(One intermediate revision by the same user not shown) | |||
Line 711: | Line 711: | ||
# Amma wadanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan gara ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mfai alheri ga masu biyayya. --[[Quran/3/198]] | # Amma wadanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan gara ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mfai alheri ga masu biyayya. --[[Quran/3/198]] | ||
# Kuma lalle a cikin Ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar musu, suna masu jin tsoron Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani d'an farashi qanqani. Wadannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne. --[[Quran/3/199]] | # Kuma lalle a cikin Ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar musu, suna masu jin tsoron Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani d'an farashi qanqani. Wadannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne. --[[Quran/3/199]] | ||
# Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi hakuri, kuma ku jure matuqa ga yin hakuri, kuma ku tsare iyakokin qasa, kuma ku tsoraci Allah ko kwa sami rabauta. --[[Quran/3/200]] | # Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi hakuri, kuma ku jure matuqa ga yin hakuri, kuma ku tsare iyakokin qasa, kuma ku tsoraci Allah ko kwa sami [[rabauta]]. --[[Quran/3/200]] | ||
Tafsiri: | Tafsiri: | ||
A wadannan ayoyi Allah swt yana yi wa Annabinsa SAW kashedi da rudawa da kai-komon kafirai a duniya da tinqahon da suke | A wadannan ayoyi Allah swt yana yi wa Annabinsa SAW kashedi da rudawa da kai-komon kafirai a duniya da tinqahon da suke yi da bunqasar harkar kasuwanci da qarfin tattalin arziki da qarfin sojoji. Duk wadannan wani dan taqaitaccen jin dadi ne; nan da nan zai qare, sannan daga qarshe wutar jahannama ce makomarsu tir kuwa da irin wannan makoma. | ||
To amma masu bin dokokin Ubangijinsu ta hanyar aikata abin da ya wajabta musu da barin abin da ya haramta musu; to an tanadar musu gidajen Aljanna wadanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, kuma su zauna cikinsu har abada. Wannan wata liyafa ce Allah ya shirya musu. Don haka abin da yake wurin Allah na kyakkyawan sakamako ga wadanda suka bi shi, ya fi alheri fiye da wani d'an gajeren jin dad'i na duniya. | |||
Sannan Allah swt ya bayyana cewa, a cikin Ma'abota Littafi akwai wadanda sun yi imani da Allah, suna kad'aita shi da bauta, kuma sun yi imani da Manzonsa da Alqur'anin da aka saukar masa da kuma littattafan da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah, ba sa canza abin da yake cikin littattafansu, ba sa kuma b'oye gaskiyar da take ciki, domin samun d'an wani taqaitaccen jin dad'i na duniya; to wadannan suna da babban sakamako a wurin Allah swt. Lalle kuma Allah mai gaggawar sakamako ne. | |||
An karb'o daga Anas d'an Malik rA ya ce: Lokacin da labarin rasuwar Najjashiy ta zo mana, Annabi SAW ya ce mana: "Ku yi masa salla." Sai Allah ya saukar da fad'arsa: "Kuma lalle cikin ma'abota Littafi, tabbas akwai wadanda suka yi imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kansu ga Allah." | |||
It was narrated from Anas bin Malik (may Allah be pleased with him) that: When the news of the death of Najjashi reached us, the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said to us: "Pray for him." Then Allah revealed: "And among the People of the Book are those who believe in Allah and what has been revealed to you and what has been revealed to them, and they humble themselves before Allah." [https://sunnah.com/bukhari:1327 See also: https://sunnah.com/bukhari:1327] | |||
Sai kuma Allah swt ya umarci bayinsa muminai da yin haquri da kuma dauriya a kan rinjayar maqiya addinin Allah, su jajirce har su ma su sami nasara a kan maqiyansu kuma su tsare kan iyakokin da ake tsoron shigowar maqiya daga gare su, sannan su kiyaye dokokin Allah, ta hanyar aikata umarninsa da barin haninsa; da wannan ne za su sami rabauta duniya da lahira. | |||
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Hani ga Musulmi da kar ya rud'u da irin ni'ima da jin dad'i da kafirai suke mora; wannan d'an wani abu ne qanqani, kuma mai gushewa da gaggawa. | |||
# Samun arziki da jin dad'in duniya ba shi yake nuna yardar Allah da soyayyarsa ga wanda ya wwa baiwar ba. Ma'aunin yarda da soyayyar Allah ita ce yi wa Allah da Manzonsa SAW d'a'a. | |||
# Babu wata hanyar samun rabo daga Allah, sai ta yin haquri da juriya da jajircewa da kuma biyayya ga Allah da taimakon addininsa. | |||
# Addinin Musulunci ya tattara ne a kan abubuwa guda uku: | |||
## Aikata abin da aka yi umarni da shi | |||
## da barin abin da aka hana | |||
## da kuma haquri a kan abin da Allah ya qaddara faruwarsa. | |||
pg491 | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |