bbchausa verticals/107 how whatsapp makes money
More actions
| # | English | Hausa |
|---|---|---|
| 1 | How does WhatsApp make money? It's free - with some tricks | Ta yaya dandalin WhatsApp ke samun kuɗi? |
| 2 | https://www.bbc.com/news/articles/c8j7nrppny2o | https://www.bbc.com/hausa/articles/cglk7dyp30eo |
| 3 | 16 October 2024 | 21 Oktoba 2024 |
| 4 | The main messaging apps are all free to use, so what is in it for them? | Kyauta ake ake amfani da yawancin shafukan sada zumunta, amma abin tambayar shi ne da me masu dandalin ke karuwa? |
| 5 | In the past 24 hours I’ve written more than 100 WhatsApp messages. | Cikin awa 24 na rubuta sakonnin WhatsApp 100. |
| 6 | None of them were very exciting. | Babu wani mai armashi a cikinsu. |
| 7 | I made plans with my family, discussed work projects with colleagues, and exchanged news and gossip with some friends.
Perhaps I need to up my game, but even my most boring messages were encrypted by default, and used WhatsApp’s powerful computer servers, housed in various data centres around the world. It’s not a cheap operation, and yet neither I nor any of the people I was chatting with yesterday, have ever parted with any cash to use it. The platform has nearly three billion users worldwide. So how does WhatsApp – or zapzap, as it’s nicknamed in Brazil - make its money? |
Mun tsara abubuwa tare da iyalina, mun tattauna kan aiki da abokan aikina, mun gaisa da wasu, mun yi musayar labarai, mun kuma yi gulma da abokaina.
Ƙila ya kamata na sake tunani, amma yawancin sakonnin da nake da su a wayata ba su da armashi, amma kuma sakonni ne da babu wanda ya isa ya karanta su ban da mu, saboda an yi amfani da manyan na'urori masu kwakwalwa wajen ɓoye su (end-to-end encryption). Sai kuma fa ba abu ne mai araha ba. Dandalin WhatsApp na da masu amfani da shi kusan biliyan uku a sassan duniya. Abin tambayar shi ne ta ina WhatsApp – ko zapzap, kamar yadda matasan Brazil suke ma sa lakabi - yake samun kudi? |
| 8 | Admittedly, it helps that WhatsApp has a massive parent company behind it – Meta, which owns Facebook and Instagram as well.
Individual, personal WhatsApp accounts like mine are free because WhatsApp makes money from corporate customers wanting to communicate with users like me. Since last year firms have been able to set up channels for free on WhatsApp, so they can send out messages to be read by all who choose to subscribe. But what they pay a premium for is access to interactions with individual customers via the app, both conversational and transactional. The UK is comparatively in its infancy here, but in the Indian city of Bangalore for example, you can now buy a bus ticket, and choose your seat, all via WhatsApp. “Our vision, if we get all of this right, is a business and a customer should be able to get things done right in a chat thread,” says Nikila Srinivasan, vice president of business messaging at Meta. “That means, if you want to book a ticket, if you want to initiate a return, if you want to make a payment, you should be able to do that without ever leaving your chat thread. And then just go right back to all of the other conversations in your life.” Businesses can also now choose to pay for a link that launches a new WhatsApp chat straight from an online ad on Facebook or Instagram to a personal account. Ms Srinivasan tells me this is alone is now worth “several billions of dollars” to the tech giant. |
Maganar daya ce, ko ma yaya abin yake WhatsApp yana da uwargijiya wato kamfanin Meta, wanda ya mallaki dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram.
Ɗaiɗikun mutane irina na samun damar yin amfani da WhatsApp a kyauta ne saboda dandalin na samun kuɗaɗe ne daga manyan kamfanoni da ke son su kai ga mutane irina. A shekarar da ta gabata kamfanoni suka fara iya buɗe tasha (channel) a kyauta domin tura wa dubban mutane saƙonni, musamman ga wadanda suke bibiyar abubuwan da kamfanin ke yi. Amma suna biyan wani dan kaso mai kama da na goro kafin samun damar tattaunawa da abokan huldarsu da kuma biyan kuɗi ta manhajar. Har yanzu abin bai yi ƙarfi ba a Birtaniya. Misali a birnin Bangalore na kasar Indiya, mutum zai iya sayen tikiti hawa motar bas har ma ya zaɓi kujerar da yake so duka ta WhatsApp - kamar dai yadda ake shiga shafin intanet na kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama ko na ƙasa. “Burinmu shi ne samar da komai ta hanyar da ta dace, tun daga kasuwanci, mu'amala da abokan hulda ta yadda za su dinga tuntubar juna ta sassaukar hanya,'' in ji mataimakiyar shugabar fannin kasuwanci ta kamfanin Meta, Nikila Srinivasan. “Hakan na nufin idan kana son sayen tikiti na zuwa da komawa, za ka iya biyan kuɗin zuwa da dawowa ta hanyar aikewa da sakon WhatsApp. Sai ka ci gaba da sabgoginka kawai.” Su ma 'yan kasuwa suna da damar zaɓar tsarin sanya wurin biyan kudi a sabon madannin da aka sanya a manhajar da zai kai mutum kai-tsaye daga dandalin Facebook ko Instagram zuwa asusun kamfanin. Mis Srinivasan ta ce ana samun makudan kudade a nan. |
| 9 | Other messaging apps have gone down different routes.
Signal, a platform renowned for its message security protocols which have become industry-standard, is a non-profit organisation. It says it has never taken money from investors (unlike the Telegram app, which relies on them). Instead, it runs on donations – which include a $50m (£38m) injection of cash from Brian Acton, one of the co-founders of WhatsApp, in 2018. “Our goal is to move as close as possible to becoming fully supported by small donors, relying on a large number of modest contributions from people who care about Signal,” wrote its president Meredith Whittaker in a blog post last year. Discord, a messaging app largely used by young gamers, has a freemium model – it is free to sign-up, but additional features, including access to games, come with a pricetag. It also offers a paid membership called Nitro, with benefits including high-quality video streaming and custom emojis, for a $9.99 monthly subscription. Snap, the firm behind Snapchat, combines a number of these models. It carries ads, has 11 million paying subscribers (as of August 2024) and also sells augmented reality glasses called Snapchat Spectacles. And it has another trick up its sleeve - according to the website Forbes, between 2016-2023 the firm made nearly $300m from interest alone. But Snap’s main source of revenue is from advertising, which brings in more than $4bn a year. |
Sai dai wasu manhajojin aika sakonni na amfani da wata hanyar ta daban.
Manhajar Signal da ta shahara da tsaro wajen tura saƙonni, masu kamfanin sun ce ba su taɓa karɓar kuɗin wani mai zuba jari ba. Tana aiki ne bisa kyautar kuɗaɗe da kamfanin ke samu daga mutane - ba kamar Telegram ba da ya dogara kan masu zuba jari. Manhajar Discord da matasa masoya wasannin game ke amfani da ita, kyauta ake shiga amma da zarar za ka kurda wasu bangarorin ciki - kamar samun damar shiga sashen manyan wasannin game - sai ka biya wani kaso. Sannan ana yi wa masu amfani da shafin tayin mallakar katin zama mamba a dandalin wanda shi ma za ka biya wasu kudade da suka kai kusan dala 10 a kowane wata. Kamfanin Snap, da ya samar da manhajar Snapchat na ba da damar zama mamba a a dandalin da ake kira Nitro, wanda shi ma sai an biya wasu kudade idan mutum na son yin bidiyo kai-tsaye da kuma yada shi, da 'yan alamomin nan masu kama da zanen kayan wasan yara. A kowacce shekara Snapchat na samun kudaden shiga daga tallace-tallacen da ya ke yi da suka haura dala biliyan huɗu. |
| 10 | The UK-based firm Element charges governments and large organisations to use its secure messaging system. Its customers use its tech but run it themselves, on their own private servers. The 10-year old firm is in “double digit million revenue” and “close to profitability”, its co-founder Matthew Hodgson tells me.
He believes the most popular business model for messaging apps remains that perennial digital favourite - advertising. “Basically [many messaging platforms] sell adverts by monitoring what people do, who they talk to, and then targeting them with the best adverts,” he says. The idea is that even if there is encryption and anonymity in place, the apps don’t need to see the actual content of the messages being shared to work out a lot about their users, and they can then use that data to sell ads. “It's the old story - if you the user, aren't paying, then the chances are that you are the product,” adds Mr Hodgson. |
Kamfanin Element na Birtaniya na karbar maƙudan kudade daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu don aikewa da sakonni. Kamfanin da aka samar shekara 10 da suka gabata, na samun miliyoyi na kudaden shiga, kamar yadda mai kamfanin Matthew Hodgson ya shaidawa BBC.
Ya yi amanna yawancin manhajojin kasuwanci ba sa taka rawa kamar ake tsammani ta fuskar bunkasar kasuwanci. “Wato fa abin da yawancin dandalin nan ke yi shi ne sayar da tallace-tallace ta hanyar bibiyar abubuwan da mutane ke so ko suke yawan ddubawa, da zarar sun shiga intanet, shikenan sai su samu wurin labewa, a yi ta tallace-tallace kamar babu gobe," in ji Hodgson. Mr Hodgson ya kara da cewa: “Maganar duk guda daya ce, idan kai mai amfani da shafin ba ka biyan ko sisi, to hakan na nufin kai ne ka hajar dandalin.” |