Toggle menu
24.2K
670
183
158.8K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/18/IRIB Hausa Tafsir: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
 
(11 intermediate revisions by the same user not shown)
Line 1: Line 1:
== IRIB Hausa Tafsir ɗin Suratul Kahf ==
== IRIB Hausa Tafsir ɗin Suratul Kahf ==
[[Category:Quran]]
[[Category:Quran]]
[[Category:Quran/18]]
[[Category:IRIB_Hausa_Tafsir]]
<html>
<html>
<iframe width="100%" height="20" scrolling="no" frameborder="no" src="https://w.soundcloud.com/player/?url=https%3A//api.soundcloud.com/tracks/254962851%3Fsecret_token%3Ds-KfFbp&amp;color=ff5500&amp;inverse=false&amp;auto_play=false&amp;show_user=true"></iframe>
<iframe width="100%" height="20" scrolling="no" frameborder="no" src="https://w.soundcloud.com/player/?url=https%3A//api.soundcloud.com/tracks/254962851%3Fsecret_token%3Ds-KfFbp&amp;color=ff5500&amp;inverse=false&amp;auto_play=false&amp;show_user=true"></iframe>
Line 315: Line 317:


To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
===Suratul Kahfi, Aya Ta 22-26 (Kashi Na 503)===
<html>
<iframe width="100%" height="20" scrolling="no" frameborder="no" src="https://w.soundcloud.com/player/?url=https%3A//api.soundcloud.com/tracks/247836124%3Fsecret_token%3Ds-VrY3Q&amp;color=ff5500&amp;inverse=false&amp;auto_play=false&amp;show_user=true"></iframe>
</html>
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/503.mp3
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/503.html
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 22:
سَيَقُولُونَ ثَلَاثَةٌ رَّابِعُهُمْ كَلْبُهُمْ وَيَقُولُونَ خَمْسَةٌ سَادِسُهُمْ كَلْبُهُمْ رَجْماً بِالْغَيْبِ وَيَقُولُونَ سَبْعَةٌ وَثَامِنُهُمْ كَلْبُهُمْ قُل رَّبِّي أَعْلَمُ بِعِدَّتِهِم مَّا يَعْلَمُهُمْ إِلَّا قَلِيلٌ فَلَا تُمَارِ فِيهِمْ إِلَّا مِرَاء ظَاهِراً وَلَا تَسْتَفْتِ فِيهِم مِّنْهُمْ أَحَداً{22}
"Zã su ce: "Su uku ne, na hudunsu shi ne karensu." Kuma sunã cẽwa, biyar ne na shidansu ne karensu don lalube cikin duhu, (wasu) kuma sunã cẽwa su bakwai ne na takwas dinsu kuma karensu. Ka ce: 'Ubangijĩna shi ya fi sanin yawansu, bã wanda ya san lamarinsu sai yan kadan." To kada ka yi jãyayya game da alamarinsu sai dai a kan abin da yake fili kuma kada ka bai wa wani daga cikinsu fatawa game da su.
Wannan aya tana bayanin cewa, bayan abinda ya faru da mazauna kogo, zamani zai zo da jamaa zasu yi jayayya dangane da su. Maimakon su yi tunani kan manufar wannan lamari sun tsaya suna jayayya kan adadin mutanen da suyka zauna a cikin kogon, kowanne suna cewa adadinsu kaza ne, alhali kuwa ko su uku ne ko biyar ko bakwai ne bas hi da wani babmbamci kuma ma zai yi tasirin komai ba a imaninsu ko ainiknsu ba. Amma yawa yawn mutane suna zato ne kawai kuma ko da akan abinda ba su sani ba ma suna son su fadi raayinsu a kansa. A wannan aya Allah ya na fada wa manzon sa cewa kada ya yi jayayya da muatne kuma kada ya tambayesu komai, Allah ne ya san adadin mazauna kogon.
Darusa:
1-Abinda ba mu sani ba kada mu yi ta zato da kame kame, kuma mu guji yin jayayya a kansa.
2-Wajen binciken alamuran da suka faru a tarihi ya kamata mu yi tunani da daukar darasi ba wai mu tsaya jayayya kan adadi ko mutane ba.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 23 da ta 24:
وَلَا تَقُولَنَّ لِشَيْءٍ إِنِّي فَاعِلٌ ذَلِكَ غَداً{23} إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ وَاذْكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلْ عَسَى أَن يَهْدِيَنِ رَبِّي لِأَقْرَبَ مِنْ هَذَا رَشَداً{24}
"Kada kuma ka ce ga kowane, "Hakikazai aikatã wannan gõbe."
"Sai dai ka ce 'Idan Allah Ya so'. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "Ina kaunar Ubangijĩna ya shirye ni zuwa ga mafi kusa da daidai gane da wannan."
Wadannan ayoyi suna bayanin wata doka da ta shafi kowa da kowa koda yake suna Magana ne da Annabi kai tsaye, amma dukan Musulmi dole ne su kiyaye dokar. Ayoyin suna baynin cewa a duk Magana ko aiki da za a yi a nan gaba ya kamata mumini ya ce in sha Allah a duk lokacin da zai ce zai aikata wato y ace idan Allah ya so. Dalilin wannan shi ne saboda mai magana da mai ji duk su san mahinta cewa abionda mai magana yake fadi said a yardar Allah ne zai iya aikata shi, idan kuwa Allah bai so ba babu abinda yake faruwa. Wato masu imani suna dogara da Allah kuma suna cewa in sha Allah, kamar dai yanda Alkurani ya kawo a cikin maganganun wasu annabawa kamar Yakubu, Shuaibu, Haliru da Ismail. Fadar wannan magana ba wai a kan fatar baki ne kawai, hakan yana bayyana imani da mahangar Musulmi ne wanda ya ke ganin cewa babu abinda zai iya faruwa said a izinin Allah.
Ko da yake kowane mutum yana da nufi da zabi amma faruwar kowani aiki baya dogara kan nufin mutane saboda akwai wasu dalilai da hujjoji da ya wadanda suke da tasiri wajen faruwar wannan abu. Lallai ba bu abin da zai tabbata sai idan Allah ya so.
Darusa:
1-Ka da mu dogara kan kokarinmu da dabararmu. Ka da mu dauka muna da yancin ya ba ikon Allah cikinsa saboda haka kada mu manta da Allah wajen daukar ko wane mataki.
2-Idan annabawa suna bukatar shiryarwa daga Allah a alamuransu na rayuwa, ina ga batun mud a ba annabawa ba? Saboda haka har a kullum mu nemi Allah ya nuna mana mafi kyawun hanya.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 25 da ta 26:
وَلَبِثُوا فِي كَهْفِهِمْ ثَلَاثَ مِئَةٍ سِنِينَ وَازْدَادُوا تِسْعاً{25} قُلِ اللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا لَبِثُوا لَهُ غَيْبُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ أَبْصِرْ بِهِ وَأَسْمِعْ مَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا يُشْرِكُ فِي حُكْمِهِ أَحَداً{26}
"Suka kuwa zauna cikin kõgonsu shẽkaru darĩ uku kuma suka kara tara.
"Ka ce: 'Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.' Asirin da yake cikin sammai da kasa na sa ne. Wa yake da ji da gani irin na sa! Bã su da wani mataimaki in ban da shi; ba ya kuma tãrayya da wani a cikin hukuncinsa."
Wadannan ayoyi suna ci gaba da bayani kan mazauna kogo wato Ashabul Kahfi tana cewa, Da ikon Allah sun zauna cikin kogon nan shekaru 309. Bisa dabi'a su da suka yi wadannan shekaru suna barci da kuma sauran mutane, ba wanda yake da labarin wannan tsawon lokaci, Allah kadai ne ya san da wannan labari kuma shi ya san yanda suka zauna a cikin kogon ya kuma kiyaye su suna barci. Babu shakka rayuwa har shekaru 300 da doriya ba tare da cin abinci da ko shan ruwa ba mujiza ce daga mujizojin Allah. Hakika Allah ya kare rayuwar mutanen kogo a duk wannan zamani domin ya zama darasi ga masu zuwa nan gaba.
Darusa:
1-A duk wurin da adadi ko alkaluma suke da muhimmanci wajen fassara wani abu to ya kamata a ba da alakluman daidai. Adadin shekarun da Ashabul kahfi suka zauna cikin kogo yana nuni da girman ikon Allah a wannna alamari.
2-Ubangiji shi ne mamallakin komai shi ne kuma mai ba da doka, shi ne masanin komai ko bayyane ko boye saboda haka ba mai iya gudu a tsere wa ikonsa a fake a bayan wani, sai dai a gudu daga wani a fake a wurin Allah.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
===Suratul Kahfi, Aya Ta 27-31 (Kashi Na 504)===
<html>
<iframe width="100%" height="20" scrolling="no" frameborder="no" src="https://w.soundcloud.com/player/?url=https%3A//api.soundcloud.com/tracks/247836122%3Fsecret_token%3Ds-kbUYl&amp;color=ff5500&amp;inverse=false&amp;auto_play=false&amp;show_user=true"></iframe>
</html>
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/audio/18/504.mp3
* http://hausa.irib.ir/quran/hoosa/programs/text/18/504.html
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 27:
وَاتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِهِ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِ مُلْتَحَداً{27}
"Ka karanta abin da aka yi wo maka wahayi da shi daag littãfin Ubangijinka. Bãbu mai canja kalmõminSa kuma bã zã kã sãmi wata mafaka ba in ba ta wurinsa ba.
A karshen labarin Ashabul Kahfi wannan aya tana magana da Annabin Musulunci Muhammadu dan Abdullahi (tsira da amincin Allah su ntabbata a gareshi da alaten gidansa) tana cewa, maganganu marasa hujja da surkulle dangane da wadanan suna da yawa, amma ka fada wa mutane bayanin da ya zo maka cikin wahayi ka fita sha’anin abinda wasu suke fada. Masu saba wa Annabi saboda dalilai daban daban suna bukatar ya sauya wasu ayoyi ko ya canya su domin su yarda da abinda suka kunsa, amma wadannan ayoyi suna nuna cewa kada Annabi ya kula su ya kuma ce musu Alkurani zancen Allah ne kuma baya yiwuwa a canja shi kuma duk wanda ya aikata haka ba zai sami kariya daga azabar Allah ba.
Darusa:
1-Alkurani maganar Allah ce ba ta mutum ba, saboda haka babu hanyar sauya shi a da balle kuma a yanzu.
2-Alkurani shi ne littafin Allah na karshe kuma an kare shi daga dukkan nau’o’in canji kuma ba ya bukatar wani littafi saukakke domin gyara abinda hala mutane zasu sauya daga cikinsa, domin ba bu canjin da zai same shi.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 28:
وَاصْبِرْ نَفْسَكَ مَعَ الَّذِينَ يَدْعُونَ رَبَّهُم بِالْغَدَاةِ وَالْعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجْهَهُ وَلَا تَعْدُ عَيْنَاكَ عَنْهُمْ تُرِيدُ زِينَةَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَلَا تُطِعْ مَنْ أَغْفَلْنَا قَلْبَهُ عَن ذِكْرِنَا وَاتَّبَعَ هَوَاهُ وَكَانَ أَمْرُهُ فُرُطاً{28}
"Ka kuma hakura wa kanka (da zama) tare da wadanda suke bauta wa Ubangijinsu sãfe da maraice, sunã neman yardarSa. Kuma kada ka kawar da idanunka daga gare su kanã neman adon rãyuwar dũniya. Kuma kada ka bi wanda Muka shagaltar da zũciyarsa daga ambaton Mu, kuma ya bi son ransa, wanda kuma al'amarinsa ya zama ketare haddi ne.
