Toggle menu
24K
664
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/28 Fulani Education

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/28)

Overview

  1. CONTENT SOURCE: Host (Kabiru Fagge ); Reporter (Ibrahim Ka-Almasih); analyst Dr. Ibrahim Tahir; Author of the book un (2006 September 29). Fulani Education. Washington, D.C.: Voice of America, Hausa Service.
  2. Objective: Demonstrate your core comprehension.
  3. Lesson Title: Fulani Education - This presentation discusses a report on the introduction of Western education to the Fulani people in Nigeria.
  4. Language: Hausa
  5. Topic: Culture/Society
  6. ILR Level: 2+/3
  7. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  8. Modality: Listening
  9. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  10. Subject Area: Language
  11. Material Type: LO
  12. Publication Year: 2007
  13. ObjectID: HAUS_11718

Transcript


Original Translation

Fulani Education

  1. A: Masakin da hukumomin Nijeriya suka ɗauka
  2. domin bunƙasa
  3. ilimin ƴaƴan Fulani musamman ma makiyaya,
  4. shekaru ƙaɗan da suka gabata, yanzu ya fara samun Allah son barka, domin kuwa wani gawatacen Bafulatani ya wallafi littafi domin bunƙasa hikimomi watau bayanai da halin zaman rayuwa bafu, Fulanin Nijeriya suke a ƙunshe a cikin wani littafi.
  5. Ibrahim Garba Ka’almasi waƙilin sashen hausa na Muryar Amurka ya hallaci gangamin a damar da shirye-shiryen harhaɗa waɗannan maganganu ko kuma bayanai da halin zaman rayuwar Fulani, ga shi kuma da cikakken bayani daga Kaduna:
  6. B: A ci gaba da ƙoƙarin kwaɗaitawa al’umma Fulani fa’idar neman ilimi, musamman ma na boko, wani likitan dabbobi kuma shugaban shiyya na bankin bayar da rance ga ƙananan masu sana’a {NACRPP [English]} a taƙaice dokta Bappa Anin ya ɓullo da wani sabon salo.
  7. Wannan sabon salo kuwa ya ƙunshi tattara maganganun azanci, da hikima, da manyan zantuttuka na Fulanin daji waɗanda shi dokta Bappa Usman Anin ya wallafa a matsayin littatafai har guda biyar cikin turanci da kuma fulatanci. Masu jawabai ɗai bayan ɗaya, da suka halarci ƙadamar da waɗannan littatafai biyar. Sun yi ta tashi suna cewa littatafan za su ƙara bayar da sha’awar karance-karance da neman ilimi ga Fulani da ma sauran jama’a, saboda sun ƙunshi bayanai na yadda ɗan Adam ya fahimci abubuwan halitta da ke zagaye da shi, da kuma yadda suke tasiri kan tunaninsa. Dokta Ibrahim Tahir, taliban Bauchi, na dai daga cikin ma’abuta ilimi da suka yi jawabai a wurin.
  8. C: Ainihin rayuwar Fulani, ainihin al’adunsu, ainihin shigan abun da suke su je, da yadda suke kallon duniyarsu, suke kallon abubuwa da yanda suke da ilimi kan abubuwa dabam-dabam, watau … wata duniya ce mai daula, mai ado, mai kyawa, mai ban sha’awa amma mutane ba … kuma ba a san abun da ɗan Fulo yake faɗi ba in yana faɗa ko yana hirashi shi kaɗansa daddare, ko shi da budurwa su suna zance irin yadda maganarsu ke tafiya, ta ce kaza, ya ce kaza, ta ce kaza, ya ce kaza kuma da inda shi yake duban sama ya yi magana wata tauraruwa, ko yanda yake duban bakin kogi ya yi magana wani ciyawa da rauna-rauna shawage dangane da shanu, da dabbobin sa ya dubi wani ice, ya san abubuwa game da shi, ya yi waƙashi ya yi magana a kai, mutanen sa da suke tafiya, haka da ƙwarya a kansu sharaf-sharaf da ƙwada da me …
  9. B: Dokta Ibrahim Tahir ke nan, taliban Bauchi. Shi kuwa mawallafin littatafan dokta Bappa Usman Anin ya bayyana min dalilansa na wallafa waɗannan littatafai.
  10. D: Ai, na yin ai saboda kaman yadda ka ce saboda ingiza su su tashi tsaye, su san zamani ya canza saboda a tafi da su a duniya a san manufan gwamnati, kuma su san al’adunsu. Ah … ya zamanto su ma an yi da su. Muhimmancin karatu musamman na zamani, ah … ya kasance su ma Fulani su tashi ko Fulanin daji yanzu, su ma ba wai kiwo kawai ba, hadda karatun, a iya haɗa guda biyun. To, shi ya sa ake da … ai … hukumar… ai ... na makiyaya taimakama, makiyaya ana tallafa musu, ana gina musu gina masu manyan makarantu a daji, ana kai musu malamai, ana koyar da su duk ya kasance saboda su zama mutane na gari, ana yi da su.
  11. B: Dokta Bappa Usman Anin ke nan, mawallafin littatafan. Su kuwa wasu matasan Fulani a wurin taron, sun bayyana mana ra’ayinsu kamar haka:
  12. E: Na ƙara ma ƴaƴan Fulani muhimmancin digi, muna ina kira ga Fulani ƴan’uwana da su cinmatu, su saka ƴaƴayensu a makarantu domin ilimi yana da amfani ƙwarai da gaske.
  13. F: Ni ne {((-))} Issa, ina kira ga Fulani ƴan’uwanmu game da wannan littafi da aka ƙadamar, Allah ya sanya albarka ciki. Ina kira kuma ga ƴan’uwanmu Fulani domin ilimi shi ne gishirin zaman duniya, daga nan har lahira. Ina kira ga ƴan’uwanmu su ƙoƙari su harɓi kansu su shiga ga wannan ilimi, don wannan ilimi nawa shi ne zai bar mu a ta tafi muna zaune hankalinmu, ya ɓata bayan ana lura da mu a ko’ina da ko’ina. Muna so mu ma mu fito fili mu yi {((-))} da kanmu a san da mu a cikin wannan Nijeriya tamu.
  14. G: Salamu alaikum, ni ne Ɗan Sule Abdullahi. Wannan littafi haƙiƙa ya faranta mini rai, ya yi kyau, ina fata Fulani wanda suke nan gari Kaduna su ƙoƙarta su sa ƴaƴayensu a makaranta saboda ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Ilimi addini da na boko shi ne cikkake. Kiyo da …
  15. B: Wasu matasan Fulani ke nan, a bikin ƙadamar da waɗannan littatafan. Ibrahim Ka’almasi Garba, Muryar Amurka, daga Kaduna a Nijeriya.

