Toggle menu
24.9K
757
183
164.8K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/022 mid career break

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: The surprising benefits of a mid-career break [1] <> Ka san amfanin ajiye aiki? [2]

#: Once considered career suicide, sabbaticals are now not only accepted[3] <> Abinda a baya ake dauka tamkar wani gagarumin ganganci, ajiye aiki na tsawon lokaci, a hankali na samun karbuwa [4]

#: but encouragedby some employers. Heres how to take one and still get ahead. [5] <> har ma wadansu maaikatun su na goyon bayan yin hakan. Ga matakan da ya kamata ka bi wurin samun nasarar hutun aiki. [6]

#: When Winston Chen told his friends that he had quit his job [7] <> Lokacin da Winston Chen ya shaidawa abokansa cewa ya ajiye aikinsa [8]

#: His job as chief technology officer at a software company [9] <> Aikinsa na babban jamiin fasaha a wani kamfanin shirya manhajar kwamfuta [10]

#: to move to a small island in Arctic Norway with his family for a year, [11] <> domin komawa wani karamin tsibiri a cikin hamadar kankarar Norway tsawon shekara guda tare da iyalinsa, [12]

#: few people called him crazy. [13] <> kadan daga cikinsu ne su ka ce bai yi daidai ba. [14]

#: Instead, most people simply replied: [15] <> Maimakon haka, yawancin abokansa kan [16]

#: I wish I had the guts to do that.” [17] <> ce: “Ina ma ni ma zan iya.” [18]

#: While many people dream of taking time off mid-career, few actually do it. [19] <> Yayinda mutane da yawa ke burin ajiye aiki kafin lokacin ritaya, kadan ne ke iya gwadawa. [20]

#: But the number of people taking lengthy sabbaticals later in life is increasing, according to experts. [21] <> Amma adadin masu daukar dogon hutun aiki bayan sun girma da ci gaba da karuwa, a cewar kwararru a harkar. [22]

#: Thats in part due to companies becoming more open to the idea and the higher rate at which people are changing jobs. [23] <> A bangare daya, ana samun kamfanoni da dama da ke amincewa maaikatansu su ajiye aiki da niyyar komowa bayan wani dogon lokaci, a daya bangaren kuma mutane su na yawan sauya aiki fiye da shekarun baya. [24]

#: And depending on how you play your cards, you can return with a better job than when you left. [25] <> Kuma, bisa laakari da abinda ka yi da hutun na ka, ka na iya samun aikin da yafi wanda ka bari tun san da ka tashi komawa. [26]

#: Time for a change [27] <> Lokacin sauyi [28]

#: For Chen, who had been with the same company for a decade when he quit in 2011, [29] <> A tsarin Chen, wanda ya kwashe shekaru goma ya na aiki a kamfani guda kafin aje aikin a 2011, [30]

#: it was time for a change, he said. [31] <> gani ya yi lokaci ya yi da zai samu sauyi a rayuwarsa. [32]

#: His original plan was to find a new job, [33] <> Niyyarsa ita ce ya nemi aiki a wani kamfanin dabam, [34]

#: but the idea of taking time offinspired by a TED talk[35] <> amma bayan da ya saurari wani jawabi karkashin tsarin TED [36]

#: got him seriously thinking about a sabbatical. [37] <> sai ya fara nazari sosai akan daukar dogon hutu. [38]

#: At first, he said he was concerned that time away from the industry might hurt his career. [39] <> Sai dai da fari ya yi fargabar cewa idan ya dau tsawon lokaci baya aiki, zai iya samun cikas duk san da ya dawo neman wani sabon aikin. [40]

#: That's the main reason that keeps people from doing this, and I was no different,” he said in an email. [41] <> Ya ce: “Wannan ne babban dalilin da ke hana mutane ajiye aikinsu, ni ma haka lamarin ya kasance gare ni. [42]

#: But you have to create the urgency for living the life you want.” [43] <> Amma sai ka kalli muhimmincin gudanar da rayuwa irin yadda ka ke so.” [44]

#: After quitting, Chen did look for another job[45] <> Bayan ajiye aikin, Chen ya fara neman wani aikin na dabam[46]

#: until a family friend mentioned that a small island in Arctic Norway was looking for a teacher. [47] <> har sai da wani abokin huldarsa ya shaida masa cewa ana neman malamin makaranta a wani karamin tsibiri da ke yankin hamadar kankara a Norway. [48]

#: Chens wife, who was born in Norway, [49] <> Matar Chen, wacce aka haife ta a Norway [50]

#: wanted to go back to work after being at home with their kids for five years. [51] <> kuma na shaawar komawa bakin aiki bayan da ta ajiye domin rainonyayanta tsawon shekaru biyar. [52]

#: She called and basically got the job,” said Chen. “So, very quickly, we decided that was it.” [53] <> “Ta kira makarantar ta waya su ka dauke ta aikin,” in ji Chen. “Don haka nan da nan mu ka yanke cewa abinda zamu yi ke nan.” [54]

#: Increasingly popular [55] <> Karin karbuwa [56]

#: Paul Payne, managing director of UK-based rail [57] <> Paul Payne, manajan darakta na wani kamfanin daukan maaikatan sufurin jirgin kasa [58]

#: and construction recruitment firm OneWay, [59] <> da harkar gine-gine da ke Birtaniya, mai suna OneWay [60]

#: is one of a growing number of professionals in the recruiting field [61] <> na daya daga cikin kwararru kan daukar maaikata [62]

#: who have seen a number of clients opting for a gap year or sabbatical midway through their careers. [63] <> wanda ya lura cewa abokan huldarsa da dama kan dauki hutun shekara guda su na tsaka da aiki. [64]

#: Its an interesting idea, [65] <> Ya ce: “Wannan lamari abin lura ne, [66]

#: particularly when firms are looking to hire and, crucially, retain millennial talent [67] <> musamman a wannan lokaci da kamfanoni ke bukatar rike maaikatan da su ka horar, [68]

#: who tend to get itchy feet quicker than their predecessors,” he said in an email. [69] <> yayinda su kuma maaikatan ba sa son zama wuri daya. [70]

#: While its not for every business, [71] <> Duk da dai ba za a ce tsarin ya dace da kowacce irin sanaa ba [72]

#: more and more are offering sabbaticals [73] <> amma dai kamfanoni da dama na bai wa maaikatansu damar daukar dogon hutu [74]

#: as a retention tool by giving their employees paid leave to travel, volunteer or simply to take time off to recharge their batteries.” [75] <> tare da ci gaba da biyansu albashi don su wataya su sake dawowa bakin aiki cike da karsashi.” [76]

#: Slacker label? [77] <> Tambarin lalaci [78]

#: Explaining a year off on your CV doesnt have to be a bad thing, said Payne. [79] <> Daukar shekara guda ba ka aikin komai ba dalili ba ne da zai sa a yi maka tambarin lalaci, in ji Payne. [80]

#: Taking the time off can highlight to an organisation that you want to further your skill set and try new experiences,” he said. [81] <> “Ajiye aiki alama ce da ke nun aka na son koyon sababbin abubuwa.” Ya kuma kara da cewa: [82]

#: It could also mean that youll come back from your break with a different perspective, [83] <> “Hakan kuma zai iya sa ka dawo bakin aikinka da sabon tunani, [84]

#: which is likely to aid your job performance.” [85] <> wanda zai iya taimaka wa wurin kara inganta aikinka.” [86]

#: Of the 500 people interviewed for Reboot Your Life[87] <> Daga cikin mutane 500 da aka tattauna da su domin rubuta littafinReboot Your Life[88]

#: a 2011 book which offers practical advice on career breaks[89] <> wanda aka wallafa a 2011 domin ba da shawara game da daukar dogon hutun aiki, [90]