A cikin labaran tarihi an bayyana cewa wasu manyan mutanen kabilar Kuraishawa sun gabatar wa Annabi da sharadin sai ya kori talakawa marasa daraja a idon jamaa da kuma maida hankalinsa ga sauraron manyan gari da mnasu hamnnu da shuni don su yi imani da sakon Manzon Allah. A cikin tsurin ido da rashin ladabi suka ce da Annabi, ‘Ba zamu taba zuwa majilisinka ba kum aba zamu saurtari maganaerkja ba idan dai wadsnmnan mutane makasta\\kantya suna taree da kai.’ A zamanin Annabi Nuhu ma mutaensa masu jin ceewaa su manya nne sun yi irin wanna bukata, shi kuma sai ya mayar musu fda martini cewa ba zai rab u tad a munminai saboda talkaucinsu ba. Wanna aya tana sukar irin wanna tunani , tana cewa kada Annabi ya saurari wannan yaudara tasu ya kuma kori muminai na gari kamar Abu Zar da Salman ya kore su saboda talauci ko karancin abin hannunsu, ko kuma ya yi ta fama yana bin mutanen da duniya ta aure ko kuma suka mance da ambaton Allah wai dominsu yi imani, wadanda kuma uske bi son zuciyarsu kuma basu da niyar barin bauta wa duniya.
Darusa:
1-Zama da tausaya wa talakawa ya na da wahala amma muminai talakawa sun fi kafirai masu dukiya daraja kuma alummar Musulmi su yi cikakkiyar kulawa da talakan Musulumi.
2-Hadarin da neman duniya yake yi wa jagorannin alummar Musulmi ya kai munin da har Allah yana yi wa Annabinsa kashedi a kansa.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 29:
وَقُلِ الْحَقُّ مِن رَّبِّكُمْ فَمَن شَاء فَلْيُؤْمِن وَمَن شَاء فَلْيَكْفُرْ إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَاراً أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاء كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءتْ مُرْتَفَقاً{29}
"Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." To wanda ya so sai ya ba da gaskiya, wanda kuma ya so sai ya kãfirta, hakika kam Mun tanadar wa azzãlumai wuta wadda katangarta ta kẽwaye su, idan kuma suka nẽmi taimako to za a taimake su ne da ruwa irin na narkakkiyar darma wanda yake toye fuskoki; abin sha ko ya yi mũgunta, makoma kuma ta munana.
Domin amsa maid a martabi kan bukatun wadannan gafalallun masu dukiya wannan aya ta bmna cewa, ai ba wanda yake bukjatar imanin da zasu yi balle nma su sanya wannan sharadi. Maganar gaskiya ta sauka dagha kuma duk wanda ya ga dama ya yi imani duk kuma wanda ya ga dam aya kafirce. Imani ai ba abinda zaa roki wani ya yi bane; mumini daya na hakika ya fi kafirai dubu da zasu ce wai sai da wani sharadi zasu imani. Dadin dadawa ma, mutanen da suka nitse cikin fasadi da bautar ciki a nan duniya, zasu gamu da wurin zama da abinci da abin sha mafiya muni a lahira. Ka da ka dubi rayuwarsun ta wannan duniya wacce gajera ce mai wucewa.
Darusa:
1-Kafirci ko imaninn mutane bas u da wani tasirei wajen tabbatar da gaskiyar addini. Alkurani gaskiya ne koda dukkanin mutane zasu kafrice masa.
2-Koda yake mutane suna da yancin zabar imani ko kuma kafirci amma a karshen aikin kowane daya wadannan daga cikinsu zai hadu da sakamakon daban da na dayan kuma a lahira kafirai zasu gamu da azabar wuta.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 30 da ta 31:
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجْرَ مَنْ أَحْسَنَ عَمَلاً{30} أُوْلَئِكَ لَهُمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهِمُ الْأَنْهَارُ يُحَلَّوْنَ فِيهَا مِنْ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٍ وَيَلْبَسُونَ ثِيَاباً خُضْراً مِّن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ نِعْمَ الثَّوَابُ وَحَسُنَتْ مُرْتَفَقاً{31}
"Lalle ne wadanda suka yi ĩmãni kuma suka yi aiki na gari hakika Mu ba Mu tõzarta lãdan wanda ya kyautata aiki."
"Wadannan sunã da gidãjen Aljanna na dawwama wadanda kõramu ke gudãna daga karkashinsu, anã sanya musu kawa, a cikinsu, daga mundãye na zinariya, kuma sunã tufantar wadansu tũfãfi kõre, na alharĩni rakĩki da alharini mai kauri sunã kishingide a cikinsu,a kan, karagu. Mãdalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutãwa."
Wadannnan ayoyi suna bayanin matsayin muminai sana cewa, su wadannan talakawan da ku ke gani a nan duniya , idan masu biyayya ne ga Annabi da rikon da tafarkin Allah kamar yanda ya dace, a ranar alkiyama zaa saka musu da mafi kyaun wurin zama, wurin da masu dukiya a nan duniya zasu yi dokin su zauna a cikinsa koda na dan lokaci ne. Idan a yau masu mukami suna sanya tufafi na alfarma da kayan ado masu tsada, suna daukar kansu masu girma, to ai su kuma matalauta a ranar lahira zasu sami tufafi da kayan ado wadanda ba za a iya kwatantasu da kayan adon wannan duniya ba. Amma fa marasa galihun zasu sami wannan jin dadi a lahairan ne idan sun yi imanin kwarai da ayyuka na gari, wanda kuma su ma masu dukiya idan sun yi biyayya ga Allah suka nisanci girman kai da sauda yawa dukiya take sa mutum, zasu sami sakamako mai kyau da jin dadi a lahira.
Darusa:
1-Abin da muminai suka rasa a nan duniya saboda bioyayya ga dokokin Ubangiji, a ranar alkiyama Allah zai mayar musu da gurbinsa da abin da fi shi dadi da kuma kyau.
2-Mu yi aiki domin Allah, aikin da ba zai rage mana ladanmu ba kuma ladansa ba irin ladan nan ne mai karewa nan take ba.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
<!-- Begin Massive Paste -->
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 32-36 (Kashi Na 505) ===
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 32 da ta 33:
وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلاً رَّجُلَيْنِ جَعَلْنَا لِأَحَدِهِمَا جَنَّتَيْنِ مِنْ أَعْنَابٍ وَحَفَفْنَاهُمَا بِنَخْلٍ وَجَعَلْنَا بَيْنَهُمَا زَرْعاً{32} كِلْتَا الْجَنَّتَيْنِ آتَتْ أُكُلَهَا وَلَمْ تَظْلِمْ مِنْهُ شَيْئاً وَفَجَّرْنَا خِلَالَهُمَا نَهَراً{33}
"Kuma ka buga musu misãli da wadansu [[maza]] biyu. Mun sanya wa dayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka [[kewaye|kẽwayesu]] da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin)."
"Kõwace gõna daga biyun, tã bãyar da amfãninta, kuma ba ta yi zãluncin kõme ba daga gare shi. Kuma Muka bubbugar da [[koramu]] a tsakãninsu.
Wadannan ayoyi da wasu masu biyo musu suna bayanin wani misali ne da Allah ya kawo domin shiryar da mutane, misalin dai na [[bangarorin]] alumma ne guda biyu. Na farko masu dukiya ne wadanda Allah ya yi wa arziki mai yawa amma maimakon su bauta masa su yi godiya sai [[girman kai]] ya same su har su ka [[kafirce]] wa Allah. Bangare na biyun kuma [[matalauta]] ne wadanda a ko da yaushe masu dukiyar suna musu [[izgili]] suna wulakantasu sun ... a komai ba ne, alhali kuwa [[matalautan]] nan sun kai matsayi mai girma na imani kuma sun zabi kyautata aikin lahira bisa ga neman duniya.
Darusa:
1-Ruwa da kasa da rana da itatuwa da dukkakn abin da ake shukawa daga Allah suke gudana.
2-Fifikon da mutane suke da shi wajen mallakar dukiya da sauran abubuwan da wani ya fi wani da su kamar karfi da lafiya da basira, dukkan wannan hikima ce ta Allah, kuma bai kamata wannan fifiko ya sa mai dukiya ya yin girman kai ko [[talaka]] yanke kauna ba.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 34 da ta 35:
وَكَانَ لَهُ ثَمَرٌ فَقَالَ لِصَاحِبِهِ وَهُوَ يُحَاوِرُهُ أَنَا أَكْثَرُ مِنكَ مَالاً وَأَعَزُّ نَفَراً{34} وَدَخَلَ جَنَّتَهُ وَهُوَ ظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ قَالَ مَا أَظُنُّ أَن تَبِيدَ هَذِهِ أَبَداً{35}
"Kuma dan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a."
"Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: 'Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada."
Bayan ayoyin da suka gabata sun bada labarin mai gona da itatuwansa, wadannan ayoyi kum asuna cewa girman kai ya shiga zuciyar mai gona har yana alfahari da gonarsa a gaban abokinsa wanda ba shi irin wannan gona. Yana ganin girman wannna gona ta sa har ya dauka ba zata kare ba har abada kuma har abada zai kasance mai dunika da niimomi, alhali kuwa sabon day a ek yi ne ya sanya wannna tunani na kuskure wanda kuma ba shi da samuwa.
Darusa:
1-Hankoro kan abin duniya da dukiya da iko suna jawo aikata zalkunci.
2-Daukar cewa mtum mya fi wani da wulakanta wasu, zalunta kai ne kafin ma ya zama zalunci ga wasu domin kuwa wannan hali yana nisanta mutu daga Ubangioji ya kusata shi da dabbanci.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 36:
وَمَا أَظُنُّ السَّاعَةَ قَائِمَةً وَلَئِن رُّدِدتُّ إِلَى رَبِّي لَأَجِدَنَّ خَيْراً مِّنْهَا مُنقَلَباً{36}
"Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma."
Wanna aya tana bayani kan karshe wanda ya yi maye da son duniya da bauta mata, wadanna mutane suka inkarin lahira su kuma yi tsammanin cewa duniya ce kadai samamma. Jin mutum ya fi nwasu da jiji da kai da wadannan suke fama das hi ya kai har ma suna fada wa muminai cewa idan ma maganar ku gaskiya ce kuma akwai ranar alkikyama a can ma mu ne zamu sami jin dadi ba ku ba. Wadannan mutane suna tsammanin cewa niimomin da dukiyar da suke da ita hakkinsu kuma dole ne a kullum Allah ya basu niimiomin. Sun dauka su wani jinsin bil Adama ne da ya fi saura asali kuma sunn fi saura cancantar komai ko a duniya ko a lahira, alhali kuwa lahira sakamakon wanna duniya ne ba ci gaban halin da mutum yake a cikinta ba, kumna a kotun Ubangiji mai adalci mutane zasu sami sakamakon ayyukansu ne, ko lada ko azaba, ba wai matsayinsu ko ikon da suek das hi aduniya ne za a duba ba.
Banda haka kuma, dukkan dama da mutum ya samu a duniya ai daga kyautar Allah ne, ba wai saboda mutune suna da wani hakki a kan Allah ba, amma abi takaici wadanda suka kafirce sun jahilci wannan.
Darusa:
1-Idan dukiya da iko ba kan tafarkin imani suke ba zasu kai masu su ga kafircewa da karyata addini, har su kai mutum ga shiga Jahannama.
2-Burace-burace marasa kan gado basu da kima, kuma ana samun aljanna ne da aiki.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 37-44 (Kashi Na 506) ===
Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu alaikum jamaa masu saurare. Barkan mu da sake saduwa a shirin Hannunka mai Sanda shirin da yake kawo muku sharhi na ayoyin Alkurani mai girma. Zamu ci gaba da bayani ne a cikin Surar Kahfi, ta fatar Allah ya bamu hasken Alkur’ani mai girma ya kuma taimaka mana wajen aiki da koyarwarsa.
