No edit summary |
|||
(19 intermediate revisions by the same user not shown) | |||
Line 443: | Line 443: | ||
Tafsiri: | Tafsiri: | ||
A wadannan ayoyi, Allah yana sanar da Manzonsa SAW cewa, ya umarci mala'iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (AS), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu sajjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa'u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci 'ya'yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da Allah ya [[gindaya]] musu. | ==== 📘 Sheikh Abubakar Mahmud Gumi: ==== | ||
<blockquote>Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriya ta, to babu tsoro a kansu, kuma ba su yi baƙin ciki."</blockquote> | |||
==== 📗 Dr. Aliyu Kamal Junaidu: ==== | |||
<blockquote>Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriyarTa, babu tsoro a kansu, kuma ba su yi baƙin ciki."</blockquote> | |||
==== 📕 Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo: ==== | |||
<blockquote>Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriyarTa, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba." | |||
version 2 | |||
Muka ce: "Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan '''idan wata shiriya ta zo muku, to wadanda suka bi shiriyata, babu wani tsoro a tare da su, kuma ba za su yi [[baƙin ciki]] ba. --[[Quran/2/38]]'''</blockquote>A wadannan ayoyi, Allah yana sanar da Manzonsa SAW cewa, ya umarci mala'iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (AS), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu sajjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa'u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci 'ya'yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da Allah ya [[gindaya]] musu. | |||
Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci 'ya'yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu. | Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci 'ya'yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu. | ||
Line 814: | Line 825: | ||
# Idan aka ce da su: "Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar", sai su ce: "Mu muna yin imani ne da abin da aka saukar mana". Kuma suna kafircewa da duk wani abu da ba shi ba, alhalin shi gaskiya ne, kuma mai gaskata abin da ke tare da su ne. To ka ce: "Me ya sa a da kuke kashe annabawan Allah idan kun kasance muminai?" --[[Quran/2/91]] | # Idan aka ce da su: "Ku yi imani da abin da Allah Ya saukar", sai su ce: "Mu muna yin imani ne da abin da aka saukar mana". Kuma suna kafircewa da duk wani abu da ba shi ba, alhalin shi gaskiya ne, kuma mai gaskata abin da ke tare da su ne. To ka ce: "Me ya sa a da kuke kashe annabawan Allah idan kun kasance muminai?" --[[Quran/2/91]] | ||
# Hakika | # Hakika Musa ya zo muka da hujjoji bayyanannu, sannan kuka bauta wa dan maraƙi bayansa alhalin kuna azzalumai. --[[Quran/2/92]] | ||
# Kuma ku tuna lokacin da Muka dauki alkawari da ku, Muka kuma daga dutsen Ɗuri a kanku, Muka ce: "Ku riƙi abin da muka ba ku da karfi, kuma ku saurara". Sai suka ce: "Mun ji kuma mun saɓa". Kuma aka sanya musu tsananin son bautar dan maraƙi a zukatansu saboda kafircinsu. Ka ce: "Tir da abin da imaninku yake umartar ku da shi, idan har kun kasance muminai." --[[Quran/2/93]] | |||
Tafsiri: | |||
A nan Allah SWT ya bayyana mana yadda Banu Isra'ila suke iqrarin cewa, su sun yi imani ne da Attaura kawai, kuma ta wadatar da su, ba sa bukatar sai sun yi imani da Alkur'ani. To shi ne a nan Allah yake karyata su, yana bayyana cewa, hatta ita ma Attaurar ba wani cikakken imani suka yi da ita ba. Duk da cewa shi Alkur'ani Allah ya saukar da shi ne bayan Attaura, kuma yana gaskata abin da yake cikin Attaura na Tauhidi da rukunnan imani. Wannan magana tasu tubka da warwara ce, domin duk wanda ya karyata Alkur'ani, to ya karyata sauran littattafan ma gaba daya. | |||
