- Clubhouse: What is it and how do you get invited?
- Published 24 February 2021
- Less than a year old,
- Clubhouse already ticks the boxes for being the next big thing [1]:
- Here's what you need to know.
- Why should I care?
- Tesla and SpaceX billionaire Elon Musk has been using Clubhouse
- It's causing waves around the world, from the US (where the app started), to China, Brazil and Turkey.
- Wherever you are, you'll probably be hearing about it soon.
- Some of the world's super-rich and famous are already big names on the app:
- And inevitably this rush of hype and fame has been followed by money,
- with venture capitalists already valuing Clubhouse at over $1bn (£0.7bn), according to the Financial Times,
- How does Clubhouse work?
- What makes the app stand out is the lack of text, pictures and videos.
- It is audio only.
- Also, everything happens live, in real time.
- You can start a virtual room yourself or join one other people are speaking in.
- Generally, a certain number of people only can speak.
- Everyone else has only the option to listen.
- But you can raise your hand and ask to be allowed to talk.
- Within the app, conversations aren't recorded or made available to play back later.
- So you have to catch everything as it happens.
|
- Clubhouse: Mene ne shi kuma ta yaya ake shiga?
- 30 Mayu 2021, 04:00 GMT
- Ƙasa da shekara daya,
- Clubhouse ya kai ya kawo a matsayinsa na abin da ake yayi:
- Ga abubuwan da ya kamata ku sani.
- Me ya sa zan damu da shafin?
- Mai kamfanin Tesla da SpaceX kuma attahirin nan Elon Musk ya jima yana amfani da Clubhouse
- Ana ta magana a kan shafin a faɗin duniya, daga Amurka (inda aka ƙirƙiri manhajar) zuwa China da Brazil da Turkiyya.
- Duk inda kuke a faɗin duniya, babu mamaki kwanan nan za ku fara ji ana maganarsa.
- Wasu daga cikin shahararrun mutane a duniya na amfani da shafin:
- Attajirai a ɓangaren fasaha Elon Musk da shugaban Facebook Mark Zuckerberg
- Mawaƙan rap Drake da Kanye West
- Shaharrariyar mai gabatar da shirye-shiryen talabijin Oprah Winfrey
- Kuma babu shakka wannan tururuwar da ake yi wa shafin dole kuɗi ya biyo baya,
- inda masana ke ganin darajar Clubhouse ta haura dala biliyan 1, a cewar jaridar Financial Times.
- Ya Clubhouse ke aiki?
- Abin da ya sa manhajar ta fita daban shi ne rashin rubutu da hotuna da bidiyo.
- Murya ce kawai.
- Haka kuma, komai kai tsaye yake faruwa a shafin.
- Kana iya buɗe 'ɗaki' da kanka ko kuma ka shiga wani ɗakin da mutane ke magana.
- Akwai iya adadin mutanen da za su iya magana.
- n/a
- Amma kana iya 'ɗaga hannunka' ka buƙaci a ba ka damar yin magana.
- A cikin manhajar, ba a naɗar hirar da ake yi ko kuma a ajiye ta don saurare daga baya.
- Don haka dole ka saurari komai a lokacin da ya ke gudana.
|