To madalla. Da farko bari mu saurari aya ta 37 da ta 38:
قَالَ لَهُ صَاحِبُهُ وَهُوَ يُحَاوِرُهُ أَكَفَرْتَ بِالَّذِي خَلَقَكَ مِن تُرَابٍ ثُمَّ مِن نُّطْفَةٍ ثُمَّ سَوَّاكَ رَجُلاً{37} لَّكِنَّا هُوَ اللَّهُ رَبِّي وَلَا أُشْرِكُ بِرَبِّي أَحَداً{38}
"Abõkinsa ya ce da shi yana mai muhãwara da shi, "Yanzu ka kãfirce wa wanda Ya halicce ka daga kasa, sannan (kuma) daga digon maniyi, sa,an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?"
"Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba"
A shirin da ya gabata mun ji bayani kan muhawarar mutane biyu gudan mai arziki amma ya kafircewa Allah duk da niimomin da ya ba shi, gudan kuma matalauci ne amma mumini. Kafirin Allah ya yi masa arzikin gona mai yayan itatuwa da dabinai da shuke shuke, amma maimakon ya yi wa Allah godiya sai ya yi ta alfahari da wannan dukiya yana izgili wa abokinsa muminin nan saboda talaucinsa. Wadanna ayoyi kuma sun ambaci martanin da muminin nan ya mayarwa abokinsa yana cewa, me ya sa ba zai yi wa Allah godiya ba kan niimoin da ya ba shi, kuma a maimaikon haka ma har yana kafirce wa Ubangiji? Amma a maganganun mai gonan babu karyata samuwar Allah, abinda ya ce shi ne ba bu ranar alkiyama. Amma abokinsa muminin ya ce ya karyata Allah domin kuwa bisa hakika inkari ko karyata cewa Allah yana da ikon tayar da matattu yana daidai da karyata mahalicci Allah.
Darusa:
1-kaunar dukiya har ya wuce haddi tana iya jawo wa mutum kafirce wa Allah wato ya karyata in day a fito da inda zaya wato dai ya musanta cewa Allah ne halicce shi kuma akwai ranar alkiyama da zai tashe shia cikinta. Saboda haka dole ne ko da yaushe mu kasance muna taka tsantsan da son dukiya.
2-A wajen muhawara da wadanda ba Musulmi ba dole ne mu yi amfani da kwararan hujjoji na hankali saboda hakan ya zama hanyar shioriyarsu
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 39 da ta 40 da ta 41:
وَلَوْلَا إِذْ دَخَلْتَ جَنَّتَكَ قُلْتَ مَا شَاء اللَّهُ لَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ إِن تُرَنِ أَنَا أَقَلَّ مِنكَ مَالاً وَوَلَداً{39} فَعَسَى رَبِّي أَن يُؤْتِيَنِ خَيْراً مِّن جَنَّتِكَ وَيُرْسِلَ عَلَيْهَا حُسْبَاناً مِّنَ السَّمَاءِ فَتُصْبِحَ صَعِيداً زَلَقاً{40} أَوْ يُصْبِحَ مَاؤُهَا غَوْراً فَلَن تَسْتَطِيعَ لَهُ طَلَباً{41}
"Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani karfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi karanci daga gare ka a wajen dũkiya da diya."
"To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turbãya mai santsi."
"Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari fakakke, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta."
A ci gaban muhawarar mutanen nan biyu muminin ya ce; Me ya sa ba ka dauka cewa gonarka da niimomin da suke cikinta duka ba ka dauka Allah ne ya baka sub a balle ma ka yi godiya? Shin ba ka san cewa komai da ikon allah ne ya ke tabbata ba? Ka na dauka kai ne mamallakin na hakika ga wannan gonad a itatuwanta kuma ba hannun Allah a ciki? Ai Allah ne yake tsirar da itatuwan da shuke shuken, kuma kai kam ba abinda ka yi in banda bunne iri da zuba masa ido. Ba Allah ne ya aiko da isaka da ruwa, ya samar da hasken rana da ma kasar da ka yi shuka a cikinta ba? Kai kanka ma da duk abinda ka mallaka daga Allah ku ke kuma ba abinda zai tabbata in ba tare da ikon Allah ba.
Miuminin ya ci gaba da cewa, ai idan Allah yana so zai ba ni gonar da ta fi taka, kai kuma ya hallaka gonarka, saboda haka kada ka kallafa rai a akanta kuma kada ka yi ji isa saboda ba abinda kake da iko a kansa. Ba mamaki tsawa daga sama ta kona maka gona ko kuma kamfan ruwa ya sa ruwan kasa ya yi nisan da komin tonawa ba zaka iso shi balle ma ka shayar da gonar.
Darusa:
1-Idan mun sami niimomin irin na dabi’a ko kuma muka dubi itatuwa da tsirrai masu ban shaawa to sai mu tuna da Allah kuma mu ambace shi da harsunan.
2-Mutum mumini ba ya rena kansa ko ya ji kaskanci saboda kawai yana cikin talauci domin kuwa yana dogara ne da Allah.
Yanzu kuma sai mu saurari aya ta 42 da ta 43 da kuma ta 44:
وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِ فَأَصْبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيْهِ عَلَى مَا أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَى عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُشْرِكْ بِرَبِّي أَحَداً{42} وَلَمْ تَكُن لَّهُ فِئَةٌ يَنصُرُونَهُ مِن دُونِ اللَّهِ وَمَا كَانَ مُنتَصِراً{43} هُنَالِكَ الْوَلَايَةُ لِلَّهِ الْحَقِّ هُوَ خَيْرٌ ثَوَاباً وَخَيْرٌ عُقْباً{44}
"Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!"
"Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, wadanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba.
"A can taimako da jibinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kuma Mafĩ fĩci ga ãkiba.
Muhawarar mutanen biyun mumikni da kafiri ta kawo karshe amma kafirin bai yi imani ba, bai kuma bar jin isa da girman kai da karyatawa ba.
Azabar Allah ta sauka ta hallaka itatuwa da shukar duk da take cikin gonar kuma a lokacin da ga yanda gonarsa ta zamo sai ya yi tab akin ciki tyana cizon yatsa saboda dukiyar da ya kashe a gonar. A wannan lokaci ne fa ya gane kuskurensa ya yi ta nadama yana cewa, in ama da ban gafala na mance da Allah ba, ina ma da ban yi wa Allah tarayya da wani a cikin aikinsa ba, ina ma da na yi imanin cewa komai aikinsa ne shi kadai.
Sai dai yanzu kam nadama ba zata yi amfanium ba kuma ba wanda zai iya kawo masa dauki. A nan komai ya bayyana cewa ikon dukkan abunbuwa yana hannun Allah kamar yanda a ranar alkiyama ma komai yana hannun sa kuma yana sakantawa da lada ko kuma azaba duk a hannnun Allah suke.
Darusa:
1-Azabar Allah ba ta kebanci lahira ba, wani lokaci a nan duniya ma tana kama mutane masu girman kai da jiji da kai.
2-Masu neman duniya kadai suna mancewa da Allah idan suna nazarin alamuran dukiya.
To a nan zamu dakata a shirin Hannunka mai Sanda sai kuma shiri na gaba da yardar Allah zaku ji bayanai akan wasun ayoyin na Surar Kahfi. Tare da fatar Allah Madaukakin Sarki ya haskaka zukatanmu da hasken Alkurani. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi taaala wa barakatuhu.
Suratul Kahfi, Aya Ta 45-49 (Kashi Na 507)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa cikin shirimmu na hannunka mai sanda . Shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu kasar yadda aka saba.
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 45 daga cikin saratul Kahfi kamar haka.
وَاضْرِبْ لَهُم مَّثَلَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا كَمَاء أَنزَلْنَاهُ مِنَ السَّمَاءِ فَاخْتَلَطَ بِهِ نَبَاتُ الْأَرْضِ فَأَصْبَحَ هَشِيماً تَذْرُوهُ الرِّيَاحُ وَكَانَ اللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ مُّقْتَدِراً{45}
45-Ka buga musu misãlin rãyuwar dũniya, kamar ruwa ne wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirran kasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wãyi gari busasshe, iska tanã kada shi ko ta ina. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ĩko ne a kan dukan kõme.
A cikin shirimmu da ya gabata Allaha ya bada misalai da dama ga na muminai da kuma kafirai a rayuwarsu ta duniya.
Wannan ayar tana bayyana yadda yanayi yake sauyawa a rayuwarmu da duniya. Tana cewa misalin rayuwar duniya din nan kamar ruwan sama ne wanda ya sauko daga sama ya garwaya da iri sai ya sama kore car, amma bayan wani lokaci kuma tsirran suka bushe iska na kadsu ko ta ina.
Wannan lamarin yana faruwa a gaban idommu a ko wani lokaci. Idan damina ta zo kasa ta rayu tare da ruwan sama da ke saukowa amma da zaran baraza ko rana ta shigo sai kada tsirrai sun bushe sun yada ganyayyakinsu sun mace iska na kadasu.
To rayuwa duniya kadance kamar yadda rayuwar wadannan halittun Allah suke. Don haka yakamata mai hanakali ya dauki darasi a cikin wannan misalin ya san cewa rayuwar duniya ba mai dawwama ce ba.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Littafin Alkur'ani littafi ne na bada tarbiyya. A cikin misalai da yake bayarwa, yana farkar da mutane kan gaskiya da kuma abinda ya shafi rayurawu.
2. Kada mu bar gajuruwar rayuwarmu ta duniya ta tafi a banza. Mu yi amfani da ita don samun rayuwa madawwami a rahira.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 46 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
الْمَالُ وَالْبَنُونَ زِينَةُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَالْبَاقِيَاتُ الصَّالِحَاتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّكَ ثَوَاباً وَخَيْرٌ أَمَلاً{46}
46-Dũkiya da diya, sũ ne kawar rãyuwar dũniya, kuma ayyuka mãsu wanzuwa na kwarai sun fi zama alhẽri a wurin Ubangijinka ga lãda kuma sun fi alhẽri ga bũri.
Bayan misalin da alkur'ani ya bayar na takaitaccen rayuwar tsirrai don mutum ya dauki darasi daga wannan. Wannan ayar kara da cewa, banda wannan, yaya da dukiya a duniya bazasu yi wa mutum wani amfani a lahira ba. Abinda yake amfani shi ne ayyuka na gari. Banda wannan Allah yana ninninka ayyukan bayi wadanda suka sanya burinsu zuwa gareshi. Don haka ladar ubangiji ya fiye maka kan duk abinda zaka samu a duniya.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Samu da rashi a duniya ba shi ne abin lura a lahira ba. Ayyuka na alkhairi sune zasu zama abin da ke daga darajar mutum a lahira.
2. Lamura a duniya duk ba tabbatattu bane. Abinda zai wanzu shi ne ayyuka na gari. Kuma shi ne kadai Allah ya yi alkawarin tabbatarsu.
Yanzun kuma mu saurari ayoyi na 47, 48 da kuma 49 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَيَوْمَ نُسَيِّرُ الْجِبَالَ وَتَرَى الْأَرْضَ بَارِزَةً وَحَشَرْنَاهُمْ فَلَمْ نُغَادِرْ مِنْهُمْ أَحَداً{47} وَعُرِضُوا عَلَى رَبِّكَ صَفّاً لَّقَدْ جِئْتُمُونَا كَمَا خَلَقْنَاكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ بَلْ زَعَمْتُمْ أَلَّن نَّجْعَلَ لَكُم مَّوْعِداً{48} وَوُضِعَ الْكِتَابُ فَتَرَى الْمُجْرِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَا وَيْلَتَنَا مَالِ هَذَا الْكِتَابِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةً وَلَا كَبِيرَةً إِلَّا أَحْصَاهَا وَوَجَدُوا مَا عَمِلُوا حَاضِراً وَلَا يَظْلِمُ رَبُّكَ أَحَداً{49}
47-Kuma a rãnar da Muke tafiyar da duwãtsu, kuma ka ga kasa bayyane, kuma Mun tãra su baMu bar kõ guda daga cikinsu ba.
48-Kuma za'a bijirosu ga Ubangijinka sunã sahu sahu, (Mu ce musu), "Lalle ne hakĩka kun zo Mana, kamar yadda Muka halicce ku a karon farko. Ã'a, kun riya cẽwa bã zã Mu sanya muku wani lõkacin haduwa ba."
49-Kuma aka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽ ya faru ga wannan littãfi, bã ya barin karama, kuma bã ya barin babba, fãce yã kididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa.
Bayan da alkur'ani ya bayyana rashin tabbaci da ke cikin rayuwar duniya. Wadannan ayoyin suna bayyana yadda ranar kiyama take. Da fako duk abinda kuke gani na manya manyan halittun Allah kamar duwatsu da kasa da rana da wata, duk zasu bace.
Sannan mu sami kammu a wata sabuwar duniya wacce ake kira lahira. Ita lahiya tana da tsarinta badan da ta wannan duniyar da muke ciki.
Dukkan mutane tun farkon halittarsu har zuwa na karshensu zasu hadu a wuri guda a lokaci guda.
A nan ne kowa zai ga ayyukansa da yayi a rayuwar duniya, a fili, basu karami babu babba duk zasu bayya. Masu laifi sai su fara jin tsoro don sun san cewa babu mafita, kuma basu isa suyi inkarin ayyuka marakyau da suka aikata ba.
Muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi kamar haka
1. Tashin mutane a lahira kamar yadda suke a duniya ne. Wato da jikunkunansu na duniya.
2. Rashin kula da lamarin lahira a duniya shi ke sanya mutum ya shiga cikin tsoro da firgici a ranar kiyama.
3. A lahira , abinda zia bayyana na mutum shi ne ayyukansa daga cikin dukkan abinda ya mallaka.
Masu sauraro anan zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.
Suratul Kahfi, Aya Ta 50-53 (Kashi Na 508)
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa sikin shirimmu na hannunka maisanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu kamar yadda muka saba.
To bari mu fara shirimmu nay au tare da sauraron karatun aya ta 50 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ الْجِنِّ فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ أَفَتَتَّخِذُونَهُ وَذُرِّيَّتَهُ أَوْلِيَاء مِن دُونِي وَهُمْ لَكُمْ عَدُوٌّ بِئْسَ لِلظَّالِمِينَ بَدَلاً{50}
50-Kuma a lõkacin da Muka ce wa malãiku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada fãce Iblĩsa, yã kasance daga aljannu sai ya yi fãsikanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kunã rikon sa, shi da zũriyarsa, su zama majibinta kuna bariNa?, alhãli kuwa su makiya ne a gare ku? Tir da wannan musanya ga azzãlumai.
Kissar sujadar mala'iku ga Adam (a) da kuma yadda shaitan ya bijeirewa umurnin Allah ya zo a cikin waurare da dama a cikin alkur'ani mai girma. Amma a ko wani wuri aka zo da labarin akwai wani darasi da ake son fitarwa a cikinsa.
Wannan ayar tana bayyana cewa, ku mutane yayan annabi Adam (a) kada ku zaci cewa batun shaitan da bijirewarsa ga umurnin Allah an yi an gama. A'a yakamata ku sani cewa da farko shi ba mala'ika bane. Shi Aljanni ne kuma yana haihuwa. Sannan da shi da zuriyyarsa duk makiyanku ne. A yanzun zaku rikeshi da zurriyarsa a matsayin masoya mai makon Allah ma daukaki. Amma kuwa azzaluman da suka yi haka daga cikinku sun yi mummunan musanya.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Mutum wanda Allah ya fitita shi a kan mala'iku. Shi ne wanda Allah ya umurci mala'iku suyi masa sujada, me yasa zai yi biyayya ga shaitan wanda ya ki ya girmama shi.?
2. Don sabawa Allah na yi wa Adam (a) sujada na girmamawa da ya yi. Allah ya kori shaitan daga rahamarsa. Don haka wadanda suka ki yin sujada ga Allah mahalicci ya ya zai yi da su ranar kiyama.?
Yanzun kuma mu saurarin karatun aya ta 51 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
مَا أَشْهَدتُّهُمْ خَلْقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَلَا خَلْقَ أَنفُسِهِمْ وَمَا كُنتُ مُتَّخِذَ الْمُضِلِّينَ عَضُداً{51}
51-Ban shaida musu halittar sammai da kasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rãyukansu ba kuma ban kasance mai rikon mãsu batar da wasu su zama mataimaka ba.
A ci gaba kan ayar da ta gabata. Wannan ayar tana bayyana cewa shaitan da masu taimaka masa basa da wata masaniya dangane da halittun sama da kasa. Suma masu rauni ne kamar ku. Don haka me yasa kuke neman jingina da su? Amma mala'iku su ne Allah ya dorawa nauyin kula da halittu da dama. Daga cikinsu hark u mutane.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Ba wanda ya cancanci ya jibanci lamuran halittu in banda Ubangiji wanda ya haliccesu.
2. Wadanda suke kan tafarkin Allah basa basa neman taimako a wajen wanin Allah.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 52 da kuma 53 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَيَوْمَ يَقُولُ نَادُوا شُرَكَائِيَ الَّذِينَ زَعَمْتُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا لَهُمْ وَجَعَلْنَا بَيْنَهُم مَّوْبِقاً{52} وَرَأَى الْمُجْرِمُونَ النَّارَ فَظَنُّوا أَنَّهُم مُّوَاقِعُوهَا وَلَمْ يَجِدُوا عَنْهَا مَصْرِفاً{53}
52-Kuma (ku tuna) da rãnar da Allah zai cẽ, "Ku kirãyi abõkan tarayyãTa, wadanda kuka riya." Sai su kirãye su, bã zã su amsa masu ba, kuma Mu sanya Mahalaka a tsakãninsu,
53-Kuma mãsu laifi zasu ga wutã, su tabbata lalle ne, sũ mãsu, auka mata ne, ba su sãmi majũya ba daga gare ta.
A ci gaba da bayyana halin masu bautar shaitan a duniya, wadan nan ayoyi biyu suna bayyana halin da wadanda suka riki shaitan da masoyansa abin bi a duniya zasu shiga.
Manya manyan shuwagabannin da kuma masu iko da kudi da suke bi a duniya baz zasu tsinanawa kansu kome ba ballanta na su taimakwa wani. Don haka ko da sun nemi taimakonsu babu wanda zai masa masu dag cikinsu.
A ranar kiyama ba wanda yake iya tsamar da mutane daga halin da zasu shiga sais hi Allah. Sannan wuta mai zafi yana ne makomar masu sabon Allah ta'ala a duniya.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Idan mun kira Allah ko a duniya ko a Lahira zamu sami amsa ga bukatummu. Amma idan mun kira waninsa, mai yuwa mu sami amsa daga wajensa a rayuwar duniya amma a lahira babu amsa da zamu samu daga wajensu.
2. Jibantan wanin Allah shi ne mafarar shirka. Mutane masu hankala basa amincewa su fada cikin tarkin shirka ga Allah madaukakin sarki.
Masu sauraro a nan zamu da sa a ya a cikin shirimmu nay au sai kuma wani lokaci idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 54-56 (Kashi Na 509) ===
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa sikin shirimmu na hannunka maisanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu kamar yadda muka saba.
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 54 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِي هَذَا الْقُرْآنِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٍ وَكَانَ الْإِنسَانُ أَكْثَرَ شَيْءٍ جَدَلاً{54}
54-Kuma lalle ne, hakika, Mun buga dukkan misalai ga mutum a cikin wannan Alkur'ãni, amma mutum yã kasance mai yawan jidãli ne cikin mafi yawan abubuwa.
A ci gaba kan shirye shiryemmu da suka gabata da kuma don bada sakamakon kan abinda ayoyin da suka gabata suka bayyana na kafircin al-ummun da suka gabata ga ayoyin Allah. Wannan ayar tana bayyana cewa Allah ya kawo misalai da dama a cikin alkur'ani mai girma. Masu dadi da marasa dadi ga mutum don ya dauki misali daga garesu. Amma abin bakin ciki shi ne wasu mutanen basa daukan darasi cikin misalan. Banda wannan sukan yi kokarin jayayya da gaskiya. Don samarwa kansu nutsuwa da kuma kwanciyar hankali. Wannan ba za su taba samu ba.
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Alkur'ani mai girma ya bada misalai da dama na al-ummu da suka gabata da kuma wasu daddaiku don shiryatar da dan adam zuwa kan hanyar gaskiya.
2. Idan mutum bai da ruhin karban gaskiya duk misalign da aka bashi sai ya yi jayayya da shi. Karin wasu misalan sai dai su kara masa yi jayayya ne kawai.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 55 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَمَا مَنَعَ النَّاسَ أَن يُؤْمِنُوا إِذْ جَاءهُمُ الْهُدَى وَيَسْتَغْفِرُوا رَبَّهُمْ إِلَّا أَن تَأْتِيَهُمْ سُنَّةُ الْأَوَّلِينَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ الْعَذَابُ قُبُلاً{55}
55-Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, sai tafarkin mutanen farko ya zo musu kõ kuma azãba nau'i-nau'i sun zo masu.
Wannan ayar ta bayyana cewa mutane da dama suna fahintar gaskiya amma basa amincewa da ita. kuma ta kara da cewa ba abinda zai gasu ga amincewa da gaskiya sai har idan abinda ya faru da al-ummun da suka gabata na azaba ta zo masu.
Sai dai a bayyane yake cewa a duk lokacinda azabar uabangiji ta zowa mutane to imaninsu a lokacin ba zai yi wani amfani ba.
Wannan ayar tana dauke da bushara guda kuma tana dauke da gargadi guda. Bushara ita ce, idan kun tuba kun bi tafarkin Allah zai karbi tuban ku. Gargadi kuma shi ne cewa idan har kun yi taurin kai to ku sani cewa makomarku irin ta wadanda suka gabace ku ne.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Tare da aiko da annabawa da kuma littafai tattare da su ubangiji ya tabbatar da hujja kan mutane.
2. Tuba daga zunubai da kuma komawa kan tafarkin Allah yana dakatar da azabar Allah kan mutane.
3. Yin gargadi da kafa hujjoji ga kafirai wani lokacin bayan amfani. Wani lokacin azabar ubangiji ne kasai yake tilastawa mutane yarda da gaskiya.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 56 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَمَا نُرْسِلُ الْمُرْسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَيُجَادِلُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِالْبَاطِلِ لِيُدْحِضُوا بِهِ الْحَقَّ وَاتَّخَذُوا آيَاتِي وَمَا أُنذِرُوا هُزُواً{56}
56-Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargadi, wadanda suka kãfirta sunã jayayya da karya dõmin su bãta gaskiya da ita, kuma suna rikon ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargadi da shi abin izgili.
A ci gaba da bayani kan gwagwarmayan da annabawa suke yi da masu fada da gaskiya. Wannan ayar tana bayyanawa manzon Allah (s) cewa kada da matsawa kanka dangane da rashin amincewar mutanensa da gaskiyan da ka zo da ita.
Ai muna aiko da manzanni ne don su yi bushara da kuma gargadi ga mutane. Imani da rashin imanin mutanen ba zai shafesu ba. Mutane suna da 'yencin yin imani ko rashin yi.
Amma mai makon su yi imani suna yin matukar kokarinsu na karyata gaskiya. Daya daga cikin hanyoyin fada da ita gaskiya shi ne wulakanta ayoyin Allah da kuma izgili da su.
Sukan karyata iyayin da suke bayyana tashin kiyama da kuma samuwar wutan jahanma.Suna fada cewa " wa ya je ya ga lahira ya dawo ya fada cewa gaskiya ce.".
Muna iya daukan darussa a cikin wannan ayar kamar haka.
