children: because of this Malam Shekarau must make a special plan in this new government for resolving these kinds of problems among the women of Kano.; Even though he did this before, he should do it again, since the people have said he’s their only hope.” A strong source for Aminiya that is close to the state government informed our representative that the governor has promised to do much more for the people of Kano than what he did for them four years ago in his first term. . “At present, the governor is making plans to change all his commissioners and also establish a committee that will prepare him an outline for administering his second-term government, together with the kind of work that will be undertaken in each year for the benefit of the people,” explained Aminiya’s source. Whatever is in store, only time will tell whether or not Malam will repay the people who came out to vote and cast their ballots, who protected their ballots and waited for the election results in the State of Kano to be announced. |
Glossary
Hausa | Hausa Meaning | English Meaning |
---|---|---|
huɗubar | Wannan na kira ko gargaɗi da janaral yake yi ga talakawa. | This means sermon, but in the text it refers to the general's continuous call, speech, or call to the states. |
tsoro da firgita | Rawar jiki sakamakon tsoro. | Being shaky as a result of fear |
komai matsin lamba | Kamai aka yi, tursasawa. | Regardless of the pressure |
ƙwarin guiwar. | Wannan na nufin yarda. | Gwiwa means knee. In Hausa culture, the knee is an important part of the body. It is generally used with other words to give it meaning, mostly illustrating how the knee indicates support, confidence, cooperation, reassurance or strength, depending on the context. In this context, it means confidence or belief. |
uƙuba iri-iri | azaba daban-daban. | All kinds of pain or anguish |
ƙememe | Wannan na nufin suka yi tsaya da gaske. | This is a regional slang, mostly used in Northern Nigeria, which means to stand firm on something, or to be resistant. |
sha duka | shan bugu | To be severely beaten (literal meaning: to drink punches) |
Cibiyar | Wannan na nufin tsakiyar abu. | This means bellybutton or navel, but the word is frequently used in Hausa when referring to the root or source of something. |
kwalliya za ta biya kuɗin Sabulu | Ko aikin zai cacanci sakamakon da aka samu. | If the work, or input, is worth what one gets out of it (literal meaning: if the facial make-up is worth the price of the soap used to wash it off) |
Muƙarrabensa | Abokansa na kusa da shi. | This means his close friends but in the text refers to those who work closely with him. |
wuraren shige da ficen al’umma | Inda ake shiga da fita | People's entrances and exits (literal meaning: places of coming in and going) |
Gwagwarmaya | Yaƙin neman wani abu. | Struggles toward achieving a goal |
Jajurcewa | Haƙiƙancewa, watau mutum ya tsaya kan ra'ayinsa. | Strict opinion, stand, decision, etc. |
Note
Hausa | English |
---|---|
Tsinkayen Shekarau ya tabbata ranar 14 ga watan Afrilu, lokacin da aka ce ya yi nasarar zaɓen gwamnan jiha inda ya wuce sauran ‘yan takara da ƙuri’a 671,184. Ko da yake mutane musanman ‘yan jam’iyya PDP sun yi ta suka akan sakamakon zaɓen Kano, wata jihar arewacin Nigeria da cewa an yi maguɗi wajen ƙwatar akwatunan jefa ƙuri’a, yin ta’ada da makamai, da yi ma ‘yan zaɓe dodorido da ‘yan dabar jami’iyyu ke yi, jarida “Sunday Independent” kuma ta samo labarin cewa akwai wasu dalilai da suka ƙara sa rashin nasarar jam’iyyar waɗanda kuma suka haɗa da harakokin adawa, taruwar asusun kamfe, da ɗorin ‘yan takara ba cikin ka’ida ba. http://www.independentngonline.com/?c=185&a=25438 |
The prediction of politician Shekarau came true on April 14th, when he was declared winner of the gubernatorial election, beating fourteen other candidates with 671,184 votes. However, the election results in Kano, a northern state of Nigeria, have been severally criticized, particularly by the People’s Democratic Party (PDP). PDP has continued to allege that massive electoral fraud occurred, including theft of ballot boxes and violent intimidation of voters by the opposition party. A Nigerian newspaper called "Sunday Independent" gathered that there were other factors that played prominent roles in the party’s defeat at the polls, some of which include international conspiracy, under-funding of political campaigns, and the imposition of candidates. http://www.independentngonline.com/?c=185&a=25438 |
<activity>
<problemset>
<problem correctindex="0">
<choices>
<opt>
<eng-response>The writer of this editorial explains what the people of Kano did to ensure a fair gubernatorial election. After casting their votes, they followed every step of the election procedure, resisting violent beatings by the authorities, who tried to stop them from the follow-up. In the end, the public’s efforts paid off. Some are confident about the governor’s leadership, while others are just hopeful. The governor, in return, promised to work for them. In conclusion, the author states that time will tell what the people will get in return.</eng-response>
<response>Marubucin wannan rahoton na bayyani ne akan gwagwarmayar da jama’ar kano suka shiga don tabbatar da cewa an yi zaɓen wanda suke so ya zama gwamnansu bisa gaskiya. Bayan sun kaɗa ƙuri’unsu, sai suka bi dukan matakan zaɓe sau da ƙafa kuma suka daddage ma dukan gargaɗi da hukuma ta yi musu wajen ƙoƙarin hana su rakiyar ƙuri’unsu. A ƙarshe ƙakorin jama’a ya biya masu buƙatar. Wasunsu sun yi imani da shugabancin gwamnan, wasu kuma na fata ne kawai, shi kuma gwamnan ya yi alkawalin yi musu aiki. A ƙarshe marubucin ya bayyana cewa lokaci zai faɗi sakamakon da jama’a za su samu.</response>
<eng-fdbk>Correct! The author believes the people of Kano played an important part in ensuring a free and fair election in their state. The public expects good service from their governor in return for their fight to give him a second turn.</eng-fdbk>
<fdbk>Daidai! Marubucin na bayyani ne akan rawar da Kanawa suka suka taka mai muhinmanci don tabbatar da an yi zaɓe da gaskiya cikin jihar su. Jama’a na tsammanin kyakyawan aiki wajen aikin shi sakamokon gwagwarmayar da suka yi don hawan mulki na biyu.</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>This editorial is about the people of Kano State, and the governor they elected for their state. The election process was a difficult struggle for the people because of their determination to ensure a fair election, and also because of the authorities’ violent reactions against them. The author talked about his interview with some inhabitants of Kano, who mainly hope the governor plays his part in doing what he promised to do for them. Others are doubtful of his promises, and just want to wait and see if he will maintain the good works he did in his first term.</eng-response>
<response>Wannan rahoto na bayyani ne akan Kanawa da gwamnan da suka zaɓar ma jihar su. Harkokin zaɓen sai suka kasance ma jama’a wata mawuyaciyar fama saboda aniyar da suka sa gaba ta tabbatar da cewa an yi zaɓe cikin gaskiya kuma da kuma matakan da hukuma ta dauka na ƙuntata musu. Marubucin ya tattatauna da wasu Kanawan da musanman fatan su shine kawai gwaman ya yi aikin shi kamar yadda ya yi musu alƙawali. Wasu ma na shakkun alƙawalinshi kuma kawai suna son su sa ido ne su gani ko ya ci gaba da irin aikin da ya yi a karo na fari.</response>
<eng-fdbk>Incorrect! The public is not doubtful of the governor's second term. What did the interviewees say about their expectations for the governor?</eng-fdbk>
<fdbk>Wannan ba daidai ba ne saboda jama’a basu shakkar shugabancin gwamnan na karo na biyu ba. Mi masu amsa tambayoyi suka faɗa game da irin aikin da suke jira daga gwamnan?</fdbk>
</opt>
<opt>
<eng-response>According to the author of this editorial, the people of Kano State followed General Muhammadu Buhari’s advice to Nigerians about casting their votes and protecting them from miscount by opponents. As a result, they were able to reelect their governor, and in an interview, some citizens said they believe his second term will be just as good as the first term, if not better. Others believe they should pray for him because they do not approve of his commissioners, but the author concluded that time will tell, and that democracy will be better practiced if other states follow Kano’s example.</eng-response>
<response>Bisa ga bayyanin marubucin wannan rahoton, Kanawa sun bi shawarar da janaral Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Nieriya akan jefa ƙuri’ar zaɓe da tsare ƙuri’unsu daga maguɗi wajen ƙilgo. Sakamakon haka ne suka iya sake zaɓen gwamnan su kuma bisa ga ganawa da su marubucin ya ce wasu kanawan sun yarda da cewa mulkinsa a karo na biyu zai kasance da kyau kamar na farko idan ma bai fi shi ba. Wasu ma na ganin cewa ya kamata su yi masa addu’a saboda basu goyi bayan kwamishinonin sa ba. Amma marubucin ya kamala da cewa lokaci zai nuna kuma za’a yi kyakyawan anfani da dimokuraɗiyya idan sauran jihohi sun bi sawun Kano.</response>
<eng-fdbk>Incorrect! The author did not compare the governor’s first term to his next term in office. What was his comment about the governor’s success?</eng-fdbk>
<fdbk>Ba daidai bane saboda marubucin bai bambanta tsakanin mulkin gwamnan a karo na farko da na biyu. Wanne irin bayyani ya yi game da nasarar gwamnan?</fdbk>
</opt>
</choices>
</problem>
</problemset>
<instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
<instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
<finish>Do you think Nigerians will follow the steps Kano State took to ensure a successful election in their state? Why or why not?</finish>
<finish>What step should the Nigerian government take to ensure better election procedures in future elections?</finish>
<finish>Why do you think other states of Nigeria did not follow the General's advice to protect their votes and ballot boxes?</finish>
<finishtl>Kuna ganin 'yan Nijeriya za su bi sawun jihar kano don tabbatar da nasarar zabe a jihohinsu? Don mi?</finishtl>
<finishtl>Wanne irin matakai kuke ganin ya kamata gwamnatin Nijeriya ta ɗauka don tabbatar da zaɓen mafi dacewa nan gaba?</finishtl>
<finishtl>A ganin ku mi yasa sauran jihohi ba su bi shawarar janaral ba ta tsare ƙuri'un zaɓen su ba?</finishtl>
</activity>