Toggle menu
24.9K
762
183
165K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/037 electric car etiquette

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: Electric car charging etiquette: The dos and don'ts of fuelling your petrol-saving vehicle [1] <> Hanyar caza sabuwar mota mai aiki da lantarki [2]

#: These cities, along with college and corporate campuses, [3] <> Akwai birane da kwalejoji da jami'o'i, [4]

#: were demonstrating their commitment to preserving the environment, [5] <> da suka jajirce wajen inganta muhalli [6]

#: offering free power [7] <> kuma suna bayar da makamashi kyauta [8]

#: and prime parking [9] <> da wajen ajiye ababen hawa [10]

#: to those citizens who were willing to spend a lot of extra money for a low-range, underpowered, unsexy vehicle. [11] <> ga 'yan ƙasa da suka shirya sayen abin hawan maras ƙayatarwa kuma ba ya buƙatar makamashi da yawa. [12]

#: Those charger-augmented spots were often empty, [13] <> Mafi yawan lokuta irin waɗannan wuraren cajin abin hawa sai ka gan su fayau, [14]

#: simply because there werent enough PEVs on the road to fill them. [15] <> babu motoci masu aiki da lantarki (PEVs) da ke hawa hanya, ballantana su je su cika wuri. [16]

#: Today, theres likely to be a flock of passive-aggressive drivers circling for a spot. [17] <> A yau, akwai yiwuwar samun ɗumbin direbobin da ke ta kewaye-kewaye don neman wurin tsayawa. [18]

#: And the problem isnt just that PEVs are more popular because they have longer ranges, ludicrous power, and (in some executions) some serious sexiness. [19] <> Kuma matsalar ba wai ta ababen hawa masu aiki da lantarki da suka yi yawa ba ce. [20]

#: Plan ahead. [21] <> Da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe. [22]

#: If your battery icon is flashing red, [23] <> Idan baturinka ya fara nuna alamar ja, [24]

#: an occupied spot is apt to turn you the same colour. [25] <> wurin da ke cunkushe (da ababen hawa) zai iya janyo maka irin wannan launi. [26]

#: With ranges of more than 300 miles on new vehicles, [27] <> Tun da ana samun sabbin motoci masu cin mil 300, [28]

#: running low on electrons is no longer an issue of technological limits; [29] <> bai kamata ma a bari cajin batur ya yi ƙasa ba. Bisa la'akari da bunƙasar fasahar ƙereere; [30]

#: its one of personal responsibility. [31] <> nauyi ne na ƙashin kai da ya kamata mutum ya ɗauka wajen shawo kan matsalar. [32]

#: Forget that last 20 percent. [33] <> Mantawa da caji ya ragu zuwa kashi 20 cikin 100. [34]

#: EV batteries [35] <> Nau'o'in baturan EV [36]

#: charge quickly when theyre low, [37] <> suna da saurin caji da zarar sun yi ƙasa; [38]

#: slowing down as they pass the halfway point. [39] <> suna saurin zuƙewa da zarar ƙarfinsu ya ragu ƙasa da rabi. [40]

#: Beyond 80 percent, the charging slows to a trickle. [41] <> Ƙasa da kashi 80 cikin 100 (na caji) na zurarewa a hankali. [42]

#: So while it may feel good to pump an additional 50 miles worth of electrons into your range, [43] <> Da yake, za ka iya yin tafiyar mil 50 cikin nishaɗi da caji, [44]

#: the time you spend topping off is obnoxiously inefficient. [45] <> lokacin da za ka shafe wajen ƙara caji na da cin rai. [46]

#: Dont hog the free-parking rewards for your virtuousness when there are other deserving drivers in need of electrons. [47] <> Kada ka mamaye wurin ajiye mota na kyauta, ka kyautata musammam saboda direbobin da suka fi ka buƙatar caji. [48]

#: Dont personalise it. [49] <> Kada ka kankane. [50]

#: Yes, youve parked there since you bought your Bolt, [51] <> E, ka saba ajiye mota a nan tun lokacin da ka sayi motar Bolt. [52]

#: but now Tricia from accounting needs the plug occasionally. [53] <> Ga Tricia daga sashen lissafin kuɗi za ta buƙaci abin cajin daga lokaci zuwa lokaci. [54]

#: Rather than mourn the loss of your private parking spot, [55] <> Maimakon takaicin rasa wurin ajiye motarka da ka mamaye, [56]

#: rejoice in the discovery of a new friend[57] <> za ka yi farin cikin samun sabon aboki [58]

#: one that you know will text you as soon as shes charged [59] <> da za ta aike maka da saƙon waya cewa, ta gama caji [60]

#: (and vice versa, we hope). [61] <> (kamar yadda muke sa ran ku riƙa yi). [62]

#: If youre not plugged, dont park. [63] <> Idan ba caji za ka yi ba, kada ka ajiye (motarka). [64]

#: Though this should go without saying, [65] <> Ba ma sai an faɗa ba, [66]

#: that prime parking is for powering up only. [67] <> jigon ajiye abin hawa dai caji ne kawai. [68]

#: Merely parking there doesnt help the planet, [69] <> Ajiye abin hawa haka kawai ba zai taimaki ƙasa ba, [70]

#: though it may help the citys power bill. [71] <> ko da yake, yana iya taimaka wa birni wajen ƙara samun kuɗin shiga. [72]

#: Use an app. [73] <> Yi amfani da kwamfuta. [74]

#: There are a variety of apps that list charging stations [75] <> Akwai ɗumbin kwamfuta da ke fito da jerin wuraren caji [76]

#: (free and otherwise), [77] <> (na kyauta da akasinsu), [78]

#: which can take some stress out of finding a refuel[79] <> waɗanda ba sai an sha wata wahala ba, wajen ƙara mai[80]

#: and there are all sorts of hidden charging stations in a typical city grid. [81] <> sannan akwai ɓoyayyun tashoshin caji a cikin birni. [82]

#: For-profit networks of charging stations have apps that that not only point you to stations, [83] <> Tashoshin cajin da ake biyan kuɗi, akwai kwamfuta dab da wurin, [84]

#: but tell you if a spot is occupied, [85] <> har ma za su sanar da kai cewa ana amfani da wurin, [86]

#: and even send you alerts when your car is charged. [87] <> kuma suna iya aike maka da saƙon cewa cajin motarka ya cika taf. [88]

#: Charge up in down times. [89] <> Yi caji yanzu, saboda lokacin da ba ka da damar yi. [90]

#: Dont expect to find a spot at your local strip mall during prime shopping hours. [91] <> Ba ka tsammanin samun wurin caji a katafaren shagon unguwa lokacin da hada-hadar ciniki ta kankama. [92]

#: Rather, think about pulling in during the less busy evening, while youre dining or taking in a movie. [93] <> Maimakon haka, yi tunanin zuwa wurin lokacin da babu cikowa, da maryace, kamar lokacin da kake cin abincin dare ko kallon fim. [94]

#: Look to the future. [95] <> Yi hangen gaba. [96]

#: Realise that the technology and the social environment are changing, [97] <> Fahimci cewa fasahar ƙereere da yanayin zamantakewa na sauyawa, [98]

#: and that more PEVs will mean more charging spots[99] <> kuma ƙaruwar motoci masu amfani da cajin lantarki (PEVs) na nuni da samar da ƙarin wuraren caji, [100]

#: but they are unlikely to be free, [101] <> amma ba lallai ne su zama kyauta ba, [102]

#: and less likely to be in prime locations. [103] <> sannan da wuya a same su a wuraren da ake yawan hada-hada. [104]

#: Plan now for the coming eco-utopia, perhaps by buying comfortable shoes. [105] <> Yi hanƙoron inganta muhalli, ta yiwu ta hanyar sayen takalmi mai daɗin sha'ani. [106]

#: Shoulder the burden yourself. [107] <> Ɗauki nauyin da ya rataya da kanka. [108]

#: If you bought an EV for purely economic reasons, this doesnt apply to you. [109] <> Idan ka sayi mota mai aiki da lantarki don tattalin abin hannunka. [110]

#: But for those of you that have some interest in conservation, [111] <> Amma waɗanda ke ra'ayin kyautata muhalli, [112]

#: you can do your part by charging up overnight in your garage. [113] <> ka iya yin caji a gareji. [114]

#: Youll be doing the planet a double favor if you attach your home charging station to a home solar array. [115] <> Kana ƙara kyautata muhalli idan ka haɗa wurin cajinka da wurin zuƙar makamashin rana. [116]

#: Buy a new car. [117] <> Sayi sabuwar mota. [118]

#: When autonomous vehicles arrive, [119] <> Lokacin da ababen hawa masu sarrafa kansu za su shigo. [120]

#: theyll likely be able to drop you at the front door of your destination, [121] <> Ta yiwu masu sauke ka a bakin ƙofar inda za ka ne, [122]

#: then drive themselves to some out-of-the-way spot to charge[123] <> sannan su tuƙa kansu zuwa wani gefen hanya don yin caji, [124]

#: probably through induction plates in the cement, [125] <> ko ma ta hanyar amfani da faya-fayan caji da ake kafe su a suminti, [126]

#: with no human assistance. [127] <> ba tare da taimakon wani mutum ba. [128]

#: Once that happens, you wont care about whether or not Tricia is going to text you soon[129] <> Da zarar haka ta auku, ba za ka damu da cewa Tricia za ta aike maka da saƙon waya ba, [130]

#: unless shes meeting you for coffee. [131] <> sai dai in kun haɗu a wajen shan shayi. [132]

Contents