1. Aikin annabawa shi ne shiryatarwa zuwa tafarkin gaskiya. Basa tilastawa mutane karban gaskiya.
2. kafirai suna fada da gaskiya ne ta jayayya da ita da kuma isgili.
3. Mu yi hankali kada mu wulakanta ayyoyin ubangiji a maganganummu. Don yin haka alamu na na kafirci.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu wassalamu alaikum.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 57-61 (Kashi Na 510) ===
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa sikin shirimmu na hannunka maisanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu kamar yadda muka saba.
Bara mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 57 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ فَأَعْرَضَ عَنْهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ إِنَّا جَعَلْنَا عَلَى قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْراً وَإِن تَدْعُهُمْ إِلَى الْهُدَى فَلَن يَهْتَدُوا إِذاً أَبَداً{57}
57-Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar da shi game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, har abada.
A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana cewa aikin annabawa shi ne shiryatar da mutane zuwa ga shiriya. Amma basa tilastawa mutane imani da abinda suka zo da shi.
Don da dama daga cikin mutane suna kin bin gaskiya a lokacinda ta zo masu. Banda haka wasu kamma sukan kara zurafafawa zuwa ga cutar da annabawan da kuma mabiyansu.
Suna fito na fito da gaskiya suna son ganin bayansa. Suna nan kamar wadanda aka toshe zukatansu. Idanunsu basa gani kunnuwansu basa jin gaskiya. Wadanda suka zama haka dama, da wuya su kai ga shiriya. Gaskiyan lamarin ma basa son gaskiyan.
Akwai bambanci tsakanin wanda ya yi barci mai zufi da kuma wanda yake gyengyedi. Duk kiran da zaka yiwa wanda yake barci ba zai tashi daga barcinsa ba, amma mai gyengyedi kana iya farkad da shi da kira daya zuwa biyu.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka
1. Gafala daga sanin gaskiya da kuma mummunan ayyukan sukan kange mutum daga karban gaskiya idan ta zo masa.
2. Kange wasu mutane daga karban gaskiya, na daga cikin sakayyan da Allah yakewa wadanda suka gafala daga ayoyin Allah.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 58 da kuma 59 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَرَبُّكَ الْغَفُورُ ذُو الرَّحْمَةِ لَوْ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُوا لَعَجَّلَ لَهُمُ الْعَذَابَ بَل لَّهُم مَّوْعِدٌ لَّن يَجِدُوا مِن دُونِهِ مَوْئِلاً{58} وَتِلْكَ الْقُرَى أَهْلَكْنَاهُمْ لَمَّا ظَلَمُوا وَجَعَلْنَا لِمَهْلِكِهِم مَّوْعِداً{59}
58-Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka aikata, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin da aka kawalta masu, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.
59-Kuma wadancan alkaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, Muka sanya ayyanannen lõkacin, ga halakar su.
A ci gaba daga kan ayar da ta gabata. Wadan nan ayoyi biyu sun cewa sakamakon ubangiji ga kafirai da kuma wadanda suka saba maSa a nan duniya yana da ka'ida. Ka'idar kuwa ita ce rahamar Allah ta rinjayi fushinsa, da yana gaggauta azabtar da kafirai ko wadanda suke saba masa da ya halaka tuni. Amma yaba basu lokaci don su tuba su dawo kan tafarkin gaskiya, sai dai idan basu yi hakan ba, to ya sanya wa ko wannen lokacin kama shi. Lokaci wanda ba za su tsallaka shi ba. A lokacin zai kamasu tare da adalcinsa, bayan ya tabbatar masu da hujjoji kuma ya basu damar komawa ga gaskiya.
Muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi biyu kamar haka.
1. A tsarin da ubangiji ya tsarawa kansa ta yadda zai fuskanci masu saba masa shi ne tausaya masu da kuma basu damar tuba. Sai dai idan sun yasar da damar da ya basu.
2. Masu sabon Ubangiji kada su rudu da daurin tatalan da Ubangiji ya yi masu. Don a lokacin da wa'adin ubangiji ya isa to kuwa basa da mafita.
3. Yaduwar fasadi a bayan kasa shi ne yake jawo lalacewar ci gaba a cikin ko wace alumma.
4. Kada masu samu su dabe kauna daga samun rahamar Ubangiji da gafararsa, kamar yadda kuma kada su rudu da jinkirin da ubangiji yake masu a lokacinda suke saba masa.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 60 da kuma 61 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِفَتَاهُ لَا أَبْرَحُ حَتَّى أَبْلُغَ مَجْمَعَ الْبَحْرَيْنِ أَوْ أَمْضِيَ حُقُباً{60} فَلَمَّا بَلَغَا مَجْمَعَ بَيْنِهِمَا نَسِيَا حُوتَهُمَا فَاتَّخَذَ سَبِيلَهُ فِي الْبَحْرِ سَرَباً{61}
60-Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahadar koguna biyu, kõ in shũde da tafiya shekara da shẽkaru."
61-To, a lõkacin da suka isa mahadar tsakãninsu, sai suka manta da kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin kogi kamar bĩga.
Tare da wadannan ayoyi guda biyu, muke fara shiga kisser annabi Musa da kuma Khidir(a). Akwai darussa masu muhimmanci da zamu koyi cikin kisser wadannan bayin Allah biyu.
Kamar yadda yazo cikin hadisi, Ubangiji ya yi alhami ga annabi Musa (a) cewa a doron kasa akwai wani bawa na wanda ya daraka ilmi. Da haka annabi Musa (a) ya yi anniyar haduwa da wannan bawan Allah don ya sami karuwa da ilmin da Allah ya yi masa.
Ubangiji ya bayyana masa inda zai hadu da wannan bawan nasa. Ya ce masa zai same shi a wani yanki mai mahadar koguna. Kuma ya sami kifi ya tafi da shi. A duk lokacinda ya rasa kifin nasa to nan ne mahadarsu da wannan bawan nasa.
Don haka annabi Musa (a) tare da abokin tafiyarsa Yusha'u. sun kama hanyar neman Halluru tare da kifi a wajensu kamar yadda aka umurcesu.
A kan hanyarsu sai suka je wani wuri kusa da kogi, sai annabi musa (a) ya mike kan wani dutse yana barci, amma abokin tafiyarsa bai yi barci ba. Yana ganin kifin nasu ya yi tsalle ya fada cikin ruwa ya tafi. Amma tunda annabi Musa (a) yana barci bai tashe shi ba.
Sai kuma bayan tashinsa daga barci ya manta ya fada masa ga abinda ya faru da kifimmu, har said a suka kama hanya. Sai annabi Musa (a) ya ce masa ka kawo abincimmu da mu ci. Anan ne ya tuna sai ya fadawa annabi musa (a) abinda ya faru da kifinsu. Sauran labarin yana cikin ayoyi na gaba.
Muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi biyu kamar haka.
1. Annabawan Allah ma suna neman karin sani a wajen Allah kuma sukan sha wahala wajen nemansa.
2. Mai neman ilmi dole ne ya je nemansa. Ba wai ya jira ilmi ya zo ya same shi ba.
Masu sauraro anan zamu dasa aya cikin shirimmu na yau sai kuma wani shirin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 62-66 (Kashi Na 511) ===
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa sikin shirimmu na hannunka maisanda shiri wanda yake yin dubi a cikin wasu ayoyin alkur'ani mai girma don su zama fitila a cikin rayuwarmu da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu kamar yadda muka saba.
To bari mu fara shirimmu na yau tare da sauraron karatun aya ta 62 da kuma aya ta 63 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
فَلَمَّا جَاوَزَا قَالَ لِفَتَاهُ آتِنَا غَدَاءنَا لَقَدْ لَقِينَا مِن سَفَرِنَا هَذَا نَصَباً{62} قَالَ أَرَأَيْتَ إِذْ أَوَيْنَا إِلَى الصَّخْرَةِ فَإِنِّي نَسِيتُ الْحُوتَ وَمَا أَنسَانِيهُ إِلَّا الشَّيْطَانُ أَنْ أَذْكُرَهُ وَاتَّخَذَ سَبِيلَهُ فِي الْبَحْرِ عَجَباً{63}
62-To, a lõkacin da suka wuce ya ce wa yãronsa, "Ka kãwo mana kãlãcinmu. Lalle ne hakĩka mun hadu da wahala a cikin wannan tafiyar tamu."
63- (Yãron) ya ce: "Kã gani! A lõkacin da muka sauka kan falalen nan, lalle nĩ, na manta an fada maka dangane da kĩfin nan, kuma bãbu abin da yamantar da nĩ shi, fãce Shaidan, dõmin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin kogi, yana mãmãki!"
A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda annabi Musa (a) tare da abokin tafiyarsa suka kama hanyar neman halluru dauke da kifi. A lokacinda suka kaiga wata falale kusa da kogi suna hutu annabi musa (a) yana barci kifin nasu ya yi tsalle ya fada cikin ruwa, amma abokin tafiyar nasa ya manta ya fada masa bayan ya tashi daga barci har sai daga baya ya tuna.
Wadannan ayoyi sun dora da cewa, a lokacin da suka kama hanyarsu bayan hutawa, sai annabi musa (a) ya bukaci abokin tafiyarsa Yusha'u da ya kawo masu kifin nan su dafa su ci. A nan ne ya tuna da abinda ya faru da kifin sai ya fadawa annabi musa (a).
A cikin wannan ayar annabi Musa (a) ya bayyana tafiyarsu wannan a matsayin tafiya wanda suka sha wahala a cikinsa.
Annabi musa (a) ya sha yin tafiye tafiye masu tsawo. Tafiyarsa ta farko ita ce wacce ya tsere daga kasar Masar don kada ya fada hannun Fir'auna ya je Madyana inda ya hadu da annabi Shu'aib (a) sannan ya auri diyarsa. Ta biyu kuma ita ce ta dawowa kasar Masar tare da iyalansa inda ya zama annabin Allah manzo. Sai kuma tafiya ta ukku wacce ya yi ya don karban umurnin ubangijinsa a cikin littafin Attaura a dutsen Sina.
Wannnan tafiyar ta neman ilmi ita ce ta hudu, amma ya sifanta tata a matsayin mai wahalarwa.
Muna iya daukan darussa daga cikin wadannan ayoyi biyu kamar haka.
1. Tafirkin neman ilmi bata da sauki. Har annabawan Allah suna shan wahala kafin su kai ga samun ilmin sanin ubangiji.
2. Shaidanu suna kange mutane kan hanyar sanin gaskiya da kuma neman sanin Allah ta hanyoyi daban daban.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 64 da kuma ta 65 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
قَالَ ذَلِكَ مَا كُنَّا نَبْغِ فَارْتَدَّا عَلَى آثَارِهِمَا قَصَصاً{64} فَوَجَدَا عَبْداً مِّنْ عِبَادِنَا آتَيْنَاهُ رَحْمَةً مِنْ عِندِنَا وَعَلَّمْنَاهُ مِن لَّدُنَّا عِلْماً{65}
64-Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance munã nema." Sai suka kõma a kan gurãbunsu, sunã bĩbiya.
65-Sai suka sãmi wani bãwa daga bãyinMu, Mun bã shi wata rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gureMu.
Da jin labarin kifi nasu sai annabi musa (a) ya cewa a bokin tafiyarsa ai abinda muke nema kenan. Daga nan si suka koma inda suka huta, sai kuma suka hada da Halluru wanda Allah ya bashi ilmi wanda annabi musa (a) baisada su ba.
Duk da cewa malamai sun sami sabani kan cewa Halluru annabi ne ko dai wani bawan Allah ne. Sai dai abinda ya fi dacewa shi ne malam annabin Allah shi ma ya kasance annabi ne don maganarsa ta zama hujja ga shi annabi musa (a). Tare da wasu dalilai, kamar kasancewa Allah yana ambaton annabawasa da sunan "bayi na sau da dama a cikin alkur'ani mai girma. Da kuma kamar yadda ya zo cikin wannan ayar cewa ilminsa daga Allah ne. Wanda ilminsa daga Allah ne yakamata a ce shi annabi ne. da dai wasu dalilai da dama.
Muna iya daukan darussa daga cikin wadan nan ayoyi kamar haka.
1. Wasu ilmoma basa samuwa ta hanyar jarrabawa da kuma amfani da tunani. Dole ne sai da an sami taimako daga wajen Allah. Kamar dai ilmin annabawa. Da sauran ma'asumai.
2. Ilmin addinin yana samuwa ne a wajen bayin Allah ba wajen duk wanda yake riya ilmi ba.
3. Allah ta'ala yana da wasu bayinsa masu ilmi, amma a boye. Mai so dole ne ya je ya nemo inda suke don ya amfana da ilminsu.
Yanzun kuma mu saurari karatun aya ta 66 daga cikin suratul Kahfi kamar haka.
قَالَ لَهُ مُوسَى هَلْ أَتَّبِعُكَ عَلَى أَن تُعَلِّمَنِ مِمَّا عُلِّمْتَ رُشْداً{66}
66-Mũsã ya ce masa, "Ko in bĩ ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?"
Bayan wahalar tafiya daga karshe annabi Musa (a) ya sami haduwa da Halluri. Sannan ya bayyana masa dalilin zuwansa, wato na neman ilmi wanda zai kaishi ga kamala. Kuma ya zo masa a matsayin dalibi mai ladabi ga malaminsa. Ya roke shi da ya bashi damar binsa don ya amfanu da ilmin da Allah ta'ala ya yi masa. Ladabi ga lamami wajibi ne ko da kuwa dalibin annabin Allah ne.
Annabi musa (a) annabi ne manzo daga cikin manya manyan manzannin Allah mai wanda aka saukarwa littafi. Amma ya kaskantar da kansa a gaban wani bawan Allah wanda zai shiryatar da shi zuwa ga karin sanin Allah wanda ya boyu a gareshi.
Muna iya daukan darussa daga cikin wannan ayar kamar haka.
1. Matsayi da kuma yawan ilmin annabawa sun bambanta. Ilminsu na da iyaka kuma yana karuwa daga lokaci zuwa lokaci.
2. Shiriya da kamala basa samuwa sai da ilmi daga wadanda suka san shi.
3. Dole ne dalibi ya zama mai tawaliu da ladabi ga malaminsa don samun ilmi mai amfani.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wani lokacin idan Allah ya kaimu a huta lafiya wassalamu alaikum warahmatullahi …….
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 67-73 (Kashi Na 512) ===
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.
Za mu fara da a saurarren ayoyi na 67 da 68 a cikin suratul Kahfi kamar haka:
قَالَ إِنَّكَ لَن تَسْتَطِيعَ مَعِيَ صَبْراً{67} وَكَيْفَ تَصْبِرُ عَلَى مَا لَمْ تُحِطْ بِهِ خُبْراً{68}
67- Ya ce: "Lalle ne kai bã zã ka iya yin hakuri tãre da nĩ, ba."
68- "Kuma yãya zã ka yi hakuri a kan abin da ba ka kẽwayeda shi ba ga jarrabãwa?"
A cikin shirin da ya gabata mun bayyana cewa; Annabi Musa (AS) domin karin ilimi da sanin abubuwan gaibi ya bukaci saduwa da Khidr da Allah ya bawa dinbin ilimi da sani don haka ya shiga nemansa har zuwa lokacin da ya sabdu da shi kamar yadda wannan ayar ke cewa: da farko sai Khidr ya cewa annabi Musa (AS) duk abin da zai aikata yana tattare da daurin kai da ban mamaki dole sai ka yi hakuri idan ka yi hakuru zan fahimtar da kai abubuwan da suka kumsa na sirri da hikimar da ke tattare da su.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:
Na farko:Malami da almajirinsa dole su kasance suna da mahanga guda kan shinfida guda ta fahimtar koyarwa da daukan darasi wani lokaci ana fuskantar matsala tsakani malami da dalibinsa sai an hada da hakuri da juriya kamar yadda za mu gani hatta Annabi Musa (AS) bai jurewa abubuwan da Khidr ke ya aikata ba.
Na biyu:Wani lokaci rashin sani ne ke haddasa jayayya da kasa cimma nasara kan wani hadafi da burin da ake son cimmawa.
Sai a saurari karatun ayoyi na 69 da 70 a cikin suratul kahfi kamar:
قَالَ سَتَجِدُنِي إِن شَاء اللَّهُ صَابِراً وَلَا أَعْصِي لَكَ أَمْراً{69} قَالَ فَإِنِ اتَّبَعْتَنِي فَلَا تَسْأَلْنِي عَن شَيْءٍ حَتَّى أُحْدِثَ لَكَ مِنْهُ ذِكْراً{70}
69- Ya ce: "Za ka sãme ni, in Allah Yã so mai hakuri kuma bã zan sãba maka ba ga wani umurni."
70 - Ya ce: "To idan ka bĩ ni to kada ka tambaye ni daga kõme sai na lãbarta maka ambato daga gare shi."
Ko ba komi Annabi Musa (AS) ya bayyanawa Annabi Hidre ashirye yake ya bi shi ya amince ba zai yi tambayar sanin dalilin da ya aika wani aiki kawai zai rika kallo da saurara kuma ya aikata duk abin da Annabi Hidre ya ce masa;
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:
Na farko: idan za mu aikata wani aiki da yin alkawali kar mu mance da cewa In Allah ya yarda za mu aikata ko za mu cika Alkawali.
Na biyu:mu rika biyayya ga waliyan Allah kuma ko da ba mu fahimci hikima a kan wani abu da suka aikata kar mu nuna adawa da su.
Sai a saurari karatun ayoyi na 71 da 72 da 73 a cikin suratul kahfi kamar:
فَانطَلَقَا حَتَّى إِذَا رَكِبَا فِي السَّفِينَةِ خَرَقَهَا قَالَ أَخَرَقْتَهَا لِتُغْرِقَ أَهْلَهَا لَقَدْ جِئْتَ شَيْئاً إِمْراً{71} قَالَ أَلَمْ أَقُلْ إِنَّكَ لَن تَسْتَطِيعَ مَعِيَ صَبْراً{72} قَالَ لَا تُؤَاخِذْنِي بِمَا نَسِيتُ وَلَا تُرْهِقْنِي مِنْ أَمْرِي عُسْراً{73}
71- Sai suka tafi har a lõkacin da suka hau a cikin jirgi, ya hũje shi, ya ce, "Kã hũje shi dõmin ya nutsar da mutãnensa? Lalle ne, hakĩka,kã zo da wani babban abu!"
72 - Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, bã za ka iya yin hakuri tãre da ni ba?"
73 - Ya ce: "Kada ka kãma ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarĩna."
Kamar yadda muka fahimta a yoyin da suka gabata ilimin da Annabi Musa (AS) ke son koya a gurin Annabi Hidre (AS) ba ilimi ban a na Magana da nazari wani nauyin ilimi a aikace day a dace da sharadinsa da yanayinsa. Haka ne Annabi Musa (AS) ba shi da masaniya da sanin sirrin abubuwan da Annabi Hidre (AS) ke aikatawa ba kuma ba zai iya yin shiru da gum kan abubuwan da yake aikatawa na ban mamaki da al'ajabi duk da cewa ya yi masa alkawalin ba zai yi adawa da abin da yake yi ba ko yin tambaya.
Abu na farko day a faru shi ne da shigarsu jirgin ruwa bad a wata wata sai Annabi Hidr (AS) bad a wani dalili na zahiri ya fara aibata wannan jirgi da jawowa masu jirgin hasara kuma zai iya nutsar da jirgin da hallakar da mutanan da ke cikinsa.A zahiri wannan aiki ya sabawa shari'a da kuma hankali kuma ko ba komi rayukan wadanda ke cikin jirgin na cikin hadari.Annabi musa (AS) bai yi zaton mutum zai aikata haka balantana malaminsa da Allah ya kallafa masa daukan karatu a gurinsa yana aika aikin ban mamaki don haka ya manta alkawalin da ya yi masa ya yi kokarin hana shi wannan aiki da ya ke ganinsa a matsayin mummunan aiki. Amma sai Annabi Hidr (AS) ya amsa masa da cewa ba ka yi alkawlin yin gum da bakin ba kan duk wani aiki da na ke aikatawa ba.sai annabi Musa (AS) ya yi nadama ya kuma bukaci Khidr da ya manta abin da ya faru.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:
Na farko:Idan mun yi imani ilimi da hikimar waliyan Allah kar mu yi mamakin wani abu da suke aikatawa ko yin adawa ko da ba mu san dalilin yin hakan ba har sai sun bayyana mana dalilin yin hakan.
Na biyu:Yin shiru kan abubuwan da ba su dace ba bai kamata ba don adawar lalata jirgin ruwa da Annabi Musa (AS) ya yi ya dace sai dai kawai ya sabawa alkawalin da ya yi na ba zai cewa Annabi Khidr kan wani aiki da zai aikata ba.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 74-78 (Kashi Na 513) ===
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.
Za mu fara shirin na hannunka mai sanda a yau da sauraren aya ta 74 da 75 da kuma 76 a cikin suratul Kahfi:
فَانطَلَقَا حَتَّى إِذَا لَقِيَا غُلَاماً فَقَتَلَهُ قَالَ أَقَتَلْتَ نَفْساً زَكِيَّةً بِغَيْرِ نَفْسٍ لَّقَدْ جِئْتَ شَيْئاً نُّكْراً{74} قَالَ أَلَمْ أَقُل لَّكَ إِنَّكَ لَن تَسْتَطِيعَ مَعِي صَبْراً{75} قَالَ إِن سَأَلْتُكَ عَن شَيْءٍ بَعْدَهَا فَلَا تُصَاحِبْنِي قَدْ بَلَغْتَ مِن لَّدُنِّي عُذْراً{76}
74- Sai suka tafi, har suka hadu da wani yãro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe kã kashe rai tsarkakakke, bã da wani rai ba? Lalle ne hakĩka ka zo da wani abu na kyãma."
75- Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai bã zã ka iya yin hakuri tãre da nĩ ba?"
76- Ya ce: "Idan na tambaye ka daga wani abu a bãyanta, to, kada ka abũce ni. Lalle ne, kã isa ga iyakar uzuri daga gare ni."
A cikin shirin da ya gabata mun kawo labarin abin day a faru tsakanin Annabi Musa Da Hidr (AS) da yadda suka hau jirgin ruwa da yadda ya lalata jirgin da suke ciki da kuma yadda Annabi Musa yace masa me yasa yake yin haka To itam wannan ayar na ci gaba da cewa; bayan sun sabka daga jirgin ruwan sun isa wani yanki babu wani dali sai Annabi Hidr (AS) ya kashe wani karamin yaro babu wata wata sai Annabi Musa (AS0 ya nuna adawarsa da wannan aiki nasa kuma a dabi'ance ya yi gaskiya musamman ma'aikin allah ba zai iya jurewa wannan aiki na kisan kai kamar yadda ya zo a cikin ruwaya ma'aikin Allah Muhammadu dan abdullahi (SWA) na cewa; idan da Musa ya yi hakuri da ya ga abubuwan mamaki masu yawa daga Hidre.
Duk da cewa Annabi Musa (AS) ya yi masa alkawali yin shiru ba zai ce komi ba amma kan aikin da ya aikata a zahiri ya sabawa shariya bai dace ba yin shiru dole a yi kokarin hana mukari.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:
Na farko:kiyaye hukumce-hukumce na shari'a shi ne yafi muhimmanci da kiyaye kyawawan dabi'u da na zamantakewa kuma babu wani alkawali da yarjejeniya da za ta hana isar da sakon Allah.
Na biyu:Duk wani aiki da ya sabawa zahirin rayuwa da hankali dole ne a kalubalance shi sai an gabatar da dalili gamsarshe.
