Toggle menu
24K
665
183
158.2K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Talk:scripture

Discussion page of scripture

Then the disciple James read a passage of Scripture that helped all in attendance to discern Jehovah’s will in the matter. —Acts 15:4-17.

Sai almajiri Yaƙub ya karanta aya ta Nassi da ta taimaki dukan waɗanda suka halarta su fahimci nufin Jehovah a batun.—Ayukan Manzanni 15:4-17.



Instead of simply presenting the latest issue of The Watchtower, the brother decided to read a scripture found in that issue.

Amma maimakon ya ba shi mujallun kawai, sai ya karanta wani nassin da ke cikin Hasumiyar Tsaron da ya kawo masa.



Many of the lyrics of our songs are tied to passages of Scripture, so learning the words of at least some of the songs can be an excellent way to sound down the truth into our hearts.

Kalmomin waƙoƙinmu da yawa suna da jigon Nassi, saboda hakan koyon kalmomin wasu cikin waƙoƙin zai iya kasance hanya mai kyau na sa gaskiya ta kasance a zukatan mutane.



Just read the Gospel accounts, and note how often Jesus said “it is written” or in other ways referred to specific passages of Scripture.

Ka karanta labaran Lingila, kuma ka lura ko sau nawa ne Yesu ya ce “an rubuta” ko kuma ya ambaci wasu wurare cikin Nassi.



11 On this subject, perhaps no passage of Scripture is quoted more often than Deuteronomy 6:5-7.

11 Maimaitawar Shari’a 6:5-7 ne ayoyi na Nassosi da ake amfani da su sau da yawa a kan wannan batu.



Unless otherwise indicated, Scripture quotations are from the modern-language New World Translation of the Holy Scriptures —With References.

Sai ko an ba da alama, an ɗauko dukan Nassosi daga Littafi Mai Tsarki ne kuma an yi amfani da haruffan zamani.



Scripture: [Listed on page 2 of the tract]

Nassi: [Waɗanda ke shafi na 2 na warƙar]



Also, since “all Scripture is inspired of God and beneficial,” our study should include “every utterance coming forth through Jehovah’s mouth.”

Tun da “kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani” ne, ya kamata nazarin da muke yi ya ƙunshi “kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.”



So perhaps you can show them the scripture in the Bible at Psalm 83:18.

Wataƙila ka nuna nassi da ke cikin Littafi Mai Tsarki a Zabura 83:18.



1:19) If a scripture is read, follow along in your Bible.

1:19) Idan ya karanta nassi, ka bi da naka Littafi Mai Tsarki.



Initial Call: (2 min. or less) wp16.3 16 —Read a scripture from a mobile device.

Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) wp16.3 shafi na 16.



Unless otherwise indicated, Scripture quotations are from the modern-language New World Translation of the Holy Scriptures —With References.

Sai dai ko an ba da alama, an ɗauko dukan Nassosin da aka yi amfani da su ne daga Littafi Mai Tsarki.



The yeartext for 2013 is drawn from what scripture, and how do you feel that those words will help you?

Daga wace aya ce aka samo jigo na 2013, kuma yaya kake ganin zai taimake ka?



Third Return Visit: (3 min. or less) Choose your own scripture and linking question.

Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi kuma ka yi tambaya don ziyara ta gaba.



“All Scripture is inspired of God.” —2 Timothy 3:16

“Kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne. —2 Timotawus 3:16



“The scripture 2 Corinthians 2:17 always encourages me.

Nassi na 2 Korinthiyawa 2:17 kuma tana ƙarfafa ni.



Worship at the Synagogue The worship program at the synagogue included praise, prayer, the reading of Scripture, as well as teaching and preaching.

Bauta a Cikin Majami’ar Tsarin ayyuka na bauta a majami’ar ya ƙunshi yin waƙoƙin yabo, addu’a, karanta Nassosi, tare da koyarwa da kuma yin wa’azi.



19 Finally, consider the context of our theme scripture: “Wives be in subjection to [your] husbands.”

19 A ƙarshe, ka yi la’akari da nassi na jigonmu: “Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku.”



I then understood the scripture that says: ‘God is not partial, but in every nation the man that fears him and works righteousness is acceptable to him.’ —Acts 10:34-35.

A lokacin ne na fahimci nassin nan da ya ce: ‘Allah ba mai tara ba ne, amma a cikin kowace al’umma wanda yake tsoron sa, yana aika adalci kuma, abin karɓe ne a gare shi.’—Ayyukan Manzanni 10:34-35.



What a cited scripture teaches

Ka yi kalami a kan nassin da ke sakin layin



(Psalm 104:5) That scripture and others assure us that God will neither destroy the earth nor allow it to be destroyed —ever! —Ecclesiastes 1:4; Isaiah 45:18.

(Zabura 104:5) Wannan ayar da kuma wasu ayoyi cikin Littafi Mai Tsarki sun tabbatar mana cewa Allah ba zai halaka doron ƙasa ba kuma ba zai taɓa ƙyale a halaka ta ba!—Mai-Wa’azi 1:4; Ishaya 45:18.



Third Return Visit: (3 min. or less) Choose your own scripture, and offer a study publication.

Komawa Ziyara ta Uku: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka zaɓi nassin da za ka yi amfani da shi, bayan haka, ka ba shi ɗaya daga cikin littattafan da muke nazari da su.



Show the article on the back of the February 1 Watchtower, and consider the first paragraph and the cited scripture.

Ka karanta sa’an nan ka tattauna sakin layi na 2 da 3 na talifin da ke shafi na 12 tare da mutumin.



As you discuss the scripture, keep your Bible open.

Ka bar Littafi Mai Tsarkinka a buɗe yayin da kake bayyana nassin.



After reading a scripture, highlight the words that relate directly to your main point.

Bayan ka karanta nassi, ka ambata kalmomin da suka shafi abin da kuke tattaunawa.