Fulani Education

  1. A: … and the week that the Nigerian authorities take up
  2. the advancement of education for
  3. Fulani children,
  4. particularly those involved in herding, for the coming years, now that it has received God’s blessings, because an enterprising Fulani man has published an authoritative book that explains the details of Fulani life, and the Fulani of Nigeria are included in the book.
  5. Ibrahim Garba Ka’almasi, representing the Voice of America Hausa Service, appears regularly for the purpose of programs about these discussions or explanations about the nature of Fulani life, so here he is with a full explanation from Kaduna:
  6. B: To advance the effort to interest the Fulani community in the usefulness of education, particularly Western education, a veterinary doctor and regional director of the small business loan operation NACRPP, Doctor Bappa Anin, came up with a new model.
  7. This new model involved collecting practical information, and the major issues facing the rural Fulani, which Doctor Bappa Usman Anin published in a series of five books in both English and Fulani. A few speakers went on a campaign with these five books. Several stood up to say that these books would provide interesting educational lessons for the Fulani and other people, because they included explanations about the human understanding of the natural world around them and also the benefit of these ideas. Doctor Ibrahim Tahir from Bauchi was one of the educators who gave talks on these occasions.
  8. C: The real lives of the Fulani, their actual customs and awareness of their surroundings, and the way they see their world, how their beliefs stem from a unique way of understanding things, in other words … this is a world of richness and beauty, of great interest, that people don’t … we don’t know what a Fulani man says when he is talking or when he is thinking to himself in the middle of the night, or when he and his girlfriend are having a conversation, how their talking progresses: she says such-and-such, he says such-and-such, she says such-and-such, he says such-and-such. Or when he’s gazing at the sky, what he says about the stars, or when he looks at a river bank, what he says about a certain kind of grass growing there and its suitability for his cattle and other animals, or looking at a certain tree, he knows things about it, he sings his song and talks to himself. And when herding people travel, with sloshing calabashes on their heads and their games and such …
  9. B: That was Doctor Ibrahim Tahir from Bauchi. Then the publisher of these books, Doctor Bappa Usman Anin, explained to me his reasons for publishing these books.
  10. D: Well, I did it in order to, as you might say, encourage them to stand tall. They know that times are changing, because one goes with them out into the world, one sees the government policies, and they know their customs. Ah … it was time to do something for them. Most importantly modern education, ah … for the Fulani to advance, even now the rural Fulani, they can’t just be herding anymore, they need education, and one can bring these together. So, this is why the … authority was granted … for assisting them with grazing land, for protecting their grazing land, and building them a few large rural schools, bringing them teachers, and teaching them; everything was done in order for them to become town dwellers.
  11. B: That was Doctor Bappa Usman Anin, who published the books. And then some Fulani youths at the assembly explained to us their opinion like this:
  12. E: For raising Fulani children in these important first stages, I’m calling upon my Fulani brothers to take heed and place their children in schools, because knowledge is truly beneficial.
  13. F: I’m Issa, I’m calling out to our Fulani brothers about this book that was launched, God has put his blessings in it. I’m also calling out to our Fulani brothers that knowledge is the key to living, from here to the next world. I’m calling out to our brothers to try and devote themselves to accessing this knowledge, because it is this knowledge of ours that will allow us to go out and live intelligently. We want to go out into the world and better ourselves, and have others understand us in this Nigeria of ours.
  14. G: Salamu alaikum, I’m D’an Sule Abdullahi. This book really makes me happy, it’s great, and I hope that the Fulani here in Kaduna will make an effort to put their children in school, because knowledge is the key to living. It is full of religious and Western knowledge. Herding animals and …
  15. B: Those were some Fulani youths, at the presentation ceremony for these books. I’m Ibrahim Ka’almasi Garba, Voice of America, from Kaduna, Nigeria.

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
Samu Allah son barka. Ana ganin abubuwa masu kyau da suke faruwa bayan an yi wani abu. Something is done and good results are showing
Gawatacen bafulatani. Wannan kalma tana iya nufin masani, ko gwani, ko kuma mai ƙoƙari mutun wanda shike na ƙabila fulani. This word may imply an expert, or an educated, respected, or powerful man from the Fulani tribe.
Kwaɗaitawa Ba da marmarin abu. To have or feel an urge or need for something. It can also mean to attract or to lure.
Fa'idar neman ilimi. Anfanin ko daɗin neman ilimi ga rayuwa mutun. The importance or the advantage of knowledge
Taliban Bauchi Wannan suna ne ko matsayi da ake kiran wasu maza fulani. Title, such as "scholar", given to a male in societies like the Fulani society.
Wata duniya ce mai daula wata duniya ce daban, mai abubuwan al'ajibi. In the context this describes a different world rich in its cultures and wonders, with powers that only those who belong to it will understand. (It may not make sense to outsiders).
Ɗan Fulo Namijin Fulani. This means the son of a Fulani, but refers to a male Fulani in this context.
Ingiza su su tashi Tura su su yi abun da ya kamata. Pushing them to do what they need to do or pushing them to stand up for themselves
'Ya'yayensu Wannan wata hanya ce ta cewa yaransu This refers to their children or their kids and is spelled in two different ways.
Ilimi shine gishirin zaman duniya. Wanna karin magana yana nufin ilimi muhimmin abu ne ga rayuwar mutun cikin zaman jama'a. This saying means knowledge is important in a person's life. Knowledge is compared to salt because it is almost impossible to cook without salt in this culture. Could also be "knowledge is the spice of life."