Na uku: Waliyan allah ma ba daidai suke bat a fuskar ilimi da fahimta kuma kowa da karfin ilimi da fahimta da Allah ya bashi sabanin dan uwansa.
Sai a saurari karatun aya ta 77 a cikin suratul kahfi kamar:
فَانطَلَقَا حَتَّى إِذَا أَتَيَا أَهْلَ قَرْيَةٍ اسْتَطْعَمَا أَهْلَهَا فَأَبَوْا أَن يُضَيِّفُوهُمَا فَوَجَدَا فِيهَا جِدَاراً يُرِيدُ أَنْ يَنقَضَّ فَأَقَامَهُ قَالَ لَوْ شِئْتَ لَاتَّخَذْتَ عَلَيْهِ أَجْراً{77}
77 - Sai suka tafi, har a lõkacin da suka je wa mutãnen wata alkarya, suka nẽmi mutãnenta da su bã su abinci, sai suka ki su yi musu liyãfa. Sai suka sãmi wani bango a cikinta yanã nufin ya karye, sai (Halliru) ya tãyar da shi mĩke. (Mũsã) ya ce: "Dã kã so, lalle ne dã kã karbi ijãra a kansa."
Bayan lalata jirgin ruwan da suke ciki da kasha karamin yaro da dukansu biyu a zahiri sun sabawa hankali kuma abin kama ne a gurin Annabi Musa (AS) sai suka isa wani kauye sai suka ga wata Katanga tana kokarin faduwa gashi dukansu biyu suna cikin gajiya da yunwa amma mutanan kauyan nan babu wani day a bas u ko da abin sha. A cikin wannan hali da yanayi da suke cikin sai Annabi Hidr (AS) ya shiga gyra wannan gatangar bayan Annabi Musa (AS) bai taimaka masa ba sai ma ya ke sukan wannan aiki nasa me ya sa kake yi wa mutanan da ko ruwa balantana abinci ba su ba mu ba wannan aiki na alheri kyauta ko ba komi ai sai ka amshi wani ladan kudi a gurinsu ko ma sayi abincin da za mu ci .
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:
Na farko:Kar mummunan aikin wasu ya sa mu kasa aikata alheri da kyautatawa domin ba a maida lala da lala .Idan Annabi Hidre (AS) bai gyara wannan Katanga ba bai yi laifi ba domin ba bu nauyin yin haka a kansa ba kuma bai aikata liafi ba amma ya aikata hakan ne a matakin taimako da aiakta alheriri.
Na biyu:Idan muka ga akwai bukatar aikata alheri kar mu jira sai an bukace yi kuma kar mu yi la'akari da sukan wasu ko kulawa da abin da za su ce na suka.
Na uku: Waliyan Allah ba su aiki ba ne don kar bar kudi a gurin mutane ko da a halin yunwa da kishirwa suna taimakawa mabukata.
Sai a saurari karatun aya ta 78 a cikin suratul kahfi kamar:
قَالَ هَذَا فِرَاقُ بَيْنِي وَبَيْنِكَ سَأُنَبِّئُكَ بِتَأْوِيلِ مَا لَمْ تَسْتَطِع عَّلَيْهِ صَبْراً{78}
78 - Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Zã ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin hakuri ba a kansa."
Annabi Musa (AS) ya yi alkwalin zai yi hakuri ba zai ce komi ba amma a dukan abubuwa uku da suka faru sai da ya nuna adawarsa kuma rashin shirunsa wani lamari ne na dabi'a bai kamata bay a yi shiru a bangare guda na nuni da cewa waliyan Allah akwai sabani a tsakaninsu ta fuskar ilimi da fahimta da hakuri.Annabi musa duk da cewa ya san Annabi Hidre (AS) Allah ne ya aiko shi domin ya ilmantar da shi abubuwa na gaibi amma ya kasa hakurin abubuwan da yake gani na al'ajabi saboda haka dole wannan tafiya a tsakaninsu ba za ta yuyuwa sai kowa ya kama hanyarsa.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda biyu akalla:
Na farko:Kar mu rika kollon abubuwa na zahiri kawai mu rika kokarin sanin abubuwa da hikimar da ke tattare da su ba kokawa ba.
Na biyu:Akwai yuyuwar waliyan Allah guida biyu su raba hanya kowa ya tafiyarsa da ci gaba da aikinsa na shiryar da jama'a babu wani laifi domin manufarsu daya ce isar da sakon Allah da shiryar da mutane.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 79-82 (Kashi Na 514) ===
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.
Za mu fara da a sauraren aya ta 79 a cikin suratul Kahfi kamar haka:
أَمَّا السَّفِينَةُ فَكَانَتْ لِمَسَاكِينَ يَعْمَلُونَ فِي الْبَحْرِ فَأَرَدتُّ أَنْ أَعِيبَهَا وَكَانَ وَرَاءهُم مَّلِكٌ يَأْخُذُ كُلَّ سَفِينَةٍ غَصْباً{79}
79-"Amma Jirgin, to, ya zama na wadansu matalauta ne sunã aiki a cikin tẽku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhãli kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yanã karbẽwar kõwane jirgi (lãfiyayye) da kwãce.
A shirin da ya gabata mun yi bayani ne kan abubuwa uku na ban mamaki da annabi hidr (AS) yayi shi kuwa Annabi Musa (AS) ya kasa hakuri da jurewa wadannan lamari inda ya nuna dawarsa kan abubuwan da ya aikata .Nan fa sai Annabi Hidre (AS) ya ce masa: to ba zan iya tafiya da kai ba don ka kasa hakuri dole mu raba hanya amma ba ri in bayyana maka hikimar da ke lullube a cikin ayyukan da na aikata.
Jirgin ruwan da muka shiga na wasu muskinai ne da suke aikin in wannan ya yi ya bawa wannan da kuma suke jigilar masu bulaguro kuma ni ina da masaniya a dayan bangare na ruwan akwai azzalumin sarki da ke amshe duk wani jirgin mai kyau da karfin zalunci don haka na aibata jirgin don kar ya amshe masu wannan jirgin da suke neman abinci da shi bayan sun wuce gurin wannan azzalumi daga baya sai su gyara wuraren da na lalata. Kai kana kollon zahirin aikin da na aikata ne amma ni ina kollon sakamakon abin da na aikata ne don hana amshe wa wadannan bayu Allah hakinsu .wani abu Annabi Hidre bai lalata jirginba ta inda zai kai ga nutsewarsu kawai ya aibata shi ne da zai hana azzalumin sarki ya kwace masu jirginsu kuma wannan aiki na sa yana matsayin hana mafi munin aikin da mummuna kuma hakan yayi daidai da hankali.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:
Na farko:Mutum mai hikima ba ya barin wani aikinsa do da kuwa dukan mutane za su nuna adawa da hakan.
Na biyu: waliyan Allah suna tausayawa nakasassu da mabukata kuma suna kokarin hana azzalumi ya cuce su.
Na uku:kiyaye mafi muhimmanci da muhimmi lazumi ne a ayyukanmu na yau da kullum kuma hana mafi muni da mai muni ya yi daidai da hankali.
Sai a saurari karatun aya ta 80 da 81 a cikin suratul kahfi kamar:
وَأَمَّا الْغُلَامُ فَكَانَ أَبَوَاهُ مُؤْمِنَيْنِ فَخَشِينَا أَن يُرْهِقَهُمَا طُغْيَاناً وَكُفْراً{80} فَأَرَدْنَا أَن يُبْدِلَهُمَا رَبُّهُمَا خَيْراً مِّنْهُ زَكَاةً وَأَقْرَبَ رُحْماً{81}
80-"Kuma amma yaron, to, uwãyensa sun kasance mũminai, to, sai muka ji tsõron ya kallafa musu kangara da kãfirci."
81 - "Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alhẽri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi."
Annabi Musa (AS) Allah ya umarce ce da ya yi aiki da ilimi da hikima ba ilimi na zahiri ba saboda haka kashe wannan yaro ya sabawa dokoki da shari'a saboda har yanzu wannan yaro bai aikata wani laifi ba da za a ganshi a matsayin kafiri kuma za a iya cewa Abin da Annabi Hidr (AS) ya yi na kashe wannan yaro hukumci ne kafin laifi amma idan muka yi la'akari da Allah shi ne mai kashewa da iko kan kowa da komi to yanada hakkin yin hakan karkashin hikimarsa. Don haka Allah ya umarci Annabi Hidre (AS) da ya aikata domin hana wannan matashi zama kafiri a nan gaba kuma Allah zai masanyawa uwayen yaron salihai da wani yaro salihi da zai samar da zuriyar saliha kamar yadda ruwaya ta nuna.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:
Na farko:Mutuwar yaron nan tafi zama alheri da ya girma ya zama kafiri da yada fasadi da banna a doran kasa.
Na biyu:Idan Allah ya amshi wani abu a gurin mumuni yana bashi wani abu da yafi haka alheria a gare shi don haka sai mu yi hakuri da tawakkali da lamarin Allah a kullum.
Na uku: Yayan ya kamata su kasance na gari daidai da uwayensu masu kyauna da soyayya da biyayya.
Sai a saurari karatun aya ta 82 a cikin suratul kahfi kamar:
وَأَمَّا الْجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَامَيْنِ يَتِيمَيْنِ فِي الْمَدِينَةِ وَكَانَ تَحْتَهُ كَنزٌ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَالِحاً فَأَرَادَ رَبُّكَ أَنْ يَبْلُغَا أَشُدَّهُمَا وَيَسْتَخْرِجَا كَنزَهُمَا رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ وَمَا فَعَلْتُهُ عَنْ أَمْرِي ذَلِكَ تَأْوِيلُ مَا لَمْ تَسْطِع عَّلَيْهِ صَبْراً{82}
82 -"Kuma amma bangon, to, yã kasance na wadansu yãra biyu ne, marãyu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tãsu a karkashinsa, kuma ubansu ya kasance sahĩhin mutum ne, dõmin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyãkar karfinsu, kuma sũ, su fitar da taskarsu, sabõda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnĩna. Wancan shĩ ne fassarar abin da ba ka iya yin hakuri ba a kansa."
A cikin ayar da ta gabata mun bayyana cewa: Annabi Hidr (AS) an umarce ce da ya kashe wannan yaro domin kiyaye imanin uwayensa to a cikin wannan ayar kuwa akasin wadda ta gabace ta ce domin a dalilin uwayen yaron salihai mumunai ne Allah ya tabbatar da lutifinsa kan yayansu inda ya umarci Annabi Hidre (AS) ya kare masu dukiyarsu da suka gada har sai sun girma kar a sace masu.Lamari mai muhimmanci a cikin wannan aya shi ne kalmar wa ma fa'altuhu an amri ma'ana Allah ne ya umurce ni da yin haka ba wai ya aikata hakan ba ne don radin kansa da dogaro da iliminsa. Kuma abin da ya aikata ya yi kama da aikin da Allah ya kallafawa mala'iku na tafiyar da rayuwa da kashewa karkashin kudura da iradar Allah .Kuma Annabi Hidr (AS) ya aikata haka ne domin kowa kamar annabi Musa (AS) mu sani dukan rayuka suna karkashin ikon Mahalicci ne yana zartar da abin da yaga dama.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:
Na farko:yiwa yayanmu tanadin dukiya ya dace kuma kare dukiyar marayu wajibi ne.
Na biyu:ayyukan masu kyau na uwaye na tasiri ga makomar yayansa kuma ko da ya rasu za su ga tasirin ayyukansa na alheri.
Na uku:abubuwa masu dadi ko daci a rayuwa kowane na kumshe da hikima ko da ba mu fahimta ba a zahiri don haka kar mu yi mamakin lamarin Allah idan ya zartar.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 83-88 (Kashi Na 515) ===
Jama'a masu saurare Assalamu alaikum barkarku da sake saduwa da mu a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda ,inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki ,tare da yin bayani gwargwadon iko kan abin da suke koyar da mu ,tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa da zamantakewa.Amma kafin mu shiga cikin shirin gadan gadan ga abin da aka yi mana tanadi a kan inji.