#: not one person regretted the decision to take a break [91] <> babu ko daya da ya yi nadamar daukar hutun [92]

#: (which lasted anywhere from one month to two years), [93] <> (mai tsawon wata guda zuwa shekaru biyu), [94]

#: according to Jaye Smith, co-founding partner of New York-based career consultancy Reboot Partners, LLC, and co-author of the book. [95] <> a cewar Jaye Smith, daya daga cikin marubutan littafin, kuma daya daga cikin wadanda su ka kafa kamfanin Reboot Partners a New York, mai ba maaikata shawara kan yadda za su ribaci rayuwar aiki. [96]

#: Everyone reported that their careers were enhanced as they were enhanced in their attitudes and work ethic,” she said in an email. [97] <> Ta ce: “Duk kansu sun ce sun ga ci gaba a rayuwarsu sanadiyyar dogon hutun da su ka dauka daga aiki.” [98]

#: Try something new [99] <> Jarraba sabon abu [100]

#: If youre thinking of taking a mid-career break that boosts your outlook and skills, [101] <> Idan ki na tunanin ajiye aikinki domin fadada tunaninki da samun karin kwarewa, [102]

#: consider going abroad, [103] <> kamata ya yi ki tafi wata kasar dabam, [104]

#: where you could try undertaking informal paid work or volunteering, either of [105] <> inda za ki yi aikin sa kai ko karamar sanaa, [106]

#: which could give you a fresh perspective on things upon your return, according to Payne. [107] <> wadanda za su kara mi ki kaifin tunani idan kin koma bakin aikinki na baya, a cewar Payne. [108]

#: The experience could also improve your basic competencies. [109] <> Wannan aikin kuma zai iya kara miki kwarewa akan aikin da ki ka bari. [110]

#: Who knows what you could learn from working alongside professionals whove been developed [111] <> Ya ce: “Wa ya san iya abinda za ki iya koyo idan ki ka yi aiki tare da wasu kwararrun, [112]

#: and trained in a different way to you,” he said. [113] <> da su ka samu horo a wani yanayi da ya bambanta da irin wanda ki ka taso a ciki?” [114]

#: In more general terms, taking this sort of break [115] <> Ya kara da cewa: “Irin wannan dogon hutun [116]

#: allows you to develop life experience, which can contribute to building bettersoftskills like communication and people management.” Plus, volunteer work can give your more insight into how to solve problems differently. [117] <> na iya bunkasa kwarewarki ta hulda da jamaa da dabarun warware matsaloli, [118]

#: By nature, volunteers have to buy in to what they are doing and work with limited or no resources. [119] <> duba da yadda masu aikin sa kai ke fama da karancin kayan aiki.” [120]

#: Always a risk [121] <> Akwai hatsari [122]

#: Of course, not all employers will be open to the idea of a gap year[123] <> Sai dai, ba kowacce maaikata ce za ta amince maaikatanta su dauki hutun shekara guda ba[124]

#: but there are ways to make it more appealing to them, [125] <> amma akwai hanyoyin da za ki iya nuna musu muhimmancin hakan, [126]

#: according to Holly Bull, president of Princeton, New Jersey-based gap year consultancy Center for Interim Programs, LLC. [127] <> a cewar Holly Bull, shugabar wani kamfani bai wa maaikata shawara game da daukar dogon hutu, da ke New Jersey a Amurka. [128]

#: Lay out what [[[you]] have] in mind to an employer [129] <> “Ki bayyana wa maaikatar kudirinki [130]

#: and see how much time away they might agree to [131] <> da kuma ribar da ki ke ganin za su iya samu [132]

#: if there is a clear commitment to return to the job,” she said in an email. “Enrol the employer by outlining the benefits of taking this kind of time; most people are reinvigorated by gap time and return with more to offer in their jobs.” [133] <> sakamakon wannan hutun, mai yiwuwa su amince idan su ka tabbatar bayan hutun za ki koma aiki da su.” [134]

