bbchausa verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya
More actions
- ''Hausa article: Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya'' <> English_Machine_Translation <small style="font-size:smaller;"> --[[bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya]]</small>
- HAUSA
ENGLISH --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - Ma`abota rubutu da wallafe-wallafe da ke goyon bayan jam`iyya ko `yan siyasa a Najeriya
(Fans of writing and publishers that support a party...) Writers and writers who support a party or politician in Nigeria --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - wadanda aka fi sani da `yan "soshiyal midiya" na kara karfi a siyasar kasar.
popularly known as "social media" are gaining momentum in the country's politics. --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - A halin da ake ciki sun kai matsayin da ana damawa da su a kusan kowanne matakin gwamnati da rukunin `yan siyasa.
At the same time, they have reached a tipping point at almost every level of government and political party. --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - ‘Yan soshiyal midiya a Najeriya na da karfin gaske kasancewar suna taka muhimmiyar rawa wajen daukaka jam`iyya ko dan siyasa.
Social media in Nigeria is very important as it plays an important role in the upliftment of any party or politician party. --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - Kuma su ma abubuwan da suke yi na kusanta su ga `yan siyasa, suna kuma samun rufin asiri daga harkar.
And their activities bring them closer to politicians, and they get a roof over their heads. --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - To sai dai kuma ana zargin wasu daga cikinsu da zama `yan kore ko karnukan farauta,
However, some of them are accused of being green or hunting dogs, --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - wadanda ake amfani da su wajen kazafi ko aibunta abokan hamayyar siyasa.
which are used to slander or insult political opponents. --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya - HAUSA
ENGLISH --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya
- HAUSA
Wannan dama da `yan soshiyal midiya ke samu ta ciccibawa da tura `yan siyasa zuwa kololuwar daukaka ko akasi ta sa ana kaffa-kaffa da su.
Dr Kabiru Danladi Lawanti, masanin aikin jarida a jami`ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shaida wa BBC cewa ana tsoron ‘yan soshiyal midiya saboda mutane ne wadanda suna da karfin gaske musamman idan suka fara yada abubuwa wadanda ake gani kamar nakasu ne daga dan siyasa, to wannan sai ya hana dan siyasar tasiri.
Ya ce haka kuma idan suna kaunar mutum suka fara yada manufofinsu masu kyau, ko ba a sonsa, sai kaga daga baya an zo ana sonsa.
A halin yanzu dai `yan soshiyal midiya sun kasance tamkar sojojin baka ne, wadanda ke kokarin shan gaban `yan jarida ba don rashin kwarewa na yi musu cikas ba.
Kuma ana dai zargin mafi yawan `yan soshiyal midiyan da zama `yan kanzagin `yan siyasa, saboda rashin akida.
Dr Ashir Tukur Inuwa, malami a sashen nazari da koyar da aikin jarida na jami`ar Bayero ta Kano, ya ce yawancin ‘yan soshiyal midiya basu da kwarewa ko horo na aikin jarida, da ka su kan tari abin shi ya sa ake yawan samun labaran karya da na batanci.
To amma Mallam Rabi`u Biyora, bai musanta ba, amma ya ce ba a taru aka zama daya ba.
Ya ce "Maganar cewa ana amfani da ‘yan soshiyal midiya a matsayin karnukan farauta da zage-zage da cin mutunci duk ana yin wadannan abubuwan, to amma ba duka aka taru aka zama Daya ba.”
Mallam Rabi`u Biyora, ya ce "Duk kaunar da nake yi wa siyasa ko wani dan siyasa bai isa ya sa na zagi ko aibata wani ba.”
Wata kididdiga da aka yi a bara, ta nuna cewa ana da akalla kungiyoyin `yan soshiyal midiya fiye da dubu ashirin da bakwai a Najeriya.
Kuma a yanzu ma sai abin da ya karu kasancewar an fara shiga kakar zabe a Najeriya.
ENGLISH --bbchausa_verticals/104 Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya