Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

UMD NFLC Hausa Lessons/35 In the Eyes of the World

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
(Redirected from UMD NFLC Hausa Lessons/35)

Overview

  1. Lesson Title: In the Eyes of the World-This editorial presents an expert's arguments on the role of the widely spoken African language, Hausa, in the media as well as in education.
  2. Language: Hausa
  3. Topic: Culture/Society
  4. ILR Level: 2+/3
  5. ACTFL Proficiency: Superior, Advanced-High; This ACTFL rating is an approximation based on the ILR level
  6. Modality: Reading
  7. Learning Objective: Maintenance & Improvement
  8. Subject Area: Language
  9. Material Type: LO
  10. Publication Year: 2007
  11. ObjectID: HAUS_12043

Transcript


Original Translation

In the Eyes of the World

Hausa A Idon Duniya

WANNAN shi ne ƙarshen maƙalar da muka fara kawo maku a wannan shafi a inda FUROFESA ALIYU MUHAMMAD BUNZA na Jami’ar Usmanu Ɗanfodio da ke Sakkwato ya gabatar da lacca a kan Hausa a Idon duniya. Muna fata ana biye da mu:-

IDAN mu ka fita wajen Nijeriya,za mu ga cewa, Hausa ita ce ta mamaye kafafen yaɗa labarai na duniya a cikin harsunan Afirka. Ka ɗan daga cikin gidajen yaɗa labarai na duniya da Hausa ta samu miƙe ƙafafunta sun haɗa da:

1.Gidan Rediyon BBC 2.Muryar Amurka 3.Muryar Jamus 4.Gidan Rediyon Bejin Caina(Sin) 5.Rediyon Iran(Farisa) 6.Gidan Rediyon Makka, Saudi Arebiya 7.Gidan Rediyon Nijar 8.Gidan Rediyon Ghana 9.Gidan Rediyon Misira 10.Gidan Rediyon Masko.

Abu kamar ƙaddara, inji Buzu da ya sha kayen raƙumi. Cikin harsunan duniya a yau, babu harshen da ya fi Hausa karɓuwa a gidajen yaɗa labarai a duniya harshe biyu suke ji, Hausa da Kiswahili. Izan za a gwada tsawon harsunan biyu a fagen yaɗa labarai ala tilas Kiswahili ya bada Wuri domin Sani Ɗanbalɗo cewa ya yi:

“Ta yaro ba ta kamar ta babba, Matuƙar ba....... Irin muhibba da Hausa ta samu saman harsunan Afirka ya sa nake tunawa da taken makaɗin kura lokacin da Jigji(ƙaton bunsurun tsafi) ya ce zai kokuwa da ita,makaɗin na cewa:

“Ƙashin gwiwar kura Ba lasan karnai ba A ba manya fili Bba don Allah ne ba“.

Haɗuwa wurin kokawar ke da wuya sai makaɗin Jigji ya sauya ƙiriya ya ke cewa: “Baya baya Muhammadu Baya baba Muhammadu Baya baba Muhammadu.“

SAI BANGO YA TSAGE Ko ɗaya ba zan zargi ɗalibin da bai san sirrin ilimi ba idan ya nuna tsana ga ƙin wani darasin karatu don ganin wuyarsa ko sauƙinsa da dai sauransu.Dalili kuwa shi ne, rashin sani ya fi dare duhu.

Ina ganin wauta da rashin adalci,da rashin kishi da wofintar da kai, da mai da gaba baya da rashin sanin ciwon kai, ga ɗalibin Hausa ko Malamin Hausa mai nuna rashin kishi ga abin da yake yi.

Da wane dalili ne ɗalibin Hausa ke ɓoye kansa cikin ɗaliban karatu a Jami’a? Wa ya kai shi balle ya fi shi? Me ake karatu da ya kai nasa? Assha da malamin Hausa da ke gudun a ce Hausa yake koyarwa. Wane darasi ne na Hausa da ba a iya koyar da shi da Hausa? A gaskiya babu shi.