Notes

Hausa Notes English Notes

Ƙabila Fulani na ɗaya daga cikin ƙabilun Afirka kuma ana samun yawancin su wajajen yammacin Afirka. Ko da yake yanzu ana samunsu cikin birane, asalin ayyukan fulani kiyo, noma da kuma kasuwanci. Wasu masana kuma sun yarda da cewa asalin fulani Sene-Gambia, daga baya sai suka watsu cikin dazuzzukan yamacin Afirka. Fulani sun taka mahimiyya rawa cikin tarihin ƙasashen da ke cikin iko ko kuma daula kamar ƙasar Ghana, Mali, Songhai da Mossi. Fulani kuma na da hannu wajen yaɗuwar musulunci a yammacin Afrika. Farawar ƙarni na 19, fulani sun ƙirƙiro sarakuna biyu masu muhimanci, ɗaya na kula da wajajen Timbuktu, ɗaya kuma na kula da ƙasashen hausa da wasu ɓangarorin Borno amma sarkin na zama tsakiyar Sokoto (cikin Nijeriya) da yammacin Cameroon. http://www.jamtan.com/jamtan/fulani.cfm?chap=1 http://education.yahoo.com/reference/encyclopedia/entry/Fulani

The Fulani tribe is one of the many tribes in Africa. Its people are mostly found in the western parts of Africa. Originally described as nomadic herders, traders and farmers, the Fulani people are now found even in urban areas. There are varied opinions about their origins, and some experts believe they originated from Sene Gambia regions and that, over centuries, they migrated with their cattle, occupying vast areas of West Africa’s Sahel and savannah regions. The Fulani played a significant role in the rise and fall of ancient African empires in Ghana, Mali, Songhai and Mossi. They are also known to have contributed to the spread of Islam in West Africa. During the first part of the 19th century, the Fulani carved out two important emirs. One, based in Massina, for a time controlled Timbuktu. The other, centered in Sokoto, included the Hausa states and parts of Bornu (in Nigeria) and western Cameroon. The Fulani emir of Sokoto continued to rule over parts of northern Nigeria until the British conquest in 1903. http://www.jamtan.com/jamtan/fulani.cfm?chap=1 http://education.yahoo.com/reference/encyclopedia/entry/Fulani

