Toggle menu
24.2K
670
183
158.8K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/26/IRIB Hausa Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
 
Line 3,342: Line 3,342:
[[Category:Quran/26]]
[[Category:Quran/26]]
[[Category:Quran]]
[[Category:Quran]]
[[Category:IRIB_Hausa_Tafsir]]

Latest revision as of 03:48, 19 September 2017

Suratush Shu'ara Aya Ta 1-6 (Kashi Na 649)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




To madallah a yau za mu fara shirin ne da sauraren karatun aya ta 1 zuwa 3 a cikin suratul Shu’ara’i:


طسم


1-Da Sin Mim ,Allah ne Ya san abin da Yake nufi da wannan.

تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْمُبِينِ

2-Wadancan ayoyi ne na littafi mabayyani.


لَعَلَّكَ بَاخِعٌ نَّفْسَكَ أَلاَّ يَكُونُوا مُؤْمِنِينَ

3-Kamar dai za ka kashe kanka don ba su ba da gaskiya ba.

Wannan sura ta Shu’ara’I it ace sura ta 29 daga cikin jerin surorin kur’ani da suka fara da haruffan da babu wani da ya san ma’anarsu sai Allah mai hikima gwani masani.wannan kuma shi ke kara tabbatar da mu’ujizr kur’ani da girman Allah kuma babu wani marubuci da masani da ya san fassarar wadannan haruffa.

Ci gaban ayoyi na fayyace mana girma da daukakar littafin Allah ,littafin da ke rarrabe mana gaskiya da karya, daidai da ba daidai ba kuma wannan lamari ma na nuna mana daukaka da girman kur’ani da mu’ijizarsa.Aya ta uku na fayyace mana kauna gami da damuwa da kuma jan kokarin da manzon Rahama yake yi wajen shiryar da al’umma tafarkin gaskiya. Duk da babaken kalamai da takurawa da kuntatawa da barazana da mushrikai da kafirai key i wa Manzon allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa bai daina ko yin kasa a guiwa daidai da kwayar zarra a wannan kokari da kauna da damuwa ta shiryar da jama’a ba sai ma abin da ya ci gaba. Su mushrikai da kafirai a maimakon su yi imani da kadaita Allah da bauta sai ci gaba suke yi da riko da kafirci da ayyukan bata da nacewa kan haka a aikace da tunaninsu amma Manzon rahama bai daina kiransu zuwa ga tauhidi ba tamkar ransa zai fita.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: haskakawa da samar da mafita na daga cikin abubuwan da Kur’ani ya kebanta da su don haka duk lokacin da wani ya rasa mafita ya ziyarci kur’ani.

Na biyu:Manzonnin Allah (AS) a kullum na damuwa da halin da al’ummominsu ke ciki.kuma suna iyakacin kokarinsu wajen ganin sun kubutar da su da nuna masu hanyar gaskiya da shiriya.

Na uku: Idan mutane ba a shirye suke su karbi gaskiya ba to babu abin da kur’ani da manzo za su iya a kansu.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta hudu a cikin wannan sura ta Shu’ara’i.

إِن نَّشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِم مِّن السَّمَاء آيَةً فَظَلَّتْ أَعْنَاقُهُمْ لَهَا خَاضِعِينَ


4-Da Mun so da sai Mu saukar musu da aya daga sama sai wuyoyinsu su zamo masu Kankan da kai gare ta.

A cikinayar da ta gabata ta yi nuni da yadda manzon Rahama (SWA) yayi ta kokari tamkar ransa zai fita amma kafirai da mushrikai ba a shirye suke ba da su yi imani da abin da ya zo masu da shin a shiriya. Sai wannan ayar ta ci gaba da cewa;Kars u kafirai da mushrikai su yi zaton za su iya tsira daga kudura da hukuncin Allah madaukakin sarki.Saboda Allah ne ya so mutane su yi imani ta hanyar zabi da yardarsu babu tilastawa amma idan da ya so yana da karfi da ikon ya nuna masu karfin ikonsa inda tsoro zai mamaye su da tilasta masu yin imani amma ba zai yi hakan ba.

Daga cikin wannan aya za mu iya ilmantuwa da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Shi imani dole ya zo karkashin zabin mutum ba tilastawa ba. Kuma babu wani da ke da ikon tilastawa wani yin imani .

Na biyu:Wanda suka ki yin imani wata rana za ta zo da za su yi imani a daidai lokacin da guri ya kure da ba a karbar imani a wannan rana.


                    • MUSIC*************

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 5 da 6 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i:


وَمَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّنَ الرَّحْمَنِ مُحْدَثٍ إِلاَّ كَانُوا عَنْهُ مُعْرِضِينَ


5-Kuma ba wani gardi sabo da zai zo musu daga Allah arrahamanu sai sun kasance masu bijire masa.


فَقَدْ كَذَّبُوا فَسَيَأْتِيهِمْ أَنبَاء مَا كَانُوا بِهِ يَسْتَهْزِؤُون

6-To hakika sun karyata ,ba da dadewa ba labarum akibar abin da suke yi wa izgili zai zo musu.

Wadannan ayoyi na bayani ne kan abubuwa da bas u dace ba da Mushrikai da kafiran Makka ke nunawa Manzon Rahama (SAW) da cewa: a duk lokacin da wata aya ta sabka ga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka domin fadakar da su Mushrikai amma a maimakon su fadaka sai su nuna adawa hatta ba a shirye suke bas u saurari ayoyin Allah. Ayoyin da suka zo gada gurin Allah Alrahman ,Allan da rahamarsa ta mamaye duniya baki daya da duk wani abu mai rai da ya hada da mutum kuma rahamarsa ba ta da iyaka.

Mushrikai da zucciyarsu ta toshe da bakar adawa bas u tsaya a nan b aba tare da sun gabatar da wani dalili ba suna karyata ayoyin allah mafi muni ma bayan sun karyata sakon gaskiya da manzo ya zo masu da ita da alkawalin da yay i masu ,suna yi masa izgili a duk lokacin da ya ambaci kiyama,aljanna da wutar azaba da cewa wannan wani mafarki ne da hassahe kawai manzon Allah yake yi. Sai wannan ayar ta amsa masu da cewa; ba dadewa ba za ku gani da dannawa wannan azabar ta Allah da aka yi maku alkawali kuma za ku gani abin da kuke wa izgili da karyawa zai riskeku babu makawa kuma hakika a ranar babu damar kubucewa.

A cikin wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa masu yawa amma zamu takaita da guda uku.

Na farko:Mutum sannu a hankali yake kaucewa hanya da farko zai kamaci gaskiya sai kuma ya fara adawa da ita daga karshe ya karyata gaskiyar sai kuma ya karyata gaskiya da ma’abuta imani da yi masu izgili.

Na biyu:Ayoyin Kur’ani masu tunatarwa da kashedi ne amma ga masu zucciya da ke a shirye ta karbi gaskiya ba mai jayayya da kin karbar gaskiya ba.

Na uku:Yin izgili yafi karyatawa muni ,wadanda suke yi wa gaskiya da ma’abuta gaskiya izgili sai an mayar masu da mummunan aikinsu tabbas.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri nay au a madadin dukan wadanda suka tallafa mani a cikin shirin ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa :wassalam….

Suratush Shu'ara Aya Ta 7-13 (Kashi Na 650)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                • MUSIC********

To madallah yanzu kuma za mu fara shirin nay au da sauraren karatun ayoyi na 7 zuwa 9.


أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الْأَرْضِ كَمْ أَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ كَرِيمٍ


7-Shin ba sa tunani game da kasa ,da yawa Muka tsirar da dangogin tsirrai masu kyau daga cikinta?


إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ


8-Hakika a game da wannan lallai akwai aya mai nuna cikar ikon Allah ,kuma yawancinsu ba su zamanto masu ba da gaskiya ba.

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ


9-Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi Mabuwayi ne gas aka wa hafurai ,Mai rahama ne ga muminai.

A cikin shirin da ya gabata ayoyi sun yi bayani kan yadda kafirai da mushrikai ke nunda bakar adawa da karyata Annabin Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma yadda suke yi masa izgili da karyata shi to wadannan ayoyin na cewa:Kafirai suna gani alamomi na kudura da karfin iko na Allah da girmansa amma ba su yin imani da Allah saboda bas u da kunnuwa na sauraren gaskia koi do na ganin gaskiya.Idan mutum na kollon itatuwa da tsirrai kawai kallon basira zai fahimci alamomi na girman Allah da daukakarsa .Saboda su kansu tsirrai da itatuwa suna tafiyar da rayuwarsu ne ta hanyar aure don akwai mata da zama a cikinsu ga kuma tsari mai kyau abin kayatarwa.

Abin mamaki yadda tun shekaru dubu daya da dari hudu da suka gabata Kur’ani yayi nuni da tsarin rayuwar tsirrai tamkar rayuwar ma’aurata amma sai gashi a tsakiyar karni na 18 miladi Lina wata masaniyar tsirrai da itatuwa ta yi sa’ar gano da wannan lamari cewa su kansu tsirrai suna rayuwa ne tamkar dabbobi akwai mace da namiji a cikinsu kuma suna samar da yaya ne ta wannan hanyar da zama wannan ma wata mu’ujizar kur’ani ce ta fuskar ilimi.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu :

Na farko:yin nazari da bincike a cikin abubuwan da Allah ya halitta wata hanya ce ta sanin girma da Mahalicci Allah.

Na biyu:Kasancewar tsirrai mace da namiji daya daga cikin alamomi ne da ke nuni da girman Allah a dabiance.

Na uku: Idan yawancin mutanan duniya kafirai ne ba dalili ba ne na karyata hakika .Misali idan yawancin mutanan duniya na busa taba sigari ba dalili ne ba cewa sigari abin kirk ice.

Na hudu: Allah a daidai lokaci guda mai girma da daukaka ne kuma mai rahama da jin kai ne.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 10 da 11 .


وَإِذْ نَادَى رَبُّكَ مُوسَى أَنِ ائْتِ الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ

10-Kuma ka tuna lokacin da Ubangijinka Ya kira Musa cewa:Ka tafi wajan mutanen nan azzalumai.


 قَوْمَ فِرْعَوْنَ أَلَا يَتَّقُونَ


11-Watau mutanen fir’auna Yanzu ba za su ji tsoron Allah ba?

A cikin wannan sura an kawo takaitaccen tarihin bakwai daga cikin Manzonnin Allah (AS) na farkon wanda aka fara da taricinsa shi ne Annabi Musa (AS).Tarihin rayuwar Annabi Musa (AS) da kuma maznoncinsa kuma surori da dama a cikin kur’ani sun kawo tarihin .Amma kowacce daga cikinsu ta tabo wani bangare na rayuwarsa ne a daidai lokacin da yayi daidai da rayuwar Manzon Rahama(SWA) da sauran musulmi domin su dauki darasi daga rayuwar Annabi Musa (AS).

Ayar farko a cikin wannan sura Allah madaukakin Sarki ya fara nuni da ma’amalar da ba dace ba da kafirai ke nunawa Manzon musulunci (SWA) da cewa: Su kafirai masu bakar jayayya da kiyayya ba su yi imani da kai ba to wadannan ayoyi ma na gayawa manzon Rahama cewa: Annabi Musa (AS) shi ma haka yayi fama da kafiran lokacinsa wadanda bas u daina munanan ayyukansu da zalunci da danniya da suka saba aikatawa amma duk da haka Annabi Musa (AS) bai dana kiransu zuwa ga kadaita Allah da bauta da yin tuba daga mummunan aikin da suka saba aikatawa ba.

Za mu ilmantu da abubuwa guda uku a cikin wadannan ayoyin.

Na farko:Sanin tarihin mutanan da suka gabata da Manzonnin da aka aiko masu zai taimaka mana a rayuwarmu mu musulmi da daukan darasi a yau da yin riko da addinin musuluncida fahimtar makirci da kafircin makiyanmu.

Na biyu: Domin gyaran al’umma dole masu tashi tsayin daka domin kawo gyaran ba kawai mu takaita da jawaban fatar baki ba.

Na uku: domin fuskantar zalunci da fasahi mu fara da fuskantar wadanda ke kan gaba a aikata wannan mummunan aiki don haka ne gwagwarmaya da Dagutu ke a sahun gaba a shirin annaban Allah (AS) na yaki da zalunci.

                                  • MUSIC************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 12 da 13 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i

قَالَ رَبِّ إِنِّي أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ


12-Musa ya ce : Ya Ubangijina hakika ni ina tsoron su karyata ni.


وَيَضِيقُ صَدْرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرْسِلْ إِلَى هَارُونَ

13-Kuma kirjina yana kuntata kuma harshen aba ya sakuwa sai Ka aika zuwa gad an uwana Haruna.

Bayan da Annabi Musa (AS) Allah ya umarce shi zuwa wajen fir’auna da mukarrabansa domin kiransu zuwa ga tauhidi sai ya bayyanawa Allah irin matsalolin na ciki da waje da zai iya fuskanta .Da farko da wuya su amince da wannan kira na shi Fir’auna da mukarransa za su karyata shi.Kuma isar da wannan sako abin ne mai girma da nauyi musamman Annabi Musa(AS) yana ganin yada da rauni a harshe da bayani don haka za su yi masa izgili da kaskantar da shi don haka sai Annabi Musa (AS) ya bukaci Allah da ya sanya dan uwansa Haruna shi ma yayi masa rakiya su kai wannan sako su biyu.Dukan wannan bukata dabubuwan da annabi Musa (AS) yayi bayani tun farko Allah ya san da su sai ya amsa masa wannan bukata ta sa sai suka tafi da shi da dan uwansa Haruna zuwa gurin Fir’auna.

Wadannan ayoyi na nuna mana cewa; malamai da masu Tabligi da nauyin shiryawa da isar da sako a tsakanin jama’a ke kansu ko a lokacin da suke fama da rashin lafiya ko tsufa da gajiyawa a daidai lokacin da ba za su iya isar da wannan sako yadda ya kamata , nauyin bai sabka daga kansu ba a’a sai dais u nemi taimakon matasa domin taimaka masu isar da wannan sako a tare da su.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku:

Na farko: don mutane sun karyatar da kai ba dalili ne ban a kin isar da sako da sabke nauyin da ya rataya kanka da kiransu zuwa ga kadaita Allah da bauta.

Na biyu:dukan mutane hatta manzonni kowa ne daya na da iyakarsa wajen fuskantar matsalolo da makiya don haka a kullum mu rika neman taimakon Allah.

Na uku:Manyan ayyuka na bukatar mataimaka masu girma da juriya na hakika masu tsinkaye da tunani idan bah aka ba kuwa da wuya a kai ga cimma nasara.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri nay au a madadin dukan wadanda suka tallafa mani a cikin shirin ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa :wassalam….


Suratush Shu'ara Aya Ta 14-20 (Kashi Na 651)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




                              • MUSIC**********

To madallah za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun aya ta 14 da 15 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i


وَلَهُمْ عَلَيَّ ذَنبٌ فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ

14-Ni kuma akwai wani laifi da na yi musu,sai nake tsoron su kasha ni.


قَالَ كَلَّا فَاذْهَبَا بِآيَاتِنَا إِنَّا مَعَكُم مُّسْتَمِعُونَ

15-Allah Yace A’a ko daya ba abin da zai same ka ,sai ku tafi kai da dan uwanka tare da ayoyinmu,hakika Mu ma Muna tare da ku wajan jin abin da zai gudana.

A cikin shirin da ya gabata Allah ya umarci Annabi Musa (AS) da ya tafi ya kubutar da Bani Isra’ila daga danniya da zaluncin fir’auna da makarrabansa.Wadannan ayoyi na cewa:Annabi Musa (AS) ya shaidawa Allah daya daga cikin matsalolin da zai fuskanta wajen isar da wannan sako da cewa: a baya ni a lokacin da wani daga cikin bani isra’ila ke fada da Mukarraban Fir’auna azzalumi na taimakawa wanda ake zalunta da hakan yayi sanadiyar mutuwarsa don haka ina tsoron zuwa gurinsu su kasha ni kan leifin baya na kasha mutumansu azzalumi kuma hakan ya sa in kasa isar da wannan sako mai muhimmanci.

Sai Allah ya amsa masa da cewa;Kar ka damu saboda ba za su iya cutar da kai ba kuma ba kai kadai ne z aka tafi gurinsu kamar yadda ka bukata z aka tafi tare da dan uwanka Haruna kuma ni ma ina tare da ku kuma duk abin da ke wakana tsakaninka da fir’auna da mukarrabansa ba kawai ina gani ba har iya yau ina tare da ku ne da taimaka maku.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu :

Na farko:Duk lokacin da z aka fuskanci makiyi ka yi nazarin yanayin halin da ake ciki da kuma wanda ya gabata da neman taimakon aboki ko runduna da kuke da tunani iri daya don z aka kai ga cin nasara da dacewa.

Na biyu: Bayan ka dauki aniya da kudurtawa mai kyau sai ka nemi taimakon Allah da yin tawakkali da shi domin Shi ne mai taimakawa ma’abuta imani.

Na uku:Allahyana nan a ko’ina da gani komin kan kantar abu yana da masaniya kansa.

Na hudu:a lamari na isar da gaskiya kar ka ji tsoron yawan makiya ko karamcin mataimaka.

Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 16 da 17


فَأْتِيَا فِرْعَوْنَ فَقُولَا إِنَّا رَسُولُ رَبِّ الْعَالَمِينَ

16-Ku je wajan Fir’auna sanan ku ce da shi :Hakika mu manzannin Ubangijin talikai ne.


أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ

17-Cewa,ka sako mana da Bani-Isra’ila.

A cikin wadannan ayoyi Allah ya fayyace wa Annabi Musa (AS) burin da ke kumshe a cikin wannan sako da cewa: A matakin farko a maimakon ku tafi gurin mutane kai tsaye ku tafi gurin Fir’auna ku ce masa :Mu Allah ne ya aiko mu gurinka domin isar maka da wannan sako cewa: ka kawo karshe da intar da bani Isra’ila daga zalunci da danniyarka ku za mu maida su zuwa kasarsu ta asali. Wadannan ayoyi ta fayyace a fili nauyin da ya rataya kan manzonnin Allah a gwagwarmaya da zalunci da danniyar azzalumi shi ne intar da al’ummomi da shiryar da su zuwa ga kadaita Allah da bauta.Annabi Musa (AS) sakon da yake tare da shi zuwa gurin fir’auna shi ne intar da mutanasa daga zaluncin Dagutu.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko:Manzonni wajen kira zuwa ga gaskiya da isar da sakon Allah babu wani sako sako suna fitowa haza karara ne da isar da wannan sako dari bisa dari.

Na biyu:Duniya baki daya Allah ne ke tafiyar da lamarinta kuma dole duk wani da ke raya karya a kalubalance shi da fayyace masa gaskiya a fili.

                              • MUSIC**************

Daga karshe kuma za mu saurari karatun ayoyi na 18 zuwa 20 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i


قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ


18- Fir’auna ya ce :yanzu ba mu muka raine ka a cikinmu tun kana dan jinjiri ba,kuma ka zauna ka yi wasu shekaru na rayuwarka a cikinmu?


وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ الَّتِي فَعَلْتَ وَأَنتَ مِنَ الْكَافِرِينَ

19- Ka kuma aikata aikin nan naka mummuna alhali kuwa kana daga masu butulce wa ni’imata?


قَالَ فَعَلْتُهَا إِذًا وَأَنَا مِنَ الضَّالِّينَ

20- Musa ya ce : Na aikata haka ne a lokacin ina daga cikin wadanda ba su samu ilimin manzanci ba.

Fir’auna bayan da ya saurari jawabin da sakon da Annabi Musa (AS) ya zo da shi daga Mahalicci a maimakon yay i imani da amincewa da maganar gaskiya sai ya fara tuna masa da abin da ya wakana a baya domin shagaltar da magana da sakon da ya zo da shi .Da farko ya tunatar da Annabi Musa (AS) lokacin da aka same shi yana jariri a cikin ruwan maliya da yadda Fir’auan ya rene shit un yana jariri har ya girma ba a nan ya tsaya ba sai ya tunatar da shi lokacin da yana matashi a lokacin da yake kokarin raba wani yaro na Bani Isra’ila da yake Fada da wani azzalamin matashin Fir’auna yana kokarin raba su sai Musa ya kasha wannan matashi azzalumi.Fir’auna ta hanyar tunatar da Annabi Musa (AS) duka wannan yana son ce masa: Mu ne muka ciyar da kai hark a girma tata ka samu karfin guiwa hark a zo mana da wannan sako.

Abu na biyu da fir’auna ke son nuni da shin a kisan matashin azzalumi da Musa yayi yana matashi yayi haka ne don ya raunana da sanya tsoro a zucciyar Annabi Musa (AS) da bayyana shi a matsayin mai aikata kisa ba mai shiryarwa ba.Amma Annabi Musa (AS) sai ya amsawa Fir’auna da cewa: lokacin da wani daga bani Isra’ila ke fada da daya daga Kibtiyan ni nay i kokarin taimakawa wanda ake zalunta ne kan azzalumi don haka na kai masa nushi ba da niyar kasha shi ba kuma haka lamarin yake .



Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu :

Na farko:Yi wa mutane gori kan wani aikin mai kyau wata mummunan al’ada ce ta Fir’auniyawa da ma’abuta girman kai.

Na biyu: Yi wa Mutane hidima ba dalili ne ban a mallakarsu da fakewa da wannan don danne su zaluntar su.

Na uku:Shiryawa da fadakarwa a kullum da lokaci ana bukatuwa da shi kuma hatta uwaye da wanda ya dauki dawainiyarka a rayuwa ana fadakar shi a lokacin da ya dace.

Na hudu: Waliyan Allah bas u tasirantuwa da yanayi ko gurin da suke rayuwa kamar yadda rayuwar da Annabi Musa yayi a fada da gidan Fir’auna bay i tasiri a kan sa ba.



Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri nay au a madadin dukan wadanda suka tallafa mani a cikin shirin ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa :wassalam….


Suratush Shu'ara Aya Ta 21-26 (Kashi Na 652)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                            • MUSIC*********


To Madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun ayoyi na 21 da 22 a cikin suratul Shu’ara’i


فَفَرَرْتُ مِنكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكْمًا وَجَعَلَنِي مِنَ الْمُرْسَلِينَ

21- Sannan na guje muku lokacin da na tsorata da ku sai Ubangijina Y aba ni ilimi Ya kuma sanya ni daga manzanni.


وَتِلْكَ نِعْمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنْ عَبَّدتَّ بَنِي إِسْرَائِيلَ

22- Waccen ni’imar kuwa da kake goranta min ita saboda ka bautar da Bani Israila ne.

A shirin da ya gabata kun ji yadda Fir’auna key i wa Annabi Musa (AS) gori da tunatar da shi lamarin da ya wakana a baya .Kuma kun ji yadda Allah ya aika Annabi Musa da Dan Uwansa Annabi Haruna (AS) da sakon shiriya zuwa gurin Fir’auna da fadawansa domin isar masu da wannan sako da kuma kawo karshen danniya da zaluncin da yake yi wa bani Isra’ila da intar da su.Amma Fir’auna da farkon faraway sai ya amsawa Annabi Musa (AS) da cewa a bay aka kasha daya daga cikinmu yanzu kuma kana raya annabtaka ? na biyu ka girma ne karkashin mu da ciyar da kai ta yaya za ka manta da duka wannan ka zo mana da wannan magana?. Annabi Musa (AS) ya amsawa Fir’auna da cewa; Ni ban i da niyar kasha shi kuma ina kokarin kare wanda ake zalunta ne na kai masa dukan da yayi sanadiyar mutuwarsa saboda haka hadari ne ba kisa da gangan ba.

A cikin wadannan ayoyi Annabi Musa (AS) ya bayyana masa cewa: Tsoron a kama ni da yi mani hukumcin zalunci na gudu daga Masar zuwa Madyana a gurin da Allah ya bani hikima da matsayin Annabtaka da wannan falala da ya turo ni da ita ta kawo kashen zaluntar bani Isra’ila.Amma gorin da ka yi mani na yin reno na ba yana nunin falalarka a kai na ba ne a gaskiya ya samo asali ne daga zaluncinka a kai na da gidanmu saboda a bisa dabi’a ya zama wajibi in tashi da rayuwa a gidanmu gaban babana da uwata amma saboda umarnin da ka bayar ya kasha duk wani jaririn Bani Isra’ila da aka Haifa ,Uwata domin tsiratar da ni daga kisan zalunci ta sanya ni a cikin akwati da jefa ni a cikin takun maliya dake gudana don haka ka tsintse ni a cikin wannan ruwa kuma ka rike ni a matsayin da da girma a gurinka don haka duk wannan ya samo asali ne daga zaluncinka kan bani Isra’ila ba lutifi daga gare ka da kake yi mani gori.


Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :

Na farko: Idan zalunci da danniya da fasadi ya mamaye gurin da kake rayuwa kana iya yin gudun hijira zuwa gurin da za ka samu falala da rahamar Allah.

Na biyu:Allah ya taimakawa Annabawa da Manzonninsa da ilimi da hikima domin isar da wannan sako na kiran mutane zuwa ga shiriya da karbar gaskiya ta kadaita Allah da bauta.

Na uku: Yi wa mutane gori wani abu ne da dagutu da ma’abuta girman kai suka kebanta da su.Amma tsari na Allah da waliyansa a kullum suna kokarin yi wa mutane hidima da warware masu matsalolinsu ba yi masu gori ba.

To yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 23 da 24 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i


قَالَ فِرْعَوْنُ وَمَا رَبُّ الْعَالَمِينَ


23-Fir’auna yace : To wane ne Ubangijin talikai?


قَالَ رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا إن كُنتُم مُّوقِنِينَ


24- Musa yace: Shi ne Ubangijin sammai da kassai da abin da yake tsakaninsu,idan har kun kasance masu gaskata haka.

Lokacin da Fir’auna ya ji amsa ta gaskiya mai karfi da ba zai iya musantawa ba daga Annabi Musa (AS) bas hi da abin cewa face tambaya da cewa: Kana cewa Allah da ya halicci duniya ne ya turo ka da wannan sako to wane ne Shi Wannan Allah da kake cewa?

Annabi Musa (AS) ya amsawa Fir’auna da alamomin karfi da kudurar Allah ta hanyar abubuwan da ya halitta da cewa: Shi Mahaliccin sammai da kassai da abubuwan da ke tsakaninsu kuma Shi ne ke tafiyar da lamuransu cikin tsari da kwarewa duk da girman sammai da kassai da yawan halittun iri iri da ke cikinsu kuma babu wani da ya cancanci yi masa bauta face Shi kadai.Kai fir’auna idan kai ma kana son gaskiya da bin gaskiya ka yi nazari tunani a cikin wannan tsari don risker Mahlicci da bauta masa Shi kadai da gaskiya.


Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :

Na farko: Daga cikin nauyin da yah au kan masu yada addini shi ne amsa tambayoyi da abubuwan da ya shigewa mutane duhu a lamura da suka shafi Akida da rayuwar yau da kullum.

Na biyu: Sabanin mahangar mushrikai da ke ganin alloli suna da yawa ,a mahangar addinin musulunci Allah daya ne Shi ne ya halicci wannan duniya da duk wani abu da ke cikinsa.

Na uku: Ma’abuta imani a kullum suna kara kadaita Allah da bauta kara samin karfin guiwa ta hanyar halittunsa a wannan duniya baki dayanta.

                                  • MUSIC*************

Daga karshe kuma za mu saurari karatun ayoyi 25 da 26 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i


قَالَ لِمَنْ حَوْلَهُ أَلَا تَسْتَمِعُونَ


25- Fir’auna ya ce da wadanda suke kewaye da shi:kuna kuwa jin abin da yake fada ?


قَالَ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ


26- Musa yace: Shi ne Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko.


Amsa gamsshiya da rusa abin da fir’auna ke rayawa na cewa shi alla ne da Annabi Musa (AS) yayi da bayyana masa da sauran mutanan da suka kewaye shi Allah na gaskiya ya hargitsa Fir’auna da fiddo da fushi da bacin ransa a fili da yin iyakacin koarinsa na kawo karshen wannan bayani da Annabi Musa (AS) ke yi amma ya ki ya saurare shi da ci gaba da bayanisa da cewa Shi Allah ba wai kawai mahaliccin Sammai da kasai ba hatta ku da uwayenku baki daya Shi ne ya halicce ku kuma rayuwarku tana hannunsa da arzikinku hatta Fri’auna Shi ne ya halicce shi da kula da rayuwarsa kuma Fir’auna ba kowa ba ne shi ga kudurar Allah.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko:Tsari irin na dagutu bas u da wani aiki a duk lokacin da suka saurari maganar gaskiya sai ta neman hanyoyi da za kaucewa gaskiya da tambayoyi ba kan gado.

Na biyu:Duk wani a wannan duniya da ya hada da sammai da kassai da mutane da sauran halittu Allah ne ya halicce su da tafiyar da lamuransu.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri nay au a madadin dukan wadanda suka tallafa mani a cikin shirin ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa :wassalam….

Suratush Shu'ara Aya Ta 27-33 (Kashi Na 653)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC******************


To madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 27 da 28 a cikin suratul Shu’ara’I .


قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ الَّذِي أُرْسِلَ إِلَيْكُمْ لَمَجْنُونٌ

27- Fir’auna yace: Hakika Manzon da aka aiko muku ba shakka motsattse ne.


قَالَ رَبُّ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ وَمَا بَيْنَهُمَا إِن كُنتُمْ تَعْقِلُونَ


28- Musa Yace: Shi ne Ubangijin mahudar rana da mafadarta da kuma abin da yake tsakaninsu,in kun zamanto masu hankalta.

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda tattaunawa ta kasance tsakanin Annabi Musa (AS) da fir’auna inda a cikin wannan tattauanwa Fir’auna yake son kaskanta karfi da hujjojin da Annabi Musa (AS) ya zo da su da hanawa Mukarrabansa su gamsu da amincewa da wannan kira na Annabi Musa (AS).Fir’auna cikin rashin ladabi ya ci mutuncin Annabi Musa (AS) da kiransa da wanda ya samu tabuwar hankali wato mahaukaci da cewa mukarrabansa da cewa:Wanna mutum da Allah ya aiko don shiryar da ku bas hi da hankali.Amma Annabi Musa (AS) cikin ladabi da mutuntawa sai ya amsa masu da cewa: ku da kuke da hankali idan kuka zurfafa tunani za ku fahimci Allah da ya kamata ku bautawa Shi ne mahaliccin da ikon wannan duniya baki dayanta .Ba Fir’aunawa da y ace Nine allanku mafi girma alhali kawai shi yana ikon wani guri da bai huce Masar da kewayenta ba to sauran gurare mai yawa na duniya bay a karkashin ikonsa ko bah aka ne ba.

Wannan bayani na Annabi Musa (AS) a gaskiya maida wa Fir’auna martani ne da cewa: kai ne mahaukaci kuma nib a mahaukaci ba ne ,mahaukaci shi ne wand aba ya ganin girma da daukakar Mahalicin wannan duniya wanda ya halicce shi da duk wani abu a wannan duniya.


Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :

Na farko:Mutane masu girman kai da kin karbar gaskiya a maimakon tunani da nazari na hankali suna yin riko da hanyar cin fuska da kaskantar da waliyan Allah.

Na biyu:A kullum masu adawa da annabawa da waliyan Allah na zarginsu da masu tabuwar hankali.

Na uku:Daga tsari da tafiyar da wannan duniya da fitowa da faduwar rana da wata cikin tsari za mu iya gamsuwa da fahimtar girma da daukakar mahaliccin wannan duniya da abin da ke cikinta.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 29 da 31


قَالَ لَئِنِ اتَّخَذْتَ إِلَهًا غَيْرِي لَأَجْعَلَنَّكَ مِنَ الْمَسْجُونِينَ


29- Fir’auna yace: Na rantse in har ka riki Allah bani ba, lallai zan jefa ka cikin kurkuku.


قَالَ أَوَلَوْ جِئْتُكَ بِشَيْءٍ مُّبِينٍ


30- Musa ya ce: Ko da na zo maka da wata hujja bayyananniya?


قَالَ فَأْتِ بِهِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ


31- Fir’auna yace : To ka zo da ita din in ka kasance daga masu gaskiya.


Lokacin da Fir’auna ya ga kaskantarwa da cin mutuncin da yake yi Annabi Musa (AS) bai hana Shi ci gaba da bayaninsa ba sai ya sake wani salon a baraza da kama shi da azabtar da shi da cewa;Kar ka yi zaton za mu yi shiru da duk abin da kake fada da barinka haka kawai ka isar da wannan sako ga mutane .Kuma ka sani kai Musa idan ka zabi bauta wa wani Allah ban i ba da kiran mutane ga bauta mas aba za mu bark aka fita daga wannan fada ba ,za mu kakaba ka a cikin kurkuku da azabtar da kai har sai ka daina wannan kira da kake rayawa.

Amma Annabi Musa (AS) domin fuskantar wannan babbar barazana daga Fir’auna sai ya bayyana masa karfi da kudurar Allah madaukakin sarki da cewa: Ni Allah ne ya aiko ni kuma nay i imani da ni da bauta masa kuma alamominsa a fili suke da kai da fadawanka suka kasa gani da fahimta.Fir’auna bai yi zaton samin amsa cikin sauri daga Annabi Musa (AS) ba tare da ya shirya ba sai Fir’auna ya ce: Idan Allan da kake fada yana da karfi sai ka nuna mana muma mu gani.


Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku :

Na farko:Nuna karfi da zalunci na daga cikin tsarin mulkin Dagutu da jimirin sauraren magana da jawabi na gaskiya ba.Daga sun fadi sai barazanar kakaba mutun a gidan kurkuku da azabtarwa.

Na biyu:Barazana it ace babban abin da tsarin zalunci ya dogara ita don haka jagororin addini dole su shiryawa hanyar gwagwarmaya da zalunci da fasadi da duk wani tsanani da ke tattare da hakan.

Na uku: Mu’ujiza daya daga cikin hanyoyin tabbatar da gaskiya da sakon gaskiya da kuma Manzonnin Allah ke amfani da ita don kaucewa karyatawart masu karyata gaskiya.

                                    • MUSIC**********

Daga karshe kuwa za mu saurari karatun aya ta 32 da 33 a cikin wannan sura ta Shu’ara’i


فَأَلْقَى عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ


32- Sannan Musa ya jefa sandarsa sai ga ta ta zama kumurci kuru-kuru.


وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاء لِلنَّاظِرِينَ


33- Ya kuma zaro hannunsa daga cikin rigarsa sai gas hi fari fat ga masu duba.

Karkashin umarnin Allah Annabi Musa (AS) ya jefa sandar da ke hannunsa a gaban Fir’auna da fadawansa inda mu’ijiza babba da ke nuni a fili da sakon da yake dauke da shi .Cikin ikon Allah wannan sanda ta koma macijiya babba abin tsoro ta inda daga wannan lokaci Fir’auna ba zai kara tsoratar da Annabi Musa (AS) da gidan kurkuku da azabtar da shi da fahimtar ba zai iya yi wa Annabi Musa (AS) wani abu ba duk da girman mulkinsa.

Dukan mutanen da ke fadar kama daga shi kansa Fir’auna da fadawansa sun samu kansu cikin tsoro da mamaki abin da Annabi Musa (AS) ya nuna masu na mu’ujiza kuma wannan lamari ya raunana hukumar Fir’auna da neman hanyar da zai kubuta daga wannan kalubale da halin kaka nikan yi da ya samu kansa a ciki.


A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: masu girman kai da zalunci da danniya a kullum sai an yi shiri mai karfi kafin fuskantarsu da yin nasara kansu.

Na biyu: a kullum ana bukatuwa da abubuwa masu jan hankali wajen gamsar da mutanen da ake so su fahimta da karbar gaskiya kamar yadda Annabi Musa (AS) ya fito da hannunsa yana haske fari fes da hakan ya dauki hankalin mutanan da ke fadar Fir’auna da shi kansa Fir’aunan.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri nay au a madadin dukan wadanda suka tallafa mani a cikin shirin ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa :wassalam….

Suratush Shu'ara Aya Ta 34-40 (Kashi Na 654)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                • MUSIC**********


To Madallah za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun


قَالَ لِلْمَلَإِ حَوْلَهُ إِنَّ هَذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ


34- Sai Fir’auna yace da waziran da suke kewaye da shi :Hakika wannan lallai gwanin mai sihiri ne.


يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ


35-Yana so ne ya fitar da ku daga kasarku da sihirinsa,to me za ku ce?


A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda fir’auna yayi wa Annabi Musa (AS) barazanar kakaba shi a gidan kurkuku da azabtar da shi da kuma yadda Annabi Musa (as) ya jefa sandar da ke hannunsa da zama macijiya babba da hakan ya cusa tsoro da fargaba a zucciyar fir’auna da mukarrabansa a fadarsa a maimakon ci gaba da aiwatar da barazanar da yayi wa Annabi Musa (AS) to wandannan ayoyi da muka saurara na ci gaba da bayani kana bin da ya wakana a fadar fir’auna da cewa;Fir’auna da yaga ya fadi da kasa cimma nasara kan muujizar da Annabin Musa (AS) yayi nuna a fadarsa sai yak e shaidawa fadawansa da mukarrabansa cewa; Yanzu ta bayyana musa babban mai sihiri ne masani kuma duka wannan wani makirci ne da ya shirya don sanin matsayi da daukaka fiye da ku don haka ku yi tunani da nazarin dakule wannan makirci nasa da bada shawarar matakin da za mu dauka.

Abin mamaki a nan ta yaya fir’auna da ke raya shi alla ne mai hukunci a hannunsa ba ya iya taimakawa kansa ko waninsa idan matsala ta taso face neman taimako daga fadawansa da mukarrabansa samin mafita daga wannan hadari da ke tunkararsa da hukumarsa.


A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka;

Na farko:Masu girman kan bayyana gaskiya da amincewa da ita a kullum na amfani da zargi da tuhumar mutanan kirki kamar yadda fir’auna yayi amfani kan Annabi Musa na jifansa da Kalmar mahaukaci lokacin da ya bayyana masa mu’ujiza a fili karara.

Na biyu:Son kasa wani lamari ne da ya shafi dukan mutane don haka fir’auna yayi amfani da wannan salo don hargiza mutane kan annabi Musa (AS) cewa : yahna son fitar da ku ne daga kasarku kuma wannan salon ne makiya ke anfani da shi kan jagororin gaskiya.

To yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun aya ta 36 da 37 a cikin wannan sura ta Shura’u


قَالُوا أَرْجِهِ وَأَخَاهُ وَابْعَثْ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ


36- Suka ce: ka dakatar da shi tare da dan uwansa ,kuma ka aika manzanni cikin birane su tattaro maka masu sihiri.


يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ


37-Su zo maka da duk wani gwanin sanin sihiri.


Fadawa da mukarraban Fir’auna bayan sun yi shawara da tuntubar junansu sun bayyanawa Fir’auna cewa:ka karawa Musa da dan uwansa haruna lokaci da jinkirta azabtar da su ka aika sako a fadin kasar Masar a tawo da duk wani mashahurin boka da mai sihiri da zai kalubalanci Musa da abin da ya zo da shi.Wannan shawara da mukarraban fir’auna suka bas hi na nuni a fili cewa suma sun amince da yarda da cewa Musa mai sihiri ne boka da neman mulki da dukiya.Alhali da sun surfafa tunani da sun fahimci gaskiyar magana cewa Musa ba mai sihiri ba ne. Saboda a tsawon tarihi babu wani mai sihiri da ya kirayi mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta asalima suna kiran mutane zuwa gare su ne da neman mukami da dukiya da zama mashahurai da tara dukiya don amfanin kansu amma Shi Musa abin da ya bukata daga fir’auna ya kawo karshen azabtarwa da zaluntar mutane ma’ana ya yantar da sub a tare da ya bukaci wani abu don amfanin kansa ba.Sabanin Masu sihiri da bokaye da za mu gani a aya ta gaba yadda kafin sun yi wani abu sai da suka bukacin sakayya daga Fir’auna idan sun yi nasara kan Musa sabanin Manzonni da annabawan Allah masu son yantar da mutane da tsiratar da sub a tare da sun nemi wani abu ko sakayya a gare su ko waninsu ko da kuwa za su yi shahada ne.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:A tsarin zalunci irin na dagutu da murabansa suna daukan mataki ne don amfanin kansu da hukumarsu ba wai mutane da al’ummar da suke shugabanta ba.

Na biyu: Dagutai a kullum na kokarin maida masana masu yi masu hidima kawai tamkar bayunsu.

                                            • music********

To madallah yanzu lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 38 zuwa 40 a cikin wannan sura ta Shu;ara’a.


فَجُمِعَ السَّحَرَةُ لِمِيقَاتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ


38-Sai aka tattara masu sihirin don su zo a kayyadajiyar rana sananniya.


وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلْ أَنتُم مُّجْتَمِعُونَ


39- Aka kuma ce da mutane :Ai ya kamata duk ku zo.


لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ السَّحَرَةَ إِن كَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَ


40- Don mu goyi bayan masu sihiri idan har suka kasance masu galaba.

Fir’auna ya amince da shawarar da mukarrabansa da fadawansa suka bayar inda ya sa a nemo masa duk wani mashahurin boka da mai sihiri a fadin kasar Masar kuma ya kasance a babban birnin Masar kuma bokaye da masu sihiri masu yawan gaske ne suka amsa wannan gayyata ta fir’auna don haka aka shaidawa mutane rana da gurin da za a yi wannan babban taro na kalubale tsakaninsu da Musa don haka mutane su zo kallo.

Fir’auna da mukarrabansa sun yi haka ne don amfani da wannan hanya ta kunyatar da Annabi mUsa (AS) idan aka yi nasara a kansa a wannan rana,ta haka mutane za su fahimci karfin mulkin fir’auna da kara yin imani da shi kuma taruwar jama’a sun karya zucciya da ruhin Annabi Musa da Haruna (AS) sun ji cewa su kadai ne a gurin amma wannan a tunanin da makircin fir’auna da mukarrabansa kuma bugu da kari mutane da karawa bokaye da masu sihiri karfin guiwa da hakan zai sa su ci nasara. Ta wata mahangar cin nasarar masu sihiri kan Annabi Musa (AS) tamkar nasarar allolinsu ne kan Allan Musa ne ta haka Musa ba zai iya kiran mutane zuwa ga kadaita Allansa da bauta wannan shi ne tunaninsu .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko :Dagutai domin cimma manufofinsu wani lokaci suna amfani da mutane domin nuna karfin ikonsu amma a gaskiya ba don suna girmama mutanen ba ne.


Na biyu:A tsarin mulki irin na dagutai domin hana da dakile koyarwar addinin Allah suna amfani da yada karya da yaudara da gurbata tunani.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin Injiniyanmu Malam Aminu Ibrahim Ni tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa:wassalam…

Suratush Shu'ara Aya Ta 41-48 (Kashi Na 655)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




                                • MUSIC**********

To madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 41 da 42 a cikin suratul Shuara’a.


فَلَمَّا جَاء السَّحَرَةُ قَالُوا لِفِرْعَوْنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ الْغَالِبِينَ


41-Sannan lokacin da masu sihirin suka zo sai suka ce da Fir’auna :Shin muna da wani lada da za a ba mu in har mun zama mu ne masu galaba?


قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ إِذًا لَّمِنَ الْمُقَرَّبِينَ


42-Fir’auna yace: Na’am,kuma ma a yayin nan lallai za ku zama daga makusanta.


A cikin shirin da ya gabata mun kawao bayanin cewa lokacin da fir’auna ya ga mu’ujizar da Annabi Musa (as) ya zo da ita sai y ace mai sihiri ne da daukan matakin gayyatar duk wani mashahurin mai sihiri da boka a fadin Masar domin kalubalantar Annabi Musa (AS) a gaban mutane a babban dandali.

To wannan ayar na cewa;Bokaye da masu sihiri lokacin da suka taru da jin cewa tabbas sune za su yi nasara kan Musa sai suka ce: me cece kyautar da za a ba mu idan muka yi nasara kan Musa da biya maka bukatarka? Ganin yin nasara kan Musa lamari ne mai girma da farantawa fir’auna don haka ya amsa masu da cewa:Ba wai kawai kyautar kudi ba za ku zama makusanta na masu bani shawara don haka za ku samu kudi da makami kawai abin da nake so a gare ku kar ku bari Musa yayi nasara a kanku.


