Toggle menu
24.9K
762
183
165K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/039 proverbs reflect who we are

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

#: We need proverbs because they reflect who we are [1] <> Ko ka san asalin karin magana? [2]

#: Proverbs. Theyre old-fashioned, folksy, pithyand everywhere. [3] <> Karin Magana, kalmomi ne 'yan kilalan amma masu kunshe da zunzurutun ma'ana. Ana amfani da su kuma a tsakanin kowace al'ummar duniya. [4]

#: there seems to be a proverb for everything. [5] <> Kusan za a iya cewa babu wani abin da babu karin magana a kansa. [6]

#: Proverbs have many names: they can be called axioms, old saws, sayings and adages. [7] <> Karin Magana na da suna iri daban-daban da suka hada da Salon Magana da dai sauransu. [8]

#: Defining a proverb isnt easy, [9] <> Saboda haka fassara ma'anar karin magana ba abu ne mai sauki ba. [10]

#: Generally, its an older saying without a known author thats considered wise. [11] <> To amma wasu na fassara ta da maganganun zamani na da, da ba a iya tantance mutumin da ya kago su ba. [12]

#: If your sibling lost a job [13] <> Idan aka kwace aiki daga hannun dan uwanka [14]

#: to a friend of the boss, [15] <> aka damka shi a hannun abokin shugaban wurin aikin, [16]

#: you might say, [17] <> ana iya jefa karin maganar da zai dace da wannan yanayi. Misali [18]

#: Its not what you know, its who you know.” [19] <> "Mai uwa a gindin murhu, ba ya cin tuwonsa gaya." [20]

#: If your son loses a football match, you say, [21] <> Idan kuma misali danka na cikinka bai yi nasara ba a wasan kwallon kafa, za ka iya cewa [22]

#: You cant win them all.” [23] <> "Ba kullum ake kwana a gado ba." [24]

#: If your friend goes through a painful breakup, youre likely to say, [25] <> Misali ace abokinka ya rabu da maidakinsa kuma ya kasance a cikin zullumi, za ka iya fadin [26]

#: There are plenty of fish in the sea.” [27] <> "Abu kamar Jamfa a Jos." [28]

#: For a native speaker, [29] <> Ga mutumin da yake magana da harshensa, [30]

#: the worst thing about a proverb [31] <> za a iya cewa babbar matsalar karin magana a gare shi, [32]

#: is probably its overuse. [33] <> ita ce yawan yin amfani da ita a yayin zantawa. [34]

#: A 2015 article in the Journal of Judgement and Decision Making [35] <> Wata kasida da aka wallafa a mujallar "Judgement and Decision Making" [36]

#: found a correlation between pseudo-profound malarkey and low intelligence. [37] <> ta gano alakar da ke akwai tsakanin maganganu marasa ma'ana da karancin basira. [38]

#: Proverbial verse at work [39] <> Karin Magana a kan ayyuka [40]

#: Theres a proverb for everything, of course, [41] <> An ce akwai karin magana a kusan komai da dan adam yake yi, [42]

#: but theyre perhaps nowhere as plentiful as in our daily work life. [43] <> to amma za a iya cewa b su da yawa a irin aikace-aikacen da muke yi na yau da kullum. [44]

#: Business and proverbs are natural partners for several reasons, [45] <> Karin magana da kasuwanci ɗanjuma ne da ɗanjummai saboda wasu dalilai, [46]

#: says Fred Shapiro, editor of The Yale Book of Quotations and co-editor, [47] <> in ji editan wani littafi da ake kira "Book of Quotations", Fred Shapiro. [48]

#: As Shapiro puts it, “In business, time really is money,” therefore brevity is a plus. [49] <> Ya ce " A harkar kasuwanci, lokaci tamkar kudi ne, kuma haka ma 'yan kasuwa sun fi son takaice magana saboda ba su da lokaci." [50]

#: That could explain all the jargon we face every day, too. [51] <> Hakan ne ya sanya muke jin duk ire-iren kalmomi a kullum. [52]

#: Proverbsmuch like Twitter, which [53] <> Karin magana 'yan kil, kamar yadda ake rubutu a kafar sada zumunta ta Twitter a wannan zamanin, [54]

#: is useful for spreading themare perfect for this time-crunched world. [55] <> suna gamsar da jama'a wajen sadarwa. [56]

#: Shapiro also cited the memorability of proverbs and a certain simplicity in the corporate world: “Theres not a lot of subtlety in business. There are basic goals.” [57] <> Shapiro ya kara da yadda mutane ba sa manta karin magana. [58]

#: The timelessness of proverbs is comforting [59] <> Karin magana ba ya tsufa [60]

#: Whats more, in our work, the timelessness of proverbs is comforting. [61] <> Wani abin da yake ba wa mutane sha'awa shi ne yadda karin magana ba ya tsufa. [62]

#: John Latham, a PhD in organisation architecture and author of [[[Re]]]Create the Organization You Really Want!, [63] <> John Latham, wani mai matakin ilimin PhD, [64]

#: says that proverbs are useful in getting across ideas because [65] <> ya ce karin magana na da amfani sosai wajen isar da sako saboda" [66]