XML


 
 <activity>
    <problemset>
       <problem correctindex="1">
          <choices>
             <opt>
                <eng-response>This report discusses the outcome of Nigerian government’s effort in the past years to promote Fulani education. Doctor Bappa Usman, a Fulani veterinary doctor, wrote several books to support the Fulani people in rural and urban areas of Nigeria. According to the doctor, his intention was to make them understand the need to take part in today’s society and to understand their own culture. Based on Ibrahim Garba’s interview with some of those who attended the launching of the books, there is support for Fulani education, and some of the youths interviewed urged that Fulani children be sent to school, especially those in Kaduna. Doctor Bappa concluded that a Western education will make them part of society.</eng-response>
                <response>Wannan rahoto na Magana ne akan sakamakon ƙoƙarin hukumar Nigeria wajen inganta ilimi ‘ya’yan fulani. Wani likitan dabbobi kuma Bafilace mai suna Dokta bappa Usman ya wallafa wasu littattafai don goyon bayan fulanin cikin daji da na birni. Likitan ya bayyana cewa ya yi wannan ne don ‘ya’yan fulani su gane cewa ya kamata a yi da su cikin jama’a kuma su gane al’adunsu. Bisa ga tattaunawar Ibrahim Garba da wasu da suka kasance wannan taron, mutane na goyon bayan ilimin ‘ya’yan fulani kuma wasu matasan fulani na ƙarfafa fulani da su sa ‘ya’yensu makaranta.Dokta bappa ya kamala da cewa ilimin boko zai sa su shiga cikin jama'a.</response>
                <eng-fdbk>Incorrect. This is wrong because the report did not mention specific areas where Fulani children should be sent to school. What are the interviewees’ comments about Fulani people and their children?</eng-fdbk>
                <fdbk>Ba daidai ba ne. Wannan ba daidai ba ne saboda rahoton bai bada inda ya kamata fulani su je makaranta ba. Mi masu amsa tambayoyi suka faɗa game da fulani da ‘ya’yansu?</fdbk>
             </opt>
             <opt>
                <eng-response>According to this report by Ibrahim Garba, a Fulani veterinary doctor wrote five books in English and Fulani to encourage and support Fulani education in rural and urban areas. At the launch of the books, the reporter interviewed Doctor Tahir, one of the speakers, who described the Fulani people’s way of life as an amazing and different world rich in its own culture. Some of the Fulani youth interviewed by the reporter also supported Doctor Bappa Usman’s books and urged the Fulani population to send their children to school. Other speakers also supported the books, commenting that both the Fulani people and the non-Fulani will benefit from them.</eng-response>
                <response>Cikin wannan rahoto na Ibrahim Garba, wani likitan dabbobi kuma bafilace ya wallafa littattafai guda biyar cikin harshen turanci da filatanci don ya ƙarfafa bunƙasa ilimin fulani cikin daji da birni. Wajen biki ƙadamar da littatafan, ɗan jaridar ya tattauna da ɗaya daga ciki masu jawabi  mai suna Dokta Tahir wanda ya kwatanta rayuwar fulani da wata duniya mai daula da ban sha’awa.Wasu matasan fulani da ɗan jarida ya ma tambayoyi sun bayyana goyon bayansu ga littatafan kuma suna roƙon fulani da su sa ‘ya’yansu makaranta. Sauran masu jawabi wajen taron ma sun bayyana goyon bayansu da cewa littatafan za su anfana fulani da waɗanda ba fulani ba.</response>
                <eng-fdbk>Correct. The report talks about promoting Western education for the Fulani people in Nigeria, and the interviewees’ opinions support Doctor Bappa’s books.</eng-fdbk>
                <fdbk>Daidai ne. Wannan rahoton na bayyani ne bisan ilimin  fulani a Nijeriya, kuma waɗanda aka yi ma tambayoyi sun bada ra’ayinsu na goyon bayan littatafan Dokta Bappa.</fdbk>
             </opt>
             <opt>
                <eng-response>According to this report, some years ago, the Nigerian government began an initiative to see that the Fulani population in Nigeria receives a Western education like every Nigerian citizen. A doctor supported the initiative by writing five books containing informative stories about Fulani culture and everyday life. Some of the speakers who attended the launch of the books praised the doctor’s efforts, and those interviewed by reporter Ibrahim Garba also supported the writer. The writer also stated the need for the Fulani people to go beyond cattle-rearing, and asked authorities to build schools for them in rural areas and to send teachers to help them.</eng-response>
                <response>Shekaru kaɗan da suka gabata, hukumar Nijeriya ta yi fasaha tabbatar da cewa ta ilmantar da fulanin Nijeriya kamar dai na sauran jama’ar ƙasar kamar yadda wannan rahoto yake nunawa. Wani dokta ya nuna goyon bayanshi ga hukumar wajan wallafa littatafai guda biyar da ke ƙunshe da  zantatukan azanci, da hikima da kuma al’adun funlani da rayuwarsu ta yau da kullum. Masu Magana wajan taruwar bikin da waɗanda suka tattauna da Ibrahim Garba sun goyi bayan marubucin. Ma wallafin kuma ya bayyana cewa ya kamata hukumomi su gina makarantu cikin daji,  su aika malamai kuma kada fulani su tsaya ga kiyo kawai.</response>
                <eng-fdbk>Incorrect. This is wrong because the report did not compare the Fulani education to that of Nigerian citizens. What did the presenter say about the Nigerian authority’s goal?</eng-fdbk>
                <fdbk>Ba daidai ba ne. Wannan ba daidai ba ne saboda rahoton bai yi banbanci ba tsakanin ilimin fulani da na sauran 'yan Nijeriya. Mi mai gabatarwa ya faɗa game da maƙasudin hukumar Nijeriya?</fdbk>
             </opt>
          </choices>
       </problem>
    </problemset>
    <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
 Choose the best summary.</instr>
    <instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
    <finish>How could the introduction of Western education affect the Fulani people's tradition of cattle rearing?</finish>
    <finish>How can the Fulani people benefit from the books written by Doctor Bappa if most of them have not received a Western/formal education?</finish>
    <finish>What do you think will be the Fulani people's reaction to having schools in the rural areas?  How would they compare to those in the urban areas?</finish>
    <finishtl>Yaya ilimin boko ke iya shafar al'ada fulani ta kiyo?</finishtl>
    <finishtl>Yaya fulani za su iya samun ƙaruwa da littatafan da Dokta bappa ya rubuta in ba su taɓa yin karatun boko ba?</finishtl>
    <finishtl>Yaya kuke ganin fulani za su ɗaukar buɗewar makarantu cikin dajin su? yaya za su banbanta da na birni?</finishtl>
 </activity>