A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:Wadanada suka rungumi wannan duniya ba sanin gaskiya da karya ya dame sub a kawai amfanin kansu da dukiya suke kallo kamar yadda bokaye da masu sihiri suke suna kollon amfanin kansu da kansu ba waninsu ba ko gaskiya da karya ba.

Na biyu:Masu mulkin danniya da zalunci na amfani da duk wata dama da karfi da suke da shi wajen kalubalantar gaskiya da ruguza ta.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 43 zuwa 45


قَالَ لَهُم مُّوسَى أَلْقُوا مَا أَنتُم مُّلْقُونَ


43- Sai Musa yace da su: Ku jefa duk abin da za ku jefa.


فَأَلْقَوْا حِبَالَهُمْ وَعِصِيَّهُمْ وَقَالُوا بِعِزَّةِ فِرْعَوْنَ إِنَّا لَنَحْنُ الْغَالِبُونَ


44- Sai suka jefa igiyoyinsu da sandunansu suka kuma ce: Hakika da albarkar fir’auna lallai mu za mu yi galaba.


فَأَلْقَى مُوسَى عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ


45- Sai Musa ya jefa sandarsa.Sai ga ta tana lankwame duk abin da suka kago na sihiri.

Ranar da aka kebe domin kalubalantar juna ta zo yau ,fir’auna da mukarrabansa da bokaye da masu sihiri a kefe guda ,ga kuma mutane sun taru masu yawan gaske sai kuma Annabi Musa da dan uwansa Haruna (AS) suma suna wannan guri da dandalin fayyace gaskiya da karya.Kuma babu wani tsoro ko fargaba da Annabi Musa da dan uwansa suka nuna domin sun yi imani Allah yana tare da su da ganin komi kuma mai taimaka masu ne tabbas. Su ma Masu Sihiri sun jin su ne za su yi nasara da nuna jiji da kai da girman kai.Nan fa suka fara aikin bokanci da sihiri da ajiye kayan aikinsu a kasa da suka hada da itatuwansu na bokanci da iggiya . Ba da jimawa ba sai ga macije kanana da manya masu yawa na yawo akasa a wannan fili mutane na gani. Mutane ganin wadannan macije sai tsoro da fargaba ya mamaye zukatansu amma jin masu sihiri sun yi nasara kan Musa sai suka ji wani dadi da dan kwantar masu da hankali a gefe daya. Sai dai wannan farin ciki nasu bai dauki dogon lokaci ba domin jefa sandar da Annabi Musa (AS) sai ta kowa macijiya babba mai ban tsorota fara hadeye duk wani maciji da ke wannan guri karaminsa da babbansa kafin kace kabo babu wani abu da yayi saura a wannan fili.Dukan wani mutum da ke wannan guri sai mamaki da al’ajabi ya kama shi da mamaye tunani da zucciyarsa domin abin da yake gani yafi karfin hankali da tunaninsa da imaninsa kuma ta yaya cikin sauki za a ci nasara kan bokaye da masu sihiri masu yawa da suka shahara.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Mutanan kirki na gari waliyan Allah na dogaro ne da Allah kawai a filin dag aba su la’akari da yawan jama’a da makiyansu.

Na biyu:Ma’abuta imani dole a kullum su kasance cikin shiri da daukan mataki na tunkarar makiya da rusa makirci da karyar da suke yadawa.

Na uku; Makaryata da mabannata babu wani abu da suka yi dogaro da shin a tunkarar gaskiya da hasken imani kamar yadda bokaye da masu sihiri suka kasa cin nasar kan Annabi Musa (AS)>

                                • MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 46 zuwa 48


فَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ


46-Sai aka durkusar da masu sihirin suna masu sujjada.



قَالُوا آمَنَّا بِرَبِّ الْعَالَمِينَ

47- Suka ce: Mun ba da gaskiya da Ubangijin talikai.


رَبِّ مُوسَى وَهَارُونَ


48- Ubangijin Musa da Haruna.

A wannan fili kawaibokaye da masu sihiri da ke suna da ilimi da masaniya kan ayyukan sihiri da bokanci ba da bata lokaci da wata wata ba suka fahimci mu’ujizar da annabi ba sihiri kuma yayi hannun riga da aikinsu na sihiri kuma wannan ba daga aikin mutum ba ne domin babu wani mutum da zai iya wannan aiki na maida sanda macijiya da kuma lakume macijen da suka yi sihirinsu ba tare da sun shirya ba sai suka yi sajjada da yin imani da Allah da mika wuya ga gaskiya da hanyar gaskiya da Annabi Musa (AS) ya zo da ita sun manta da bukatar da suka gabatarwa fir’auna nay i masu kyautar dukiya da makami .Duk sun yi watsi da haka da yin imani dari bisa dari da Allah Annabi Musa (AS).

Wannan sauyi da canji na gaggauawa na ruhi bayan fahimtar gaskiya da aminci na zucci da ganin mu’ujizar da Annabi Musa (AS) ya nuna a wannan fili ya sa hatta mutanan da ke guri suka fahimci abin da Musa ya zo da shi ba sihiri ba ne.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar:

Na farko:Idan abin da hankali ya fahimta zucciya kuma ta karba da gaskata gaskiya zai kai ga imani na hakika.

Na biyu: Shi mutum an bas hi ikon zabi kuma yana da karfi da ikon canja salon tafiyarsa da aikinsa daga lala zuwa mai kyau ko akasin hakan .


A madadin wadanda suka hada mana sauti har shirin ya kamala ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam….

Suratush Shu'ara Aya Ta 49-52 (Kashi Na 656)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




                                • MUSIC**********

To madallah za mu fara shirin nay au da sauraren karatun aya ta 49 a cikin suratul Shuara’a.


قَالَ آمَنتُمْ لَهُ قَبْلَ أَنْ آذَنَ لَكُمْ إِنَّهُ لَكَبِيرُكُمُ الَّذِي عَلَّمَكُمُ السِّحْرَ فَلَسَوْفَ تَعْلَمُونَ لَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَافٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ أَجْمَعِينَ


49- Sai fir’auna yace: Yanzu kw aba da gaskiya da shit un kafin in ba ku izni? Hakika lallai shi ne babbanku wanda ya koya muku sihiri,to lallai kuwa kwa sani,ba shakka zan yanyanka hannayenku da kafafuwanku a harde,kuma lallai zan tsire ku gaba daya.

A cikin shirin da ya gabata kun yadda masu sihiri suka yi imani da mu’ujizar da Annabi Musa (AS) ya gabatar a filin kalubale da cewa tabbas wannan ba sihiri ba ne da aikin bokaye .Don haka dukansu kasa yi imani a gaban mutane da suka taru a wannan dandali.Fir’auna wanda manufarsa masu sihiri su kumyatar da Annabi Musa (AS) da yin nasara a kansa kuma sai gashi gawo ya juye da mujiya kuma akwai yuyuwar mutanan gurin suma su yi imani da muujizar da Annabi Musa (AS) ya zo da ita da yin imani da Allan Musa saboda haka bas hi da zabi da ya fice zargin Masu sihiri da cewa sun yi baki guda ne da Musa kuma shi ne babbansu da ya koya masu sihiri da yin barazanar yanke masu hannu guda da kafa guda daga cikin irin azabtarwar da zai yi masu da zama darasi ga sauran da kuma hakan zai hana wani yayi imani da Annabi Musa (AS).

A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa guda biyu:

Na farko:A hukumomi irin na dagutu mutane ba su da yancin akida a irin wadannan hukumomi shugaba na cimma burinsa ne ta hanyar danniya da hana al’umma yancin tunani.

Na biyu: Ran mutum a gurin mahukumta azzalumai da danniya bas hi da wata kima don haka duk wani da ya sabawa manufarsu za a zubar da jininsu da daukan ransa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 50 da 51 a cikin shuara’a.


قَالُوا لَا ضَيْرَ إِنَّا إِلَى رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ


50- Sai suka ce: Ai ba damuwa,hakika mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu.


إِنَّا نَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَايَانَا أَن كُنَّا أَوَّلَ الْمُؤْمِنِينَ


51- Hakika mu muna kwadayin Ubangijinmu Ya gafarta mana kurakuranmu saboda zamnatowarmu farkon muminai.

Bayan barazana mai tsanani da Fir’auna yayi wa masu sihiri da bokaye da shi da kansa ya gayyace su ,bayan masu sihri da bokaye bas u ji tsoro ba da janye imani da amincin da suka yi wa Annabi Musa (AS) sai ma wani haske ya kara mamaye zukatansu da kara masu karfin guiwa cikin aminci babu fargaba suka maida wa fir’auna da amsar cewa: Mu ba mu tsoron azabtarwa ko mutuwa ? shin ko b aka sani ba mu muna maraba lalle ne da kasha mu kan tafarkin Allah.Saboda muna fatar da haka mu samu sa’ar yafe mana leifuffukan ayyukan da muka aikata a baya da lissafa mu a cikin na farkon wadanda suka yi imani da Annabi Musa (AS) da samun falala mai girma ta musamman.Abin da kake gani a matsayin barazana mu a gurinmu bushara ce da abin iftikhari.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:Imanin da ya samu asali da tushe daga ilimi da masaniya bay a raunana daga barazana sai ma ya karawa mutum jarunta da tsayin daga.

Na biyu:karshen rayuwa shi ne ke da muhimmanci ba farkonta ba.Masu hiri da suka gudanar da rayuwarsu cikin bata sai gashi sun yi imani da muujizar Annabi Musa (AS) da dacewa a karshen rayuwarsu .kamar yadda ake samun akasin haka a tsakanin musulumi da wani zai kasance a tsawon rayuwa yana salla da azumi amma a karshen rayuwarsa ya fada tarkon shaidan da barin wannan duniya ba tare da imani ba.


                            • MUSIC******

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 52 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


وَأَوْحَيْنَا إِلَى مُوسَى أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِي إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ


52- Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã ne.

Bayan abin da ya faru a dandalin kalubale da kashin da Fir’auna ya sha a gaban dubban mutane don haka ya dauki matakin azabtar da Musa da duk wadanda suka yi imani da shi kuma ta haka zai hana yaduwar tunani da koyarwa Annabi Musa (AS) a tsakanin jama’a.


A dabra guda Allah yayi wa Annabi Musa (AS) wahayi cewa; ba wai kawai kubuta daga zaluncin fir’auna kai kadai ba hatta yan uwanka da sauran bani Isra’ila da ake bautarwa da azabtarwa a Masar da rayuwa cikin kumci za su kasance tareda ke da fitar da su daga masar zuwa yankin Sham .Bani Isra’ila sun ga yadda karfin muujizar Annabi Musa (AS) da yadda yayi nasara kan Fir’auna ya kara masu karfin guiwa da nucuwa da imani da kai Musa. Kuma za su amsa kiranka da kubutar da su daga zalunci da danniyar fir’auna.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:Idan fasikanci ya mamaye al’umma idan kana da kafi sai ka kalubalancin wannan zalunci da fasadi da yin gwagwarmaya idan kuma b aka da wannan karfi da ikon tunkarar wannan matsala to sai ka yi hijira da gujewa wannan al’umma fasika.

Na biyu:Yantar da al’umma daga zalunci da danniyar hukuma azzaluma daya ne daga cikin shiri da dalilin aiko da annabawa da manzonni karkashin shiryarwar Allah.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin nay au a madadin wadanda suka taimaka a cikin wannan shirin musamman injiniyanmu Muhammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa wassalam….

Suratush Shu'ara Aya Ta 53-62 (Kashi Na 657)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




                                • MUSIC**********

To Madallah za mu fara shirin nay au da sauraren aya ta 53 zuwa 56 a cikin suratul Shu’ara’a.


فَأَرْسَلَ فِرْعَوْنُ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ


53-Sai Fir’auna ya aika zuwa birane don a tattaro mayaka.


إِنَّ هَؤُلَاء لَشِرْذِمَةٌ قَلِيلُونَ


54- (Fir’auna yana cewa):Hakika wadannan lallai yan tsirarin jama’a ne.


وَإِنَّهُمْ لَنَا لَغَائِظُونَ


55-Kuma Hakika su lallai suna musguna mana.


وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَاذِرُونَ


56-Hakika kuma mu lallai masu kwana cikin shiri ne.

A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda Allah ya umarci Annabi Musa (AS) ya fice tare da bani Isra’ila zuwa yankin Sham kuma ya isar da wannan umarni a fadin Masar ga bani Isra’ila kuma suka tattaru a fadar mulkin Masar ta kowane hali da yanayi domin kubuta karkashin jagorancin Annabi Musa (AS) daga zaluncin Fir’auna azzalumi mai danniya ,fasiki.

Fir’auna bayan samin labarin wannan shiri na Annabi Musa (AS) ya sa aka tattaro masa yan sa kai daga fadin Masar don hada runduna da za ta tunkari wannan shiri na Annabi Musa (AS) kuma ya sa aka yada labaran farfaganda cewa Musa da sahabbansa yan tsuraru ne idan aka katamta su da rundunar Fir’auna kuma duk wanda ya bijirewa umarnin Fir’auna daga Bani Isra’ila makomarsa mutuwa da azabtarwa ta wannan hanya zai karawa rundunarsa karfin guiwa.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko:Hukumomi da gwamnatocin Dagutu na amfani da farfaganda da yada karya wajen bankama karfi da ikonsu domin hana a kalubalance su.

Na biyu:Hukumomin zalunci da dagutu na amfani da dukiya mai yawa wajen neman amincewar jama’a amma a kullum ana kara tsanantar su ne a maimakon a so su.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 57 zuwa aya ta 59 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a:


فَأَخْرَجْنَاهُم مِّن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ


57- Allah ya ce: Sai Muka fitar da su daga gonaki da kuma idandunan ruwa.


وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ


58-Da taskoki da kuma mazaunai na alfarma.


كَذَلِكَ وَأَوْرَثْنَاهَا بَنِي إِسْرَائِيلَ


59-Kamar haka ne Muka gadar da su ga Bani Israila.

Wadannan ayoyi na nuni da yadda makomar Fir’auna ta kasance da kuma yadda annabi Musa (AS) da sahabbansa suka yi nasara da cin nasar kan Fir’auna da mukarrabansa da kowa ya gani da idonsa a fadin Masar da kunyatar da shi a idon jama’a duk da nuna karfin iko da dukiya kan Bani Isra’ila amma karfin imani yayi nasar kan karfin kafirci.

Da farko burin Annabi Musa (AS) shi ne kubuta da yantar da bani Isra’ila Amma sai Allah ya mallaka masa kasar Masar da kaskantar da Fir’auna da mukarrabansa duk da karfi da yawn dukiya da mulki kuma ko a tunani Sahabban Annabi Musa (AS) ba su yi tunanin hakan ta wakana ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko:Zalunci da danniya mabudi ne na rugujewar ko wace hukuma ma’ana hukumar zalunci ba ta dawwama.

Na biyu:Daya daga cikin sunnar Allah masu rauni da ake zalunta za su ci nasar kan azzalumai.

Na uku:Karfin iko da dukiya komin yawansu idan ba ta hanyar Allah da gaskiya ba za su watse.

                                                • music*************

To madallah daga karshe za mu saurari karatun aya ta 60 zuwa 62 a cikin wannan sura ta Shuara’a.


فَأَتْبَعُوهُم مُّشْرِقِينَ


60-Sai suka riske su a lokacin fitowar rana.


فَلَمَّا تَرَاءى الْجَمْعَانِ قَالَ أَصْحَابُ مُوسَى إِنَّا لَمُدْرَكُونَ


61-To lokacin da jama’ar biyu suka ga juna,sai sahabban Musa suka ce: Hakika lallai mu za a cim mana.


قَالَ كَلَّا إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهْدِينِ


62- Musa ya ce: A’a ko daya ba za su riske mu ba,Hakika Ubangijina yana tare da ni,zai kuwa shiyar da ni hanyar tsira.

Kamar yadda Allah ya umarci Annabi Musa (AS) cikin dare ya umarci Bani Isra’ila su fice daga Masar zuwa takun maliya da safiya tayi shi ma Fir’auna dauke da babbar rundunarsa suka bi sahunsu.Ganin suna saman dawakin yaki cikin sauki suka kusa riske su . Kuma a fili take Annabi Musa (AS) da sahabansa da bas u da kariya ta yaki da kare kansu ko dawakin da za su tsiratar da rayuwarsu sai dakarun makiya suka killace su ma’ana ga dakarun makiya na bin su a baya a gabansu kuma ga ruwan maliya. Sai sahabbansa suka tafi gurin Annabi Musa (AS) suna ganin shi ne ke da alhakin wannan hali da suka samu kansu a ciki da cewa: yanzu za mu fada karkashin mamayar rundunar fir’auna kai da ka kawo mu wannan guri ko kayi tunani da hasshen wannan halin kunci? Annabi Musa (AS) wanda ya fito ne karkashin umarnin Allah cikin nucuwa da tawakkali da Allah sai ya amsa masu da cewa;Kar ku yi zaton Allah da ya umarce ni da fitar da ku ba zai bar mu ba cikin wannan yanayi ba da jimawa ba zai kubutar da mu tabbas.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Idan muka yi aiki da umarnin Allah ba zai taba barinmu cikin kunci da halin kaka ni kan yi .Don haka kar mu taba kai wag a tunanin kaka nikan yi face a kullum mu kasance masu dogaro da Allah.

Na biyu:Idan muka yi imani da alkawalin Allah ba za mu taba samin kanmu cikin damuwa da halin kaka ni kan yi sai dai rahama da lutifin Allah su lullube da nucuwa a matsayin jarinmu.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 63-68 (Kashi Na 658)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************

To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 217 zuwa 220 a cikin wannan sura ta shuara’a.


وَتَوَكَّلْ عَلَى الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ


217- Ka kuma dogara ga Mabuwayi Mai rahama.



الَّذِي يَرَاكَ حِينَ تَقُومُ


218- Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi don yin salla.


وَتَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ

219- Da kuma yayin jujuyawarka cikin masu sujjada.


إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

220- Hakika Shi Mai ji neMasani.


A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda Allah madaukakin sarki ya bawa manzonsa umarnin mayar da amsa kan maganganun maras tushe da ya kamata da makiya kafirai da mushrikai ke fada.To a yau ayoyin da muka saurare ci gaban wannan umarni ne da cewa manzon rahama da yayi hakuri da kokarin yin tawakkali da Allah saboda Shi Allah mai nasara da galaba ne kan komi da kowa ,Idan ya kudurta babu wani abu ko wani da zai iya jurewa kudurasa. Idan kuka yi dubi a cikin tarihin annabawa da manzonnin da suka gabata za ku fahimci haka ku kalli makomar fir’auna da namrudu duk da karfin ikoknsu da tarin dukiya sun hallaka da daukaka annabi Musa (AS) kamar yadda aka hallakar da al’ummomin da suka kafircewa kiran annaba da manzonni (AS) a baya.

Ci gaban ayar na cewa:Allah madaukakin sarki a kullum da kowa ne lokaci yana tare da kai ko da a lokacin da kake sallah da ibadodi a tsakanin jama’a ko da a lokacin da kake kiran mushrikai zuwa ga kadaita Allah da bauta.Ma’ana a dukan lokaci yana ji yana ganin abin da kake yi kuma masani ne kan komi ko zai taimaka maka don haka ka yi tawakkali da allah da ci gaba da riko da hanyar shiryar da al’umma da jurewa adawar kafirai .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:a maimakon ka yi dogaro da dukiya da matsayi na sahiri mafi dacewa shi ne dogaro da Allah madaukakin sarki wanda babu wani abu ko wani a wannan duniya da zai yi galaba kansa.

Na biyu: waliyan Allah suna cikin kulawa ta musamman ko da a lokacin da suke cikin yin ibada.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 221 zuwa 223.


هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَى مَن تَنَزَّلُ الشَّيَاطِينُ


221- Shin ba Na ba ku labara ba game da wanda shadanu suke saukar masa?


تَنَزَّلُ عَلَى كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ


222- Suna sauka ne kan duk wani makaryaci fajiri.


يُلْقُونَ السَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَاذِبُونَ


223- Suna kasa kunne gamaganganun shaidanun ,yawancin su kuwa makaryata ne.


Wadannan ayoyi da muka saurara sun sake kawo wani daga cikin zargin makiya maras tushe da mushrikai da kafirai key i kan Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarka kuma suna cewa shaidan ne yake gayawa manzo wasu maganganu bugu da kari cewa: Shaidan yana rudar matane makaryata da karfafa masu yada fasadi da sabo da yada karyayyaki. To wannan zargi nasu ya sabawa hankali da tunani na hakika domin Shi Manzon a rayuwarsa ba a taba saminsa da karya kuma su kansu Mushrikan makka sun shaida hakan da saninsa a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana da aikata gaskiya.Shi kum taba saminsa da yin karya da yanzu za ku zarge shi da raya karya da cewa sakon da ya zo maku da shin a alheri daga shaidan ne ? Bugu da kari abubuwan da ke kumshe a cikin kiransa babu wani abu face tsarkake zucciya ,alheri da aikata ayyukan alheri da kuma nisantar zalunci da fasadi .alhali shi shaidan yana maida hankali ne wajen yada banna da fasadi da batar da mutane da sanya wasiwasi a cikin zukatansu.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Zukatan da suka gurbata wasiwasin shaidan yana ratsa su.

Na biyu: Karya da makaryaci wani babban gumshiki ne na aikata banna da sabo da aikin shaidan da kuma yake ratsa zucciyar mutum shi shaidan din.

                                • MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 224 zuwa 227 a cikin shu’ara’a.


وَالشُّعَرَاء يَتَّبِعُهُمُ الْغَاوُونَ


224- Mawaka kuwa batattu ne suke bin su.


أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ


225- Ba ka san cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne lamari ba?


وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ


226- Hakika kuma suna fadar yin abin da ba sa aikatawa.


إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَذَكَرُوا اللَّهَ كَثِيرًا وَانتَصَرُوا مِن بَعْدِ مَا ظُلِمُوا وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ


227- Sai dai wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki nagari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan an zalunce su. Wadanda suka yi zalunci kuwa ba da dadewa ba za su san kowace makomar za su koma.

Wadannan ayoyi sun zo ne a karshen surar Shu’ara’ kuma suna bayani ne kan daya daga cikin zargin makiya kan manzon Rahama (SWA) da amsa masu da cewa:Manzo shi ba mawaki ba ne kuma dukan maganganunsa gaskiya kwai suka kumsa ba hassashen mawaka ba .

Abin lura a nan a lokacin da manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya bayyana .mawaka da dama ne ke rayuwa a yankin Hijaz kuma duk wakokinsu sun kumshi ta’assubanci jahiliya da soyayya tamkar mafarki da yake yake a tsakanin kabilu da fifita wani ko wata kabila kan karya da hakan ke kara masu karfin guiwa da nuna jarumta kuma a duk shekara a birnin Makka ana tara mawaka domin nuna da zabar wakar da tafi fice da kafa ta a jikin dakin Ka’aba. Don haka Mushrikan maka suke danganta sakon da Manzon Rahama ya zo da shi da wake irin na su domin kaucewa gaskiya da gangan da kaucewa karbar gaskiya da kawao rudani a tsakanin jama’a.Shi wake bisa al’ada bay a aiki da hankali da hujjoji na hankali kawai kawo misali da yayi hannun riga da hakika kamar cewa wani zaki ne ,giwa ko nuna shi da wata dabba mai rauni da zurfafawa ko da kuwa aikin wannan mutum sam bai daidai da abin da wannan mawaki ke fada ba. Daga cikin mawaka ana samin wadanda ke yin tunani da fadin gaskiya da fadin kusan abin da wani ke aikatawa amma sai sun kasance ma’abuta tunani da aiki na alheri kamar yadda kur’ani yayi nuni da su da cewa; mawaka mumunai salihai wakokinsu na karfafawa mutane ga tunawa da Allah da fadakar da su daga barci kan aikata sabo da banna a tsakanin jama’a ,su azzalumai su sani za su hallaka ,su kuwa mumunai su ci nasara.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Ita kwarewa nada amfani musamman wadda aka yi tunani kanta da taimakwa jama’a isa da tsira ba wadda za ta kai mutane ga bata ba.

Na biyu: a musulunci wake yanada matsayi amma wanda ke fadin gaskiya da karfafawa mutum ga karba da aiki da gaskiya da ruhin imani.

Na uku:Kur’ani ya sabawa wake domin Shi kur’ani littafi ne na shiriya da shiryarwa da karfafa ruhin mumunai da sanya nutsuwa a ciki da wajen zukatan mumunai.

Na hudu:Allah bay a zaluntar kowa sai dai ya shirya amma ga wanda ya so shiriyar.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 69-77 (Kashi Na 659)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                            • music************************


To madallah yanzu kuma za mu fara shirin na yau da sauraren karatun aya ta 69 zuwa 71 a cikin suratul Shu’ara’a.


وَاتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ إِبْرَاهِيمَ


69-Kuma ka karanta musu labarin Ibrahimu?


إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَا تَعْبُدُونَ


70-Lokacin da yace da Abbansa da kuma mutanensa: Me kuke bauta wa ?


قَالُوا نَعْبُدُ أَصْنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَاكِفِينَ


71-Suka ce: Muna bauta wa gumaka ne , sannan za mu ci gaba da bauta musu.

A cikin shirin da ya gabata mun yi bayani ne kan tarihin Annabi Musa (AS) da mutanansa to yau kuma za mu fara tarihin Annabi Ibrahima (AS).kuma kamar yadda ya zo a cikin littatafen tarifi a gaskiya Azar ba shi ne ma’aifin Annabi Ibrahim aba shi kanan ma’aifinsa ne ko shugaban kabila kamar yadda al’adarsu take da kiristoci suna kiran babban kabila ko aminsu da Uba. Hatta shi ma shugaban addini suna kiransa da wannan suna.Kuma mushrikan Makka suna da labara da masaniya kan Annabi Ibrahima da yin ayyukan Hajji a kowace shekara da yin dabi’o’insu na shirka saboda haka Allah ya cewa Manzonsa ,Annabin rahama cewa: don sanin tun farkon rayuwarsa yayi fada da yakar masu bautawa gumaka ne. Tun lokacin da annabi Ibrahima yana matashi ne ya fara fada da bautawa gumaka da tada mutanensa daga barci da yin tambayoyin fadakarwa ga mutanansa da sanya masu shaku da kankanto kan gumakan da suke bautawa da suka sassaka dahannunsu da kuma ba za su amfanar da su da komi ba ko cutar da su. Mushrikan lokacin Annabi Ibrahim aba su da wani abu da amsa gamsarshiya .

A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar:

1-Karanta tarihi da yin nazari a cikin tarihi zai ilmantar da mu abubuwa da dama da sanin mutanan kirki da lala domin zame mana darasi a rayuwa.

2-A gwagwarmaya da yakar wadanda suka kaucewa hanya ta akida da tunani a maimakon tunkararsu kai tsaye mu yi amfani da salon a jan hankali da fadakarwa da zai taimaka masu komowa kan hanya.

3-A kullum mu rika sanya tunani da hankali ba yin biyayya ido rufe ba.

4-Yawa ko rashin mataimaka kar ya zama zari’a ta hana mu tunkarar mabannata da fasike domin Annabi Ibrahim (AS) shi kadai ne ya tunkari mushrike da shugabanninsu.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 72 zuwa 74 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


قَالَ هَلْ يَسْمَعُونَكُمْ إِذْ تَدْعُونَ


72-Ibrahim yace : Shin suna jin ku kuwa lokacin da kuke kiran su?


أَوْ يَنفَعُونَكُمْ أَوْ يَضُرُّونَ


73- Ko kuwa suna amfanar ku ne ko suna cutarwa?


قَالُوا بَلْ وَجَدْنَا آبَاءنَا كَذَلِكَ يَفْعَلُونَ


74- Sukace : A’a mun sami iyayenmu ne suna aikata kamar haka.


A cikin wadannan ayoyi suna nuna mana yadda Annabi Ibrahima (AS) ta hanyar tambayoyi na fadakar da mutanansa cewa abubuwan da suke bautawa Gumaka suna saurarensu kuma ko suna amfanarsu da cutar da su da kuma amsar da suka bayar suna sun tarar da uwayensu da kakannunsu suna bautawa idan hakaai kuwa bas u amsawa Annabi Ibrahima (AS) tambayoyinsa ba kuma wannan zai sanya su zurfafa tunani da fahimtar gaskiya da kuma binta idan gaskiyar suke nema da son aiki da ita.Abin mamaki su kansu mushrikai sun san gumaka bas u da wani amfani da cutarwa amma suka nace da ci gaba da bauta masu kawai don yin riko da ta’assibanci da kabilanci iyaye da kakannu .Hakan ya hana su aiki da hankali da tunanin da Allah ya huwace masu kuma hakan ya sanya sun koma baya da fadawa cikin duhun jahilci da kafirci.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: dole mu bautawa wanda ya san halin da muke ciki da zai iya warware mana da amfanar da mu kuma babu wani in ba Allah wanda ya halicce mu.

Na biyu:A tsawon tarihin duniya nan jahilci da riko ido rufe na taassubanci da kabilanci ke kai wag a fadawa tarkon bata da tabewa.


                                          • music*****************

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 75 zuwa 77 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


قَالَ أَفَرَأَيْتُم مَّا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ


75- Ibrahim yace :Yanzu kam ga abin da kuka kasance kuna bauta wa din nan .


أَنتُمْ وَآبَاؤُكُمُ الْأَقْدَمُونَ


76-Ku da iyayen naku da suka gabata.


فَإِنَّهُمْ عَدُوٌّ لِّي إِلَّا رَبَّ الْعَالَمِينَ


77-To hakika su abokan gabata ne sai fa Ubangijin talikai.

Wadannan ayoyi na nuna ma yadda tattaunawa ta kasance tsakanin Annabi Ibrahima (AS) da shugabannin mushrikai na mutanansawadanda duk da kokarin da yayi na fadakar da su sun ki su fahimta da amince da karbar gaskiya.Inda suka nace da cewa suna riko da abin da uwaye da kakannunsu suke bautawa duk da cewa sun sani sare babu wani abu da ya cancanci a bauta masa bace Allah wanda babu wani bau taimaka mana da zai iya cutar da mu bayansa duk wani abu da ke a wannan duniya ba zai iya amfanar da mu ku cutar da mu ba matukar Allah bai bas hi wannan iko ba .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubu uku kamar haka:

Na farko:Yin imani da Allah mahalicci mai ikon wannan duniya dole ya kasance ta hanyar hankali da karfin imani ba ta hanyar takalidin iyaye da kakannnu ba da hakan ba shi da wani amfani .

Na biyu: Yin bahasi da jayayya a addini dole ta kasance karkashin ma’auni na hankali da girmamawa kamar yadda annabawa da manzonnin Allah (AS) suke yi.

Na uku:Masu yin shirka da bautawa abubuwa kan karya da hassashe su ne makiya da hana mutum kai wa ga sa’ada.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 78-82 (Kashi Na 660)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.





To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 78 zuwa 80 a cikin suratul Shu’ara’a.


الَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهْدِينِ

78-Wanda Shi ne Ya halicce ni ,sannan Shi Yake shiryar da ni.


وَالَّذِي هُوَ يُطْعِمُنِي وَيَسْقِينِ


79- Kuma Wanda Shi ne Ya Ke ciyar da ni kuma Ya shayar da Ni.


وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ


80- Idan kuma na yi rashin lafiya,to Shi ne zai warkar da ni.


A cikin shirin da ya gabata kun ji irin tambayoyi na hankali da annabi Ibrahima yayi wa masu bautawa gumaka da bayanin yadda gumaka bas u tabuka mana komi a rayuwa da yadda suka kasa amsa masa tambayoyinsa face cewa suna bin abin da uwaye da kakannunsu suka bar masu.

To a shirin nay au za mu ji yadda tattaunawa ta ci gaba da wakana tsakanin masu bautawa gumaka da Annabi Ibrahim (AS) da ya cewa masu: Haka allan da kuke bautawa yake da bay a iya tabukawa kansa balantana waninsa komi.Amma Ni Allan da na ke bautawanShi ne ya halicce ne kuma rayuwa ta baki daya tana hannunsa.Shi ne y aba ni hankali da tunanin zabar hanya mai kyau da banbanta ta bata da tabewa.Kuma y aba ni hankali ma sanin mai kyau da maras kyau da zabar shiriya. Bayan haka y aba ni wadata da ciyar da ni da kuma shayar da ni .Idan ban i da lafiya ya warkar da ni .Gabobin jikina da ruhina ba ki daya suna karkashin ikonsa



A cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa biyu masu matukar muhimmanci a rayuwarmu da addininmu.

Na farko:Bayan ni’ima ta halitta babbar ni’ima it ace ta shiryarwa daga Allah ga mutum.

Na biyu:Magana wata hanya ce ta waraga amma lafiya tana hannun Allah kuma shi ne yay i gangar jikinmu ya kuma yi rashin lafiya da kuma lafiyar da ba mu ilimi da hankalin sanin maganin da za mu sha don haka komi yana hannunsa.

                  • MUSIC***********

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun ayoyi na 81 zuwa 82 a cikin wannan sura ta Shu’ara


وَالَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحْيِينِ


81- Kuma wanda zai kashe ni sannan Ya sake raya ni.


وَالَّذِي أَطْمَعُ أَن يَغْفِرَ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ


82-Wanda kuma nake kwadaayin Ya gafarta min kurakuraina ranar alkiyama.


A cikin ayoyin da suka gabata Annabi Ibrahima (AS)yayi nuni da yadda rayuwarmu baki daya ke hannunn Allah a wannan duniya to wannan ayyoyi ci gaban bayanin ne amma tasirin Allah a rayuwarmu bayan mutuwa domin ta haka masu bautawa gumaka su sani rayuwa a wannan duniya da bayan mutuwa da ita kanta mutuwa da ita kanta wannan duniya da duk wani abu da ke cikinta suna hannun Allah mai iko da kudura kan komi da kowa.Ko da mutuwa ta dauki raina Allah bay a bari na yana tare da ni a kullum a ko’ina da sake rayar da ni da kowa a wata duniyar da yiwa kowa sakayya na ayyukan alheri da ya aikata ko kuma azabar mummunan aikin aikinsa.

Allah mai rahama da jin kai yayi mani komio ba wai kawai a wannan duniya bay a ya lullube ni da ni’imomi hatta a lahira lutifinsa ne zai lullube ni da fatar ya yafe mani duniya da lahira. Su Annabawa da manzonni (AS) bas u sabo amma a kullum suna neman gafara da rahamara Allah.Kuma burinsu shiryar da dukan al’umma kan tafarkin Allah duk da cewa lamari ne mai matukar wuya dominn yawancin mutane sun zabi bin tafarki da tarkon shaidan .

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka.

Na farko: Mutuwa ba karshen rayuwa b ace ga mutum sai dai bude sabuwar rayuwa.

Na biyu:Kar mutum ya nuna jiji da kai da dogaro da aikinsa kawai ya rika neman taimakon Allah.

Na uku:Neman gafarar Allah da rahamarsa salo da tushe ne na Annabawa da manzonnin Allah (AS)

Na hudu: dukan abin da mutum ke bukata na zahiri da badini yana hannun Allah ne.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 83-89 (Kashi Na 661)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                      • MUSIC*********

To Madallah masu saurare za mu fara shirin nay au tare da sauraren karatun aya ta 83 da 84 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


رَبِّ هَبْ لِي حُكْمًا وَأَلْحِقْنِي بِالصَّالِحِينَ


83-Ubangiji ka hore min sani kuma ka risker da ni da bayinka nagari.


وَاجْعَل لِّي لِسَانَ صِدْقٍ فِي الْآخِرِينَ


84-Kuma ka sanya abin kyakyawan Ambato gare ni ga na baya.

A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda Annabi Ibrahim (AS) ya kwatamta Allansa da na masu shirka domin ya fadakar da su masu bautawa gomaka cewa Allansu babu wani abu da yak e tabukawa ko cutarwa dukan lamura suna hannun Allah da ya halicci wannan duniya abin da ke cikinta.

A cikin wadannan ayoyi da muka saurara da sauran ayoyi Annabi Ibrahima 9AS) ya gabatar da wasu bukatu nasa ga Allah wanda ya fara ambatonsa da Kalmar Rabbi da hakan ke nuni da dangantaka ta kusa da kusanci tsakanin mutum da mahaliccinsa. Kuma ba wai kawai Allah ya halicci wannan duniya da abubuwan da ke cikinta ,yana kuma tare da mu a kullum da kuma amsa mana a duk lokacin da muka Ambato shi da gabatar da bukatarmu a gare shi kuma ya fi komi kusa da mu.

Annabi Ibrahim (AS) daga farko ya bukaci Allah da y aba shi hikima ta fahimtar hakika ta hanyar ilimi da sanin ya kamata karkashin ma’auni na hankali da hikima. Bukatarsa ta biyu kuwa mataimakansa su kasance salihan bayun Allah da za su taimaka masa wajen sabke nauyin manzonnci.Har ila yau ya bukaci Allah da ya taimaka masa wajen zartar da wannan ayyuka na tunani da aikace da kare shi daga kasawa ko yin kasa a guiwa ya kuma kara daukaka shi ta fuskar ilimi da aiki.Bukatarsa ta uku ma’ana wannan aiki nasa da tunaninsa ya ci gaba a tsakanin al’ummomi ko da a bayan ransa ne.Wannan hanya tasa ta kadaita Allah da bauta ta ci gaba da tunawa da shi da aikin alherin da ya bari .a takaice yana son zama abin koyi a tsakanin mutane da kuma salihan bayun Allah su ci gaba da riko da ta farkinsa.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu:

Na farko:A duk wani aiki musamman na kamala da ya shafi ilimi da ma’anawiya mu nemi taimakon Allah.

Na biyu:Ilimi da hikima wata kyauta ce ta Allah da yake cusawa a cikin zukatan bayunsa.

Na uku:Farkon aiki da bayi mai kyau niya mai kyau da tunani mai kyau da hangen nesa mai kyau.

Na hudu:Samin hikima da abukai salihai a cikin jama’a babbar sa’a ce ta isa da kamala ta karshe.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 85 da 86.


وَاجْعَلْنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ النَّعِيمِ


85-Kuma ka sanya ni cikin magada Aljannar ni’ima.


وَاغْفِرْ لِأَبِي إِنَّهُ كَانَ مِنَ الضَّالِّينَ


86-Kuma Ka gafarta wa Abbana,hakika shi ya zamo cikin batattu.

Wadannan ayoyi na nuni da ci gaba da adu’o’in Annabi Ibrahima da gabatar da bukatunsa ga Allah kuma bukatarsa ta hudu ta shafi lahira ce bayan mutuwa.Dukanmu dole a dabra da duk wani kokari da za mu a wannan duniya mu tuna da rayuwar lahira da yi mata tanadi.Don haka mu nema a gurin Allah da ya lullebe mu da lutifinsa da falalarsa da sanya mu cikin bayunsa da za su shiga gidan aljanna mai cike da ni’imomi ba karewa ,aljannar da lambunta ya ni’imantu da yayan marmari iri-iri. A wannan duniya da na gadon lambu cike da itatuwa da yayan marmari ba iyaka daga ubansa ba tare da ya wahala ba. To Haka Allah ma yayi wa bayunsa salihai gidan aljanna ba don aikinsu ba sai don falala da lutifinsa .Da fatar Allah ya sa muna daga cikin bayunsa salihai da za su shiga wannan aljanna a ranar lahira.

Annabi Ibrahima (AS) ya ci gaba da yin addu’a a ma wannan karon neman gafarar Allah ga baffansa da yake daya daga cikin shugabannin mushrikan zamaninsa kuma Annabi Ibrahima (AS) yana tunanin zai yi imani da Allah don haka yayi masa alkawalin nemar masa gafara a gurin Allah.To Annabi Ibrahim (AS) ya cika alkawalinsa da nemar masa gafarar ,amma baffansa yak i yin imani da Allah da kadaita shi da bauta daga karshe Annabi Ibrahim(AS) yayi bara’a da shi.

A cikin wadannan ayoyi za mu dauki darasin abubuwa biyu:

Na farko:Niimomi maras maras karewa masu dawwama ,Allah yayi wa bayunsa salihai tanadi ba don aikinsu sai don falala.

Na biyu: Addu’a da makusanta da uwaye da kakannnu yana daga cikin sunnar annabawa da manzonnin Allah.


                  • MUSIC************

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 87 zuwa 89 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


وَلَا تُخْزِنِي يَوْمَ يُبْعَثُونَ


87- Kada kuma ka kunyata ni ranar da za a tashe su.


يَوْمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ


88-Ranar da dukiya da yayaye ba sa amfani.


إِلَّا مَنْ أَتَى اللَّهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ


89-Sai dai wanda ya zo wa Allah da tsarkakkiyar zuciya.

Daga karshe addu’o’in Annabi Ibrahim (AS) sun kasance kan damuwa da nauyin da ya rataya a kansa na annabci da fatar ganin ya sabke wannan nauyi kamar yadda ya kamata kamar yadda Allah ya bukace shi ba tare da wani kuskure ba daidai da kyayar zarra duk da ganin wannan aiki nada nbauyi da muhimmanci matuka kuma ba karamin aiki ba ne domin duk wannan ya kasa isa da aiwatar da aikin da ya kamata babu wani da zai iya taimaka masa musamman a lahira domin idan a wannan duniya mutum na iya saye komi da kudi hatta idan da kudi mai leifi a wanke shi tamkar bai yi leifi ba da bada cin hanci da rashawa to a lahira duk wata dukiya da matsayi na zahiri bas u da wani amfani kuma bas u da wani abu da za su iya yiwa wani mutum .Idan a wannan duniya da yana iya taimakawa uwayensa to a lahira kowa ta kansa yake yi ba zai iya taimakawa waninsa ba .Hatta uwa da a wannan duniya da ta fi kowa son danta da nuna masa kauna tana sha’afa da danta domin ta kanta take ba ta da lokacin waninta. Kawai abin da ke taimakawa mutum shi ne zucciyarsa da aikinsa na alheri da mutum ya aiwatar da niyar neman kusanci da Allah da zucciya mai tsarki a ranar lahira.Kuma wanda zucciyarsa ta gurbata da sabo da shirka da kafirci da riya ba shi da wani rabo a lahira rabonshi yana nan a wannan duniya.

A cikin wadannan ayoyi za mu iya ilmantuwa da abubuwa hudu:

Na farko: Mutum a kullum kar ya kasance mai jiji da kai da takama da aikinsa .Ya kasance mai neman taimakon allah a wannan duniya da gobe kiyama.

Na biyu:Damuwa a ranar kiya it ace damuwa mafi tsanani .

Na uku:Duk wani abu na mada a wannan duniya da ya hada da dukiya,yaya da mukami bas u da wani amfani a lahira.

Na hudu:Ayyukan alheri sune abin garbuwa da aka tsarkake zucciya da niya ba wadanda suka gurbata da shirk aba.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.

Suratush Shu'ara Aya Ta 90-101 (Kashi Na 662)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




                            • Music**********

To Madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 90 zuwa 93 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


وَأُزْلِفَتِ الْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ


90-Aka kuma kusantar da Aljanna ga masu tsoron Allah.


وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِلْغَاوِينَ


91-Kuma aka bayyanar da wutar Jahannama ga batattu.


وَقِيلَ لَهُمْ أَيْنَ مَا كُنتُمْ تَعْبُدُونَ


92-Aka kuma ce da su: Ina abubuwan da kuka kasance kuna bauta wa.


مِن دُونِ اللَّهِ هَلْ يَنصُرُونَكُمْ أَوْ يَنتَصِرُونَ


93-Wadanda ba Allah ba ? Shin za su taimake ku ,ko za su taimaki kansu?

Wadannan ayoyici gaban bayani ne kan ayoyin da ke bayani kan rayuwar Annabi Ibrahim (AS) kuma yana siffanta Aljannna da kuma wutar jahannama inda ya fara da da gungun biyu na wadanda za su shiga aljanna da kuma gungun batattu wadanda za su shiga wuta da aka yi masu tanadi .Su wadanda suka shiga aljanna sun samu wannan damar ce saboda tsoron Allah da ayyukan alheri da suka aikata karkashin kyakkyawar niya ta nesan kusancin Allah.Amma su yan wuta kuwa sun samu kansu cikin wannan azaba sakamakon mummunan aikin da suka aikata a wannan duniya da kuma ganganci. Kuma lokacin da suka ga wutar azaba a gabansu babu wani da zai kubutar da su da kare su daga shiga wutar hatta abubuwan da suka bautawa ba Allah b aba zai iya taimakon kansa ba balantana su.Amma su mumunai na cikin falala da ni’ima.

