bbchausa/Yobe at TeenEagle English competition
More actions
https://www.bbc.com/hausa/articles/cdd3eypzlr0o [1]
Bayanan hoto, Ɗalibai daga jihar Yobe Nafisa Abdullahi da Rukayya Muhammad 15 da kuma Hadiza Kashim
Wasu ɗalibai mata uku daga jihar Yobe da ke Najeriya na ci gaba da shan yabo sanadiyyar rawar da suka taka a wata gasar duniya da aka gudanar a ƙasar Birtaniya.
Nafisa Abdullahi ƴar shekara 17, da Rukayya Muhammad mai shekara 15 da kuma Hadiza Kashim mai shekara 16 sun ciri tutu a zagaye na ƙarshe na gasar TeenEagle da aka gudanar a birnin London.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na facebook, kwalejin Nigerian Tulip International Colleges Yobe, ta ce:
"Gasar TeenEagle da ta samu halartar sama da ɗalibai 900 daga ƙasashen duniya 46 - wadda aka fara ta intanet har zuwa zagaye na ƙarshe da aka yi a tsakanin 27 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agusta a Jami'ar Surrey da ke Birtaniya - ɗalibanmu sun sa mu alfahari."
Sanarwar[2] ta ƙara da cewa ɗaliba Nafisa Abdullahi Aminu daga Yobe ta yi zarra a matakin gasar TeenEagle 3, Rukayya Mohammed Fema, ita ma daga Yobe ta yi zarra a ɓangaren muhawara, sai kuma Hadiza Kashim Kalli wadda ta samu kyautar mai basira ta musamman.
Baya ga ɗaliban makarantar da suka fito daga jihar Yobe, akwai kuma wasu ɗaliban da suka yi zarra waɗanda suka fito daga Abuja.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Yobe ta fitar ta hannun mai taimaka wa gwamnan jihar Mai Mala Buni kan yaɗa labarai, Mamman Mohammed, ta ce za ta karrama ɗaliban uku bisa ƙwazon da suka nuna.
Sanarwar ta ce "gwamna Mai Mala Buni ya amince da gudanar da ƙasaitacciyar walimar karrama Nafisa Abdullahi da Rukayya Muhammad da kuma Hadiza Kashim" saboda zarrar da suka yi a gasar TeenEagle ta duniya ta 2025 a Birtaniya.
Dukkanin ɗaliban "na ƙarƙashin shirin tallafin ilimi na gwamna Mala Buni, inda ake ɗaukar dukkanin ɗalibai 890 a kwalejin Nigeria Tulip International College".
Manyan mutane a faɗin Najeriya, kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ministan harkokin waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, da tsohon ministan sadarwa Ali Pantami sun taya ɗaliban murna.
TeenEagle gasa ce da ake gudanarwa ta harshen Ingilishi wadda ke karɓar masu neman shiga daga dukkanin ƙasashen duniya.
Manufar gasar ita ce "haɓɓaka haɗin gwiwa da hulɗa da al'adu mabanbanta da kuma ƙirƙira," kamar yadda bayanin yake ƙunshe a shafin intanet na gasar.
Shafin ya ce gasar takan "shirya ɗalibai ta hanyar ba su ƙwarewa kan yadda za su tunkari ƙalubale na rayuwa a fadin duniya."