Toggle menu
24K
663
183
158.1K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/2/Rijayar Lemo Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
 
(10 intermediate revisions by the same user not shown)
Line 443: Line 443:
Tafsiri:
Tafsiri:


A wadannan ayoyi, Allah yana sanar da Manzonsa SAW cewa, ya umarci mala'iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (AS), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu sajjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa'u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci 'ya'yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da Allah ya [[gindaya]] musu.  
==== 📘 Sheikh Abubakar Mahmud Gumi: ====
<blockquote>Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriya ta, to babu tsoro a kansu, kuma ba su yi baƙin ciki."</blockquote>
 
==== 📗 Dr. Aliyu Kamal Junaidu: ====
<blockquote>Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriyarTa, babu tsoro a kansu, kuma ba su yi baƙin ciki."</blockquote>
 
==== 📕 Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo: ====
<blockquote>Mun ce: "Ku sauka daga gare ta gaba ɗaya. To idan wata shiriya ta zo muku daga wurina, to wanda ya bi shiriyarTa, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba."
 
version 2
 
Muka ce: "Dukkanku ku sauko daga cikinta, sannan '''idan wata shiriya ta zo muku, to wadanda suka bi shiriyata, babu wani tsoro a tare da su, kuma ba za su yi [[baƙin ciki]] ba. --[[Quran/2/38]]'''</blockquote>A wadannan ayoyi, Allah yana sanar da Manzonsa SAW cewa, ya umarci mala'iku da su faɗi su yi sujjada ga Annabi Adamu (AS), kuma nan take suka karɓa umarninsa suka faɗi suka yi masa sujjada, sai Iblis shi kaɗai ya nuna girman kai, ya bijire wa umarnin Allah ya ƙi yi wa Annabi Adamu sajjada. Sai Allah ya umarci Annabi Adamu da matarsa Hawwa'u da su shiga Aljanna su zauna a cikinta, ya yi musu izini da su ci komai na kayan marmari da ke cikinta a wadace, in ban da wata itaciya guda ɗaya wadda ya nuna musu ita ya ce, su nisance ta kada su ci 'ya'yanta domin idan har suka ci to sun ƙetare iyakokin da Allah ya [[gindaya]] musu.  


Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci 'ya'yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu.   
Sai Shaiɗan ya yaudare su ta hanyar yi musu waswasi ya sa suka ci 'ya'yan wannan bishiyar, wanda a dalilin haka Allah ya fitar da su daga gidan Aljanna, ya umarce su da su dawo bayan ƙasa su zauna, wanda a nan ne ƙiyayya za ta bayyana a tsakaninsu, kuma nan ne wurin rayuwarsu, idan kuma sun mutu a cikinta ne za a binne su har zuwa lokacin tashin alƙiyama. Bayan haka kuma sai Allah ya laƙanta wa Annabi Adamu wasu kalmomi da zai faɗa Allah ya yafe masa laifinsa, sai ya faɗa shi da matarsa, kuma Allah ya karɓi tubansu domin shi ne mai yafe wa muminai duk wani laifi da za su yi su nemi ya yafe musu.   
Line 861: Line 872:
Tafsiri:
Tafsiri:


Imamut Tirmizi #3117 da Imam Ahmad #2483 sun ruwaito hadisi daga Abdullahi dan Abbas rA ya ce: "Yahudawa sun zo wurin Manzon Allah SAW suka ce masa: "Ya Baban Alqasim, mun zo ne mu yi maka tambaya a kan abubuwa guda biyar, idan ka ba mu amsarsu, to mun fahinci kai Annabi   
Imamut Tirmizi #3117 da Imam Ahmad #2483 sun ruwaito hadisi daga Abdullahi dan Abbas rA ya ce: "Yahudawa sun zo wurin Manzon Allah SAW suka ce masa: "Ya Baban Alqasim, mun zo ne mu yi maka tambaya a kan abubuwa guda biyar, idan ka ba mu amsarsu, to mun fahinci kai Annabi ne, kuma za mu bi ka. Sai Annabi SAW ya kafa musu shaida da Allah, kamar yadda Annabi Yakubu AS ya yi da 'ya'yansa, lokacin da suka ce: "Allah ne wakili bisa duk abin da za mu fada." Sai Annabi SAW ya ce: "To ku yi tambayoyinku." Sai suka ce: "Ka fada mana mece ce alamar annabi?" Sai ya ce: "Alamarsa ita ce, idanuwansa za su yi barci, amma zuciyarsa ba za ta yi ba." Sai suka ce: "To ka fada mana mene ne ya sa mace wani lokaci ta haifi 'ya mace, wani lokaci kuma ta haifi ɗa namiji?" Sai ya ce: "Idan ruwan 'ya mace ya rinjayi ruwan ɗa namiji, to sai ta haifi 'ya mace, idan kuwa namijin ne ya rinjayi na matar , sai ta haifi ɗa namiji." Sai suka ce: "To faɗa mana, wane irin abinci ne Isra'ilu (Ya'aƙub) ya haramta wa kansa?" Sai ya ce: "Ya yi fama da cutar ciwon kwankwaso da kafafu (Sciatica), bai samu wani magani da ya yi masa amfani ba, sai nonon abu kaza da abu kaza. (Imam Ahmad ya ce wasu sun ce nonon rakumi ne ya samu). Daga lokacin sai ya haramta wa kansa cin namansu." Sai suka ce: "Ka yi gaskiya."  
 