A cikin wadannan ayoyin za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko:Aljanna da wutar jahannama a lahira na zuwa ne a daidai lokacin da an rufe kofofin ayyuka balantana a gyara ko a kara ayyukan alheri.

Na biyu: Matsayin mumuni da tsoron Allah ya kais hi matsayin da hatta lahira za ta gabatar da kanta a gabansa.

Na uku: Gumaka da mutum da bas hi da wani karfi na kare kansa yaya zai yi a ranar lahira ?.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun aya ta 94 zuwa 98 >



فَكُبْكِبُوا فِيهَا هُمْ وَالْغَاوُونَ


94- Sannan aka kikkifa su cikinta watau su da batattu.


وَجُنُودُ إِبْلِيسَ أَجْمَعُونَ


95-Da kuma rundunar Iblis gaba daya.


قَالُوا وَهُمْ فِيهَا يَخْتَصِمُونَ


96- Sai suka ce,alhali suna jayayya da juna.


تَاللَّهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ


97-Hakika mu mun kasance a duniya cikin bata bayyananne.


إِذْ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ


98-Domin muna daidaita ku da Ubangijin talikai.

Kamar yadda wasu ayoyin kur’ani suka yi bayani a ranar lahira ,Allah zai tambayi gumaka amma ba za su iya bada amsa ta kare kansu kuma bas u da wani karfi na kare kansu balantana mushrikai da suka bauta masu kuma dukansu baki daya za a sanya su wuta da kona su. Bayan shiga wutar za su rika zargin junansu inda shaidan da mushrikai da gumaka kowa zai zargi dan uwansa a daidai lokacin da wannan zargi bas hi da wani amfani bayan samin kansu cikin wutar jahannama.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko: Abukan da aikata sabo ya hada su a wannan duniya da nuna kauna ta zahiri a tsakaninsu a lahira za su tsani juna da zargin juna a lokacin da suka ga azabar wuta a gabansu babu makawa za su shiga cikinta.

Na biyu:Mutum a lahira zai farga da tashi daga barci amma a daidai lokacin da guri ya kure babu wani amfani.

                          • music*************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 99 zuwa 101 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


وَمَا أَضَلَّنَا إِلَّا الْمُجْرِمُونَ


99-Ba kuwa wadanda suka batar da mu sai shaidanun shugabanninmu.


فَمَا لَنَا مِن شَافِعِينَ


100.To yau ba mu da wani mai ceton mu.


وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ


101-Ba kuma wani aboki na jika.


Daga karshe mushrikai da gumaka za su ce:Babu wadanda suka tunkuda mu a cikin wannan hanyar da batar da mu kamar masu kudi da mukami da suka yi mummunan amfani kanmu da fadawa ytarkonsu na bata da yi mana alkawalin samin dacewa da jin dadi.Amma yau mun fahimci mun tabe saboda babu da wani da zai ceto mu ko abokin da zai kasance tare da mu .Ba ga gumaka ba ko wani da muka yi shirka tare ko kuma wani daga cikin mumunai da zai taimaka mana da kubutar da mu daga cikin wannan kumci da tabewa gas hi Allah yayi fushi da mu.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko: A lahira babu wani da zai karbi leifinsa shirkai da gumaka da shaidan za su rika zargin juna ne.

Na biyu: A ranar kiyama akwai ceto amma ba za ta shafi mushrikai ba.Manzonnni da Annabawa da Ma’asumai kawai za su ceto mumunai ne da suka cancanci ceton.

Na uku:Mutum a kiyama yana bukatuwa da aboki na gari da zai taimaka masa kuma aboki na gari shi ne da zai taimaka maka a wannan duniya da kuma gobe kiyama kuma su ne ma’abuta imani.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 102-109 (Kashi Na 663)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




                  • MUSIC***********

To madallah da farko za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun aya ta 102 zuwa 104 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


فَلَوْ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ


102- To ina ma da za mu samu damar komawa ,sai mu zamanto daga muminai.


إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ


103-Hakika a game da wannan lallai akwai aya ,kuma yawancinsu ,bas u zamanto masu ba da gaskiya ba.


وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ


104-Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi ne Mabuwayi Mai jin kai.


A cikin shirin da ya gabata mun ji yadda mushrikai da kafirai za su yi nadama lokacin da suka ga azabar wutar jahannama a gabansu da zargin juna. To a wadannan ayoyi Allah madaukakin sarkiza su yi fatar Allah y aba su damar sake komawa duniya don aikata ayyukan alheri da zama mumunai suna ma su cewa: kashe dama mu samu wata dama ta komawa duniya da zamantowa cikin mumunai.Yanzu mun fahimci hanyar da muka bi a duniya ta bata da tabewa ce ,hanyar hallaka.Amma duk wata nadama wannan rana ba ta da wani amfani domin kuwa babu dama da hanyar komawa wannan duniya.Kamar yadda kur’ani ke cewa:A duniya akwai alamomi masu yawa na shiriya amma sun ki bi da fahimtar gaskiya ko karbarta.Duk da tsawon kwanaki da Allah ya ba su don barkin bata da rungumar hanyar gaskiya ,sai dai sun ci gaba da yin riko da hanyar bata da hallaka har zuwa lokacin da mutuwa ta riske su .Wata nadama ce suke bayyanawa ta fatar baki ko da kuwa an bas u damar komawa duniya ba za su kasance cikin muminai ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Ranar kiyama ba ranar nuna da dam aba ce mai amfani domin babu damar gyara leifi da kuskuran baya.

Na biyu: Idan mutum mai jayayya ne da kin karbar gaskiya ko ayoyi da manyan alamomi na Allah ba za su taimaka masa kai wa da karbar shiriya.

Na uku:Allah a daidai lokaci guda mai rahama da jin kai ne haka kuma mai kudura da izza ne ,yana azabtar da mutum mai jayayya da kin karbar gaskiya.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun ayoyi na 105 zuwa 107 .


كَذَّبَتْ قَوْمُ نُوحٍ الْمُرْسَلِينَ


105-Mutanen Nuhu sun karyata manzanni.


إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ


106-Lokacin da dan uwansu Nuhu ya ce da su:Yanzu ba za ku ji tsoron Allah ba?


إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ


107-Hakika ni Manzo ne amintacce a gare ku.

Bayan da muka ji takaitaccen tarihin annabi Ibrahim (AS) da mutanansa yanzu kuma za mu fara da ayoyin da suke bayani kan takaitaccen tarihin annabi Nuhu (AS) da abubuwan da manzanncinsa ya kumsa. Abin lura akarkashin tarihi Annabi Ibrahima (AS) ya zo ne bayan annabi Nuhu (AS) kuma hatta a kur’ani ma Annabi Ibrahima (AS) yayi aiki ne da shari’ar da aka turo Annabi Nuhu (AS).To amma shi kur’ani da yake ba littafin tarihi ne ba bai yi aiki da tsarin rubutun tarihi bay a fara da kawo tarihin annabi Nuhu (AS) kafin ya kawo tarihin rayuwar annabi Ibrahima (AS).

A cikin kur’ani an ambaci sunan Annabi Nuhu (AS) so 43 kuma Allah ya aika masa da sallama da aminci na musamman don girma shi. Sai dai kash ,Al’ummar da aka turo wa Annabi Nuhu (AS) sun karyata shi.Alhali kur’ani mai girma ke cewa;al’ummar annabi Nuhu(AS) sun karyata dukan annabawa da manzonnni saboda dukan annabawa hadafinsu guda ne kuma karyata daya daga cikinsu tamkar karyata sauran ne.Duk annabi a lokacinsa mutum ne mai gaskiya da rikon amana kuma mutanansa sun yi ammana kan hakan .Amma girman jayayya da girman kai ke sanya kafirai da masu adawa da annabawa kin amincewa da maganar da bayanin gaskiya da hakika daga annabi da manzon Allah kawai don kare jin dadin wannan duniya da makamin da suke kai.

Manzonni suna kollon dukan mutane a matsayi guda nuna masu kauna da tambayarsu :mi yasa ba ku jin tsoro da kunyar wanda ya halicce ku da komowa daga rakiyar abin da kuke bauta ta hanyar shirka? Amma su kafirai da mushrikai hatta lokacin sauraren annabawa da manzonni ba su da shi sai su rika guje masu da nisantarsu ta haka ba za su ji abin da suke fada masu ba ko za su shiriya.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Dukan annabawa da manzonnin allah burinsu daya don haka karyata daya daga cikinsu tamkar karyata dukansu ne.

Na biyu:Su annabawa da manzonnin Allah na rayuwa ne daidai da sauran mutane ba tare da sun nuna su sun fi ba ko nuna kansu fiye da sauran mutane,ko nuna su shugabanni ne.

Na uku:Domin fadakar da mutane ko mutum daga barci ana amfani da salon dora ayar tambaya ba salon bada umarni ba.

Na hudu:Manzonnin Allah a tsakanin al’ummominsu mutane ne masu tarihi mai kyau da mutane ke girmamawa .

                      • MUSIC**********


Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 108 da 109 a cikin suratun Shu’ara’a.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ


108-To ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى رَبِّ الْعَالَمِينَ


109- Ba na kuma tambayar ku wani lada a game da shi isar da manzancin.Ladana yana wajan Ubangijin talikai kawai.


A wannan karon ma magana ce ta tsoron Allah saboda abin da ke sanya mutum aikata sabo da mantawa da Allan da ya halicce shi da irin ni’imomin da ya mana masu tarin yawa.kuma ta wannan salo ne Annabi Nuhu (AS) ke son fadakar da mutanasa da cewa; Ta yaya ne za ku bijirewa umarnin Allah alhali a kowace rana da dare shi ke arzita ku ci da sha da umarninsa kuke rayuwa.Don haka ku nisanta da hanyar sabo ku rungumi hanyar gaskiya da samin tsira inda y ace masu: Ni Allah ne ya turo ni domin shiryar da ku idan kuka saurari abin da na ke cewa da aiki da shi za ku samu tsira da dacewa domin amfanin aikin da kuka yi zai koma hgare ku ne ban i ba.Ni ba ina neman suna da makami ko dukiya ba ne kuma ban a son wata sakayya ko lada a gare ku .Idan na aiwata da nauyin da aka dora mani na manzonci Allah ne zai ba ni ladan da babu wani da zai iya ba ni shi.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:a lamari na shiryar da tarbiyartar da mutane a rika tunatar da su jin tsoron Allah a kai akai don kar su fada tarkon gafala da kaucewa hanya.

Na biyu:Masu yada addini kar su yi kwadayin wani abu a gurin mutane kawai su yi abu saboda Allah tare da dogaro da Allah ta haka abin da suke fadi zai yi tasiri da ratsa zukatan mutane da fatar Allah ya sa mu dace amin.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 110-115 (Kashi Na 664)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




To madallah masu saurare za mu fara shirinmu nay au ne da sauraren karatun aya ta 110 da 111 a cikin suratul Shu’ara’.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ


110- To ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


قَالُوا أَنُؤْمِنُ لَكَ وَاتَّبَعَكَ الْأَرْذَلُونَ


111-Suka ce : Yanzu ma ba da gaskiya da kai alhali mabiyanka wulakantattu ne?

A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa;Annabi Nuhu (AS)ya kirayi al’ummarsa da su ji tsoron Allah da yadda ya nuna masu hanya madaidaiciya ta rayuwa mai inganci da zama abin koyi a rayuwarsu a matsayinsa na manzo daga Allah.To wadannan ayoyi ma abin da suke nuni a kai ke nan amma masu adawa da annabi Nuhu daga cikin mutanansa sun nuna bakar adawarsu kan wannan bayani na shirya da cewa; wadanda suka yi imani da kai da kuma suke tare da ke mutane ne talakkawa masu rauni ,bas u da dukiya bas u da mukami kuma su ne mutane dake karkashin ikonmu bas u da wani matsayi a cikin al’umma don haka ta yaya z aka yi zaton za mu zama daya da su da binka tamkarsu.

Su kafirai da masu adawa da waliyan Allah a kullum suna kollon rayuwar duniya a ma’auni na zahiri,da daura ta a ma’aunin dukiya da mukami da shahara sai gashi mabiya annabi Nuhu (AS) ba su da daya daga cikin wannan ma’auni na su. Alhali a gurin Allah madaukakin sarki da manzonsa Annabi Nuhu (AS) matsayi da daukakar mutum ,ma’auninta Takawa da tsarki zucciya da aiki ne .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Dukiya da shahara na dama nata muni daga ciki akwai sanya mutum girman kai da jiji da kai da kollon sauran mutane masu rauni da talakkawa.

Na biyu: Kowane mutum yay i wa kansa hisabi na neman gaskiya tun kafin lokaci ya kure masa.

Na uku; a koyarwa irin ta annabawa da waliyan Allah dukan mutane matsayi guda suke da shi babu wani banbanci a tsakaninsu.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari karatun ayoyi na 112 da 113.


قَالَ وَمَا عِلْمِي بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ


112- Yace Ba ni da sani game da abin da suka zamanto suna aikatawa.


إِنْ حِسَابُهُمْ إِلَّا عَلَى رَبِّي لَوْ تَشْعُرُونَ


113-Ya ce: Hisabinsu kawai yana wajan Ubangijina ne ,da za ku gane.

Su kafirai daga cikin mutanan annabin Nuhu(AS) na fakewa da guzuma ne su harbi karsana don haka Annabi Nuhu(AS) ya ba su amsa da cewa:Nauyin da ya rataya a kai ne shi ne isar da sako ga dukan mutane da fahimtar da su gaskiya daga cikin karya da nuna masu hanya madaidaiciya.Wata kungiya ko gungun mutane zai yi imani da bada gaskiya ,bay a karkashin ikona ,har ila yaumai suka aikata baya shi ma bay a karkashin ikona.Abu mai muhimmanci a yanzu mai suke aikatawa da yin imani.Idan ku ma ku yi tunani za ku fahimci sakayyar ayyukan da suka aikata yana gurin Allah ban i ba saboda haka kar ku fake da abin da suka aikata a baya da matsayinsu ya hana ku yin imani da bayyana adawarku a fili.

A tsari da al’adar addini mu ba mu da hakki na yin bincike a cikin ayyukan mutane da raunata su da fallasa su.Mu muna aiki ne da zahirin rayuwa da ayyukan da suke aikatawa kuma idan mutum yayi imani ba mu da hakkin kin karbar imaninsa saboda aikinsa na baya sai mu barwa Allah yanke hukumci.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu.

Na farko: Ilimin Manzonni kan ayyukan da mutane suka aikatawa da suke aikatawa kuma Allah ne ke sanar da su .

Na biyu: Hisabin mutane yana hannun Allah ne mu da sauran mutane babu wanda yake da ikon hukumta wani kan aikinsa sai Allah da ya halicce mu.

                                  • music*********

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 114 da 115.


وَمَا أَنَا بِطَارِدِ الْمُؤْمِنِينَ


114-Ni kuma ba mai korar muminai ba ne.


إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ

115- Ni mai gargadi mabayyani ne kawai.

Masu adawa da Annabi Nuhu (AS) kafin su yi imani da shi sun gitta sharadin cewa sai ya kori wadanda suka yi imani da shi talakkawa da masu rauni na zahiri idan yayi haka za su yi imani da shi .Saidai wannan sharadi nasu fakewa ce kawai domin kuwa ko da Annabi Nuhu (AS) ya aikata abin da suka ce ba za su yi imani ba za su kawo wani sabon sharadi. Amma Annabi Nuhu (AS) ba da wata wata ba kai tsaye yayi watsi da wannan bukata tasu da cewa;aikina shiryarwa da fadakarwa kan hanya madaidaiciya ta gaskiya. Ni ban i da burin tara dukiya da neman shahara balantana ya bani damar korar talakkawa da neman masu kudi da mukami.


A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda biyu .

Na farko:A kullum idan makiya suka gabatar da wata bukata da ba ta dace ba kai tsaye a ba su amsa kar a bas u damar da za ta bakantawa mumunai rai.

Na biyu:A mahanga da koyarwar annabawa da manzonni da waliyan Allah imani ne ke da matsayi da daukaka ba dukiya da mukami na zahiri ba da shahara a cikin al’umma.




Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 116-127 (Kashi Na 665)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 116 zuwa 118.


قَالُوا لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَا نُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ الْمَرْجُومِينَ

116-Suka ce: Ya Nuhu,wallahi idan ba ka daina fadar abin da kake fada ba,lallai za ka zamanto daga cikin wadanda za a jefa.


قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوْمِي كَذَّبُونِ


117-Ya ce: Ya Ubangijina,hakika mutanena sun karyata ni.


فَافْتَحْ بَيْنِي وَبَيْنَهُمْ فَتْحًا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِي مِنَ الْمُؤْمِنِينَ


118- Ka yi hukunci tsakanina da sun a gaskiya,kuma ka tserar da ni da wadanda suke tare da ni daga muminai.

A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda Annabi Nuhu (AS) ya kirayi mutanensa zuwa ga kadaita Allah da bauta da nuna tsoran Allah amma masu adawa da shi sai suka ki amincewa da wannan kira nasa na gaskiya tare da fakewa da cewa wadanda suka yi imani da shi talakkawa ne da bas u da wani matsayi a tsakanin al’umma don haka sub a za su yi imani da shi ba. To wadannan ayoyi na nuni da fushi da bacin ran da masu adawa da Annabi Nuhu suka nuna a fili da yi masa barazanar idan bai daina wannan kira nasa ba za su dauki mataki mai tsanani kansa.Amma Shi Annabi Nuhu (AS) ganin masu adawa kafirai mushrike ba za su taba yin imani da shi ba,sai ya bukaci Allah Madaukakin Sarki da iko kowa da ya shika tsakaninsu da tsirar da Shi da sauran mumunai daga sharrin mushrikai.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:barazanar duka da zagi da kisa daya ne daga cikin salo da maganganun masu adawa da manzonni da waliyan Allah a tsawon tarihi.Amma wannan barazanar ba ta sawa waliyan Allah daina yin riko da hanya madaidaiciya .

Na biyu:A kullum mu rika neman taimakon allah a hanyar gwagwarmaya da makiya Allah da masu girman kai da dagawa da zalunci.Ta haka sai mu samu tsira da dacewa daga Allah.

Yanzu za mu saurari karatun aya ta 119 zuwa 122


فَأَنجَيْنَاهُ وَمَن مَّعَهُ فِي الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ


119- Sai Muka tserar da shi da wadanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwan da aka makare.


ثُمَّ أَغْرَقْنَا بَعْدُ الْبَاقِينَ


120- Sannan bayan haka Muka nutsar da sauran.


إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ


121- Hakika a game da wannan lallai akwai aya ,yawancinsu kuwa bas u kasance masu ba da gaskiya ba.


وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ


122- Hakika Kuma Ubangijinka lallai Shi ne Mabuwayi Mai jin kai.

Kamar yadda ya zo a cikin wasu ayoyin kur’ani .Allah ya umarci Annabi Nuhu (AS) yak era wani babban jirgin ruwa bayan da ya kamala ya sanya kowane jinsi na halittun Allah mace da namiji da kuma hada da mumunai da suka yi imani da shi.Kuma wannan jirgin duk wanda ya shiga cikinsa ya samu tsira lokacin da azabar allah ta sabka kuma lokacin azabar ya zo kan wadanda suka kafircewa kiran shirya da Annabi Nuhu (AS) yayi masu inda Allah ya umarci kasa da ta fito da ruwan da ta kumshe a cikinta ita sama aka umarce ta ta zuwar da ruwan sama da hakan ya haddasa gagaramar ambaliyar ruwa da hallakar da mushrikai da kafirai sai wadanda suka shiga cikin jirgin tsira na Annabi Nuhu(AS). Ko shakka babu hallakar kafirai da tsirar mumunai wata babbar ay ace da ke nuni da iko da karfin Allah ,amma wasu dake cikin wannan jirgin tsira bas u yi imani da annabi Nuhu (AS) ba da yin imani da Allah kamar yadda masu iya magana hausawa ke cewa: dan adam butulu.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko:A kullum Allah na amsa addu’o’in annabawa da manzonninsa da tsiratar da su.

Na biyu:kaucewa hanya da tafarkin Annabawan allah na kai mutum ga hallaka da tabewa.

Na uku:haka sunnar Allah take yana tsiratar da mumunai da hallaka tababbu.

                            • MUSIC********

To madallah za mu ci gaba da sauraren karatun aya ta 123 da ta 124 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


كَذَّبَتْ عَادٌ الْمُرْسَلِينَ


123-Adawa ma sun karyata manzanni.


إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ


124- Lokacin da dan uwansu Hudu y ace da su: yanzu ba kwa jin tsoron Allah ne?

Bayan ayoyin da suka yi bayani da takaitaccen tarihin Annabi (AS) da mutanansa yanz za mu fara bayani da abin da ya wakana tsakanin Annabi Hud (AS) da mutanansa daAllah ya aiko shi a tsakanin al’’ummar Adawa. Kuma wannan al’umma ta rayu ne a kuduncin Saudiya ta yanzu a wani yanki da ake kira da Ahkaf kuma wani bangare ne na kasar Yaman a yanzu to a nan ne Adawa suka rayu.

Wadannan ayoyi da muka saurara na cewa:al’ummar da ake kira adawa kamar sauran al’ummomin da suka gabace su sun karyata annabawa da manzonnin Allah (AS) daka aka turo masu kuma ba a shirye suke ba da su amsa kiransu.Duk da cewa kiran dukan annabawa da manzonni da ya hada da kiran Annabi Hud(AS) abu daya kira zuwa kadaita Allah da bauta da tuba daga aikata ayyuka mummuna da ya hada da shirka da zalunci amma suka karyata manzonnin Allah (AS).

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka;

Na farko:Duk da tushen kiran Annabawa da manzonnin Allah abu daya ne kuma suka kira ne zuwa ga kadaita Allah da bauta amma kafirai da masu adawa da sun ki yin imani da su.

Na biyu:Manzonnin Allah (AS)suna kollon mutane da idon rahama da yan uwantaka ba suna kollon su shugabannin su ne ba da hakan ke nuni da tawadu’unsu da gaskiyarsu da damuwa da halin da mutane ke ciki da tausayawa jama’a.