Sannan sai Allah ya umarci Annabinsa Muhammad SAW da ya tambaye su, idan har da gaske suke sun yi imani da Attaura, me ya sa suke kashe annabawan Allah wadanda su ma suna gaskata abin da yake cikinta? Kuma a cikin Attaura an haramta kashe kowane Annabi. | |||
A karshe sai Allah ya nuna a fili cewa, karya suke yi, ba su yi imani da Attaurar ba, domin tun farko da Annabi Musa ya zo musu da hujjoji bayyanannu masu tabbatar da gaskiyar annabcinsa, sai suka koma suna bautar dan maraqi lokacin da ya tafi ganawa da Ubangijinsa saboda qetare iyaka da zalunci. | |||
Sannan Allah SWT ya sake tuna wa Banu Isra'ila labarin lokacin da ya dauki alkawarin mai karfi a wurinsu, har ya daga dutsen D'uri a samansu, kamar ya rufto ya fado musu, domin a tsoratasu a kan dole su yi aiki da umarnin da aka ba su na cewa lalle su rike Attaura gamgam da himma da nashadi, kuma su saurari maganar Allah, sauraro na karba da mika wuya, amma sai suka amsa wa Allah SWT da cewa, sun ji da kunnuwansu, amma kuma sun sab'a da ayyukansu. Son bautar dan maraqi ya riga ya ratsa zukatansu, sun kwankwad'e shi da gaske, kamar yadda mai jin qishirwa yake kwankwad'ar ruwa idan ya samu, har ya ratsa ko'ina a jikinsa. | |||
Bayanan da suka gabata sun tabbatar da cewa, imanin Yahudawa na jabu ne, tun da bai hana su kashe annabawan Allah ba, bai hana su bautar dan maraqi ba, bai kuma hana su bijire wa umarnin Ubangijinsu ba. Don haka sai Allah ya yi tir da wannan imani nasu, ya tabbatar da cewa, imani na qwarai shi yake sanya mai shi ya aikata alheri ya kuma kauce wa sharri. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Qaryar Yahudu wajen da'awar sun yi imani da Attaura, alhalin suna sab'a mata a fili da ayyukansu. | |||
# Wajibi ne ga mumini ya karbi shari'ar Allah da karfi da nishadi, ba da kasala ba. | |||
# Wajibi ne mutum ya karbi gaskiya daga bakin duk wanda ya fad'e ta. | |||
== Baqara 94-96 == | |||
# Ka ce: "Idan gidan lahira ya kasance kebantacce a gare ku a wurin Allah ku kadai ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa idan har ku masu gaskiya ne." --[[Quran/2/94]] | |||
# Ba za su tab'a burin mutuwa ba har abada, saboda abin da hannayensu suka aikata. Kuma Allah Masani ne ga azzalumai. --[[Quran/2/95]] | |||
# Kuma za ka same su sun fi kowa kwad'ayin tsawon rai, fiye ma da wadanda suka yi shirka. Kowane d'ayansu yana burin ina ma za a raya shi shekara dubu. Kuma Allah Mai ganin abin da suka kasance suna aikatawa ne. --[[Quran/2/96]] | |||
Tafsiri: | |||
A nan Allah yana fada wa Annabinsa cewa, idan Yahudawan Madina suna da'awar cewa, don su kadai Allah (SWT) ya tanadi ni'imar gidan Aljanna a lahira, ban da sauran mutane, to ga wata hanya da za a bi a gane mai gaskiya, ita ce su hadu su yi addu'ar tsinuwa, wato su roqi Allah ya halaka maqaryaci daga cikinsu. Allah SWT ya nuna cewa, sam-sam Yahudawa ba za su tab'a karb'ar wannan kira nasa ba, saboda suna sane da irin laifuffukan da suka tabka na kafirce wa Annabi da boye gaskiya, kuma suna sane da cewa hanyar haduwa da mummunan sakamakon miyagun ayyukansu ita ce mutuwa; da zarar sun mutu, to sun fada cikin abin qi ke nan har abada. Wannan kadai ya isa ya hana su son mutuwa. To amma fa kada su manta da cewa, Allah yana sane da duk wani azzalimi mai keta dokarsa a bayan qasa, kuma komai dadewa sai Allah ya damqe shi ya nuna masa sakamakonsa. | |||
Daga nan sai Allah ya tabbatar da cewa, ai babu wani jinsi na mutane da yake gudun mutuwa irin jinsin Bayahude, domin ya san abin da yake jiran sa a lahira na azaba, don haka za ka ga kowane dayansu yana son ya yi tsawon rai a duniya, ta yadda soyayyarsu da rayuwa a nan duniya, har ta zarce ta mushrikai wadanda ma ba su yi imani da akwai ranar lahira ba, ballantana har su yarda da cewa akwai wani sakamako da zai biyo baya. Ai shi Bayahude burinsa shi ne ya rayu shekara dubu a duniya, to amma ya manta cewa, ko da an ba shi tsawon rai irin wannan, ba zai hana shi mutuwa ba, kuma da zarar ya mutu wuta ce makomarsa. Allah kuma yana ganin duk abin da suke aikatawa na miyagun ayyuka, ba abin da yake buya a gare shi kuma zai yi musu sakayya a kansu daya bayan daya. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Tsawon rai idan ya kasance cikin sab'on Allah ne, to ba shi da wani amfani ga mutum. Don haka ka roka wa wanda kake kauna jinkiri mai amfani, kamar yadda ya zo cikin addu'o'in da Annabi SAW ya koyar da al'ummarsa: | |||
