(7 intermediate revisions by the same user not shown) | |||
Line 678: | Line 678: | ||
# Babu laifi a yaba wa mutum a kan aikin da ya yi na alheri, don qarfafa masa gwiwa, idan kuma babu jin tsoron girman kai ya shige shi. | # Babu laifi a yaba wa mutum a kan aikin da ya yi na alheri, don qarfafa masa gwiwa, idan kuma babu jin tsoron girman kai ya shige shi. | ||
# Babu laifi mutum ya yi farin ciki a kan yabonsa da aka yi bisa wani aikin alheri, matuqar ba ya yi ne domin riya ba, kuma bai yarda jiji da kai ya kama shi ba. | # Babu laifi mutum ya yi farin ciki a kan yabonsa da aka yi bisa wani aikin alheri, matuqar ba ya yi ne domin riya ba, kuma bai yarda jiji da kai ya kama shi ba. | ||
== 189-195 == | |||
# Kuma ga Allah ne mulkin sammai da qasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai. --[[Quran/3/189]]
And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth, and Allah is over all things competent. (189) | # Kuma ga Allah ne mulkin sammai da qasa yake. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai. --[[Quran/3/189]]
And to Allah belongs the dominion of the heavens and the earth, and Allah is over all things competent. (189) | ||
# Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassab'awar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma'abota lafiyayyun hankula. --[[Quran/3/190]]
Indeed, in the creation of the heavens and the earth and the [[alternation]] of the night and the day are signs for those of understanding. (190) | # Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassab'awar dare da rana, tabbas akwai ayoyi ga ma'abota lafiyayyun hankula. --[[Quran/3/190]]
Indeed, in the creation of the heavens and the earth and the [[alternation]] of the night and the day are signs for those of understanding. (190) | ||
Line 685: | Line 685: | ||
# "Ya Ubangijinmu, lalle duk wanda Ka [[shigar]] da shi wuta, to haqiqa Ka [[kunyata]] shi; kuma [[azzalumai]] ba su da mai taimakon su. --[[Quran/3/192]] Our Lord, indeed whoever You [[admit]] to the Fire - You have [[disgraced]] him, and for the [[wrongdoers]] there are no helpers. (192) | # "Ya Ubangijinmu, lalle duk wanda Ka [[shigar]] da shi wuta, to haqiqa Ka [[kunyata]] shi; kuma [[azzalumai]] ba su da mai taimakon su. --[[Quran/3/192]] Our Lord, indeed whoever You [[admit]] to the Fire - You have [[disgraced]] him, and for the [[wrongdoers]] there are no helpers. (192) | ||
# "Ya Ubangijinmu, lalle mu mun ji wani mai kira yana yin kira zuwa imani cewa: "Ku yi imani da Ubangijinku;" sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare mana [[kurakurai|kurakuranmu]], kuma Ka karb'i rayukanmu tare da mutane masu [[ɗa'a]]. --[[Quran/3/193]]
Our Lord, indeed we have heard a caller calling to faith, [saying], 'Believe in your Lord,' and we have believed. Our Lord, so forgive us our sins and remove from us our [[misdeeds]] and cause us to die with the righteous. (193) | # "Ya Ubangijinmu, lalle mu mun ji wani mai kira yana yin kira zuwa imani cewa: "Ku yi imani da Ubangijinku;" sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare mana [[kurakurai|kurakuranmu]], kuma Ka karb'i rayukanmu tare da mutane masu [[ɗa'a]]. --[[Quran/3/193]]
Our Lord, indeed we have heard a caller calling to faith, [saying], 'Believe in your Lord,' and we have believed. Our Lord, so forgive us our sins and remove from us our [[misdeeds]] and cause us to die with the righteous. (193) | ||
# | #"Ya Ubangijinmu, kuma Ka ba mu abin da Ka yi mana alqawari da shi ta harshen manzanninka, kuma kada Ka [[kunyatar]] da mu ranar alqiyama. Lalle Kai ba Ka sab'a alqawari." --[[Quran/3/194]] Our Lord, and grant us what You promised us through Your messengers and do not [[disgrace]] us on the Day of Resurrection. Indeed, You do not fail in [Your] promise." (194) | ||
#Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): "Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaqi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu krakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Wannan lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake." --[[Quran/3/195]] | |||
=== Tafsiri: === | |||