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 125 zuwa 127.


إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ


125-Hakika Ni Manzo ne amintacce a gare ku.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ

126- To ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى رَبِّ الْعَالَمِينَ


127- Kuma ba na tambayan ku wani lada game da shi isar da manzancin ,ladana yana wajan Ubangijin Talikai kawai.

Annabawa da manzonnin Allah (AS) sun rayu tare da mutane da kuma suke kollonsu mutane masu amana da riko da fadin gaskiya da kuma aminci.Mutane bas u taba saminsu da wani abu face gaskiya da amana kuma babu wani da ya cancanci isar da sakon Allah zuwa ga mutane kamar su.Karkshin ayoyin da muka saurara.Annabi Hud (AS) ya kamar Annabi Nuhu (AS) ya kirayi mutanansa zuwa kadaita Allah da bauta da tsoran allah da bin manzonni da za su nuna masu hanyar samin tsira da hanya madaidaici da za ta kai su ga sa’a .Amma masu adawa da annabi Hud (AS) da yake ba a shirye suke bas u karbi da amincewa da wannan kira na gaskiya da shirya sai suka yi ta kawo fakewa iri iri da za su killace su daga amincewa da wannan kira na shi.Da Annabi Hud (AS) ya ga haka sai ya fito masu fili karara ya kafa masu hujja da cewa; Ni babu wani abu da nake bukata a gurinku kudi ko mukami da daukaka ,Allah ya wadatar da ni kuma bukata tana gurin Allah ne ba a gurinku ba.Kuma ni ina rayuwa da dogaro da lutifinsa da taimakonsa a wannan duniya da lahira.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko:duk wanda ya bi umarnin Allah da waliyansa yana tare da sa’ada da dacewa duniya da lahira.

Na biyu: sirrin cin nasara a ayyuka na addini da ma’anawiya shi ne Ikhlasi da neman yardarm Allah ba waninsa.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 128-136 (Kashi Na 666)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.




To madallah yanzu za mu fara shirin nay au da sauraren karatun aya ta 128 zuwa 130 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


أَتَبْنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ آيَةً تَعْبَثُونَ

128- Yanzu kwa rika yin dankareren gini a kan tuddai kuna yin izgili ga mutane?


وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمْ تَخْلُدُونَ


129- Kuma ku rika gina tafkunan ruwa kamar za ku dawwama?


وَإِذَا بَطَشْتُم بَطَشْتُمْ جَبَّارِينَ


130-Idan kuma kuka yi damka sai kukan yi damkar da tsanani.

A cikin shirin da ya gabata mun ji ayoyin da suka yi magana kan tura Annabi Hud (AS) domin shiryar da Adawa a matsayinsa na manzo daga Allah da kuma nuna masu hanya madaidaiciya.To wadannan ayoyi da muka saurara na cewa:masu adawa da annabi Hud mutane ne masu wadata da neman jin dadin rayuwa babu abin da ya dame su sai nuna kai da dagawa a cikin al’umma. Duk wani lamari na jin dadin rayuwa bas u wasa da shi ko takaitawa da gina gidajen tunkahu da nitsewa a jin dadin rayuwa tamkar za su dawwama a wannan duniya ba za su mutu ba. Daga cikin siffofin masu muni na wadannan mutane kamar yadda Annabi Hud (AS) ke cewa a cikin ayoyin da muka saurara cewa: ku ba mutane ne ma’abuta yafewa da mantawa da abin da ya wuce ma’ana kuna da riko kuma ku mutane ne masu danniya da wuce gona da iri da zaluntar waninku har ila yau ku mutane ne da bas u da tausayi da sakayya da mumunan sakamako komin kankancin leifi.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:A al’ada irin ta musulunci duk wani aiki da za mu yi domin nuna kai abin kyama ne ko da kuwa yanada girma da muhimmanci.

Na biyu:Gina gidan tunkahu al ace ta rungumar wannan duniya da sha’afa da ranar kiyama.

Na uku:a kullum a bar wuce gona da iri a rayuwa da gida gidajen da za mu shiga kuma kar mu shagala da ranar lahira.

To yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 131 zuwa 134.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ


131- To ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


وَاتَّقُوا الَّذِي أَمَدَّكُم بِمَا تَعْلَمُونَ

132- Kuma ku ji tsoron Allah Wanda Ya ni’imta ku da abin da kuka sani.


أَمَدَّكُم بِأَنْعَامٍ وَبَنِينَ


133-Ya ni’imta ku da dabbobin ni’ima da yayaye.


وَجَنَّاتٍ وَعُيُونٍ


134- Da kuma gonakai da idandunan ruwa.

Annabi Hud (AS) a cikin wadannan ayoyi na fadakar da mutanensa ta hanyar zano masu irin ni’imomin da Allah yay i masu kuma da mamakin yadda suke kafircewa Allah da yayi masu irin wadannan ni’imo da wadatar da su.Ku idan suka bi umarnin allah za su dace da rayuwa mai inganci da dawwama duniya da lahira.Daga cikin ni’imomin da Annabi Hud (AS) ya Ambato masu akwai ruwan sha da mai gudana domin ayyukansu na gonaki da noman rani da samar da yayan itatuwa masu dando da sauran ayyukan gona da wadatar da su da abinci kala-kala.Har ila yau ya wadatar da su da abubuwan da za su yi jigilar kayan abinci da wadatar da su yaya da za su taimaka masu a ayyukansu na noma da kiyo.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar:

Na farko:Rashin tsoron Allah na haddasa duk wani fasadi da matsaloli na zamantakewa da na kadaitaka.Domin haka a kullum manzonni ke faraway da kiran mu da tsaron Allah.

Na biyu: tsoran Allah wani mataki ne na farko na godewa Allah kan ni’imomin da yay i mana kuma mafi kankantar godiya it ace bin umarnin Allah ba bijere masa ba.

                          • MUSIC**********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 135 da 136 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


إِنِّي أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

135-Hakika ni ina tsorace muku azabar rana mai girma.


قَالُوا سَوَاء عَلَيْنَا أَوَعَظْتَ أَمْ لَمْ تَكُن مِّنَ الْوَاعِظِينَ


136-Suka ce : Mu duk daya ne a wajenmu,ko ka yi wa’azi ko kuwa kada ka yi.

Wadannan ayoyi na nuni da yadda annabi Hud (AS) ya nuna kauna da soyayya da tausaywa ga mutanasa kamar sauran annabawa da manzonni da ce masu: abin da na ke fada amfaninsa zai koma a gare ku ne kuma ina tsoron mummunan karshen aikin da kuke aikatawa ne domin duk wannan sabawa umarnin Allah karshensa mummunan sakamako.Sai dai masu ji da dukiya da mukami da dagawa a maimakon su yi tunani mai kyau daga abubuwan da Annabi Hud (AS) ke fada cikin rashin ladabi da aiki da hankali suka ce mashi:kar ka bawa kanka wahala da damin kanka ba mu sauraren abin da kake fada da yin tasiri a zukatanmu.

Daga cikin wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: mutane da suka yi nisa a cikin sabo da sabawa Allah da fasadi da jiji da kai dole a fadakar da su ko da kuwa fadin gaskiya ba zai yi tasiri a gare su ba.

Na biyu:idan mutane ba a shirye suke su karba da sauraren gaskiya ba ko da mafi fifikon bayun Allah yayi masu wajabi ba zai yi tasiri a kansu ba da karbar gaskiyar.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 137-150 (Kashi Na 667)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                          • MUSIC*********

To madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta 137 zuwa 140 a cikin suratul Shu’ara’a.


إِنْ هَذَا إِلَّا خُلُقُ الْأَوَّلِينَ


137-Wannan ba wani abu ba ne in ban da halayen mutanen farko.


وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ


138- Mu kuma ba za a yi mana azaba ba.


فَكَذَّبُوهُ فَأَهْلَكْنَاهُمْ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ


139-Sai suka karyata shi,sannan Muka hallaka su.Hakika a game da wannan lallai akwai aya.Yawancinsu kuwa bas u kasance masu ba da gaskiya ba.


وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ


140-Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi ne Mabuwayi Mai jin Kai.


A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda kaumu Adawa suka amsawa Annabi Hud (AS) lokacin da yayi masu galgadi da tuba daga ayyukan sabo da bijirewa umarnin Allah da cewa; kana bawa kan wahala ne mu ba za mu daina ayyukan sabo da muke aikatawa ba za mu ci gaba da yin riko da hanyar da muka yi gado iyaye a gurinmu hanya ce mai kyau sabanin abin da kake fada mana kuma babu abin da zai same mu.

Allah ya amsa masu da cewa;sun karyata kiran annabi Hud (AS) da manzoncin da Allah ya aiko shi domintun a wannan duniya za su gamu da fushin Allah da hallaka saboda bas u yi imani ba da amincewa da maganar gaskiya da bin hanya madaidaiciya ta shiriya. Ci gaban ayar na cewa;wannan azaba da Allah yayi masu domin zama darasi da nuna masu kudura da iradar Allah a gare su da sauran al’ummomin duniya.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Masu girman kai da jiji da kai da fasadi a kullum ba su aiki da hankali sai ci gaba da yin riko da abubuwan da suka gada iyaye da kakannu ko da kuwa ya sabawa hankali da tunani.

Na biyu:mushrikai da kafire na kaucewa karbar gaskiya ta fakewa da ayyukan iyaye da kakannu.

To yanzu za mu saurari karatun aya ta 141 zuwa 145.


كَذَّبَتْ ثَمُودُ الْمُرْسَلِينَ


141-Samudu ma sun karyata manzanni.


إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ صَالِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ


142- Lokacin da dan uwansu Salihu yace da su : Yanzu ba kwa jin tsoron Allah ba?


إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ


143- Hakika ni manzo ne amintacce a gare ku.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ


144-to ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى رَبِّ الْعَالَمِينَ


145-Kuma ban a tambayar ku wani lada game da shi isar fa manzancin,Ladana yana wajan Ubangijin talikai kawai.

Bayan ayoyin da suka yi bayani kan abubuwan da suka wakana tsakanin al’ummomin annabi Nuhu ,annabi,Ibrahima,Annabi Musa, da Annabi Hud (AS) da annabawansu .yanzu za mu fara bayani kan annabi Salihu (AS) da salon da yayi amfani da shi wajan kiran al’ummarsa domin sryar da su Samudawa. Shi ma kamar sauran yan uwansa annabawa da manzonnin Allah (AS) ya fara kiran al’ummarsa Samudawa kan muhimman abubuwa guda uku kuma tushe.Na farkosu su tuba daga bijirewa umarnin Allah wato Takawa. Na biyu bin annabi da manzon da aka turo masu mai gaskiya amini da zai isar da su ga dacewa da wadata duniya da lahira ,sai kuma na uku: Su sani su manzonni ba su son wani abu a gare sun a lada kawai suna isar da sakon manzonnci da kokarin shiryar da su ne don neman yardarm Allah.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko:salo da tafarkin da manzonni suke amfani da shi wajan kiran mutane zuwa ga tafarkin Allah guda daya ne shi kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta da tuba daga bijirewa umarninsa.

Na biyu: Duk wanda Allah zai turo a matsayin manzo mutum ne mai gaskiya da amana a tsakanin mutanansa don haka mai yada addinin musulunci ya kasance mai bin tsarin rayuwa da kyawan halaye na manzonni ne.

                      • MUSIC*******


Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 146 zuwa 150 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


أَتُتْرَكُونَ فِي مَا هَاهُنَا آمِنِينَ


146-Yanzu zatonku za a bar ku ne cikin abin da yake a nan duniya cikin kwanciyar rai?


فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ


147- Watau a cikin gonakai da idandunan ruwa?


وَزُرُوعٍ وَنَخْلٍ طَلْعُهَا هَضِيمٌ


148-Da shuke-shuke da dabinai masu taushin yaya?


وَتَنْحِتُونَ مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتًا فَارِهِينَ


149-Kuma ku rika fafe duwatsu kuna yin gidaje kuna masu homa?


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ


150-To ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


A cikin wadannan ayoyi annabi Salihu (AS) ya galgadi al’ummarsa da tambayarsu mi yasa suke zaton za su dauwwa a cikin ni’ima da jin dadi a wannan duniya? Mi yasa kuke zaton yayan itatuwa da da wannan jin dadi zai dauma a gare ku har abada?.Mi yasa suka zamanto bayun ciki da jin dadi kawai suka sa gaba, kuma me yasa bas u godewa Allan da yayi wadannan ni’imomi a maimakon haka sais u bijirewa umarninsa ko ba komi su tuba daga bjirewa umarnin wanda ya halicce su da sauran ni’imomin. Idan kuna son dauwama da isa ga wadata duniya da lahira ku saurara da yin aiki da bayanin da nake yi maku kuma ni babu wani abu da nake fada face daga Allah ne da isar da sakonsa zuwa gare ku.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:

Na farko: mu amfana da ni’imomin da Allah ya huwace mana a wannan duniya amma kar mu sarkafa da su da shagala da lahira ko bijirewa umarnin Allah.

Na biyu:Jin dadi mai yawa na saukin kai mutum ga fasadi da rashin jin tsoron Allah don haka a kullum a yawaita tunanatarwa da kashedi kan tsoron Allah.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 157-166 (Kashi Na 669)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                  • MUSIC*******

To madallah za mu fara shirin nay au ne tare da sauraren karatun aya ta 157 zuwa 159 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


فَعَقَرُوهَا فَأَصْبَحُوا نَادِمِينَ


157-Sai suka sare ta ,sannan suka wayi gari suna masu nadama.



فَأَخَذَهُمُ الْعَذَابُ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ

158- Sai azaba ta kama su.Hakika a game da wannan lallai akwai aya ,yawaicinsu kuwa bas u kasance masu ba da gaskiya ba.


وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ

159-Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi ne Mabuyawayi Mai jin kai.


A cikin shirin makon da ya gabata kun ji yadda samudawa mutanan annabi Salihu (AS) suka bukaci mu’ujiza daga annabi Salihu (AS) da Allah ya turo don shiryar da su kuma Allah ya amsa masu wannan bukata ta umurtar wata rakuma ta fito daga babban tsaunin da ke inda suke rayuwa da kuma umurtarsu da kar su kuskura su cutar da wannan rakuma da ke sha ruwa rana guda a cikin mako.To a cikin shirin nay au za mu ji yadda ta wakana da wannan rakuma. A kwana a tashi sai wata rana a ranar da wannan rakuma ke fitowa don shan ruwa sai Samudawa mautanan annabi Salihu (AS) suka umarci daya daga cikinsu da ya sake kafa kafar gaba da ta baya ta wannan rakuma ta haka sais u kashe ta.Sun yi hakan ne domin suna gani matukar wannan rakuma tana rayuwa a cikin mutane za su yi da ci gaba da yin imani da annabi Salihu (AS).Kuma saboda sauran mutane sun amince da wannan mummunan aiki don haka kur’ani ya azabatar da dukan samudawa.Kuma ganin su da kansu ne suka bukaci mu’ujizar don haka Allah ya gaggauwa azabtar da su bayan da suka sabawa alkawalin da suka yi tsakaninsu da Annabi Salihu (AS).Lokacin da samudawa suka ga alamomin sabkar azaba kan wannan mummunan aiki nasu sai suka yi nadama da shiga cikin dimuwa amma kash lokaci ya kure da wannan nadama ba ta da wani amfani domin nadama da tuba a daidai lokacin da azaba ke sabka ba ta da wani amfani. Allah ya azabtar da su da kara mai firgitarwa da walkiya da suka hada da girgizar kasa mai karfin gaske inda gidajen da suke cikin suka rubta kansu samudawa masu sabo a doran kasa da hallakar da su baki daya sai wadanda suka yi imani da sakon da Annabi Salihu (AS) ya zo masu da shi daga Allah don shiryar da su.

Bayan da Samudawa suka hallaka sai kur’ani y ace karshen Samudawa daidai yake da makomar al’ummomin annabawan da suka gabace su Hudu,Nuhu da Ibrahim (AS). Ba su dauki darasi da amincewa da gaskiya da shiriya ba. A maimakon karbar gaskiya sai suka fifita fito na fito da jayayya da bayanin gaskiya. Su sun yi zaton za su iya cin nasara kan Allah da manzonsa alhali Shi Allah mabuwayi ne mai nasara kan komi da kowa kuma adaidai lokaci guda mai rahama da jin kan bayunsa na gari masu karba da aikata gaskiya da lullube su da lutihi da rahamarsa .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Yana daga cikin ayyukan masu adawa da annabawa da manzonnnin Allah rukuza duk wani abu da annabawan allah suka bari a doran kasa kamar yadda muke gani a wannan zamani ma.

Na biyu: Amincewa da aikin da wasu ke aikatawa daya muke da su a cikin lada da azabtarwa kamar yadda Imam Ali (AS) ke cewa: saboda sauran mutane ma sun amince da matakin kashe wannan rakuma don haka azaba ta shafe su suma.

Na uku:Azabar Allah ta na riske mu ne saboda aikin sabion da muka aikata duk da cewa Allah mai rahama da jin kai ne.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 160 zuwa 164 .


كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍ الْمُرْسَلِينَ


160- Mutanen Ludu ma sun karyata manzanni.


إِذْ قَالَ لَهُمْ أَخُوهُمْ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ


161-Lokacin da dan uwansu Ludu yace da su: Yanzu ba kwa jin tsoron Allah?.


إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ


162-Hakika ni Manzo ne amintacce a gare ku.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ



163- To ku ji tsoron Allah, kuma ku bi ni.


وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى رَبِّ الْعَالَمِينَ


164-Ba kuma na tambayar ku wani lada a kansa isar da manzancin ,ladana yana wajan Ubangijin talikai kawai.

Wadannan ayoyi da muka saurara su ma kamar ayoyin da suka gabace su a suna bayani ne kan kira da sakon da annaba da manzonnin Allah suka zo da su tushen su guda ne kuma suna kira ne zuwa ga tsoron Allah da kadaita shi da bauta da kuma bayanin cewa duk al’ummar da ta sabawa wannan kira na annabawan Annabawan Allah azaba da fushin Allah zai riske ta.Da kiran mu zuwa ga yawaita ayyukan alheri da tuba daga aikata sabo.

                                      • MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 165 da aya ta 166 a cikin wannan sura ta shu’ara’a.


أَتَأْتُونَ الذُّكْرَانَ مِنَ الْعَالَمِينَ


165-Yanzu kwa rika zaike wa maza daga mutane?


وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمْ رَبُّكُمْ مِنْ أَزْوَاجِكُم بَلْ أَنتُمْ قَوْمٌ عَادُونَ



166-Kuma ku bar abin da Ubangijinku ya halitta na matanku dominku? A’a ,ku dai mutane ne masu ketare iyaka.


Duk wani aiki na sabo da fasadi abin ki ne a gurin Allah don haka Annabi Lud (AS) mummunan aiki nay a sabawa kyawawan dabi’u da mutanansa ke aikatwa ya hana su a fili karara da mamakin wannan aiki nasu ta hanyar tambayarsu cewa: shin ba kuna da matan aure ba me yasa kuke saduwa da maza yan uwanku ne ? Wannan mummunan aiki da kuke aikatawa wane dalili za ku gabatar bayan wuce gona da yi wa dokokin Allah hawan kawara?.

Yan jinsi daya da suke saduwa da juna a wani bangare ne da bijirewa dokoki da umarnin Allah kuma babban sabo da fasadi ne a doran kasa kuma a zamanin annabin Lud(AS) al’ummarsa sun yi fice wajen aikata wannan mummunan aiki kuma suna ganin wani yanci ne nasu na aikata abin da suka ga dama . Kash wannan mummunan aiki na luwadi a wannan zamani ma abin yayi kamari ba ma a tsakanin maza a’a munin ya kai munin aiki domin har a tsakanin mata ma ya yadu kuma wadanda ke aikata wannan mummunan aikin suna fakewa da cewa : su ke da ikon sarrafa jikinsu yadda suka ga dama da biyan bukatarsu ta jinsi ta duk wata hanya da suka ga dam aba takurawa .Alhali a hanya da tafarki irin na addinin musulunci mutum bas hi ke da ikon jikinsa ba dari bisa dari ,Allah ne ke da iko kansa da jikinsa da kuma ya gittaya masa dokoki da tsari na rayuwa. Matukar ya saba zai fuskanci fushi da azabar Allah a wannan duniya ko gobe kiyama.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko: Ya kamata a binciko munanan ayyuka da ke bata tarbiya a tsakanin al’ummomin domin daukan matakan da suka dace kansu.

Na biyu: dole a nuna hanyar da ta dace a duk lokacin da za mu fuskanci mummunan ayyuka na gurbata al’umma da tsari na gari kamar yadda Annabi Lud(AS) ya fara da nunawa mutansa hanyar aure hanyar da ta dace a maimakon saduwa da yan jinsi daya a tsakaninsu.

Na uku; Allah ya samarwa da mutum hanyar da ta dace don biyan bukatarsa ta gariza da tsari na aure sabanin dabbobi.

Na hudu: aikata saboda kamar saduwar yan jinsi daya ya sabawa dokokin dabi’a kumwa wani nau’I ne na bijirewa da wuce gona da irin kan dokokin Allah da tsarinsa da mutum ke aikatawa.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 167-175 (Kashi Na 670)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                            • MUSI***************

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au ne tare da sauraren karatun aya ta 167 da ta 168 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


قَالُوا لَئِن لَّمْ تَنتَهِ يَا لُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ الْمُخْرَجِينَ


167-Suka ce: wallahi ludu idan b aka bar fadar abin da kake fad aba lallai z aka kasance daga korarru daga garin nan.


قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ الْقَالِينَ


168- Ludu yace Hakika ni ina Kyamar irin aikin nan naku.