#* "Ya Allah ka raya ni matukar rayuwa ce mafi alheri a gare ni, ka kuma karbi raina idan mutuwar ce ta fi alheri a gare ni." | |||
#* "O Allah! Keep me alive as long as life is better for me, and let me die if death is better for me.' " [[https://sunnah.com/bukhari:5671 Bukhari #5671] da Muslim #2680] | |||
# Yahudawa sun fi kowa son rayuwa a duniya, saboda yadda suka fitar da qauna daga ni'imar lahira. | |||
# Allah ya nuna mana su Yahudawa da masu halaye irin nasu, suna sha'awar rayuwar duniya ce ko ma wace iri, kuma ba ruwansu da kyanta ko rashin kyanta, sabanin Musulmi; shi yakan yin fatan rayuwa ce mai albarka a gare shi da al'ummarsa. | |||
== Baqara 97-101 == | |||
# Ka ce: "Duk wanda ya kasance maqiyi ne ga Mala'ika Jibrilu, to lalle shi ne ya saukar da shi (Alkur'ani) a kan zuciyarka da izinin Allah yana mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma shiriya ne da bushara ga muminai." --[[Quran/2/97]] | |||
# Duk wanda ya kasance maqiyi ne ga Allah da mala'ikunsa da manzanninsa da Jibrilu da Mika'ilu, to lalle Allah maqiyin kafirai ne. --[[Quran/2/98]] | |||
# Kuma haqiqa Mun saukar maka da ayoyi bayyanannu, babu kuma mai kafirce musu sai fasiqai. --[[Quran/2/99]] | |||
# Yanzu ashe duk sa'adda suka qulla wani alqawari sai wani b'angare daga cikinsu ya yi watsi da shi?! Bari! Yawancinsu ba sa yin imani. --[[Quran/2/100]] | |||
# Yayin da wani manzo daga Allah ya zo musu yana mai gaskata abin da yake tare da su (na Littafin Attaura), sai wani b'angare daga cikinsu suka jefar da littafin Allah a bayansu kamar ba su san komai ba. --[[Quran/2/101]] | |||
Tafsiri: | |||
Imamut Tirmizi #3117 da Imam Ahmad #2483 sun ruwaito hadisi daga Abdullahi dan Abbas rA ya ce: "Yahudawa sun zo wurin Manzon Allah SAW suka ce masa: "Ya Baban Alqasim, mun zo ne mu yi maka tambaya a kan abubuwa guda biyar, idan ka ba mu amsarsu, to mun fahinci kai Annabi ne, kuma za mu bi ka. Sai Annabi SAW ya kafa musu shaida da Allah, kamar yadda Annabi Yakubu AS ya yi da 'ya'yansa, lokacin da suka ce: "Allah ne wakili bisa duk abin da za mu fada." Sai Annabi SAW ya ce: "To ku yi tambayoyinku." Sai suka ce: "Ka fada mana mece ce alamar annabi?" Sai ya ce: "Alamarsa ita ce, idanuwansa za su yi barci, amma zuciyarsa ba za ta yi ba." Sai suka ce: "To ka fada mana mene ne ya sa mace wani lokaci ta haifi 'ya mace, wani lokaci kuma ta haifi ɗa namiji?" Sai ya ce: "Idan ruwan 'ya mace ya rinjayi ruwan ɗa namiji, to sai ta haifi 'ya mace, idan kuwa namijin ne ya rinjayi na matar , sai ta haifi ɗa namiji." Sai suka ce: "To faɗa mana, wane irin abinci ne Isra'ilu (Ya'aƙub) ya haramta wa kansa?" Sai ya ce: "Ya yi fama da cutar ciwon kwankwaso da kafafu (Sciatica), bai samu wani magani da ya yi masa amfani ba, sai nonon abu kaza da abu kaza. (Imam Ahmad ya ce wasu sun ce nonon rakumi ne ya samu). Daga lokacin sai ya haramta wa kansa cin namansu." Sai suka ce: "Ka yi gaskiya." | |||
Sannan kuma su ka ce: "To fada mana mene ne wannan tsawar da muke ji?" Sai ya ce: "Wannan mala'ika ne da Allah ya wakilta shi don ya kula da girgije, yana dauke da wani takobi na wuta a hannunsa, yana kora wannan girgije da shi har zuwa inda Allah ya umarce shi." Sai suka ce: "To, shi kuma wannan karar da ake ji ta mece ce?" Sai ya ce: "Muryarsa (Mala'ikan) ce." Sai suka ce, "Ka yi gaskiya." | |||
Sannan kuma suka ce masa: "To yanzu saura tambaya daya ta rage, idan ka amsa mana ita, to za mu yi maka mubaya'a, domin babu wani annabi face yana da wani mala'ika da yake kawo masa labarai. To ka fada mana kai wane ne mala'ikanka?" Sai ya ce: "Jibrilu ne (AS)." Cikin mamaki, sai suka ce: "Jibrilu? Ai wannan shi ne wanda yake saukowa da yaqi da kashe-kashe da azaba, ai wannan maqiyinmu ne! Da dai ka ce mana mala'ika ne wanda yake saukar da rahama da tsaro da ruwan sama, da abin ya yi kyau." Sai Allah SWT ya saukar da wadannan ayoyi (watau aya 97-99). | |||