Masu irin wannan halin su ke rusa Hausa da karantar da ita ga su kuma, ba su fahimci Hausar ba Turanci ya gagare su, a ƙarshe an yi haihuwar guzuma, ɗa kwance uwa kwance.Haƙiƙa idan Ka ga mutum na gudun abu bai san shi ba ne, in ya san shi tsaye zai yi in til in ƙwal rinin mahaukaciya.

RABA GARDAMA Hausawa na cewa wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokawa. Babban abin da harshe zai samu duniya a san shi, ya samu ɗaukaka shi ne malamai da masana da ke kwana a cikinsa domin kare darajarsa da martabarsa a ilimance. A taƙaice cikin harsunan Afirka babu harshen da ke da masana irin harshen Hausa. Babu harshe da ke da wallafe- malamai da masana da zai iya gogawa da kowane harshen duniya ta fannin bincike da nazari da zai amfani jama’a.

Daga cikin manyan ɓangarorin nazarin Hausa muna da: i.Harshe ii.Adabi iii.Al’ada

A cikin waɗannan fannonin, harshen Hausa na da kimanin ƙwararrun malamai masu digirin digirgirewa (Digirgir) Ph.D fiye da talatin (30) da ke koyarwa a cikin jami’o’in Nijeriya. Babu wani harshe na Nijeriya ko Afirka da ke da rabin waɗannan ƙwararru a cikin jami’o’i a yau. Ta fuskar shehunan masana kuwa bayan waɗanda Allah Ya kira,(Allah Ya gafarta masu) rayayyu Hausa na da shehunan malamai kimanin guda sha biyu da ke yi mata yaƙi a ɓangarorinta guda uku kamar haka:

HARSHE(Language) 1.Furofesa Hambali Junju- Nijar 2.Furofesa Dauda Bagari- UDUS 3.Furofesa Bello Salim BUK 4.Furofesa Abdulhamid Maiduguri 5.Furofesa Ibrahim Mukoshy UDUS 6.Furofesa Mu’azu Sani Zariya BUK 7.Furofesa Abba Rufa’i BUK

ADABI(Literature) 1.Furofesa Ɗalhatu Muhammad ABU 2.Furofesa Dandatti Abdulƙadir BUK 3.Furofesa Abdulƙadir Ɗangambo BUK 4.Furofesa U B Ahmed ABU 5.Furofesa Abdu Yahaya Bici BUK 6.Furofesa Haruna Birniwa UDUS 7.Furofesa Sa’idu Muhammed Gusau BUK

AL‘ADA(Culture) 1.Furofesa Aliyu Muhammad Bunza UDUS Tirƙashi! Wane harshe a Afirka ya tara masu yi masa kariya irin Hausa? Don haka, idan aka ce Hausa a idon duniya babu abin da za mu ce face a tambayi Gambo: “Dole nakiya ta yi zaƙi, Don da zuma aka fara yin ta.“ NAƊEWA: Bari in taya sababbin ɗalibai murna da suka samu shiga cikin wannan babban rabo na koyon harshen da ke limancin harsunan Afirka ta kowace fuska. Haka kuma bari in tabbata maku, babu mai nunin gidan su da hannun hagu, don haka Hausa ba bare ba ce a cikin harsunan duniya.

Tabbas rashin sani ne ya sa Karen Gwauro ya kori Bazawara, da ta sani da cewa, Karensu ne, da ala tilas ya yi masu tsaro. Ku sanya ido ku duba da kyau,da masu Turanci da masu tarihi da masu walwala da masu karatun siyasa da masu karatun tsimi da tanadi in dai Hausawa ne, Hausa ce suke karatu cikin rigar Turanci domin da ayyukan Hausa suke laɓewa su yi wa marasa kula wala-wala da dodorido a tauni tsakuwa a ba gyaɗa tsoro.