A cikin wadannan ayoyi Allah swt yana bayyana cewa, shi kadai ne mai mulkin sammai da qasa da abin da yake cikinsu, kuma shi ne mai cikakken iko a kan komai. Sannan ya sanar da cewa, a cikin halittar sammai da qasa da abubuwan da suka qunsa da cancanzawar dare da rana, wannan ya zo, wannan ya tafi, lalle akwai manya-manyan ayoyi da dalilai ga masu lafiyayyen hankali, da suke tabbatar da samuwar Mahalicci da siffofinsa. Wadannan kuwa su ne masu ambaton Allah koyaushe, a cikin kowane yanayi, a tsaye suke ko a zaune ko a kwance. Suna tunani game da halittar sammai da qasa, suna cewa: "Ya Ubangijinmu, mun yi imani ba ka yi wannan halittar a banza ba; ka tsarkaka daga yin wannan, don haka ka tsare mu daga da shi, kuma azzalumai ba su da masu taimaka musu." Suka ci gaba da cewa: "Ya Ubangijinmu, mun ji Annabinka yana kira zuwa ga yin imani da kai, kuma mun amsa kiransa, mun yi imani, don haka ka gafarta mana laifukanmu, kuma ka kankare mana munanan ayyukanmu, kuma ka karb'i rayukanmu tare da mutanen kirki. Ya kyakkyawan sakamako ka zartar da shi, kada kuma ka kunyata mu a ranar alqiyama a gaban halittunka; lalle mun tabbatar ba ka sab'a alqawari." | |||
Sai ko Allah swt ya bayyana cewa, ya karb'i wannan roqo nasu, kuma ya yi alqawarin ba zai tab'a tozarta aikin mai aiki ba, namiji ne shi ko mace ce. Don haka wadanda suka baro garuruwansu na kafirci ko kuma kafirai suka koro su, aka cutar da su saboda sun riqe gaskiya, sun yi imani da Allah da Manzonsa, suka kuma yi yaqi don Allah, kuma aka kashe su, to wadannan Allah zai kankare musu laifukansu, kuma zai saka su gidajen Aljanna, wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu; wannan babban sakamako ne a gare su, saboda qoqarin da suka yi na aikin alheri a duniya. Allah shi ne mai kyakkyawan sakamako ga duk wanda ya yi aikin qwarai; zai saka masa da abin da ido bai tab'a gani ba, kunne bai tab'a ji ba, zuciyar wani d'an Adam ba ta tab'a tunaninsa ba. | |||
An karbo daga Abdullahi d'an Abbas rA ya ce: Wani dare na kwana a d'akin Maimuna uwar muminai. kuma a ranar Annabi SAW yana d'akinta, domin in ga yadda yake sallarsa ta dare. Annabi SAW ya yi hira da iyalinsa na wani d'an lokaci, sannan ya kwanta ya yi barci. A sulusin qarshe na dare, sai ya tashi zaune, ya d'aga kai sama, sai ya karanta wannan aya (ta Quran/3/190), sannan ya tashi ya yi alwala, ya yi asiwaki, sannan ya yi salla raka'a goma sha d'aya, sannan Bilal ya kira sallar Asuba. Sai Annabi SAW ya sallaci raka'a biyu, sannan ya fita ya jagoranci sallar Asuba. [Bukhari #7452]. | |||
Narrated Ibn `Abbas: Once I stayed overnight at the house of (my aunt ) Maimuna while the Prophet (ﷺ) was with her, to see how was the night prayer of Allah's Apostle Allah's Messenger (ﷺ) talked to his wife for a while and then slept. When it was the last third of the night (or part of it), the Prophet (ﷺ) got up and looked towards the sky and recited the Verse:-- 'Verily! In the creation of the Heavens and the Earth....there are indeed signs for the men of understanding.' (3.190) Then He got up and performed the ablution, brushed his teeth and offered eleven rak`at. Then Bilal pronounced the Adhan whereupon the Prophet (ﷺ) offered a two-rak`at (Sunna) prayer and went out to lead the people in Fajr (morning compulsory congregational prayer. https://sunnah.com/bukhari:7452 | |||
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Kira zuwa ga yin tunani game da halittar sammai da qasa, saboda abubuwan da suka qunsa na manyan dalilai masu tabbatar da Ɗayantakar Allah da cancantar a bauta masa shi kad'ai. | |||
#Tunani da duba cikin halittar sammai da qasa yana qara wa bawa imani da yaqini. | |||
#Duk sa'adda mutum ya zama mai zurfin hankali, to saninsa ga Allah da ayoyinsa za su qara hab'aka. | |||
#Halaccin yin tawassuli da siffofin Allah da ayyuka na qwarai, kamar imani da Allah da Manzonsa SAW. | |||
#Yana daga cikin ladubban addu'a, mutum ya yawaita yabo da kirari ga Allah Ta'ala. | |||
#Babu wani bambanci tsakanin namiji da mace wajen sakamakin ayyukan ibada da kusanci zuwa ga Allah. Duk wanda ya yi aiki na gari, Allah zai yi masa sakayya da kyakkyawan sakamako, ba tare da la'akari da bambancin jinsi ba. | |||
== 196-200 == | |||
# Kada zirga-zirgar kafirai a cikin qasa ta rud'e ka. --[[Quran/3/196]]
Be not deceived by the [uninhibited] movement of the disbelievers throughout the land. (196) | |||