A cikin shirin makon jiya mun yi bayani ne dangane da munanan ayyuka da al’ummar annabi Lud (AS) ke aikatawa da kuma yadda ya hana su da yi masu galgadi to amma wadannan ayoyi da muka saurare na cewa: a maimakon mutanan annabi Lud (AS) su ji aiki da sauraren wannan hani da galgadi na manzon da aka turo masu da ke hana su saduwa da junansu yan jinsi daya sai suka yi wa annabi lud (AS) barazana da cewa idan bai daina yi masu wa’azi ba da ci gaba da damunsu za su fitar da shi daga cikin garin da yake rayuwa tare da su bayan haka su ci gaba da aikata duk abin da suka ga dam aba takurawa da galgadi. Amma a maimakon wannan baraza tasu ta tsoratar da annabi Lud(AS) sai ma ta kara masa karfin guiwa ba da wata wata bay a amsa masu da cewa: Ni ina kamar abin da kuke aikatawa kuma zan ci gaba da adawa da mummunan ayyukan da kuke aikatawa.

Abin lura a nan .Annabi Lud (AS) bai ce ba ina adawa da ku ba sai y ace ina adawa da ayyukan da kuke aikawa ma’ana idan kuka daina aikata mummunan aikin da kuke aitawa zan koma abokinku kamar da .dalilin adawata da ku mummunan aiki da kuke aikatawa na fasadi kuma b azan daina gwagwarmaya da wannan mummunan aiki da kuke aikatawa ba.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Tilastawa mutanan kirki yin gudun hijira wani salo da zaluncin azzzalumai da masu girman kai da kuma ta wannan hanya su ci gaba da cin karansu babu babbaka hankali kwance.

Na biyu: shiru da gum kan masu aikatawa mummunan ayyuka bai dace ba.Dole a yaki da tsayin daka wajen tunkarar duk wani aiki mummunan da ake aikatawa a bainar jama’a ta fatar baka ce ko a aikace dole a hana aikata irin wannan aiki na banna.

Na uku: Annabwa da waliyan Allah suna dogaro ne da Allah Shi kadai ba tare da sun ji tsoron barazanar mai barazana ba daga makiyan Allah kuma komin tsanani bas u daina yin gwagwarmaya da zalunci da fasadi ba.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 169 zuwa 171.


رَبِّ نَجِّنِي وَأَهْلِي مِمَّا يَعْمَلُونَ


169-Ya Ubangijina ,Ka tserar da ni da iyalina daga sakamakon abin da suke aikatawa.


فَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَ


170-Sai Muka tserar da shi da iyalinsa gaba daya.


إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ

171-Sai fa wata tsohuwa watau matarsa da ta kasance tana cikin hallakakku.


Bayan da annabi Lud (AS) dare da rana ya ci gaba da galgadi da wa’azzatar da mutanansa kan mummunan aikin da suke aikatawa na saduwa da junasu yan jinsi daya maza kuma ya kafa masu dukan hujjojin da ya ke iyawa da tabbatar mas aba za su yi imani ba ,uwa uba sun kudurta niyar kashe shi sai yay a daga hannunsa ya roki Allah da ya kubutar da shi da kare shi daga wannan makirci da suke son kulla masa ya kuma taimaka masa daga sharrinsu. Allah mai sauraren Annabawansa ne sai ya amsa ma Annabi Lud (AS) ta hanyar umurtar sa da dukan wadanda suka yi imani da shi da iyalan gidansa da su fice daga cikin wannan gari a cikin dare a daidai lokacin da kowa yayi barci ta inda kar a samu daya daga cikin wadanda suka yi imani a cikin wannan gari a daidai lokacin da azaba da fushin Allah zai sabka kan wadanda suka kafirta.Daga cikin wadanda azabar ta riske su da fadawa kansu akwai matar Annabi Lud (AS) ta kasance tare da kafire da goyan bayansu ba juyawa mijinta baya a yakin da yake yi da masu aikata fasadi kuma ba ta taimaka masa ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da dokan darasi n abubuwa biyu kamar haka;

Na farko: bai dace ba mutum salihi ya rayu a guri da ya gurbata da fasadi da banna dole ya nemi gurin da zai kubutar da ransa daga gurin da ya gurbata da banna da fasadi.

Na biyu: A gurin Allah kusanci da mutuman kirki ko na lala bas hi da wani tasiri kowa aikinsa ya fisshe shi kawai kamar yadda matar Annabi Lud (AS) bai amfanar da it aba sai gashi ta hallaka amma a dabra da haka matar Fir’auna da ta yi imani da Allah ta samu tsira.

                              • MUSIC*************

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 172 zuwa aya ta 175 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَ


172-Sannan Muka rugurguza sauran.


وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِم مَّطَرًا فَسَاء مَطَرُ الْمُنذَرِينَ


173-Muka kuma saukar musu ruwa na azaba,sannan ruwan azabar wadanda aka yi wa gargadi ya munana.


إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ


174-Hakika a game da wannan lallai akwai aya,yawaicinsu kuwa bas u kasance masu ba da gaskiya ba.


وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ


175-Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi ne Mabuwayi Mai jin kai.


Bayan da Annabi Lud (AS) da wadanda suka yi imani da shi daga iyalan gidansa da mutanan gari suka fice daga cikin wannan gari.Sai girgizar kasa mai karfin gaske karkashin umarnin Allah ta fadawa mutanan wannan gari suna cikin barci bayan sun share dare suka aikata fasadi ba iyaka da hallakar da su a daidai lokacin da suke cikin barcin gafala.Ba kawai girgizar kasa ta azaba ta fadawa mutanan wannan gari ba da lalata masu gidaje ,Allah yay i masu ruwan azaba na duwatsu daga sama ta inda sama na azabtar da sui ta masa kasa na azabtar da su a lokaci guda wato sama zafi kasa zafi ,Duk wani abu mai rai a cikin wannan gari ya hallaka.

Wasu malaman tarihi na cewa: ambaliyar ruwa mai karfi ta azaba aka yi masu a daidai lokaci guda an yi masu ruwa duwatsu kanana da manya daga sama da ke fadawa kansu da rakwarkwasa kwalluwarsu da gabobin jikinsu abin babu misaltuwa. Ci gaban ayoyin na cewa: sabkar wannan azaba a kansu shi ne yawancin mutanan garin duk da ayoyi da hujjoji ba a shirye suke ba sun yi imani kuma suna da shirin kulla makirci kan annabin Allah Lud (AS) da sauran waliyan Allah.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da daukan darasi guda uku kamar haka:

Na farko: Duk al’ummar da ta zunduma da zurfafawa a cikin fasadi ta saurari azabar Allah,azabar da za ta iya zo masu a kowa wane lokaci da yanayi ta sama ko ta kasa.

Na biyu: galgadi da kashedi da kafa dukan hujjoji dole ne kafin sabkar azaba.

Na uku:Kudura da irada a wannan duniya da lahira na hannu da ikon Allah da nay i yi ruwan sama kuma na iya yin ruwan duwatsu da sauran nau’I na azaba da duk wani abu da so yi .

Da fatar Allah ya shiryar da mu duniya da lahira amen summa amen.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 176-187 (Kashi Na 671)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************

To madallah jama’a masu saurare za mu fara shirinmu nay au ne da saurararen aya ta 176 zuwa 180 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


كَذَّبَ أَصْحَابُ الْأَيْكَةِ الْمُرْسَلِينَ


176-Mutanen Ailata ma sun karyata manzanni.


إِذْ قَالَ لَهُمْ شُعَيْبٌ أَلَا تَتَّقُونَ


177-Lokacin da Shu’aibu ya ce da su : Yanzu ba kwa jin tsoron Allah ne?


إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ


178-Hakika Ni Manzo ne amintacce a gare ku.


فَاتَّقُوا اللَّهَ وَأَطِيعُونِ


179-To ku ji tsoron Allah kuma ku bi ni.


وَمَا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ إِنْ أَجْرِيَ إِلَّا عَلَى رَبِّ الْعَالَمِينَ


180-Kuma ban a tambayar ku wani lada a kansa( isar da manzancin) ladana yana wajan Ubangijin talikai kawai.


A kusa da garin Madyana akwai wani yanki mai suna Aikata mutanan yankin sun yi nisa wajen aikata sabo da banna a doran kasa don haka Allah ya turo masu suma annabi Shu’aibu don shiryar da su da tashi takanas daga garin Madyana zuwa yankin don isar da wannan sako na Allah.Sunan aikata yana nufin yankin da itattuwa ya yawaita a gurin da ni’ima kuma yawan itatuwa ya sanya yankin ya zama cikin rukuku da wuyar tafiya kuma mutanan da ke rayuwa a wannan yanki na cikin ni’ima da wadata da arziki wannan ya sanya su su gafala da fadawa tarkon shaidan da nuna girman kai da dagawa.

Ayoyin da muka saurara sun nakalto jawabin da Annabi Shuaibu yayi ma mutanan aikata kamar sauran annabawa da suka gabace shi a cikin ayoyin da suka gabata ,kiran mutanasa zuwa ga tsoran Allah da kadaita Allah da bauta da tuba daga aikata sabo da banna a doran kasa. Su kuma yi riko da yin biyayya da Mahaliccinsu da bin umarnin Allah karakashin koyarwar Annabawa da manzonnin da ya turo masu don shiryar da su. Har ila yau wadannan ayoyi sun yi nuni da abubuwa biyu masu muhimmanci da Manzonnin shiriya suka kebanta da su. Na farko; sun kasance mutanen kirki da rayuwa a tsakanin mutane kan gaskiya da amana da kyautatawa da kuma kyawawan dabi’u. Na biyu bas u neman wani sakamako ko lada a gurin mutane balantana masu adawa da su su samu abin fadi mummuna kansu.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 181 zuwa 184 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


أَوْفُوا الْكَيْلَ وَلَا تَكُونُوا مِنَ الْمُخْسِرِينَ

181- Ku cika mudu kada kuma ku zamanto daga masu tauye shi.


وَزِنُوا بِالْقِسْطَاسِ الْمُسْتَقِيمِ


182-Kuma ku rika yin awon nauyi da ma’auni na adilci.


وَلَا تَبْخَسُوا النَّاسَ أَشْيَاءهُمْ وَلَا تَعْثَوْا فِي الْأَرْضِ مُفْسِدِينَ


183- Kada kuma ku tauye wa mutane wani hakkinsu,kuma kada ku yawaita barna a bayan kasa.


وَاتَّقُوا الَّذِي خَلَقَكُمْ وَالْجِبِلَّةَ الْأَوَّلِينَ


184-Kuma Ku ji tsoron Wanda Ya halicce ku da kuma al’ummu na farko.


Bayan da yayi kira na bai daya zuwa ga takawa wato tsoron Allah ,Annabi Shu’aibu kai tsaye ta fara da kaucewa hanya ta tattalin arziki a tsakanin mutanen Aikata da cewa: me ya sa kuke kobro a saye da sayarwa da cutar da kawunanku? Me ya sa kuke tauye mudu da tauyewa mutane hakkinsu? Me yasa alolkacin da za ku saye a gurin mutane sai ku aibata abin da za ku saya don rage masa daraja da ha’intarsu?

Yankin Aikata yanki ne mai yanayi mai kyau da itatuwa da iskar shaka mai kyau kuma yana kan hanyar yan kasuwa masu fatauci daga Hijaz zuwa Sham da sauran tawagogin kasuwanci daga yankuna daban daban da ke bi ta wannan yanki.Kuma ana yawan saye da sayarwa a wannan yankin. Yankin ya zama tamkar cibiyar kasuwanci da guri na hadewar yan kasuwa .To amma su mutanan wannan yanki a lokacin da suke sayen wani abu a gurin dan kasuwa da ya fito daga wani gari ko yanki sais u aibata wannan kaya nasa don kawai su saya da araha ko tauye mudu da maauni na munafinci. Don haka karshen ayar ke nuni da tauye mudu da tauye hakkokin mutane a lokacin saye da sayarwa da cewa ya haddasa yawaitar fasadi da zalunci a tsakanin al’umma.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Takawa da tsoron Allah nada fadin gaske hatta kiyayye hakkokin mutane yana cikin tsoron Allah kuma tauye hakkokin mutane alama ce ta rashin tsoron Allah.

Na biyu;Tauye hakkin mutane na haddasa rashin ciniki da bala’I alamari da ya shafi kasuwanci kuma cin zalin mutane ne.

Na uku:Tsarkake saye da sayarwa da tattalin arziki mai inganci a tsakanin jama’a daya ne daga cikin burin annabawa da manzonnin Allah saboda fasadi da tattalin arziki gurbatacce ya ingiza mutane ne zuwa zalunci da fadawa tarkon bata da tabewa da gurbata tsarin zamantakewar al’umma.

Na hudu:Adalci a dukan bangarori na rayuwa da ya hada da tattalin arzki da saye da sayarwa lamari ne da dukan addinai na annabawa da manzonnin Allah suka jaddada kansa a tsawon tarihi.

                      • MUSIC*************


قَالُوا إِنَّمَا أَنتَ مِنَ الْمُسَحَّرِينَ


185- Suka ce: Kai dai an sihirce ka ne kawai.


وَمَا أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ الْكَاذِبِينَ


186-Kuma kai ba kowa ba ne sai mutum irinmu,kuma ma lallai muna zaton kana daga makaryata.


فَأَسْقِطْ عَلَيْنَا كِسَفًا مِّنَ السَّمَاء إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ

187- Sai ka jeho mana da kinkima-kinkiman yankuna na azaba daga sama in ka zamanto daga masu gaskiya.


A maimakon sun amince da jawabin gaskiya da Annabi Shu’aibu (AS) yay i masu,Mutanen aikata da ke ba a shirye suke ba su karbi gaskiya da daina cin hakkokikin jama’a sai suka kirayi Annabi shu’aibu da sunan boka mai sihiri kuma wanda ya samu tabuwar hankali da fadar maganganu da suka sabawa hankali. Sun ci gaba da cewa: yanzu dake abin da kake fada ya sabawa hankali to sai ka tabbatar mana da kai manzo ne daga Allah kuma abubuwan da kake fada daga Allah ne alhali kai b aka da wani bambanci da mu ma’ana kai kamar mu kake mutane. Saboda haka mu ba za mu amince ba da kai a matsayin manzo daga Allah sai ka tabbatar mana da mu’ujiza da sabkar mana da manyan duwatsu daga sama da fadawa kan mu da azabatar da mu kamar yadda kake tsoratar da mu da azaba daga Allah. To fa wannan shi ne tsananin kafirci a fili karara da nemarwa kai bala’I .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:zargi da tuhuma na mutane ne da su amfani da hankali da amince da jawabi na hankali kamar yadda mutanen aikata suka amsawa annabai shuaibu (AS) da aka aiko masu inda suka zarge shi da mai sihiri wanda ya samu tabuwar hankali.

Na biyu: Wasu daga cikin masu adawa da annabawa na ganin kasancewar su mutane wani rauni ne alhali sabanin haka ne wata daukaka ce da girma a gare su da mu kanmu ,kasancewarsu mutane kamar mu da suke rayuwa tare da mu da yin koyi da su ta haka su yi tasiri a cikin rayuwarmu da zama abin koyi da aiki kan tafarkinsu.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..


Suratush Shu'ara Aya Ta 188-197 (Kashi Na 672)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************
To madallah masu saurare za mu saurari karatun ayoyi na 188 zuwa 191 a cikin suratul Shuara’a.


قَالَ رَبِّي أَعْلَمُ بِمَا تَعْمَلُونَ

188-Shu’aibu Yace: Ubangijina Yafi kowa sanin abin da kuke aikatawa.


فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمْ عَذَابُ يَوْمِ الظُّلَّةِ إِنَّهُ كَانَ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ


189- Sai suka karyata shi ,sannan sai ranar rumfa ta azaba ta kama su,hakika wannan ta kasance ran ace mai girma ta azaba.


إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً وَمَا كَانَ أَكْثَرُهُم مُّؤْمِنِينَ


190- Hakika a game da wannan tallai akwai aya ,sai dai kuma yawandinsu ba su kasance masu ba da gaskiya ba.


وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ


191- Kuma hakika Ubangijinka lallai Shi ne Mabuwayi Mai rahama.


A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa mutanan Aika da ke zaune a kusa da garin Madyana sun karyata annabi Shu’aibu da aka turo masu don shiryar da su da cewa shi boka ne mai sihiri da fadin maganganu na rashin hankali da tunani kansa da karyata manzon Allah. Ba a nan suka tsaya ba sun yi ta yi masa izgili da tsangwama da ce masa: idan gaskiya kake fada Allah ne ya turo ka kuma idan muka saba masa zai azabtar da mu to sai k ace masa ya yi mana ruwan duwatsu da azabtar da mu a wannan duniya.

To wadannan ayoyi da muka saurara sun amsa masu da cewa: Annabi Shu’aibu (AS) ya amsa masu da cewa: Allah yana gani da jin aiki da abin da kuke fada idan yayi niyar azabtar da ku zai yi ,nib a ni da iko cikin hakan ko ta yaya zai azabtar da ku . Ci gaban ayoyin na cewa:Allah ya hallakar da su da azabtar da su da azaba mafi tsanani kamar yadda ya zo a cikin ruwayoyi cewa an azabtar da su ne da tsananin zafi mai kunar da fata kuma bayan wasu kwanaki sai sama ta yi baki mutanan garin na jiran sabkar ruwan sama da iska mai sanyaya rai amma kwacam sai kara da tsawa mai tsoratarwa da kisa da haddasa gobara a tsakanin itatuwan garin da kara tsanantar kuna kansu a dabra guda tsawa da kara mai tsoratarwa suka haddasa girgizar kasa da nitsar da kafiran garin baki daya. Allah ya tsiratar da annabi Shuaibu (AS) da wadanda suka yi imani da shi kamar yadda lamarin ya wakana a sauran al’ummomi da annabawa da manzonnin da suka gabata. A cikin wadannan ayoyi Allah na cewa; duk da hallakar da wadannan mutane masu tsananin kafirci da kiyayya bai zama darasi bag a sauran mutanan da suka rage da wadanda suka zo bayansu domin yawancinsu bas u yi imani ba .Tamkar bas u san Allah mai rahama da jin kai ba ne kuma mai kudura ne. Kuma duk wanda yak i gaskiya da aiki da ita zai hallaka sai dai ita kofar tuba a kullum a bude ta ke duk wanda ya tuba zuwa ga Allah zai samu Allah mai gafara ne da sabkar da rahamarsa.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilamnatu da abubu biyu kamar haka:

Na farko:Babu wani da ke da masaniya ko bada shawarar irin azabar da Allah zai sabkar kan wadanda suka kafirta hatta annabawa da manzonni.

Na biyu: Son duniya da son tara dukiya yana canja mutum da rufe idonsa yak i karbar gaskiya da fada da manzonni da karyata su da haddasa masa sabkar azaba a wannan duniya da kuma lahira.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraran karatun aya ta 192 zuwa 195.


وَإِنَّهُ لَتَنزِيلُ رَبِّ الْعَالَمِينَ


192- Kuma lallai Shi Alkur’aani saukarwa ce ta Ubangijin talikai.


نَزَلَ بِهِ الرُّوحُ الْأَمِينُ


193- Ruhul Aminu watau Mala’ika Jibrilu ne ya sauko da shi.


عَلَى قَلْبِكَ لِتَكُونَ مِنَ الْمُنذِرِينَ


194- A bisa zuciyarka don ka zamanto daga masu gargadi.


بِلِسَانٍ عَرَبِيٍّ مُّبِينٍ


195-Ya saukar da shi da harshen Larabci mabayyani.

Bayan kawo kisser annabawa bakwai da yadda aka hallakar da mutanansu da suka kafircewa karbar gaskiya da shiriya to wannan ayar na cewa: ana bayyanawa maka da al’ummarka tarihi dfa abubuwan da suka faru kan mutanan da suka gabace ku a cikin kur’ani da harshen larabci da yadda suka aikata fasadi da banna a doran kasa kuma Allah ya tusa dukan bayanin abubuwan da suka gabata na al’ummomi a cikin zucciyar Annabin Rahama (SWA( ta hanyar mala’iuka jibril (AS) kuma manzon Allah (SWAW) ba tare da ragewa ko kari bay a bayyana mana wannan sakon kamar yadda yake. Wannan ayar tana bayani ne kan inganci n Alkur’ani da tabbatar mana cewa : Allah yak are wannan littafi nasa babu ragi ko kari cikinsa. Shi ma wanda aka aiko da wannan wahayi zuwa manzon Rahama mala’ika Jibril (AS) amini ne kuma kai tsaye ya sabkar da kur’ani a cikin zucciyar manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.Don haka ta dukan yanayi da bangarori Allah yak are mana wannan littafi mai tsarki.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: tsarin shari’a na tafiya ne kafada da kafada da tsarin dabi’a. Abin nufi wanda ya aiko Mala’ika da Manzonni (AS) da wahayi da shar’anta shari’a da sa’adar mutanae na hannun wanda ya halicci wannan duniya da tafiyar da ita.

Na biyu: Kur’ani littafi ne da ya kumshi wahayi daga Allah babu ragi ko kari a cikinsa.

Na uku: Sunnar Allah ce ta aiko da manzonni domin shiryar da mutane da fadakar da su.

                          • MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 196 da 197 a cikin wannan sura ta Shu’ara’a.


وَإِنَّهُ لَفِي زُبُرِ الْأَوَّلِينَ

196- Kuma lallai shi yana daga cikin littattafan farko.


أَوَلَمْ يَكُن لَّهُمْ آيَةً أَن يَعْلَمَهُ عُلَمَاء بَنِي إِسْرَائِيلَ


197- Yanzu bai ishe su a yaba watau kafuran Makka cewa;malama ,Bani Israila sun san shi?


Wadannan ayoyi sun kara bayyana mana karara da cewa; Mushrikan Makka idan suna shaku kan gaskiyar Kur’ani suna iya tambaya da yin bincike a gurin manyan malaman yahudawa ,ta hanyarsu sais u fahimci siffofin manzon Rahama (SWAS) da littafin da ya zo da shi da dukan bayansu yana cikin littafansu da ya hada da Attaura. A fili yake da a ce a cikin Attaura babu labara da bayanin manzon Rahama (SWA) kuma su malaman yahudawa bas u da masaniya kan haka da Allah bai umarciMushrikan makka a cikin kur’ani da su tafi su bincika a cikin Attaura da yahudawa ba. Amma saboda bayanin Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka hatta ga yahudawa ba abu ba ne boyayye da za su iya karyatawa ba.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Bushara da labarin bayyanar annabin karshe da littafinsa Alkur’ani ya zo a cikin dukan littafan manzonnnin da suka gabata.

Na biyu:Yawancin abubuwan da ayoyin kur’ani suke magana kansa ya zo a cikin littafan da suka gabata da hakan ke nufin tushensu daya ne .