#: they, “…point out that this isnt a new fad idea, but rather timeless wisdom that you can count on”. [67] <> suna nuna cewa batun da ake magana akai ba sabon abu ba ne, illaiyaka dai an yi amfani da fasaha wajen isar da sakon." [68]

#: The origin of everything [69] <> Asalin karin magana [70]

#: Every proverb has to start somewherebut where? [71] <> Dole ne a samu wurin da karin magana ya fara. To amma ina ke nan? [72]

#: Finding out exactly where in the past a proverb emerged is a tough task, [73] <> Gano daga wurin da karin magana ya fara abu ne mai matukar wahala, [74]

#: akin to looking for a needle not just in a haystack, but in the entire farmland. [75] <> kamar ace ana neman allurar da ta bace ne a cikin ruwa. [76]

#: Its hard to know exactly how old a saying could be. [77] <> Yana da matukar wuya sanin shekarar da aka fara amfani da wata karin magana. [78]

#: Lexicographers are constantly antedating wordsfinding earlier examples[79] <> Masu nazarin kalmomi dai suna kokarin ba wa kowace kalma lokacin da aka fara amfani da shi. [80]

#: Theres also rarely a single, permanent version of a proverb. [81] <> Haka zalika, ba a cika samun karin magana guda daya kacal ba da za a ce shi kadai kowa yake amfani da ita. [82]

#: Like all language, the real story is about variations. [83] <> Kamar a harsuna da dama, za ka ga kowanne karin magana yana da launi iri daban-daban. [84]

#: For example, the saying, [85] <> Misali asalin karin maganar da ke cewa [86]

#: A woman without a man is like a fish without a bicycle[87] <> "macen da ba ta da namiji tamkar kifi ne da ba shi da keke," [88]

#: has a complex history. [89] <> na da rudarwa. [90]

#: Though often attributed to American feminist Gloria Steinem, [91] <> Duk da wasu suna danganta karin maganar da 'yar Amurkar nan mai rajin 'yancin mata, Gloria Steineman, [92]

#: Shapiro recently found a new oldest example from a 1975 issue of Australias Sydney Morning Herald. [93] <> a baya-bayan nan, Shapiro ya samo wata tsohuwar ma'ana ga wani karin magana daga shekarar 1975. [94]

#: Similar phrases are much older. [95] <> Ya gano wani karin magana wanda kalmominsa suke shige da na wannan, [96]

#: Since the 1950s, people have been saying the puzzling, Zen koan-likeA man without faith is like a fish without a bicycle.” [97] <> a inda a shekarun 1950 ake fadin "namijin da ba shi da imani tamkar kifi ne da ba shi da keke." [98]

#: A folk song from 1909 provided two early models: [99] <> Har wa yau, wata waka da aka yi a 1909 ta zamo misalai har guda biyu wato [100]

#: A man without a woman is like a ship without a sail[101] <> "namijin da ba shi da mace kamar jirgin ruwa ne da ba ya yawo a kan ruwa" [102]

#: andA man without a woman is like a fish without a tail.” The phrasefish without a tailis even older [103] <> da kuma "namijin da ba shi da mace tamkar kifi ne da ba shi da jela." [104]

#: Aging gracefully [105] <> Rashin tsufan karin magana [106]

#: The ageless [107] <> Rashin tsufa [108]

#: nature of proverbs is something that can make them even more useful than quotations. [109] <> ko kuma ace an daina amfani da karin magana ne ya janyo mutane suka fi amfani da su fiye da kalaman mutane na cikin baka. [110]

#: Though quotations and proverbs [111] <> Duk da cewa karin magana da kalaman cikin baka [112]

#: have a lot of overlap, [113] <> suna da kamanceceniya [114]

#: there are some key differences between quoting Winston Churchill and repeating an African proverb. [115] <> to amma akwai banbanci tsakanin rawaito kalaman Winston Churchill da kuma nanata karin magana irin ta nahiyar Afirka. [116]

#: With quotations, [117] <> "Yin amfani da kalaman cikin baka, [118]

#: youre trying to associate with some respected figure [119] <> alamu ne na kokarin alakanta kalaman da wanda ya yi su, [120]

#: But with proverbs, youre trying to do something more elemental and deeper than that. [121] <> a inda su kuma karin magana ake yin su da manufar zurfafawa [122]

#: In our work life, [123] <> A ayyukanmu na yau da kullum, [124]

#: that wisdom is usually used to motivate colleagues and employees. [125] <> irin wannan fasaha ta kan zo ne yayin da ake kokarin karfafawa abokan aiki ko kuma ma'aikata gwiwa. [126]

#: Still, even if a proverb is truly profound and clear, that clarity can have downsides. [127] <> Sai dai kuma Shapiro yana ganin cewa yawan yin amfani da karin magana ka iya haifar da tsukewar tunani ga masu yawan amfani da ita. [128]

#: But you know what they say: “Theres always another proverb at the end of the tunnel.” [129] <> To amma an ce "A koyaushe ba a rasa nono a ruga." [130]

Contents