Allah ya ce wa Annabinsa SAW ya fada wa wadannan Yahudawa cewa, duk wanda yake gaba da Mala'ika Jibrilu, to ya sani cewa, shi Jibrilu yana saukar wa Annabi Alqur'ani ne da umarnin Allah, ba a gaban kansa yake yi ba, don haka ba shi suke nuna wa qiyayya ba, Allah ne da ya aiko shi suke nuna wa kiyayya. Sannan kuma Alkur'ani da yake saukar masa, koyarwar cikinsa tana daidai da abin da ya zo a littattafan annabawan da suka gabace shi, kamar Attaura. Wannan kuwa babban dalili ne da yake nuna gaskiyarsa, sannan shi Alkur'ani babbar bushara ce ga muminai ta irin abin da Allah ya tanadar musu na ni'ima mai d'orewar. | |||
Sannan Allah ya ci gaba da fada musu cewa, duk wanda yake qin Allah ko yake qin wani mala'ika, ko Mala'ika Jibrilu, Mika'ilu ko yake gaba da wani manzo daga cikin manzannin Allah, to wannan kafiri ne, kuma Allah zai dauke shi a matsayin abokin gabarsa, domin Allah ba ya son kowane irin kafiri. Shi ya sa ya zo a hadisi qudsi inda Allah yake cewa: "Duk wanda ya yi gaba da wani masoyina, to lalle ina yi masa shelar yaqi." [Bukhari #6502] | |||
Abdurrahman dan Abu Laila ya ruwaito cewa, wani Bayahude ya gamu da Sayyidina Umar AS sai ya ce masa: "Jibrilun nan da Annabinku yake ta fada fa makiyinmu ne." Sai Umar AS ya mayar masa da martani da cewa: "Wanda duk ya kasance maqiyin Allah da mala'ikunsa da manzanninsa... (har zuwa qarshen ayar)." Ya ce: "Sai wannan ayar ta sauka." [Duba Tafsirin Ibnu Abi Hatim 1:182, da Fathul Bari na Ibnu Hajar 8:16]. | |||
Sannan Allah ya ci gaba da fada wa Annabinsa cewa, ya saukar masa da ayoyi bayyanannu, masu nuna gaskiyar annabcinsa, babu wanda yake ja da su sai wanda ba mumini ba. Allah kuma ya fada masa cewa, Yahudawa wasu mutane ne marasa alqawari; duk sa'adda suka d'aukar wa Allah alkawarin za su yi aiki da Attaura da abin da ta qunsa na shari'a, to sai an samu wasu daga cikinsu sun warware alkawarin nan sun yi jifa da shi, ba komai ya jawo haka ba, sai domin yawancinsu ba masu imani ba ne, domin da suna da imani na gaskiya, to da sun kiyaye alkawari, ba su karya shi ba. | |||
Daga cikin ire-iren karya alkawarin da suka yi shi ne, lokacin da Allah ya aiko Annabinsa SAW ya zo kuma kamar yadda Allah ya siffanta musu shi a cikin littattafansu, kuma ya yi alkawari da su a kan za su bi shi idan ya bayyana, to sai ga shi yanzu yawancinsu sun yi watsi da wannan alkawarin, sun yi jifa da littafin Attaura can bayansu, kamar ba su tab'a sanin wani abu ba dangane da wannan Annabi da siffofinsa. | |||
== Baqara 102-103 == | |||
# Sai suka bi abin da sheɗanu suke karantawa a (zamani) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai sheɗanun su ne suka kafirta suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala'iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun faɗa masa cewa: "Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta." Sai (mutane) suka riƙa koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da she. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma haƙiƙa sun san cewa, duk wanda ya zaɓi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (haƙiƙanin makomarsu). --[[Quran/2/102]] | |||
# Da a ce su sun yi imani kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa da sakamakon (da za su samu) daga Allah shi ne mafi alheri, da a ce sun sani. --[[Quran/2/103]] | |||
Tafsiri: | |||
A nan Allah ya ci gaba da ba da labarin halin da Yahudawa suka tsinci kansu a ciki, bayan sun yi watsi da littafin Allah da [[koyarwar]] annabawansu, sai suka rungumi koyarwar shaidanu a madadin haka, wanda sakamakon haka shi ne duk wanda ya bar koyarwar annabawa da ilimi mai amfani, to lalle a madadinsa sai ya rungumi wani ilimi marar kyau mai cutarwa. | |||
pg108 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |