bbchausa verticals/pics/2021-10-08
From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
More actions
Africa's week in pictures: 8-14 October 2021 Published 15 October 2021 [1] <> Hotunan Afirka na mako 8-14 Oktoba 2021: Masu sintiri a gabar teku da magoya bayan ƙwallo (16 Oktoba 2021) [2]
- Kenya's Diana Kipyogei is crowned after winning the Boston Marathon on Monday.
An bai wa Diana Kipyogei ɗan Kenya kambu bayan yin nasara a Gasar Tsere ta Boston ranar Litinin. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - This mural of Archbishop Desmond Tutu, who turned 90 last week, is restored on Friday in Cape Town, after it was defaced with a racist slur.
A ranar Juma'a ne aka sake dawo da wannan zanen fentin na Archbishop Desmond Tutu, wanda ya cika shekara 90 a makon da ya gabata a birnin Cape Town, bayan da a baya masu wariyar launin fata suka goge shi. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - This fan makes her allegiances clear at South Africa's football World Cup qualifier against Ethiopia on Tuesday, which Bafana Bafana won 1-0.
Wannan mai goyon bayan ƙwallon ƙafar na nuna goyon bayanta ga Afirka Ta Kudu a wasan neman shiga gasar ƙwallon kafar dunuya da aka yi a Habasha ranar Talata, inda kungiyar Bafana Bafana ta ci 1-0. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - This plaque marks the entrance to the Foumban Royal Palace in western Cameroon...
Wannan hoton an manna shi ne a jikin kofar shiga Fadar Masarautar Foumban a yammacin Kamaru... --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - On Monday, 28-year-old Mfonrifum Nabil Mbombo Njoya was inaugurated as the new Sultan of Bamoun.
A ranar Litinin ne aka nada Mfonrifum Nabil Mbombo Njoya mai shekara 28 a matsayin sabon sarki wato Sultan na Bamoun. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - Spectators watch the Rally of Morocco in the Merzouga region on Sunday.
Wasu mutane na kallin tseren babura a cikin hamada a yankin Merzouga ranar Lahadi. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - Activists turned up on Tuesday to listen to proceedings at Botswana's top court, where the government is seeking to overturn a landmark ruling that decriminalised homosexuality.
Masu fafutuka a ranar Talata sun taru don sauraron shari'a a wata babbar kotu a Botswana, inda gwamnati take so a sauya hukuncin da aka yanke na halasta luwadi. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - On Sunday, 40 days after a massacre at the Chena Teklehaymanot Church in Ethiopia's Amhara region, personal items belonging to the dead sit on a windowsill. Amhara officials say Tigrayan forces are to blame, which they in turn deny.
A ranar Lahadi, kwana 40 bayan kisan kiyashin da aka yi a Cocin Chena Teklehaymanot a yankin Amhara na Habasha, ana iya ganin kayayyakin mutanen da suka mutu a kan taga. Jami'an Amhara sun ce dakarun Tigray za a zarga, su kuma sun yi watsi da zargin. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - A herd marches through Kenya's Amboseli National Park, where there has been a baby-elephant boom.
Wani garken giwaye na wucewa a cikin Gandun Daji na Amboseli na, wajen da ake samun ƙaruwar haihuwar giwaye. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - Somali marine forces patrol coastal waters on Wednesday, following a legal ruling on the disputed sea border with Kenya that largely favoured Somalia.
Jamia'n sojin ruwan Somaliya suna sintiri a bakin gabar tekun kasar ranar Laraba, sakamakon shari'ar da aka yanke kan rikicin kan iyaka tsakanin Kenya da Somalia wacce ta yi wa Somaliyan dadi. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - A flock of birds takes to the sky as a police helicopter flies over a parade in Libya's capital, Tripoli, on Saturday.
Taron tsuntsaye na shawago a sararin samaniya a daidai lokacin da wani helikwafta ke a sa shawagin a Tripoli babban birnin Libiya ranar Asabar. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - The next day in South Africa, people take part in the One Sky One World International Kite Fly.
Washe gari a Afirka ta Kudu mutane na jefa jiragen leda a sararin sama. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - And on Thursday in Mauritius, a man washes his month-old puppy in the Indian Ocean.
A ranar Alhamis a Mauritius, wani mutum ya yi wa karensa wanka a gabar Tekun Indiya. --bbchausa verticals/pics/2021-10-08 - ENGLISH
HAUSA --bbchausa verticals/pics/2021-10-08