bbchausa verticals/099 bomb blast in Kano
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
<small> --[[bbchausa_verticals/099_bomb_blast_in_Kano]]</small>
# |
Sinadaran hada bam ne suka haddasa fashewa a Kano [1] | Bomb blast in Kano |
|---|---|---|
1 |
Rest of the article <> Sauran labarin [2]
- Ranar da fashewar ta auku <> The day the explosion occurred,
- Kwamishinan 'yan-sanda Sama'ila Dikko ya gaya wa BBC <> Commissioner of Police Samuel Dikko told the BBC
- cewa tukunyar gas na walda ce ta fashe <> that the welded gas cooker had exploded.
- Rundunar 'yan-sandan Najeriya a Jihar Kano <> The Kano State Police Command
- ta ce fashewar da ta auku a wani shago a unguwar Sabon Gari da ke birnin <> says an explosion at a shop in the Sabon Gari area of the city
- a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, <> on Thursday, May 17
- wadda ta hallaka mutum tara, <> which killed nine people
- ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya hada bam da su. <> was caused by a combination of chemicals mixed to make bombs.
- A lokacin da fashewar ta auku <> At the time of the blast
- an rika yada labari masu karo da juna dangane da musabbabin abin, <> conflicting reports were circulating about the cause, <small> --[[bbchausa_verticals/099_bomb_blast_in_Kano]]</small>
- inda wasu ke cewa bam ne ya tashi <> with some saying it was a bomb
- wasu kuma ke cewa tukunyar gas ce ta mai aikin walda ta fashe a shagon. <> and others saying it was a gas cooker that exploded in the shop.
- A tattaunawarsa da wakilin BBC a wurin da fashewar ta auku, a ranar, Kwamishinan 'yan-sanda na Jihar ta Kano, CP Sama'ila Dikko, ya ce tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, "amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa." <>
- A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan-sandan Jihar SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022, rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da wadannan haramtattun sinadarai, wadanda ake hada bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar. <>
- Sanarwar ta ce, "Binciken farko-farko ya nuna cewa daga cikin mutum tara da fashewar ta rutsa da su, daya daga cikinsu yana ajiye sinadarai masu lahani da sauran abubuwa masu hadari ba bisa ka'ida ba. <>
- Mutum shi ne Michael Adejo, (wanda ya mutu)." <>
- Rundunar 'yan-sandan a wannan sanarwa ta ranar Asabar ta tabbatar da mutuwar mutum tara da kuma wasu takwas wadanda suka hada da dalibai da ta ce sun samu 'yan raunuka a sanadiyyar fashewar ta ranar Talata. <>
- 'Yan-sandan sun bayyana sunayen wadanda suku mutum kamar haka, Ejike Vincent (mai walda) da Michael Adejo (mai sayar da sinadarai) da Musa Kalla (mai sayar da shayi da Christiana Abosade da Mary da Austine Dada da Madam Owoleke da Omo Ben da kuma Bose Oladapo. <>
- Rundunar ta kuma bayyana wasu tarin durum-durum da jarkoki da ke dauke da sinadarai iri daban-daban, masu hadari da ta ce ta gano a inda lamarin ya faru. <>
- Ta ce binciken kwararrunta a kan bam, ya nuna cewa suna zargin fashewar ta auku ne a sakamakon haduwar wasu sinadari da wuta. <>
- A sanarwar, rundunar ta kuma ce ta yi kame na wasu da ke da alaka da daya daga cikin shagunan da suka rushe a fashewar, wanda ake haramtaccen kasuwancin sayar da sinadarn da ababan da take zargi ana hada bam da su. Ta kuma samu shedar sayen kayayyakin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike. <>
- Fashewar wadda ta auku a gida mai lamba 01 kan titin Aba/Court Road a unguwar Sabon Gari ya yi sanadiyyar rushewar gidan, wanda yake da shaguna hudu a kasa da kuma bene. Akwai kuma wata makarantar boko ta yara, Winner Kids Academy a tsallaken gidan, inda da farko aka rika cewa a makarantar ne aka tayar da bam. <>