Na uku: Masana yahudawa suna da masaniya da tabbacin kur’ani gaskiya ne daga Allah yake amma saboda kare matsayi da amfanin kansu sun ki yin imani da addinin musulunci da manzon Rahama (Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 198-209 (Kashi Na 673)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************

To madallah za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun ayoyi na 198 da 199 a cikin suratul Shu’ara’a.


وَلَوْ نَزَّلْنَاهُ عَلَى بَعْضِ الْأَعْجَمِينَ


198- Da kuwa Mun saukar da shi ga wani daga baibayi.


فَقَرَأَهُ عَلَيْهِم مَّا كَانُوا بِهِ مُؤْمِنِينَ

199- Sannan ya karanta musu shi,to da ba za sub a da gaskiya da shi ba.

A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda Allah madaukakin sarki ya jaddada cewa: Mu ne muka sabkar da kur’ani da harshen larabci ingantacce domin fadakarwa da shiryar da ku.To wadannan ayoyi da muka saurara sun ci gaba da cewa: Larabawan Makka na da tsananin ta’assubanci kuma da wannan kur’ani an sabkar da shi da wani yare ne ba larabci ba har abada ba za su yi imani da shi ba ko saurarensa.Kuma yanzu ma da aka sabkar da shi da Balarabe da fiyayyen mai asali da kyawawan hali da sauran littafai da suka gabata suka Ambato shi da bada busharasa ba a shirye suke bas u yi imani da shi to ina da an sabkar da wannan kur’ani da wani yare ba larabci ba.

Imam Sadik (AS) na cewa: daraja da daukakar wadanda ba larabawa shi sun yi imani da kur’ani da aka sabkar da larabci amma idan da kur’ani da wani harshe ne aka sabkar da shi ba Larabci ba da wasu da dama daga cikin larabawa ba za su yi imani da shi ba saboda ta’assubanci.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:A lamari na yada addini yana da kyau a yi la’akari da yaran wadanda ake son su yi imani da karbar gaskiya.

Na biyu: Ta’assubanci na kabilanci da nuna bambanci na daya daga cikin abubuwan da ke hana karbar gaskiya don haka mu kiyaye

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 200 zuwa 203.


كَذَلِكَ سَلَكْنَاهُ فِي قُلُوبِ الْمُجْرِمِينَ


200- Kamar irin yadda za su karyata baubawa haka Muke shigar da shi karyata Annabi cikin zukatan kafuran Makka.


لَا يُؤْمِنُونَ بِهِ حَتَّى يَرَوُا الْعَذَابَ الْأَلِيمَ


201- Ba za su ba da gaskiya da shi ba har sai sun ga azaba mai radadiز


فَيَأْتِيَهُم بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ


202- Sannan azabar za ta zo musu ba zato ba tsammani ,ba kuma da saninsu ba.


فَيَقُولُوا هَلْ نَحْنُ مُنظَرُونَ


203- Sannan za su ce : yanzu za a saurara mana?


Kur’ani ba wai kawai yana magana da wadanda suka yi imani ba ne hatta kafirai da mushrikai dole su saurari bayanin gaskiya domin tabbatar da kafa masu hujja da tushe masu kofar kafa uziri da fakewa na rashin yin imani. Don haka Allah madaukakin sarki ke cewa: Mu ne muka sabkar da kur’ani cikin yanayi da kowa zai fahimce shi amma masu ruhin jayayya da girman kai da yawaita aikata sabo da banna na hana su karba da yin imani da shi Kur’ani. Da karyata shi da nacewa kan kafirci da cewa: Mu ba za mu yi imani ba sai idan mun ga azabar da ake gaya mana da tsoratar da mu da ita da idanunmu.Amma sun manta cewa a lokacin sabkar azaba babu wani sauran lokaci na karbar imaninsu domin ba a sanar da su kafin sabkar azaba ko bas u wata dama don lokaci ya kure masu kash.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Idan mutum ba a shirye yake ba kur’ani da bayanin gaskiya bay a ratsa zucciyarsa.

Na biyu: Cig aba da aikata saboda da banna na nisantar da mu daga karbar gaskiya.

Na uku: Kar mu shagala da mantawa da yin guzuri saboda gobe tamkar za mu dawwama a wannan duniya akwai mutuwa da azabar Allah na iya risker mu ba mu shirya ba a kowane lokaci.

Na hudu: Masu sabo a lokacin da mutuwa ta riske sun a bukatar a sake bas u wata damar amma in aba zai yuyu ba.

                                              • music***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 204 zuwa 207 a cikin suratul Shuara’a.


أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ


204- Yanzu azabarmu suke neman gaggautowa?


أَفَرَأَيْتَ إِن مَّتَّعْنَاهُمْ سِنِينَ


205- Ka ba Ni labara idan Muka jiyar da su dadi shekaru aru-aru.


ثُمَّ جَاءهُم مَّا كَانُوا يُوعَدُونَ


206- Sannan kuma abin da ake yi musu narko da shi ya zo musu.


مَا أَغْنَى عَنْهُم مَّا كَانُوا يُمَتَّعُونَ


207- Abin da ake jiyar da su dadi a da ba zai amfana musu komai ba.


Ayoyin da suka gabata na cewa: masu sabo a lokacin da zaba take sabka kan sun a bukatar a bas u wata damar ta gyara halayensu da yin imani to wadannan ayoyi da muka saurara sun amsa masu da cewa: ko da a sake bas u wata damar ta shekaru aru aru ba za su yi imani ba za su karyata alkawalin Allah saboda haka babu wani abu ko karfi a wannan duniya da zai hana sabkar azaba a kansu ko kare su. Su kafirai da masu girman kai duk wani waazi da gargadi da tsoratarwar sabkar azaba da manzonni za su yi masu ba za su yi imani ba sai kara dagawa da fasadi a doran kasa da yi masu izgili da cewa idan da gaske kake ka sa a sabkar mana da azabar a kanmu mu gani da idonmu amma lokacin da suka ga alamomin sabkar azabar sai su ce za a iya ba mu wata damar ta gyara halayenmu ?.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Wadanda ke karyata alkawalin Allah a yau ,wata rana za su nemi a bas u damar su yi imani don kubuta daga azabar amma babu wani amfani da amsa masu wannan bukata ta su.

Na biyu:Lokacin sabkar azaba babu wani abu ko kudi da mukami ko shahara da zai taimaka wa mutum da kubutar da shi.

Na uku: Jin dadin duniya na karkashin lutifi da falala daga Allah kuma a lahira sai wanda yayi aikin kirki ne zai rabauta.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 208 da aya ta 209 a cikin wannan sura ta Shuaara’a.


وَمَا أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ


208- Ba mu kuma taba hallaka wata al’umma ba face ta samu musu gargadi.


ذِكْرَى وَمَا كُنَّا ظَالِمِينَ


209- Wannan gargadi ne gare su ba Mu kuwa kasance azzalumai ba.


Wadannan ayoyi ci gaban ayoyin da muka saurara baya ne da kawo doka ta bai daya da cewa; sunnar All ace ta kafa hujja kan kowa ta hanyar aiko da manzonni da yi mana galgadi da nuna mana hanya madaidaiciya ta shiriya da samnin tsira duniya da lahira amma wadanda cikin sani da gangan da bijirewa dokokin Allah ,Allah zai azabtar da su da hallakar da su cikin adalcinsa da zaluncin da suka aikata.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu.

Na farko: Allah madaukakin sarki na tura wa dukan al’ummomi da mutane wadanda za su shiryar da su.

Na biyu:Azabtarwa ba tare da yin kashedi da farko ba zalunci ne Don haka kafin Allah ya hukumta masu sabo da banna a doran kasa sai ya aiko masu da masu shiryar da su da kafa musu hujja.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 210-216 (Kashi Na 674)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************

To madallah za mu fara shirin na yau da sauraren karatun aya ta 210 zuwa 212 a cikin suratul shu’ara’a.


وَمَا تَنَزَّلَتْ بِهِ الشَّيَاطِينُ


210- Kuma shaidanu ba su saukar da shi ba.


وَمَا يَنبَغِي لَهُمْ وَمَا يَسْتَطِيعُونَ

211- Kuma bai kamace su ba, ba kuma za su iya ba.


إِنَّهُمْ عَنِ السَّمْعِ لَمَعْزُولُونَ


212- Hakika su ababen kangewa ne daga jin wahayi.


Wadannan ayoyi da muka saurara ci gaba ne na ayoyin da muka saurara a shirin da ya gabata da ke bayani kan zargi da tuhuma maras tushe da makiya Allah da manzonsa da kuma addinin musulunci key i da cewa: Annabi Muhammadu yana da dangantaka da aljannu kuma sune suke gaya masa wadannan ayoyi da koyar da shi. A kullum makiya Annabawa da Manzonni zarginsu bay a huce cewa su annabawa da manzonni suna da tabuwar hankali,mawaka ne ko masu sihiri ko dangantaka da aljanno to Allah ya amsawa mushrikan Makka kan wannan zargin nasu kan manzon Rahama da cewa: Ku masu danganta ayoyin kur’ani da shaidanu a daidai lokacin da daukaka da karfin bayani da tunani da tsarin ayoyin kur’ani sun fi karfi shaidanu da aljannu kuma bas u da karfin sabko da wani abu makamancin kur’ani . Bugu da kari tun lokacin da manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka ya bayyana aka yanke duk wata alaka tsakanin aljannu da wata duniya ba wannan ba don haka bas u iya tsegumo labarai na gaibi da bayyanawa mutane .

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko;Kur’ani littafi ne mai tsarki da daukaka da karfin bayani da tsari da yafi karfin tunanin shaidanu.

Na biyu:shaidanu na iya gayawa masu aiki da su karya da karya amma bas u da karfi ko iko isa ko gayawa manzon Allah wani abu bas u da karfi da ikon hakan.

Na uku:Idan mutum ba a shirye yake b aba zai iya sauraren kalaman gaskiya da bayani na ayoyin kur’ani.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 213 zuwa 216.


فَلَا تَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ فَتَكُونَ مِنَ الْمُعَذَّبِينَ


213- To kada ka bauta wa wani tare da Allah ,sai ka zamanto daga wadanda za a yi wa azaba.


وَأَنذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ


214- Kuma ka gargadi danginka na kusa.


وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِمَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ


215- Ka kuma tausasa ga wanda ya bi ka daga muminai.


فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّي بَرِيءٌ مِّمَّا تَعْمَلُونَ


216- To idan suka saba maka sai kace : Ni hakika baa bin da zai shafe ni game da abin da kuke aikatawa.



A cikin wadannan ayoyin da muka saurara Allah Madaukakin sarki yana magana ne kai tsaye da manzonsa kan wasu lamura masu muhimmanci da umurtarsa kan wasu abubuwa.

Na farko kan masu kiyayya da Shi Manzo da cewa: dangane da makiya mushrikai ka kasance mai tsayin daka kuma kar ka dau=ina kiransu zuwa ga kadaita Allah da bauta kuma kar ka gajiya ko bin manufarsu.

Umarni na biyu kuwa shi ne kan makusantansa da cewa; kan kiran mutane zuwa ka tauhidi na kadaita Allah da bauta ka fara da kiran makusantanka danginka da galgadinsu kan yin shirka da bautawa gumaka.

Umarni na uku ya shafi mumunai da cewa; ka kasance mau saukin kai da tawadu’u da maamala mai kyau da sahabbanka da suka yi imani da sakon da ka zo da shi.Sabanin mahukumta da dagutai masu nuna girman kai da dagawa da girman kai kan wadanda ke tare su da nuna su sun fi su amma kai da sahabbanka dangantaka ce ta nuna kauna da girmama juna da nuna soyayya.

Umarni na hudu ci gaban umarni na biyu n da cewa: idan makusanta da danginka suka ki karbar kiran da ka yi masu na karbar tauhidi na kadaita Allah da bauta suka nace kan yin riko da shirka to ka fito fili karara ka bayyana masu kai kana neman tsarki da duk wata shirka.

Kamar yadda ya zo a cikin littafan tarihi ,bayan sabkar wannan aya Manzon rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka ya kirayi makusantansa danginsa da syka hada da Abu Talib,Abu Lahabi,Hamza bayan cin abinci Abu Lahabi ya hana damar manzon allah ya isar da wannan kira zuwa ga wadanda aka gayyata. A rana ta biyu ya sake kiran makusantansa wato danginsa a rana ta biyu bayan cin abinci sai y ace masu: Allah madaukakin sarki ya umarce ni da in kira ko zuwa ga tauhidi na kadaita Allah da bauta.Ni ina son alherin duniya da lahira a gare ku kuma babu wani da ya kawo wa al’ummarsa wani alheri kamar wanda na kawo muku kuma duk wanda yay i imani da taimaka mani zai zama wasiyi a wannan aiki na yada addinin musulunci. Daga cikn wadanda suka halarci wannan gurin babu wanda ya amsa sai Ali bin Abi Talib bayan haka sai manzon Rahama ya sake ce masu: ku sani wanna shi ne dan uwana ku wasiyi na da kuma wanda zai ci gaba da aikin da aka turo ni a tsakaninku. Ku saurara da aiki da jawabinsa da kuma yi masa biyayya.Wannan lamari ya faru kuma dukan malaman tarihi ko yawancinsu sun nakalto wannan labari .

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyar kamar haka;

Na farko:Duk wanda ya riki wanin Allah ba Allah ba ya wulakanta da fuskantar azaba kuma shirka ya kai mutum ga hallaka.

Na biyu: duk mutum ya rataya a kansa ya shiryar da makusanta da danginsa kan hanya madaidaiciya da fitar da son rai kan wannan nauyi.

Na uku: Dangantaka ta jinni kar ta samu da hana mu sabke nauyin da ya rataya kanmu na nuna hanya ta gari da hani da mummuna.

Na hudu: Daga cikin siffofin da ya kamata jagora da masu yada addini ya kamata a sansu da su akwai tawadu’u da tausayi da nuna kauna da soyayya ga wadanda ke tare da shi.

Na biyar: Jagororin jama’a dole sun yaki duk wani lamari na kaucewa hanya da gurbata al’umma da fitowa fili karara na yakar duk wani lamari na kaucewa hanya da gurbata al’umma.

Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 217-223 (Kashi Na 675)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************

To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 217 zuwa 220 a cikin wannan sura ta shuara’a.


وَتَوَكَّلْ عَلَى الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ


217- Ka kuma dogara ga Mabuwayi Mai rahama.



الَّذِي يَرَاكَ حِينَ تَقُومُ


218- Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi don yin salla.


وَتَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ

219- Da kuma yayin jujuyawarka cikin masu sujjada.


إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

220- hakika Shi Mai ji neMasani.


A cikin shirin da ya gabata kun ji yadda Allah madaukakin sarki ya bawa manzonsa umarnin mayar da amsa kan maganganun maras tushe da ya kamata da makiya kafirai da mushrikai ke fada.To a yau ayoyin da muka saurare ci gaban wannan umarni ne da cewa manzon rahama da yayi hakuri da kokarin yin tawakkali da Allah saboda Shi Allah mai nasara da galaba ne kan komi da kowa ,Idan ya kudurta babu wani abu ko wani da zai iya jurewa kudurasa. Idan kuka yi dubi a cikin tarihin annabawa da manzonnin da suka gabata za ku fahimci haka ku kalli makomar fir’auna da namrudu duk da karfin ikoknsu da tarin dukiya sun hallaka da daukaka annabi Musa (AS) kamar yadda aka hallakar da al’ummomin da suka kafircewa kiran annaba da manzonni (AS) a baya.

Ci gaban ayar na cewa:Allah madaukakin sarki a kullum da kowa ne lokaci yana tare da kai ko da a lokacin da kake sallah da ibadodi a tsakanin jama’a ko da a lokacin da kake kiran mushrikai zuwa ga kadaita Allah da bauta.Ma’ana a dukan lokaci yana ji yana ganin abin da kake yi kuma masani ne kan komi ko zai taimaka maka don haka ka yi tawakkali da allah da ci gaba da riko da hanyar shiryar da al’umma da jurewa adawar kafirai .

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:a maimakon ka yi dogaro da dukiya da matsayi na sahiri mafi dacewa shi ne dogaro da Allah madaukakin sarki wanda babu wani abu ko wani a wannan duniya da zai yi galaba kansa.

Na biyu: waliyan Allah suna cikin kulawa ta musamman ko da a lokacin da suke cikin yin ibada.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 221 zuwa 223.


هَلْ أُنَبِّئُكُمْ عَلَى مَن تَنَزَّلُ الشَّيَاطِينُ


221- Shin ba Na ba ku labara ba game da wanda shadanu suke saukar masa?


تَنَزَّلُ عَلَى كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ


222- Suna sauka ne kan duk wani makaryaci fajiri.


يُلْقُونَ السَّمْعَ وَأَكْثَرُهُمْ كَاذِبُونَ


223- Suna kasa kunne gamaganganun shaidanun ,yawancin su kuwa makaryata ne.


Wadannan ayoyi da muka saurara sun sake kawo wani daga cikin zargin makiya maras tushe da mushrikai da kafirai key i kan Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarka kuma suna cewa shaidan ne yake gayawa manzo wasu maganganu bugu da kari cewa: Shaidan yana rudar matane makaryata da karfafa masu yada fasadi da sabo da yada karyayyaki. To wannan zargi nasu ya sabawa hankali da tunani na hakika domin Shi Manzon a rayuwarsa ba a taba saminsa da karya kuma su kansu Mushrikan makka sun shaida hakan da saninsa a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana da aikata gaskiya.Shi kum taba saminsa da yin karya da yanzu za ku zarge shi da raya karya da cewa sakon da ya zo maku da shin a alheri daga shaidan ne ? Bugu da kari abubuwan da ke kumshe a cikin kiransa babu wani abu face tsarkake zucciya ,alheri da aikata ayyukan alheri da kuma nisantar zalunci da fasadi .alhali shi shaidan yana maida hankali ne wajen yada banna da fasadi da batar da mutane da sanya wasiwasi a cikin zukatansu.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Zukatan da suka gurbata wasiwasin shaidan yana ratsa su.

Na biyu: Karya da makaryaci wani babban gumshiki ne na aikata banna da sabo da aikin shaidan da kuma yake ratsa zucciyar mutum shi shaidan din.

                                • MUSIC***********


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..

Suratush Shu'ara Aya Ta 224-227 (Kashi Na 676)


Jama’a masu saurare barkarmu da warhaka da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke kawo ayoyin kur’ani mai girma da yin bayani kan irin nasihohin da suke tattare da su da fatar Allah ya sa mu dace a duniya da lahira amin summa amin kuma ni ne Tidjani Malam Lawali Damagaram ne zan kasance da ku daga farko har karshe a cikin shirin da yardar Allah.



                                  • MUSIC*************


                                • MUSIC***********

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 224 zuwa 227 a cikin shu’ara’a.


وَالشُّعَرَاء يَتَّبِعُهُمُ الْغَاوُونَ


224- Mawaka kuwa batattu ne suke bin su.


أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ


225- Ba ka san cewa su kutsawa suke yi cikin kowanne lamari ba?


وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ


226- Hakika kuma suna fadar yin abin da ba sa aikatawa.


إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَذَكَرُوا اللَّهَ كَثِيرًا وَانتَصَرُوا مِن بَعْدِ مَا ظُلِمُوا وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ


227- Sai dai wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki nagari, kuma suka ambaci Allah da yawa, suka kuma yi sakayya bayan an zalunce su. Wadanda suka yi zalunci kuwa ba da dadewa ba za su san kowace makomar za su koma.

Wadannan ayoyi sun zo ne a karshen surar Shu’ara’ kuma suna bayani ne kan daya daga cikin zargin makiya kan manzon Rahama (SWA) da amsa masu da cewa:Manzo shi ba mawaki ba ne kuma dukan maganganunsa gaskiya kwai suka kumsa ba hassashen mawaka ba .

Abin lura a nan a lokacin da manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya bayyana .mawaka da dama ne ke rayuwa a yankin Hijaz kuma duk wakokinsu sun kumshi ta’assubanci jahiliya da soyayya tamkar mafarki da yake yake a tsakanin kabilu da fifita wani ko wata kabila kan karya da hakan ke kara masu karfin guiwa da nuna jarumta kuma a duk shekara a birnin Makka ana tara mawaka domin nuna da zabar wakar da tafi fice da kafa ta a jikin dakin Ka’aba. Don haka Mushrikan maka suke danganta sakon da Manzon Rahama ya zo da shi da wake irin na su domin kaucewa gaskiya da gangan da kaucewa karbar gaskiya da kawao rudani a tsakanin jama’a.Shi wake bisa al’ada bay a aiki da hankali da hujjoji na hankali kawai kawo misali da yayi hannun riga da hakika kamar cewa wani zaki ne ,giwa ko nuna shi da wata dabba mai rauni da zurfafawa ko da kuwa aikin wannan mutum sam bai daidai da abin da wannan mawaki ke fada ba. Daga cikin mawaka ana samin wadanda ke yin tunani da fadin gaskiya da fadin kusan abin da wani ke aikatawa amma sai sun kasance ma’abuta tunani da aiki na alheri kamar yadda kur’ani yayi nuni da su da cewa; mawaka mumunai salihai wakokinsu na karfafawa mutane ga tunawa da Allah da fadakar da su daga barci kan aikata sabo da banna a tsakanin jama’a ,su azzalumai su sani za su hallaka ,su kuwa mumunai su ci nasara.

A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Ita kwarewa nada amfani musamman wadda aka yi tunani kanta da taimakwa jama’a isa da tsira ba wadda za ta kai mutane ga bata ba.

Na biyu: a musulunci wake yanada matsayi amma wanda ke fadin gaskiya da karfafawa mutum ga karba da aiki da gaskiya da ruhin imani.

Na uku:Kur’ani ya sabawa wake domin Shi kur’ani littafi ne na shiriya da shiryarwa da karfafa ruhin mumunai da sanya nutsuwa a ciki da wajen zukatan mumunai.

Na hudu:Allah bay a zaluntar kowa sai dai ya shirya amma ga wanda ya so shiriyar.


Da kuma wannan ne muka kawo karshen shirin na yau a madadin wadanda suka tallafa a cikin wannan shiri musamman injiniyanmu Muahammad Aminu Ibrahim Kiyawa ,Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar nake cewa wassalam..