bbchausa verticals/097 the 80bn ngn 193m usd embezzlement
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
<small> --[[bbchausa_verticals/097_the_80bn_ngn_193m_usd_embezzlement]]</small>
# |
Yan Najeriya na yi wa gwamnatin Buhari shaguɓe kan kama Akanta Janar da EFCC ta yi [1] | Nigerians Reaction over Buhari's Government EFCC's arrest of Accountant General |
|---|---|---|
1 |
An wayi garin Talata 17 ga watan Mayun 2022 | -- |
2 |
ƴan Najeriya suna ta mayar da martani kan | Nigerians are reacting to |
3 |
kamun da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon ƙasa wato EFCC ta yi wa Babban Akantan kasar, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi har naira biliyan 80. | the arrest of the Accountant General by the Economic and Financial Crimes Comission (EFCC) for alleged embezzlement of N80 billion. |
4 |
Hukumar, | The commission, |
5 |
a cikin wata sanarwa | in a statement |
6 |
da ta wallafa a shafinta na Facebook, | posted on its Facebook page, |
7 |
ta ce ta kama Ahmed Idris ne a ranar Litinin a Kano da ke arewacin kasar. | said it had arrested Ahmed Idris on Mon in the northern city of Kano. |
8 |
EFCC na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi. | The EFCC accuses Ahmed of misappropriating funds through his friends and family and other means. |
9 |
Ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja. | -- |
10 |
An kama Ahmed Idris | Ahmed Idris was arrested |
11 |
bayan ya ƙi amsa gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa | after he refused an invitation from the EFCC to appear before it |
12 |
domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, | for questioning over allegations against him, |
13 |
kamar yadda hukumar ta bayyana. | according to the commission. |
14 |
Dandalin sada zumunta na Tuwita da Facebook | The social networking site Twitter and Facebook |
15 |
sun zama manyan wuraren da ƴan ƙasar suka bazama suna bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan lamari da ya kunno kai. | have become major forums for citizens to express their views on this emerging issue. |
16 |
Maudu'ai biyar ne da suka danganci batun suke tashe a Tuwita da suka hada da #80bn da #Ahmed Idris da #EFCC da #Accountant General da kuma #ASUU, inda dubban mutane ke tattaunawa. | Five topics related to the issue are being raised (trending) on Twitter including #80bn ($192,687,504) and #AhmedIdris and #EFCC and #Accountant General and #ASUU, where thousands of people are debating. |
17 |
A dandalin Facebook kuwa kusan mutum 25,000 ne ke tsokaci kan batun da safiyar Talatar. | On Facebook, about 25,000 people commented on the issue on Tuesday morning. |
18 |
Mutane sun fi mayar da hankali ne wajen yi wa Shugaba Buhari shaguɓe | People have been more vocal in their opposition to President Buhari |
19 |
tare da alaƙanta batun | and linked the issue |
20 |
da yajin aikin da malaman jami'a ke yi a halin yanzu, | to the ongoing university teachers' strike, |
21 |
wanda ya sanya ɗalibai zaman gidan tilas. | which has forced students to stay home. |
22 |
Yayin da wasu kuma suke ganin abin kunya ne | While others see it as a shame |
23 |
a ce ana samun irin wannan lamari na almundahana a gwamnatin Buhari, | to see such corruption prevalent in the Buhari administration, |
24 |
wacce tun kafin kafuwarta ta dinga da'awar cewa za ta yi yaƙi da cin hanci da rashawa. | which even before its inception claimed to be fighting corruption. |
25 |
Ga dai abubuwan da wasu ke faɗa a Tuwita: | Here are some comments on Twitter: |
26 |
@LadyRoza_001 ta ce: | @LadyRoza_001 said: |
27 |
"A ƙasar da ke fama da talauci, | "In a poor country, |
28 |
mutum ɗaya zai saci naira biliyan 80 cikin ƙasa | one person would steal 80 billion naira |
29 |
da shekara huɗu da ɗarewarsa kan wannan muƙami. | in less than four years of holding this position. |
30 |
Wannan lamari ne mai muni." | This is a terrible thing." |
31 |
— `ℝ𝕠𝕫𝕒😈🌶️ (@LadyRoza_001) May 17, 2022 [2] | -- |
32 |
@ifeanyidamian11 ya ce: | @ifanyidamian11 said: |
33 |
"A yanayin da ake ciki da ɗalibai ke zaune a gida saboda yajin aiki tsawon wata biyu, | "In a situation where students are living at home due to a two-month strike, |
34 |
amma wani mai son zuciyar ya sace naira biliyan 80, yayin da ita ASUU ke neman a biya ta abin da ko kusa da wancan kuɗin bai kai ba." | one volunteer stole N80 billion, while ASUU is seeking compensation for that or less. the money is not enough." |
35 |
— Ifeanyi Damian (@ifeanyidamian11) May 16, 2022 [3] | -- |
36 |
A shafin BBC Hausa na Facebook kuwa kusan mutum 3,00 ne suka yi tsokaci kan labarin. | On the BBC Hausa Facebook page, almost 3,00 people commented on the story. |
37 |
Abdullahi Auwal Sulaiman ya ce: "A daidai lokacin da ASUU suke yajin aiki a kan biliyan 200, sai ga shi mutum daya kacal ya saci biliyan 80 shi kadai. Allah ya isar mana. | Abdullahi Auwal Sulaiman said: "At a time when ASUU is on strike for over 200 billion, only one person has stolen 80 billion. God forbid. |
38 |
Abubakar Ambasador ya ce: "Kai jama'a! Wai su waye za su riƙe amana a wannan kasar de don Allah? Kowa ya samu dama kawai ya kwashe dukiyar ƙasa. Innalillahi Wa'inna Ilaihin Raji'un! | Abubakar Ambassador said: "O people! Who will be faithful in this country please? Everyone has the opportunity to plunder the land. Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un! |
39 |
Hassan Yabour ya ce: "Wato dai kowa jira ya kai ya samu dama a Lanjeriya. Ya Allah ka da ka ba duk mai son satar kudin Lanjeriya damar samun mukami. | Hassan Yabour said: "That is to say, everyone should wait for the opportunity in Nigeria. O God, do not give anyone who wants to steal Nigerian money as soon as on gets the chance. |