Sannan kuma su ka ce: "To fada mana mene ne wannan tsawar da muke ji?" Sai ya ce: "Wannan mala'ika ne da Allah ya wakilta shi don ya kula da girgije, yana dauke da wani takobi na wuta a hannunsa, yana kora wannan girgije da shi har zuwa inda Allah ya umarce shi." Sai suka ce: "To, shi kuma wannan karar da ake ji ta mece ce?" Sai ya ce: "Muryarsa (Mala'ikan) ce." Sai suka ce, "Ka yi gaskiya."   
 
Sannan kuma suka ce masa: "To yanzu saura tambaya daya ta rage, idan ka amsa mana ita, to za mu yi maka mubaya'a, domin babu wani annabi face yana da wani mala'ika da yake kawo masa labarai. To ka fada mana kai wane ne mala'ikanka?" Sai ya ce: "Jibrilu ne (AS)." Cikin mamaki, sai suka ce: "Jibrilu? Ai wannan shi ne wanda yake saukowa da yaqi da kashe-kashe da azaba, ai wannan maqiyinmu ne! Da dai ka ce mana mala'ika ne wanda yake saukar da rahama da tsaro da ruwan sama, da abin ya yi kyau." Sai Allah SWT ya saukar da wadannan ayoyi (watau aya 97-99).   
 
Allah ya ce wa Annabinsa SAW ya fada wa wadannan Yahudawa cewa, duk wanda yake gaba da Mala'ika Jibrilu, to ya sani cewa, shi Jibrilu yana saukar wa Annabi Alqur'ani ne da umarnin Allah, ba a gaban kansa yake yi ba, don haka ba shi suke nuna wa qiyayya ba, Allah ne da ya aiko shi suke nuna wa kiyayya. Sannan kuma Alkur'ani da yake saukar masa, koyarwar cikinsa tana daidai da abin da ya zo a littattafan annabawan da suka gabace shi, kamar Attaura. Wannan kuwa babban dalili ne da yake nuna gaskiyarsa, sannan shi Alkur'ani babbar bushara ce ga muminai ta irin abin da Allah ya tanadar musu na ni'ima mai d'orewar.   
 
Sannan Allah ya ci gaba da fada musu cewa, duk wanda yake qin Allah ko yake qin wani mala'ika, ko Mala'ika Jibrilu, Mika'ilu ko yake gaba da wani manzo daga cikin manzannin Allah, to wannan kafiri ne, kuma Allah zai dauke shi a matsayin abokin gabarsa, domin Allah ba ya son kowane irin kafiri. Shi ya sa ya zo a hadisi qudsi inda Allah yake cewa: "Duk wanda ya yi gaba da wani masoyina, to lalle ina yi masa shelar yaqi." [Bukhari #6502]   
 
Abdurrahman dan Abu Laila ya ruwaito cewa, wani Bayahude ya gamu da Sayyidina Umar AS sai ya ce masa: "Jibrilun nan da Annabinku yake ta fada fa makiyinmu ne." Sai Umar AS ya mayar masa da martani da cewa: "Wanda duk ya kasance maqiyin Allah da mala'ikunsa da manzanninsa... (har zuwa qarshen ayar)." Ya ce: "Sai wannan ayar ta sauka." [Duba Tafsirin Ibnu Abi Hatim 1:182, da Fathul Bari na Ibnu Hajar 8:16].   
 
Sannan Allah ya ci gaba da fada wa Annabinsa cewa, ya saukar masa da ayoyi bayyanannu, masu nuna gaskiyar annabcinsa, babu wanda yake ja da su sai wanda ba mumini ba. Allah kuma ya fada masa cewa, Yahudawa wasu mutane ne marasa alqawari; duk sa'adda suka d'aukar wa Allah alkawarin za su yi aiki da Attaura da abin da ta qunsa na shari'a, to sai an samu wasu daga cikinsu sun warware alkawarin nan sun yi jifa da shi, ba komai ya jawo haka ba, sai domin yawancinsu ba masu imani ba ne, domin da suna da imani na gaskiya, to da sun kiyaye alkawari, ba su karya shi ba.   
 
Daga cikin ire-iren karya alkawarin da suka yi shi ne, lokacin da Allah ya aiko Annabinsa SAW ya zo kuma kamar yadda Allah ya siffanta musu shi a cikin littattafansu, kuma ya yi alkawari da su a kan za su bi shi idan ya bayyana, to sai ga shi yanzu yawancinsu sun yi watsi da wannan alkawarin, sun yi jifa da littafin Attaura can bayansu, kamar ba su tab'a sanin wani abu ba dangane da wannan Annabi da siffofinsa.   
 
== Baqara 102-103 ==
# Sai suka bi abin da sheɗanu suke karantawa a (zamani) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai sheɗanun su ne suka kafirta suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala'iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun faɗa masa cewa: "Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta." Sai (mutane) suka riƙa koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da she. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma haƙiƙa sun san cewa, duk wanda ya zaɓi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (haƙiƙanin makomarsu). --[[Quran/2/102]]
# Da a ce su sun yi imani kuma sun yi taƙawa, haƙiƙa da sakamakon (da za su samu) daga Allah shi ne mafi alheri, da a ce sun sani. --[[Quran/2/103]]
Tafsiri:
 
A nan Allah ya ci gaba da ba da labarin halin da Yahudawa suka tsinci kansu a ciki, bayan sun yi watsi da littafin Allah da [[koyarwar]] annabawansu, sai suka rungumi koyarwar shaidanu a madadin haka, wanda sakamakon haka shi ne duk wanda ya bar koyarwar annabawa da ilimi mai amfani, to lalle a madadinsa sai ya rungumi wani ilimi marar kyau mai cutarwa. 


pg104
pg108
[[Category:Quran]]
[[Category:Quran]]
[[Category:Quran/2]]
[[Category:Quran/2]]
[[Category:Rijiyar Lemo]]
[[Category:Rijiyar Lemo]]