#: Bull recommends being very clear about what is most important, [135] <> Bull na ganin ke ce ya kamata ki san abinda ya fi muhimmanci a rayuwa: [136]

#: and only then going to your employer with your intent and requests. “See what happens,” she said. [137] <> N/A [138]

#: I think one has to be ready to let a job go if an employer is not at all open to the gap option.” [139] <> “Idan ba su yadda ba sai ki ajiye mu su aikin dungurungum.” [140]

#: But dont be surprised if there is pushback about the idea. “Many employers are not so keen to see someone take off for a year because of the need for business continuity and consistency,” said Reboot PartnersSmith. Have a plan showing how they could cover you in your absence. One of Smiths clients pointed out to their manager how much money they could save in the budget for that year by not having to pay their salary, yet not sacrificing the investment they had made in training them over the years. “It was a win-win for the company and the employee taking the break,” said Smith. [141] <> N/A [142]

#: Time to move on [143] <> Lokacin tafiya ya yi [144]

#: The year off may prove the stepping stone to your next job. [145] <> Daukar hutun shekara guda na iya zama hanyar samun aikinki na gaba. [146]

#: I think it's really important people ask the question [147] <> “Ina ga ya kamata mutane su tambayi kansu [148]

#: about whether their work is fulfilling. [149] <> idan sun gamsu da aikin da su ke yi. [150]

#: If it's not, it may be scary to make a change, [151] <> Idan ba su gamsu ba, mutane da yawa kan ji tsoron sauyawa, [152]

#: but it's invariably better to risk it to find something that really does light them up,” said Bull. [153] <> amma dai na tabbatar gara ki nemi aikin da ki ke so da ki makale a inda ba kya jin dadi,” in ji Bull. [154]

#: Gap options provide landing pads and a way to test the waters without making a full commitment to another job.” [155] <> Ta kuma bayyana cewaDaukar dogon hutu wata dama ce da za ki jarraba sabon aikin da ki ke shaawa, idan bai yi miki ba sai ki koma wanda ki ka ajiye.” [156]

#: For some people, [157] <> Wasu mutanen [158]

#: it can be as short as a few weeks to learn if something suits them or not. [159] <> kan gane ko aiki ya yi mu su ko bai yi mu su ba cikinyan makonni kadan, [160]

#: For Bull, it took a month of aquaculture research [161] <> amma ita Bull sai da ta yi wata guda cur ta na aikin binciken ciyayen cikin ruwa, [162]

#: to realise that she didn't have the patience for that kind of methodical work. [163] <> kafin tabbatar da cewa ba ta da juriyar da za ta iya mai da shi sanaarta. [164]

#: Unexpected results [165] <> A kan tsinci dami a kala [166]

#: In Chens case, he developed an app [167] <> Shi kuwa Chen, a lokacin hutun ne ya kirkiro wata manhajar wayar salula [168]

#: justfor funduring his time away. [169] <> domin debe wa kansa kewa. [170]

#: But it became his new careerand the precursor to voice-based mobile app company, [171] <> Wannan manhaja ita ce ta zamo tushen kafa sabon kamfaninsa, [172]

#: Voice Dreamwhen he returned to Boston a year later. [173] <> Voice Dream lokacin da ya koma Boston bayan shekara guda. [174]

#: It's not necessary to think of being away as a way to start a business or go to a new career,” he said. [175] <> Ya ce: “Ba dole ne ka dauki hutu da niyyar kafa sabon kamfani ko sauya sanaa ba. [176]

#: The point is: [177] <> Abin lura shi ne: [178]

#: What would you do if, for a while, you don't have to think about making money?” [179] <> Idan aka dauke maka bukatar kudi ta dan wani lokaci, me za ka yi domin jin dadin rayuwarka?” [180]

Contents