Toggle menu
24.9K
757
183
164.8K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/073 why-do-we-gets-bags-under-our-eyes

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations


#: Why do we get bags under our eyes? [1] <> Wane dalili ne ke sa kwarmi a ƙasan ido? [2]

#: Dark circles under the eye suggest late nights and little sleep. [3] <> Rashin baccin dare da wuri, da kuma yin bacci kadan na daga abubuwan da suke haifar da kwrmi a kasan idanun mutane. [4]

#: The upsides of having relatively hairless faces are fairly straightforward. [5] <> Daga cikin amfanin rashin gashi a jikin ɗan adam akwai cewa [6]

#: Less hair means fewer places for parasites to hide, [7] <> 'yan kananan ƙwari kamar su Kwarkwawta da kuɗin cizo da kaska ba za su damar ɓuya a jikin mu ba. [8]

#: for example, and more exposed skin allows for sweat to more efficiently do its job keeping us cool. [9] <> Ƙarancin gashi na bamu damar fitar da gumi da kuma sanyaya mana jikinmu. [10]

#: But then theres the fact that skin is basically clear. [11] <> A zahiri ta ke cewa fatar ka ta yi fes, [12]

#: While that allows us to easily communicate our emotions and feelings to others it does come with a downside: [13] <> yayin da hakan ke nunfin za mu iya isar da sakwannin cikin sauki daga fukar mu zuwa wasu mutanen, [14]

#: it is so, so easy for someone to tell when you're tired. [15] <> hakan na kuma na da ta sa illar; domin wani cikin sauƙi zai gane cewa ka gaji liƙis ko kuma kana cikin wata damuwa, domin kuwa; labarin zuciya a tambayi fuska. [16]

#: Theres nothing medically wrong when those bags appear under your eyes, at least not most of the time. [17] <> A likitance dai ba ko yaushe ne kwarmin da ke futowa a ƙarƙashin idanun mutane ke da wata illa ba. [18]

#: But in a 2007 article in the Journal of Cosmetic Dermatology, [19] <> sai dai wani rahoto da aka buga a wata mujallar gyaran fata a shekarar 2007, [20]

#: Brazilian researcher Fernanda Magagnin Freitag points out that [21] <> wani mai bincike ɗan ƙasar Brazil Fernanda Magagnin Freitag ya bayyana cewa [22]

#: while they arewithin the limit of physiology,” many patients can become quitebothered and concerned by it, [23] <> mutane da dama za su iya damuwa sosai da kwarmin na ƙarƙashin idanu, [24]

#: even relating the presence of dark circles with significant impairment on their quality of life”. [25] <> har ma su ringa danganta baƙin da wajen ke yi da rashin samun ingantacciyar rayuwa. [26]

#: Skin-related conditions that can result in psychological or emotional distress are worth exploring, even if they do not represent a threat to health in more traditional terms. [27] <> Dan haka ya kamata a bincika matsalolin fata da za su iya kaiwa ga irin wannan tunanani, da kuma haifar da matsananciyar damuwa. [28]

#: What we do know is that the skin just beneath our eyes is especially thin, [29] <> Abunda ba mu sani ba shi ne fatar da ke ƙasan idanunmu ba ta da ƙwari. [30]

#: making it especially transparent. [31] <> Kuma hakan ya sa ta zama mai fale-fale. [32]

#: That makes the underlying blood vessels more prominent, [33] <> Wannan dai ya sa jijiyoyin jini da ke a fuska ba su da wata kariya sosai, [34]

#: which can make the skin appear darker. [35] <> sannan hakan na maida fatar ta zama baƙa. [36]

#: The apparent darkness is simply a result of the way that light reflects off the surface of facial contours [37] <> Baƙin da ake gani yana kasancewa ne sakamakon yadda hasken rana ya ke dukan fatar fuskar mai rauni. [38]

#: When someone tells me they have bags under their eyes, [39] <> "Idan wani ya zo ya ce min yana da kwarmi a ƙasan idanun sa, [40]

#: I like to actually see them and do an examination,” says Hayley Goldbach, a resident physician in dermatology at UCLA. [41] <> ina so in duba shi," a cewar Haley Goldbatch wata ƙwararriyar likitar fata. [42]

#: Thats because thin skin is just one of many possible reasons someone could have POH. [43] <> Ta ce saboda rashin ƙarfin fatar na iya zama ɗaya daga dalilan da za su iya sa kwarmin ƙasan ido da kuma baƙi a wajen. [44]

#: To tease apart the possibility, [45] <> Domin kau da duk wani shakku, [46]

#: Goldbach says she likes to stretch that skin out. [47] <> Goldbach ta ce ta na so ta ringa yi wa fatar wajen aiki. [48]

#: If the appearance worsens, [49] <> Idan har baƙin ya ci gaba [50]

#: then it suggests the underlying vasculature is the culprit. [51] <> to hakan na nufin cewa akwai matsala a zubin jijiyoyin wajen. [52]

#: If it gets better, [53] <> Idan kuma ana samun raguwa, [54]

#: then the problem may lie with the skins laxity, or looseness. [55] <> to hakan na nuna cewa raunin fatar ne kawai ke janyo kwarmin da kuma baƙi a ƙarƙashin idanun. [56]

#: Right between the nose, the eye, and the cheek is a groove [57] <> A fuska, akwai hanyar da hawaye ke bi tsakanin hanci da ido da kuma kumatu, [58]

#: dermatologists call the tear trough, [59] <> wanda likitocin fata ke ambata 'hanyar hawaye. [60]

#: As we get older, [61] <> A duk lokacin da shekarun mutum su ka tura, [62]

#: everyone loses fat under the surface of the skin,” explains Goldbach, [63] <> kaurin fata yana raguwa a cewar masaniya Goldbatch, [64]

#: and that makes the tear trough appear even more hollow. [65] <> kuma a cewar ta hakan yana sa hanyar hawayen ta ƙara rarakewa. [66]

#: But Goldbach says the most common explanation for the appearance of dark circles under our eyes is structural, [67] <> Masaniyar ta ƙara da cewa babban dalilin da ya ke sa ƙasan idon mutum ya yi baƙi shi ne sauyin da jikin mutum ke samu, [68]

#: simply due to the loss of subcutaneous fat we all endure as we age. [69] <> musamman ma raguwar kitsen da ke ƙarƙashin fatar mutum idan shekarun sa su ka yi nisa. [70]

#: And that, she says, is what often makes people with bags under their eyes look tired. [71] <> Kuma a cewar ta wannan ne ya sa ƙarƙashin idonun ke yin kwarmi, kuma wajen ya yi baƙi, sannan alamun gajiyawa su bayyana a fuskar mutum. [72]

#: But these explanations cant really account for the more transitory sort of under-eye bags, the sort you get when you just havent gotten enough rest. [73] <> To sai dai wannan bayani ba zai haɗa da matasan da ke samun wannan mastala ba saboda rashin bacci, da karancin hutu. [74]

#: Its also been suggested that exposure to [75] <> Haka kuma wasu bayanai na nuna cewa yawan shiga wajen da ake amfani da [76]

#: ultraviolet radiation [77] <> tsananin hasken na'ura domin ɗaukar hotunan jiki ko ƙona wasu cututtuka, [78]

#: exacerbates POH, [79] <> na daga abinda ke haifar da kwarmin a idanu. [80]

#: as could stress, alcohol, and smoking [81] <> Haka ma shan giya da shana taba na haifar da wannan matsala. [82]

#: Another thing that can lead to bags under your eyes is adema, or swelling,” says Goldbach. [83] <> Wani dalilin kuma da ke sa wannan matsalar shi ne taruwar ruwa a fuskar mutum, musamman kusa da idanun sa, a cewar Goldbach. [84]

#: And sometimes just after waking up the skin under our eyes is puffier than normal. [85] <> Wani lokacin kuma da zarar ka tashi daga bacci za ka tarar da fatar ƙarƙashin idanun ka ta yi rauni. [86]

#: A salt-heavy meal can also lead to puffy eyes. [87] <> Yawan cin abinci mai gisihir da yawa ma na iya haifar da wannan matsala. [88]

#: So if you gorge on French fries before falling asleep, [89] <> Idan ka ci abincin da aka zabgawa gishiri ka kuma kwanta [90]

#: you could wake up with bags under your eyes, [91] <> za ka iya tashi da kwarmi a ƙasan idon ka. [92]

#: but the underlying physiology might not have anything to do with fatigue itself. [93] <> Akwai ma wasu hujjojin da ke nuna cewa idan mutum ya sosa idanun sa, ko ya yi kuka na iya haifar da wannan matsala ta kwarmin ƙasan idanu. [94]

#: Its also been suggested that exposure to ultraviolet radiation exacerbates POH [95] <> An kuma tabbata cewa mayukan ƙara hasken fuska su ma na haifar da kwarmin na ƙasan idanu. [96]

#: none of these claims have been scientifically substantiated. [97] <> To sai dai fa duk da waɗannan bayanai, babu wasu isassun hujjoji na kimiyya da za su yi bayani kai tsaye kan hanyar magance larurar kwarmin a ƙarƙashin idanu, [98]

#: Because it is so temporary, and due to the overwhelming number of underlying causes, [99] <> saboda dalilan wannan matsaloli suna da yawa, [100]

#: and also because most dermatologists think of it as primarily a cosmetic or aesthetic issue, [101] <> kuma likitocin fata na ganin matsala ce ta shafe shafe. [102]

#: Bleaching creams have been marketed for dark circles, [103] <> To amma duk da haka ana ƙoƙarin nemo magungnan wannan matsala, [104]

#: Acids have been derived from fungi and extracts have been taken from pear trees. [105] <> kamar amfani da ruwan da aka tatso ta jikin wasu bishiyoyi. [106]

#: Then there are substances that can be injected into the skin to act as fillers, [107] <> Haka kuma akwai wasu sindarai da ake yi wa mutum allurar su da, [108]

#: and there are surgical options as well. [109] <> sannan a wasu lokutan ma ana tiyata. [110]

#: One researcher even tried subcutaneous injections of carbon dioxide once a week for nearly two months, [111] <> Wani mai bincike ya taɓa bada shawarar cewa allurar wasu sinadarai da ke ƙunshe da carbon dioxide sau ɗaya a sati har tsawon wata biyu zai iya taimakawa. [112]

#: and found modest success. [113] <> Kuma masanin ya ce wannan mujarra bi ne. [114]

#: Some researchers have tried applications of vitamin C, [115] <> Wasu masu binciken sun yi ƙoƙarin amfani da sinadarin vitamin C. [116]

#: while others resort to options that might not actually help but are smart anyway: sunscreen and UV-coated sunglasses. Still, Sarkar says, “even a mild-to-moderate improvement in appearance can cause an improvement in the quality of life of the patient”. Until more evidence is available, though, another option may just be to learn to love those dark lines as distinguishing features of a wiser face. [117] <> To amma matuƙar ba a samu wani magani kaifiyyan na wannan matsala ba, a dai dai lokacin da masanan ke lalube cikin duhu kamata ya yi jama'a su yi hakurin rayuwa da wadannan kwarmin a idanunun su a matsayin wani ɓangare na halittun jikin su. [118]

Contents