Toggle menu
24.9K
757
183
164.8K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/030 chilli peppers

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Can you hurt yourself eating chilli peppers? [1] <> Cin barkono yana da amfani ko illa? [2]

#: Many of us love the burning sensation from hot chillies. [3] <> Da yawa daga cikinmu muna da sha'awar cin yaji ko barkono a abincinmu duk da tsananin zafinsa, kamar na wuta. [4]

#: But are they doing us any harm? BBC Future investigates. [5] <> To amma cinsa yana da wani amfani ko illa ga lafiyarmu? [6]

#: The delicious burn of a really good curry or salsa or Sichuanese hot pot[7] <> Yadda za ka ga wasu mutane suna cin abinci ko wani kayan kwalan da makulashe mai yaji [8]

#: that fiery goodness that makes you sweat and flush[9] <> har ka ga suna face hanci da kwankwadar ruwa kuma ido na hawaye saboda zafin yajin, [10]

#: is for many people one of lifes great pleasures. The search for the most profound scorch is a hobby of sorts, perhaps even an obsession. [11] <> wani abin sha'awa ne ga wasu mutanen. [12]

#: Its all fun and games. Right? Well, until someone gets hurt. [13] <> To amma shin duk da irin yadda irin wadannan mutanen suke fama da yajin a lokacin da suke cin abincin, a iya cewa ba ya musu illa? [14]

#: And while everyday amounts of spicy food are unlikely to do any harm, [15] <> Duk da cewa cin abinci mai yaji a kullum da wasu ke yi ba lalle ya yi musu illa ba, [16]

#: thrill-seekers have had some disconcerting experiences. [17] <> wasu da suka nemi dandana hakan ba su ji da dadi ba. [18]

#: In 2014, two journalists from The Argus, a newspaper in the British city of Brighton, [19] <> A shekara ta 2014 wasu 'yan jarida biyu daga wata jarida ta birnin Brighton na Birtaniya, mai suna Argus, [20]

#: went to test out burgers at a local restaurant rated highly on TripAdvisor. [21] <> sun je wani gidan abinci na kwalan da makulashe wanda ya yi fice wajen iya abinci da borkono, domin shedar da kwarewar. [22]

#: They each took a bite of the XXX Hot Chilli Burger, a specialty of the house made with hot sauce touted by the owner to score higher on the Scoville scale than pepper spray. [23] <> Kowanne daga cikin mutanen biyu ya zabi ya ci wani kayan kwalan da makulashe da ke da yaji domin ya sanin wanda ya fi dadi. [24]

#: The pain was unendurable[25] <> Zafin wani barkonon yana sa wa mutum yanayi kamar na ciwon zuciya [26]

#: one reporter immediately swallowed a great deal of milk to try to stave it off, the newspaper reported. [27] <> Daya daga cikin mutanen ya kasa jure zafin yajin, inda nan da nan ya nemi madara ya rinka sha domin ya daina jin zafin yajin, kamar yadda jaridar ta ruwaito. [28]

#: The other began to have severe stomach pains, [29] <> Shi kuwa dayan cin abin ke da wuya sai kawai ya gamu da ciwon ciki mai tsanani, [30]

#: lost the feeling in his hands, [31] <> sannan ya ji kamar hannunsa ba ya aiki, [32]

#: and began to shake and hyperventilate. [33] <> ya fara karkarwa, kuma numfashinsa ya fara daukewa. [34]

#: His colleague was also seized with pain despite his efforts, and [35] <> Dukkanin mutanen dai sun rika jin zafi da ciwo [36]

#: both had to go to the hospital. “I was in so much pain,” one said, “I felt like I was dying.” [37] <> abin da ya sa har suka dangana da asibiti domin a yi musu magani, domin dayansu ma cewa ya yi ji ya yi kamar zai mutu. [38]

#: Daring pepper eaters [39] <> Wasu mutanen da suka yi gasar cin wasu nau'ukan barkonon [40]

#: who consume some of the worlds hottest specimens on camera [41] <> da suka fi zafi a duniya, a Denmark, [42]

#: have found themselves vomiting for an audience. [43] <> sun rika yin amai a gaban jama'a, bayan zufa da shakuwa da suka rika yi. [44]

#: Matt Grosss account of hot debauchery for Bon Appetit, on the other hand, starts with the cold, hard numbers. “It took me 21.85 seconds to consume three Carolina Reapers, the worlds hottest chillies. And it took me approximately 14 hours to recover from the aftermath,” he says. (Spoiler: The aftermath involved the symptoms of a heart attack.) [45] <> Shi kuwa Matt Gross a bayanin da ya bayar a kan zafin barkono, inda ya ci barkonon da ya fi zafi a duniya ( Carolina Reapers), ya ce sai da ya kai sa'a 14 kafin ya dawo hayyacinsa bayan da ya ci barkonon guda uku a cikin dakika 21.85. [46]

#: The physical effects of eating peppers [47] <> Tasirin cin barkonon [48]

#: can be seen as reactions to what might befrom the bodys perspectivereal burns [49] <> ya hada da alamun ciwon zuciya, wanda daga baya aka ga hakan. [50]

#: So what is going on here? [51] <> To wai me yake sa mutum ya ji wannan zafi ne idan ya ci barkono? [52]

#: If all hot peppers are doing is fooling your body into thinking theres a small fire in your mouth, [53] <> Idan har cin barkono zai sa mutum ya ji kamar wuta ce a bakinsa, [54]

#: why can they provoke such a serious reaction? [55] <> me yake jawo hakan? [56]

#: Lets come back to the basic biology of capsaicin. [57] <> Idan aka koma kan nazarin yadda sinadarai ke haduwa su haifar da wani abu daban, musamman kwayar halittar wani sinadari (capsaicin) da ke aika wa kwakwalwa sakon zafi kamar na wuta. [58]

#: This molecule may have evolved as an anti-fungal agent for the plants that bore it. [59] <> Masana na ganin wannan kwayar halitta ta samu ne domin zama mai gadi ko bayar da kariya daga kwayoyin cuta (fungi) ga tsirran da suke samar da ita. [60]

#: But, to humansjoy and fascination and fear, it happens to activate certain neurons responsible for the perception of pain. [61] <> To amma kuma abin mamaki ga dan adam a jikinsa wannan kwayar halitta tana zaburad da jijiyoyin halittarsa ne [62]

#: Those particular neurons send a message of heat to the brain, whether the cells are activated by an actual burn or by a hot pepper. [63] <> masu aika sakon zafi na wuta ko makamancin na wutar kamar na barkono zuwa kwakwalwa. [64]

#: Its not their business to distinguish between these noxious optionsas far as the body is concerned, its better safe than sorry. [65] <> Su dai wadannan kwayoyin halitta ba ruwansu da cewa wai zafin na wuta ne ko na barkono, illa dai kawai su sanar da kwakwalwa kawai. [66]

#: But, hours or a day or so of very serious discomfort aside, there dont seem to be long-term dangers, per se, in eating very hot peppers. [67] <> Dangane da haka, shi dai cin barkono ko yaji, in ban da zafi ko rudewar jiki ko ciki ta dan wani lokaci kama daga sa'o'i ko kwana daya ko makamancin haka, ba shi da wata illa ta wani lokaci mai tsawo. [68]

Contents