Ban ga laifin Goga Sarkin Rigima ba da ya gane irin ƙwaruwar da mata ke yi wa maza, ya tura matarsa noma gona, shi kuwa ya tsaya gida ya na niƙa da rera har da waƙa ya na cewa: Ku lura da mata don ku sani. Ƙwaranmu suke yi mun gane, Ku lura da safe mu ji daji, Noma icce duk mun rame, To ga wata doka don ku sani, Kowa ya yi noma don dole, Ni ne Goga Sarkin Rigima, Eho! Mata mun dai gane (Imam,1938).

Hausa in the Eyes of the World

This is the last article in the series that we started to bring to you; in this paper, PROFESSOR ALIYU MUHAMMAD BUNZA of Usman Ɗan Fodio University in Sokoto introduces a lecture on Hausa in the Eyes of the World. We hope that you are with us:-

IF we look beyond Nigeria, we will see that Hausa dominates international broadcasting around the world among African languages. Some of the world news agencies that have helped broaden the use of Hausa include:

1. BBC Radio 2. Voice of America 3. Deutsche Welle 4. Radio Beijing (China) 5. Radio Iran 6. Radio Mecca, Saudi Arabia 7. Radio Niger Republic 8. Radio Ghana 9. Radio Egypt 10. Radio Moscow.

Something like fate, as a Tuareg who fell off a camel, would say. In the languages of the world today, there’s no language that exceeds Hausa in its adoption by the international media which mainly use two languages, Hausa and Swahili. If one was to measure the reach of the two languages in the area of news transmission, by God, Kiswahili would give way, because, as (poet) Sani Ɗanbalɗo would say:

“The boy’s is not like the father’s”

As long as... The kind of popularity that Hausa enjoys over the other African languages reminds me of a song about the hyena, when Jigji (a huge Juju goat) said he would wrestle with him, to which the drummer replied:

“Hyena’s knee bones Are not for dogs to taste The important ones must be given space And it is not necessarily for God’s sake“.

However meeting up in the wrestling place proved difficult for Jigjig’s drummer who now finds him saying:

“Back back Muhammadu Back father Muhammadu Back father Muhammadu.” (No, this has nothing to do with the Swahili. It is simply a term used to demonstrate how a goat scratches the ground as it pulls back in readiness for attack on a foe.)

UNTIL THE WALL SPLITS I won’t blame any student who doesn’t know the secret of knowledge, if he refuses to take up a course of study because of its difficulty or because the lesson appears too easy. The reason is, lack of knowledge is darker than night.

I think foolishness, injustice, and lack of enthusiasm, and self-hatred, coupled with indecision and failure to recognize one’s responsibility bedeviling a Hausa student or the Hausa teacher could be the reason for showing lack of enthusiasm.

And for what reason does the Hausa student hide himself among University students? Who will reach his level much less better him? What does one read that will equal his? Which Hausa lesson is beyond his ability to learn? In truth, there isn’t one.

These are some of the temperament that is diminishing the value of the Hausa language and the efforts to teach it to others. They don’t understand Hausa language, let alone English, giving value to the adage of “an old cow giving birth, both the mother and its newborn, are flat on the ground.”,. Undoubtedly, when you see a man running away from something, it is because of his ignorance about the quality of what he is running away from, if he knows, he would stick it out until he achieves his objectives.

SETTLING AN ARGUMENT The Hausa have a saying: it is where there is no land that one disputes wrestling. The main thing that language must attain to gain global respect is when teachers and experts spend sleepless nights trying to protect its wealth and status. Basically, among African languages, none is better known than Hausa. No other language is used more in publications by scholars and experts who use it in their respective researches which tend to benefit the most people.

Among the many areas of research in Hausa, we have:

i.Language ii.Literature iii.Culture

In these categories, the Hausa language has more than thirty (30) expert teachers with the highest degree (Ph.D.) who are teaching in Nigerian universities. No other language in Nigeria or Africa has half of these experts teaching in universities today. Turning to knowledgeable professors, besides those whom God has called (God be merciful to them), Hausa has approximately twelve professors who are battling daily to maintain its high status in three areas of study, namely:

LANGUAGE 1.Professor Hambali Junju Niger Republic 2.Professor Dauda Bagari UDUS [Usman Ɗan Fodio University Sokoto] 3.Professor Bello Salim BUK [Bayero University Kano] 4.Professor Abdulhamid Maiduguri 5.Professor Ibrahim Mukoshy UDUS 6.Professor Mu’azu Sani Zariya BUK 7.Professor Abba Rufa’i BUK

LITERATURE 1.Professor Ɗalhatu Muhammad ABU [Ahmadu Bello University] 2.Professor Dandatti Abdulƙadir BUK 3.Professor Abdulƙadir Ɗangambo BUK 4.Professor U B Ahmed ABU 5.Professor Abdu Yahaya Bici BUK 6.Professor Haruna Birniwa UDUS 7.Professor Sa’idu Muhammed Gusau BUK

CULTURE 1.Professor Aliyu Muhammad Bunza UDUS

Wow! What language in Africa has more defenders like Hausa? That’s why when one says “Hausa in the eyes of the world,” there’s nothing we would say except to suggest that Gambo be asked for more details: “The confection must be sweet, Since it was made with honey in the first place.“

SUMMARY: Let me offer new students congratulations for gaining entry into the exclusive club of those who learnt the language that is the imam (leader) of African languages in every sense. Let me also assure you that “no one points at their house with the left hand,” therefore Hausa is no stranger among the languages of the world.

Certainly it is ignorance that causes the Bachelor’s Dog to chase away a beautiful divorcee. If the dog knew, he would guard her with his life.. Open your eyes and take a good look: scholars of English and of history and of psychology and of political sciences and of economics, Hausa is what they use in a fancy fashion like English, because it is the Hausa language they adopt to swindle and trick the careless and chew gravel to make peanuts fearful.

I see no fault with Goga Sarkin Rigima when he understood how women take men for granted and take advantage of them. He sent his wife off to the farm while he stayed at home to grind and sing this song:

Pay attention to the women so you know. We understand they cheat us by taking advantage of us, Pay attention to how in the morning we head out to the farms Farming is what’s made us all thin, Well, there’s a new law so you know, Everyone now must go and work on the farm I am Goga Sarkin Rigima, Eho! Womenfolk, we really understand you now (Imam,1938).

Glossary

Hausa Hausa Meaning English Meaning
Hausa ta samu miƙe ƙafafunta Harshen hausa ya haɓaka har ana aiki da shi a ƙasashe dayawa na duniya. This expression means that Hausa language is widely spoken; it is used by the media worldwide
Abu kamar ƙaddara, inji Buzu da ya sha kayen raƙumi. Wannan salon magana ne da ya nufin akwai wani abun al'ajabi game da martaba da yaɗuwar harshen hausa. In an duba manufar karin maganar kuma sai a ce Buzu( namiji na wata ƙabila makiyaya ta Afirka ta yamma wadda take kiwon raƙuma da anfani da su kuma don sufuri domin mutanen suna yawo dayawa har dai wajen hamada Sahara) gwani ne ga hawan raƙumi, idan kuma raƙumi ya bar buzu ya faɗi, akwai ban mamaki. This is a saying that means that there is something wonderful about the Hausa language because of its popularity; the reference to "Buzu," a male Tuareg (an ethnic group of nomads living around the Sahara desert known for their expertise in riding camels which they raise and use for transportation) falling off a camel is to show the wonder around that popularity
Ta yaro ba ta kamar ta babba. Wanan salon magana yana nufin tunanin babba yafi na yaro. This is a popular Hausa proverb that means the ideas of an elder are stronger than those of a young person
Wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokawa. Wannan karin magana yana nufin abun da ba'a iya jarraba shi shine abunda za'a yi ta gardama akansa. This saying means that there is no reason to continue debating about something that can simply be tested or proven
Nake tunawa.....baya baba Muhammadu` Wanna tatsuniya tana misalta banbancin ƙarfin abu biyu da kowane ɗayansu yana da nashi muhimmanci amma kuma ana ganin mafi ƙarfin ta wurin yadda ake yaba shi. Ana nuna kuma muhimmancin muhibba. This anecdote illustrates the importance of popularity; the author compares Hausa to the hero of the story
Rashin sani ya fi dare duhu. Wannan karin magana yana nuna lahanin rashin sani yayinda ake kwatamta shi da duhun dare inda ba a ganin kome, koma yana kusa, kuma kome hatsarin shi. A kan ce Jahilci ƙuƙumi ne. This saying refers to ignorance like darkness; that a person would appreciate something better when they get to see its value, is the idea in this context
A ƙarshe an yi haifuwar guzuma,ɗa kwance uwa kwance. Wannan salon magana yana nufin wani yanayi da kowa yayi rishin nasara, watau babu mai iya taimakon wani.Ma'ana kowa yasha kayi. This saying illustrates the condition where both parties lose; no one can influence or help each other
`Dole nakiya ta yi zaƙi, don da zuma aka fara yin ta` Wannan karin magana ya nufin dole abu yayi tasiri saboda asalinsa na da asali ko amfani sosai. This saying means anything that comes from a good origin or has a solid foundation is bound to be good
Tabbas rashin sani ne ya sa Karen Gwauro ya kori Bazawara. Wannan karin magana ne da yake nufin rashin sani ya kan sa a yi kuskure ko kuma a ƙi ɗaukar wani abu da daraja. This saying means that ignorance can lead to a mistake or the missing of a good opportunity
Su yi wa marasa kula wala-wala da dodorido a tauni tsakuwa a ba gyaɗa tsoro. Cikin wannan salon magana, mai magana yana nufin Hausawa suna anfani da ilimi na cikin harshen nasu suna ƙawatar da masu sauraren su, ta hanyar amfani da harshen ta wani salo ko majigi. . With this saying, the speaker refers to the use of linguistic background knowledge in a different way by Hausa people to impress their audience
In til in kwal rinin mahaukaciya. Ma'anar wannan salon magana shine, idan mutum yasan darajar wani abu, bazai gujeshi ba komin muni ko kyawon abunba. This proverb means if one has knowledge of the value of something, that person will never run away from it whether it's in a good or bad situation

Notes

Hausa Notes English Notes

Hausawa mutane ne da aka fi samu cikin ƙasashe na yankin yamma na Afirka, watau Nijeriya, arewancin ta, da Nijer a gusum maso gabas ga ƙasar. Sun zo daga 'Nubia' ( gusumcin ƙasar Masar, da arewacin Sudan) ƙarni dayawa da sun wuce. Akwai su cikin wasu ƙasashe na yankin, kamar Kamerun da Ghana da Cote d'Ivoire. Sanu- sanu sun yi hulɗa da mutanen da sun iske kuma suka zauna tare da su. Su manoma ne , da makiyaya kuma ƴan kasuwa. Sun kafa jihohin da mamayewar Fulani a ƙarnin18 ya raunana. Sun musuluntaa ƙarni na 11, amma ba su bar addininsu na gargajiya wanda yake dogara ga ruhanni. Wajen fannin tsarin gine-gine, suna aiki mai wuya da kyau amma ba a san shi sosai amma ana ganin shi ga gidajensu. Harshesu shi ma da ake kira Hausa yana cikin gungun da ake kira ` afro-asiatic` da turanci. Hausa tana da gami da larabci.

In ana son ƙarin bayyani, ana iya duba: http://wikipedia.org/wiki/hausa-people#history_and_culture

Hausawa mutane ne da aka fi samu cikin ƙasashe na yankin yamma na Afirka, watau Nijeriya, arewancin ta, da Nijer a gusum maso gabas ga ƙasar. Sun zo daga 'Nubia' ( gusumcin ƙasar Masar, da arewacin Sudan) ƙarni dayawa da sun wuce. Akwai su cikin wasu ƙasashe na yankin, kamar Kamerun da Ghana da Cote d'Ivoire. Sanu- sanu sun yi hulɗa da mutanen da sun iske kuma suka zauna tare da su. Su manoma ne , da makiyaya kuma ƴan kasuwa. Sun kafa jihohin da mamayewar Fulani a ƙarnin18 ya raunana. Sun musuluntaa ƙarni na 11, amma ba su bar addininsu na gargajiya wanda yake dogara ga ruhanni. Wajen fannin tsarin gine-gine, suna aiki mai wuya da kyau amma ba a san shi sosai amma ana ganin shi ga gidajensu. Harshesu shi ma da ake kira Hausa yana cikin gungun da ake kira ` afro-asiatic` da turanci. Hausa tana da gami da larabci.

In ana son ƙarin bayyani, ana iya duba: http://wikipedia.org/wiki/hausa-people#history_and_culture

CONTENT SOURCE: Professor Aliyu M. Bunza (2007 February 15). In the Eyes of the World. N/A: New Nigerian Newspapers Limited (Gaskiya Ta Fi Kwabo).

Objective: Demonstrate your core comprehension.

Content description: This editorial presents an expert's arguments on the role of the widely spoken African language, Hausa, in the media as well as in education.

XML



<activity>
   <problemset>
      <problem correctindex="0">
         <choices>
            <opt>
               <eng-response>The author of this editorial sends a wake-up call to students and especially teachers, who are the guardians of the values of the most solicited and spoken African language in the media worldwide, Hausa, to proudly preserve and promote it. With illustrations and figures that reflect its cultural wealth, Professor Aliyu Muhammad Bunza asserts the merit and power of the language in comparison to even Kiswahili, another largely used language, and then discusses the timid, harmful attitude of teachers or students who, by ignoring the language, do not give credit to its importance. He exhorts them to consider its wealth in the number of knowledgeable scholars and cultural knowledge that is instrumental to the exhibition of their own wisdom.</eng-response>
               <response>Marubucin wannan shafin ra'ayi yana kira ga ɗalibai,
da musamman malamai waɗanda sune masana masu kare darajar harshen mai yawan mahibba ga  ƴan jarida na duniya duka cikin harsunan Afirka,da su yi bugun gaba da harshen Hausa kuma su ɗaukaka shi. Furofesa Aliyu Muhammad Bunza yana nuna dalla-dalla yadda Hausa take da mahibba da ƙarfi kan kwatanci ga Kiswahili, shi ma wani harshen Afirka; da yanayin ɓoye-ɓoyen wasu ɗalibai da malamai game da harshen, abinda yake zama cikas saboda bai haɓaka darajarshi sai rageta. yana jawo hankalinsu ga yawan masanan da wani harshe ba shi da, kuma da sanin iya magana dake game shi wadda za ta ƙawatar da masu saurarensu.</response>
               <eng-fdbk>Correct! That is right. You observed the author's feelings about the importance of the Hausa language, its resources, and the use of supporting illustrations involving stories and sayings specific to the language and its culture.</eng-fdbk>
               <fdbk>Daidai ne! Wannan daidai, Ku gane da yadda mai rubutun yake bada ra'ayinshi bisa muhimmancin harshen Hausa, da yawan da aikin masana, da kuma anfani da labaru da karin magana waɗanda suke da gami da al'adun Hausa don ya ƙarfafa ra'ayinshi.</fdbk>
            </opt>
            <opt>
               <eng-response>The main point of this editorial is that unless teachers and students treat the widely spoken and culturally rich Hausa language with pride and respect, the world will not see its value. Professor Aliyu Muhammad Bunza denounces the reluctance of teachers and students to effectively advocate an understanding of Hausa and greater worldwide interest in the language.  The Hausa language has the privilege of being an important media vehicle worldwide, therefore it should be respected and promoted by the people who use it. The educational system is rich in resources that are not being used to help the promotion that he mentions, but he encourages general action to restore status to the language.</eng-response>
               <response>Babban manufan wannan shafin ra'ayi shine cewa in dai malamai da ɗalibai masu magana Hausa wadda take da faɗi da arzikin al'adu, ba su ɗauke ta da alfahari da ban girma ba, duniya ba za ta ganin darajar ta ba.Furofesa Aliyu Muhammad Bunza yana Allah waddai da ji nauyin malamai da ɗalibai ga tattali faɗaka  ganewar Hausa da bada marmarin saninshi ga sauran duniya. Harshen yana da gatanci na zaman a yi aiki da shi cikin yaɗa labarai cikin duniya duka, saboda haka kuma, ya cancanta a ba shi girma kuma a haɓakar da shi. Wajen fanni koyarwa, akwai albarkatu dayawa da ba a anfani da su don ci gaba ya ce, amma yana kira ga yin motsin kowa, don a maido darajar hausa.</response>