# Wani d'an [[jin dad'i]] ne ƙanƙani, sannan makomarsu Jahannama. Kuma tir da wannan shifid'ar. --[[Quran/3/197]]
[It is but] a small [[enjoyment]]; then their [final] refuge is Hell, and wretched is the resting place. (197) | |||
# Amma wadanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan gara ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mfai alheri ga masu biyayya. --[[Quran/3/198]] | |||
# Kuma lalle a cikin Ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar musu, suna masu jin tsoron Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani d'an farashi qanqani. Wadannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne. --[[Quran/3/199]] | |||
# Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi hakuri, kuma ku jure matuqa ga yin hakuri, kuma ku tsare iyakokin qasa, kuma ku tsoraci Allah ko kwa sami [[rabauta]]. --[[Quran/3/200]] | |||
Tafsiri: | |||
A wadannan ayoyi Allah swt yana yi wa Annabinsa SAW kashedi da rudawa da kai-komon kafirai a duniya da tinqahon da suke yi da bunqasar harkar kasuwanci da qarfin tattalin arziki da qarfin sojoji. Duk wadannan wani dan taqaitaccen jin dadi ne; nan da nan zai qare, sannan daga qarshe wutar jahannama ce makomarsu tir kuwa da irin wannan makoma. | |||
To amma masu bin dokokin Ubangijinsu ta hanyar aikata abin da ya wajabta musu da barin abin da ya haramta musu; to an tanadar musu gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuma su zauna cikinsu har abada. Wannan wata liyafa ce Allah ya shirya musu. Don haka abin da yake wurin Allah na kyakkyawan sakamako ga wadanda suka bi shi, ya fi alheri fiye da wani d'an gajeren jin dad'i na duniya. | |||
Sannan Allah swt ya bayyana cewa, a cikin Ma'abota Littafi akwai wadanda sun yi imani da Allah, suna kad'aita shi da bauta, kuma sun yi imani da Manzonsa da Alqur'anin da aka saukar masa da kuma littattafan da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah, ba sa canza abin da yake cikin littattafansu, ba sa kuma b'oye gaskiyar da take ciki, domin samun d'an wani taqaitaccen jin dad'i na duniya; to wadannan suna da babban sakamako a wurin Allah swt. Lalle kuma Allah mai gaggawar sakamako ne. | |||
An karb'o daga Anas d'an Malik rA ya ce: Lokacin da labarin rasuwar Najjashiy ta zo mana, Annabi SAW ya ce mana: "Ku yi masa salla." Sai Allah ya saukar da fad'arsa: "Kuma lalle cikin ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suka yi imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah." | |||
It was narrated from Anas bin Malik (may Allah be pleased with him) that: When the news of the death of Najjashi reached us, the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said to us: "Pray for him." Then Allah revealed: "And among the People of the Book are those who believe in Allah and what has been revealed to you and what has been revealed to them, and they humble themselves before Allah." [https://sunnah.com/bukhari:1327 See also: https://sunnah.com/bukhari:1327] | |||
Sai kuma Allah swt ya umarci bayinsa muminai da yin haquri da kuma dauriya a kan rinjayar maqiya addinin Allah, su jajirce har su ma su sami nasara a kan maqiyansu kuma su tsare kan iyakokin da ake tsoron shigowar maqiya daga gare su, sannan su kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da barin haninsa; da wannan ne za su sami rabauta duniya da lahira. | |||
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Hani ga Musulmi da kar ya rud'u da irin ni'ima da jin dad'i da kafirai suke mora; wannan d'an wani abu ne qanqani, kuma mai gushewa da gaggawa. | |||
# Samun arziki da jin dad'in duniya ba shi yake nuna yardar Allah da soyayyarsa ga wanda ya wwa baiwar ba. Ma'aunin yarda da soyayyar Allah ita ce yi wa Allah da Manzonsa SAW d'a'a. | |||
# Babu wata hanyar samun rabo daga Allah, sai ta yin haquri da juriya da jajircewa da kuma biyayya ga Allah da taimakon addininsa. | |||
# Addinin Musulunci ya tattara ne a kan abubuwa guda uku: | |||
## Aikata abin da aka yi umarni da shi | |||
## da barin abin da aka hana | |||
## da kuma haquri a kan abin da Allah ya qaddara faruwarsa. | |||
pg491 | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |