Toggle menu
24.9K
757
183
164.8K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

bbchausa verticals/pics/2021-10-15

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations

bbchausa verticals/pics

Africa's week in pictures: 15-21 October 2021 Published 22 October 2021 [1] <> Hotunan Afirka na mako 15-21 Oktoban 2021: Zane da zanga-zanga da jima (23 Oktoba 2021) [2]

  1. A man walks past paintings for sale by the roadside in Nigeria's capital, Abuja, on Monday.
    Wani mutum na tafiya ta kusa da wasu zane-zanen da ake sayarwa a bakin titi a Abuja babban birnin Najeriya a ranar Litinin. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  2. Two days later, Nigerians across the country take to the streets to voice their outrage at the lack of progress made against police brutality since the killing of peaceful #EndSARS protesters exactly one year ago.
    Kwana biyu bayan nan mutane sun fita zanga-zanga a kan tituna don nuna ɓacin ransu kan rashin ɗaukar mataki daga hukumomi na magance cin zarafin da ƴan sanda ke yi a Najeriya, shekara ɗaya cif bayan zanga-zangar da ta karaɗe ƙasar ta Endsar. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  3. On Saturday a man treats leather at one of the oldest tanneries in Morocco's northern city of Fez.
    A ranar Asabar wani mutum na jimar fata a ɗaya daga cikin tsofaffin marina da ke birnin Fez na Moroko. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  4. On the same day, a model gets ready backstage at East Africa International Fashion Week...
    A wannan ranar kuma, wata mai tallar kayan ƙawa tana ƙwalisa a taron kayan ƙawa na ƙasa da ƙasa na Afrika... --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  5. The event is in its third year...
    Wannan ne karo na uku da ake taron... --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  6. And Saturday's catwalk in Nairobi showcased designers from Kenya, Uganda and Tanzania.
    A ranar Asabar a wajen taron mata ƴan ƙwalisa sun nuna adonsu musamman daga Kenya da Uganda da Tanzaniya. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  7. A supporter of Asec Mimosas wears team colours, as the Ivorian side take on CR Belouizdad of Algeria in the African Champions League on Saturday in Abidjan.
    Wani magoyin bayan Asec Mimosas ya sanya launin tawagar, a lokacin da tawagar Ivory Coast ta fafata da ta Aljeriya a gasar zakarun Afirka ranar Asabar a Abidjan. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  8. On the same day in South Africa, a man parks his car in the Bo-Kaap neighbourhood of Cape Town...
    A wannan ranar a Afirka Ta Kudu, wani mutum ya ajiye motarsa a Bo-Kaap a birnin Cape Town... --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  9. Not far away, a bridal party leaves Camps Bay beach after a Saturday wedding...
    A wani wajen kusa da nan kuma an yi liyafar auren wasu ne a bakin teku a ranar Asabar din... --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  10. Then on Sunday, Cape Town hosts a marathon.
    Sannan a ranar Lahadi kuma, an yi gasar tsere a Cape Town. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  11. On Saturday, people demonstrate in Sudan's capital, Khartoum, urging the army to take control. But days later counter-protesters turn out in support of the country's transitional government established in 2019.
    A ranar Asabar mutane sun yi zanga-zanga a Khartoum babban birnin Sudan, suna neman sojoji su karɓi iko. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  12. There are also protests on Saturday in the capital of the Democratic Republic of Congo as opposition supporters demand a neutral election commission.
    A ranar Asabar ma an yi ta zanga-zanga a babban birnin Jamhuriyya Dimokradiyyar Congo inda mutane ke neman a samar da hukumar zaɓe mai zaman kanta. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  13. Senegalese fisherman Ibrahim poses with his catch on the coast of Dakar on Tuesday.
    Wani masunci a Senegal Ibrahim yana tsaye dauke da fatsarsa a gabar teku a Dakar ranar Talata. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  14. On Saturday in London, Nigerian painter Ben Enwonwu's The Court of the Oba of Benin goes on view at Sotheby's auction house.
    A ranar Asabar a London, an kafe zanen da wani dan Najeriya Ben Enwonwu ya yi a gidan gwanjon kaya na Sotheby. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  15. Saturday also sees the opening of the Fespaco film festival in Burkina Faso, where a few days later two visitors are caught in the act of taking a selfie...
    A ranar Asabar kuma an yi bikin nuna fina-finai na Fespaco a Burkina Faso , inda kwanaki kadan bayan nan aka kama wasu baƙi biyu suna ɗaukar hoton selfie... --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  16. The pan-African film festival takes place each year in the country, this time coinciding with the opening of the murder trial of much-loved former President Thomas Sankara, seen on this mask, whose 1987 death shocked the continent...
    Bikin nuna fina-finan ya zo daidai da ranar da aka fara sauraron ƙarar kashe tsohon shugaban ƙasar Thomas Sankara, wanda kisansa ya girgiza ƙasar a shekarar 1987. Wata mata ta satakunkumin mai ɗauke da hotonsa. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  17. Three girls pose for the camera in Lomé, Togo, on Wednesday.
    An dauki hoton waɗannan yaran ne a birnin Lomé na Togo a ranar Laraba. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  18. And in Paris on Sunday, people lay a wreath in memory of Algerians murdered by French police 60 years ago whose deaths were then covered up. At least 100 people were killed, some of whom were thrown into the River Seine to drown them.
    a birnin Paris mutane sun yi ta ajiye furanni don tunawa da ƴan ALjeriyan da ƴan sanda Faransa suka kashe hekara 60 fda suka gabata. A kalla mutum 100 aka kashe, inda wasun su aka jefa su a Kogin Seine suka nutse. --bbchausa verticals/pics/2021-10-15

  19. ENGLISH
    HAUSA --bbchausa verticals/pics/2021-10-15