               <eng-fdbk>Incorrect! This choice is not correct because it gives the idea of a general action that is not conveyed in the text. Think about Aliyu's illustration in the “Goga Sarkin Rigima” story. What message is he conveying?</eng-fdbk>
               <fdbk>Ba dadai ba ne! Wannan ba daidai ba ne saboda ana maganar motsin kowa wanda ba a bayyana ba cikin karatun. Ku yi tunani bisa labarin Goga Sarkin Rigima. Minene mai rubutun yake nufi da labarin?</fdbk>
            </opt>
            <opt>
               <eng-response>In this editorial, Professor Aliyu Muhammad Bunza discusses the importance of the widely spoken Hausa language and the need for a general change in attitude to better present it to the world. He blames students and teachers who are, according to him, prevented from understanding its value due to ignorance and a lack of interest, and do not proudly present it to the rest of the world who need it because of its cultural impact on other languages. Aliyu sees a gift in the language that every speaker should cherish because it is not present in any other African language. He believes a global awareness of the language’s value and the motivation to make it known would enhance interest in it even more.</eng-response>
               <response>Cikin wannan shafin ra'ayi, furofesa Aliyu Muhammad Bunza yana bayyana muhimmancin harshen Hausa wanda shike mutane dayawa suna aiki da shi, kuma da cancantar canjin ra'ayi domin a fallasa  shi ga fuskar duniya. Ya zargi malamai da ɗalibai waɗanda a ganin shi, rashin sani da rashin kula sun tauye fahimtar tamanin harshen garesu balle su shaida shi da bugun gaba, ga sauran duniya da ke bukatar shi don yawan hikimar shi da ke shafar wasu harsuna. Aliyu yana ganin Hausa wata baiwa ce da ta cancanta kowane mai maganar ta ya yi tattalinta don dai ba kowa yake da ita ba. Ya yi imani da cewa fargar jama'a da tamanin sanantadda ita, da kuma aniya  za su ƙara marmarinta.</response>
               <eng-fdbk>Incorrect! This choice is incorrect because it misinterprets some ideas of the text. Please read the conclusion again. How does he present the communication of Hausa wisdom to a non-Hausa audience?</eng-fdbk>
               <fdbk>Ba dadai ba ne! Wannan zaɓe ba daidai ba ne saboda akwai canji ga yadda ake nufin wasu bayyanai cikin karatun. Ku karanta ƙarshen shafin. Yaya mai rubutun yake nuna yadda masanan Hausa suke aika hikimarsu ga mutanen da ba su maganar Hausa?</fdbk>
            </opt>
         </choices>
      </problem>
   </problemset>
   <instr type="eng">INSTRUCTIONS:
Choose the best summary.</instr>
   <instr type="target">Umurni:Zaɓi taƙaitawa mafi dacewa.</instr>
   <finishtl>Minene cikin wannan shafin ra'ayin yake iya sa mutun yayi marmarin koyon harshen Hausa a ra'ayin ku?</finishtl>
   <finish>What in this editorial would make a person want to learn Hausa Language, in your opinion?</finish>
   <finishtl>A ganinku, donmi mai rubutun ya yi anfani da karin magana cikin misalan shi?</finishtl>
   <finish>Why do you think the author used proverbs in his illustrations?</finish>
   <finishtl>Donmi Aliyu yake ambata sanin abin da harshen Hausa ya ƙunsa da yake iya zama abin anfani ga jama'ar da ba ta maganar ta?</finishtl>
   <finish>Why do you think Aliyu mentioned the knowledge of the cultural impact of the Hausa language even on people who don't necessarily speak it?</finish>
</activity>