Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/17 An Esteemed Media Veteran Retires

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/17)

Overview

  1. Lesson Title: An Esteemed Media Veteran Retires - This is a report about the retirement of an employee of Voice of America.
  2. Language: Hausa
  3. Topic: Culture/Society
  4. ILR Level: 1+/2
  5. ACTFL Proficiency: Advanced-Mid, Advanced-Low, Intermediate-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  6. Modality: Reading
  7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  8. Subject Area: Language
  9. Material Type: LO
  10. Publication Year: 2008
  11. ObjectID: HAUS_13049

Article: Steve Lucas Yayi Ban Kwana Da Muryar Amurka


Original Translation

A bayan da ya shafe shekaru 24 a nan Muryar Amurka, Steve Lucas yayi ban kwana da wannan gidan rediyo. Ma'aikatan Sashen Hausa ba su bar shi ya tafi haka ba, domin kuwa sun shirya masa wata babbar liyafar da ta samu halartar shugabannin sassa da dama, da darektar Afirka da kuma darektan shirye-shirye na Afirka.

Shi dai Steve Lucas ya fara aiki da Muryar Amurka a matsayin mai labaran Hausa. Daga nan ya zamo shugaban Sashen Hausa, ya kuma zamo shugaban Sashen Afirka baki daya. An nada Steve Lucas darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka.

Kafin ritayarsa kuwa, shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya na Muryar Amurka. Ofishin ya shirya masa wata liyafar ban kwana a ranar talatar makon jiya. A ranar larabar wannan makon kuma, Sashen Hausa ya karrama Steve Lucas da maidakinsa Fatouma da sauran iyalinsa a lokacin wata liyafar da ta hada da mika masa lambar yabo a zaman daya daga cikin jigogin kafawa da bunkasar Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Shugaban Sashen Hausa, Sunday Dare, ya yaba ma Steve a zaman mai basira da hangen nesa, wanda har bayan barinsa Sashen Hausa ya ci gaba da taimakawa da yin amfani da kwazonsa wajen ganin ci gaban Sashen.

Ita ma tsohuwar fardusar Sashen hausa, Donnie Butler, wadda ta yi ritaya a 'yan shekarun baya, ta yiwo tattaki musamman domin ta bayyana irin karimcin Steve Lucas da yadda ya rike mutane hannu bibbiyu a Sashen Hausa. Donnie Butler ta yi jawabi mai sosa zuciya kan irin kewar da ita da sauran wadanda suka yi aiki tare da Steve Lucas zasu yi na barinsa aiki.

Shirin "A Bari Ya Huce..." na wannan asabar, ya kunshi tattaunawa da Steve Lucas tare da maidakinsa Fatouma a kan shawararsu ta yin ritaya da kuma irin abubuwan da zasu yi nan gaba. Wakilin Sashen hausa na farko, Sani Abdullahi Tsafe, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa cikin shirin a kan halayyan dattaku na Steve Lucas.

Babu shakka, dukkanmu a nan Sashen Hausa za mu yi kewar Steve Lucas, amma da yake Nijar zai koma ya zauna, mun san cewa in sha Allahu ba ganin karshe ba ke nan da shi.

Hausa English
Original Translation

Steve Lucas yayi Bankwana da Muryar Amurka

Steve Lucas says goodbye to the Voice of America
By Ibrahim Alfa Ahmed By Ibrahim Alfa Ahmed
01/08/2008 August 1, 2008
A bayan da ya shafe shekaru 24 After serving for 24 years
a nan Muryar Amurka, here at the Voice of America,
Steve Lucas ya yi ban kwana Steve Lucas bids farewell
da wannan gidan rediyo. to the radio station.
Ma'aikatan Sashen Hausa The Hausa Service employees
ba su bar shi weren't letting him
ya tafi haka ba, leave quietly,
domin kuwa sun shirya masa as they organized
wata babbar liyafar a send-off party for him,
da ta samu halartar which was attended by
shugabannin sassa da dama, heads of several departments,
da darektar Afirka the Africa Division director,
da kuma darektan shirye-shirye na Afirka. and the Africa Division program manager.
Shi dai Steve Lucas Steve Lucas
ya fara began
aiki da Muryar Amurka working at the Voice of America
a matsayin mai labaran Hausa. as a Hausa newscaster.
Daga nan ya zamo Then he became
shugaban Sashen Hausa, head of the Hausa Service
ya kuma zamo and then
shugaban Sashen Afirka baki daya. head of the entire Africa Division.
An nada Steve Lucas Steve Lucas was then appointed as
darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka. director in charge of African Affiliate Stations.
Kafin ritayarsa kuwa, Before his retirement,
shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya he was director of the Office of Marketing and Program Placement
na Muryar Amurka. for the Voice of America.
Ofishin ya shirya masa wata This office threw him
liyafar ban kwana a farewell party
a ranar talatar makon jiya. last Tuesday.
A ranar larabar wannan makon kuma, And this Wednesday,
Sashen Hausa ya karrama Steve Lucas the Hausa Service honored Steve Lucas,
da maidakinsa Fatouma his wife Fatouma
da sauran iyalinsa and the rest of his family
a lokacin wata liyafar da ta hada da at a party that also
mika masa lambar yabo awarded him a plaque,
a zaman daya daga cikin jigogin kafawa in recognition of his role in the establishment
da bunkasar and development of
Sashen Hausa na Muryar Amurka. Voice of America's Hausa Service.
Shugaban Sashen Hausa, The head of the Hausa Service,
Sunday Dare, ya yaba ma Steve Sunday Dare, praised Steve
a zaman mai basira for his intelligence
da hangen nesa, and foresight,
wanda har bayan barinsa Sashen Hausa saying that even after his transfer to other departments,
ya ci gaba he continued
da taimakawa da yin amfani da kwazonsa wajen ganin ci gaban Sashen. to support the Hausa Service.
Ita ma tsohuwar fardusar Sashen hausa, Donnie Butler, Donnie Butler, a former producer in the Hausa Service,
wadda ta yi ritaya who retired
a 'yan shekarun baya, a few years ago,
ta yiwo tattaki musamman went on at great length
domin ta bayyana to describe
irin karimcin Steve Lucas da yadda ya rike mutane hannu bibbiyu a Sashen Hausa. how much she and others who worked with Steve Lucas continue to miss him.
Donnie Butler ta yi jawabi mai sosa zuciya kan irin kewar da ita da sauran wadanda suka yi aiki tare da Steve Lucas zasu yi na barinsa aiki. Donnie Butler, a former producer in the Hausa Service, who retired a few years ago, went on at great length to describe how much she and others who worked with Steve Lucas continue to miss him.
Shirin "A Bari Ya Huce..." na wannan asabar, Next Saturday’s edition of the "A Bari Ya Huce…" program
ya kunshi tattaunawa will feature an interview
da Steve Lucas tare da maidakinsa Fatouma with Steve Lucas and his wife Fatouma
a kan shawararsu on their decision
ta yin ritaya to retire
da kuma irin abubuwan da zasu yi nan gaba. and their future plans.
Wakilin Sashen hausa na farko, The first Hausa Service stringer,
Sani Abdullahi Tsafe, Sani Abdullahi Tsafe,
shi ma ya tofa albarkacin bakinsa cikin shirin will also participate in the program,
a kan halayyan dattaku na Steve Lucas. where he comments on for Steve Lucas' gentlemanly character.
n/a [Translator’s note: The program title "A Bari Ya Huce…" is derived from a Hausa proverb ("A bari ya huce shi ke kawo rabon wani"), which translates as "Seize the moment."]
Babu shakka, Without a doubt,
dukkanmu all of us
a nan here
Sashen Hausa at the Hausa Service
za mu yi kewar Steve Lucas, will miss Steve Lucas;
amma da yake Nijar zai koma ya zauna, But since he is moving to Niger Republic;
mun san cewa we know that,
in sha Allahu God willing,
ba ganin karshe ba ke nan da shi. we have not seen the last of him.


Background Information

  1. Ibrahim Alfa Ahmed interviewed Steve Lucas and his wife Fatouma, asking them several question regarding his retirement and moving back to Niger” Ibrahim Alfa: Why are you leaving the United States for Niger? Steve Lucas: I have a three-year-old daughter and I want her grow up with discipline, and we have a house in Niger. Fatouma Lucas: Niger is a very peaceful place and, besides, my family lives there and I miss home. http://www.voanews.com/hausa/archive/2008-08/2008-08-01-voa1.cfm?CFID=43288910 &CFTOKEN=95915679, https://www.voahausa.com/a/a-39-2008-08-01-voa1-91724104/1369301.html

Grammar

  1. _In sha Allah_ (by God willing) is a phrase used by Muslims to indicate that one cannot do anything unless God allows it.
  2. _Jawabi mai sosa zuciya_ (speech that scratches the heart) refers to speech that is touching and heartfelt.

L2 Purpose-Audience Problem Set

  1. What is the purpose of this report?
    The text gives details about the retirement of Steve Lucas, a twenty-four year employee of Voice of America, and his contributions to the Hausa news service and the company as a whole.
    Consider the occasion for the party the report describes. Please refer to the Notes for more information about Steve Lucas and VOA.

L2 Facts-Figures Problem Set

  1. How did the career of Steve Lucas at the Voice of America develop over time?
    He began as a newscaster, then he became the head of the Hausa Department until he began directing the entire African division. He retired from the Office of Marketing and Program Placement for the Voice of America.
    Consider all the positions he held in the last twenty-four years of service with VOA.
  2. What are Steve Lucas's contributions to the development of Voice of America?
    He is considered one of the major founders and developers of the Hausa service of VOA.
    Consider the reason why the plaque was given to Steve Lucas.
  3. What do his co-workers appreciate about him?
    His co-workers think of him as a smart, generous man that sees ahead and who treats people with dignity and honor.
    Note the remark of Lucas's co-worker at a Hausa program called _A Bari ya Huce_.
  4. What is Steve Lucas planning to do after his retirement and what do his colleagues think about his plans?
    Because Lucas plans to move to Nigeria, his colleagues from the Hausa service hope he will still be with them.
    In what regard is Nigeria mentioned in the report. Visit the Learn More section for the interview with Steve Lucas.