Sai a saurari karatun aya ta 83 da 84 da 85 a cikin suratul kahfi kamar:
وَيَسْأَلُونَكَ عَن ذِي الْقَرْنَيْنِ قُلْ سَأَتْلُو عَلَيْكُم مِّنْهُ ذِكْراً{83} إِنَّا مَكَّنَّا لَهُ فِي الْأَرْضِ وَآتَيْنَاهُ مِن كُلِّ شَيْءٍ سَبَباً{84} فَأَتْبَعَ سَبَباً{85}
83- Kuma suna tambayar ka daga zulkarnaini, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi."
84- Lalle ne Mũ Mun bã shi mulki a cikin kasa kuma Muka bã shi daga kõwane abu, hanya (zuwa ga murãdinsa).
85- Sai ya bi hanya.
A shirye-shiryenmu da suka gabata mun kawo labarin abubuwan da suka wakana da Ashabul kahfi da kuma wadanda suka wakana tsakanin Annabi Musa Da Hidre (AS) kuma yanzu kuma za mu dubu a cikin kimanin ayoyi sha biyar a cikin labarin Zulkarnain kamar haka: har ila yau kamar yadda muka bayyana a farkon wannan sura mushrikan makka bayan sun yi shawara da Yahudawan Madina sun kwada ma'aikin Allah kan abubuwa guda uku da ke da dangantaka da tarihi domin ganin irin amsar da zai bayar.Daga cikin tambayoyinsu akwai labarin abin da ya wakana da Zulkarnai saboda haka wadannan ayoyi da farko ke farawa da cewa: ya kai ma'aikin Allah suna tambayarka dangane da zulkarnain ka amsa masu da cewa: sai ku saurara da bude kunnuwanku ku ji dangane da shi.Shi Zulkarnain mutum ne da Allah ya ba shi wadata da ilimi domin ya amfana abubuwa na dabi'a da amfanuwa ta hanyoyi da dama kuma ya yi amfani da wannan dama da kudura da Allah ya ba shi wajan yin hidima ga al'umma. Kuma me ya sa ake kiransa da zulkarnain ,an kawo labarai masu yawa daga cikinsu akwai cewa yana daure kashin kansa gida biyu tamkar kaho wasu kuma na cewa abin nufi da karnai gabaci da yammaci saboda yana yawaita bulaguro a tsakanin yammaci da gabaci kuma yana da mulki a kansu saboda haka ake kiransa da Zulkarnain.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:
# Na farko:samara da ilimi da kere-kere ta hanyar amfani da dabi'a daya daga cikin ni'imomin da Allah ya ba wa wasu daga cikin bayunsa ne.
# Na biyu:Masaniya kan tarihin mutanan da suka gabata zai kara mana kwarewa da daukan darasi a rayuwa.
# Na uku: Tsarin da wannan duniya ke tafiya a kansa ,tsari ne na sababi da abin da ke haddasa shi kuma duk wani abu yana da sababi da dole a gano da saninsa.
Sai a saurari karatun aya ta 86 da 87 da 88 a cikin suratul kahfi kamar:
حَتَّى إِذَا بَلَغَ مَغْرِبَ الشَّمْسِ وَجَدَهَا تَغْرُبُ فِي عَيْنٍ حَمِئَةٍ وَوَجَدَ عِندَهَا قَوْماً قُلْنَا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِمَّا أَن تُعَذِّبَ وَإِمَّا أَن تَتَّخِذَ فِيهِمْ حُسْناً{86} قَالَ أَمَّا مَن ظَلَمَ فَسَوْفَ نُعَذِّبُهُ ثُمَّ يُرَدُّ إِلَى رَبِّهِ فَيُعَذِّبُهُ عَذَاباً نُّكْراً{87} وَأَمَّا مَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحاً فَلَهُ جَزَاء الْحُسْنَى وَسَنَقُولُ لَهُ مِنْ أَمْرِنَا يُسْراً{88}
86- Har a lõkacin da ya isa ga mafãdar rãnã, kuma ya sãme ta tanã bacẽwa a cikin wani ruwa mai bakar lãkã, kuma ya sãmi wadansu mutãne a wurinta. Muka ce: "Yã Zulkarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riki kyautatãwa a cikinsu."
87- Ya ce: "Amma wanda ya yi zãlunci, to zã mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azãba, azãba abar kyãma."
88-"Kuma amma wanda ya yi ĩmãni kuma ya aikata aikin kwarai to, zã mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau, kuma zã mu gaya masa sauki daga umurninmu."
Karkashin wannan ayar Zulkarnain a ci gaba da bulaguron da ya ke yi ya isa ga wani yankin a kusa da gabar ruwa daidai lokacin rana za ta fada ,mutanan da ke rayuwa a wannan yankin akwai masu aikin alheri akwai masu aikata banna.Shi Zulkarnain mutuman kirki ne kuma ma'aikin Allah Ne (AS) sai Allah ya Umarce shi da ya sakawa mutanan kirki daga cikinsu tun a wannan duniya da dandana jin dadin rayuwa a wannan duniya su kuma mabantawa ya dandana masu azaba a wannan duniya kan aikin da suka aikata. Duk da cewa azabtarwa wani lamari ne da ya kebanta da Allah da kuma guri na musamman wato lahira Amma Allah madaukakin sarki ya bawa Zulkarnain wannan dama karkashin ilimin gaibi da sanin ayyukan da kowa ya boye a cikin tunani da zukatansa saboda haka tun a wannan duniya ya san mutanan kirki da kuma mabantana kuma zai sakawa kowa daidai da aikinsa na alheri ko lalata kafin su tafi lahira.
A cikin wannan aya za mu iya daukan darasin abubuwa guda uku akalla:
Na farko:Idan yin bulaguro na neman alheri addini yana goyan bayan haka kamar yadda aka jaddada hakan a cikin ayoyin kur'ani.
Na biyu:Waliyan Allah ,Allah ya ba su wani zabi da falala da za su iya yin aiki da ita duk lokacin da suka ga dama.
Na uku:a koyarwa ta kur'ani kafirci da shirka zalunci ne ga ma'abucinsu saboda a wadannan ayoyi suna fuskantar imami.
Da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shirin na yau sai kuma shiri na gaba da yardar Allah kafin lokacin Ni Tidjani Malam Lawali Damagaram na na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 89-94 (Kashi Na 516) ===
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat kahfi, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun ayoyi na (89) zuwa (91) a cikin surat Kahfi
ثُمَّ أَتْبَعَ سَبَباً{89} حَتَّى إِذَا بَلَغَ مَطْلِعَ الشَّمْسِ وَجَدَهَا تَطْلُعُ عَلَى قَوْمٍ لَّمْ نَجْعَل لَّهُم مِّن دُونِهَا سِتْراً{90} كَذَلِكَ وَقَدْ أَحَطْنَا بِمَا لَدَيْهِ خُبْراً{91}
89 - Sa'an nan kuma ya bi hanya.
90 - Har a lõkacin da ya isa ga mafitar rãnã, ya sãme ta tanã fita a kan wadansu mutãne (wadanda) ba Mu sanya musu wata kãriya ba daga barinta.
91 - Kamar wancan alhãli kuwa Mun kẽwaye da jarrabãwa ga abin da ke gunsa.
A cikin shirin da ya gabata an ambaci cewa, Zulkarnaini daya ne daga cikin bayin Allah da Allah ya ba shi ilimi na musamman daga gare shi, ya yi tafiya zuwa yammacin duniya domin tsayar da tsari na adalci a tsakanin mutane da suke rayuwa a yankuna daban-daban na duniya. Daga nan kuma sai ya yi wata doguwar tafiya zuwa gabacin duniya mahudar rana, inda ya samu wasu mutane da suke rayuwa a cikin rana, ba su da gidaje, ba su ma da tufafi a jikinsu.
Alkur’ani mai tsarki yana yin bayani kan yanayin da Zulkarnaini ya samu mutane a wannan wuri, da kuma yanayin yadda suka kasance suna rayuwa, amma kur’ani mai tsarki bai yi bayani kan abin da Zulkarnaini ya yi a wurin ba.
Darussan da za a iya dauka daga wadannan ayoyi masu albarka:
1 – Bayin Allah a koda yaushe burinsu shi ne su ga sun taimaki wanda yake cikin halin bukata, tare da yada adalci a tsakanin mutane.
2 – Jagororin al’umma wajibi ne su shiga cikin mutane domin su san irin matsalolin da mutane suke fama da su, domin sanin hanyoyin da za su warware ma mutane matsalolinsu gwagwadon iko.
Sai a saurari karatun ayoyi na (92) zuwa (94) a cikin surat Kahfi
ثُمَّ أَتْبَعَ سَبَباً{92} حَتَّى إِذَا بَلَغَ بَيْنَ السَّدَّيْنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوْماً لَّا يَكَادُونَ يَفْقَهُونَ قَوْلاً{93} قَالُوا يَا ذَا الْقَرْنَيْنِ إِنَّ يَأْجُوجَ وَمَأْجُوجَ مُفْسِدُونَ فِي الْأَرْضِ فَهَلْ نَجْعَلُ لَكَ خَرْجاً عَلَى أَن تَجْعَلَ بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمْ سَدّاً{94}
92 - Sa'an nan kuma ya bi hanya.
93 - Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi wadansu mutãne daga gabãninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba.
94 - Suka ce: "Yã Zulkarnaini! Lalle ne Yãjũja da Majũja mãsu barna ne a cikin kasa. To, ko zã mu sanya harãji sabõda kai, a kan ka sanya wata katanga a tsakãninmu da tsakãninsu?"
Ya ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da ya isa wani yanki a tsakanin wasu manyan tsaunuka guda biyu, ya samu wasu mutane a wurin wadanda ba su fahimtar wani yare, to amma da ilhami na Allah ta hanyar isharori suka sheda ma Zulkarnain cewa akwai wasu jama’a biyu wato yajuju da majuju, wadanda suke yin barna a bayan kasa, kuma suna cutar da su cutarwa, saboda haka suna son ya gina musu wata babbar katanga ta karfe da za ta kange su daga yajuju da majuju, kuma duk abin da yake bukata na lada ko taimakonsu wajen gudanar da wannan aiki a shirye suke su yi.
Alkur’ani mai tsarki yana bayyana yanayin rayuwar wadannan mutane da cewa ba su da ci gaba irin na wancan lokacin, domin kuwa ba su san yadda za su yi magana ba sai dai ta wasu hanyoyi kawai na ishara, kuma suna rayuwa ne a tsakanin wasu manyan tsaunuka biyu, wato ba su da labarin duniya balanta sanin abin da ke wakana a cikinta, amma Zulkarnaini bai yi watsi da bukatar su ba, domin kuwa shi mutum ne mai kaskantar da kansa ga Allah, kuma ba ya ya yi ma mutane girman kai komai irin yanayin da suke ciki.
Wani abun mamaki shi ne, yadda suka amince da Zulkarnain daga ganinsa, duk kuwa da cewa ba su san shi ba, bilhasali ma jama’ar da suka sani masu cutar da su ne, wato yajuju da majuju, amma da ganinsa suka sakankance kan cewa shi ba azzalumi ba ne, kuma ya yi kama da masu taimako wadanda ake zalunta, shi yasa ba su wata-wata ba sai suka gabatar masa da matsalolinsu, kuma suka bukaci taimako daga gare shi.
Zulkarnain ya gina musu wanna katanga kamar yadda suka bukata kamar yadda za a ji a cikin bayanin ayoyi na gaba. Wannan ya nuna muhimmancin tsaro a cikin al’umma, a duk lokacin da wat aal’umma take fuskantar barazana ta tsaro, to wajibi ne kan jagorori da mutane suke mayar da lamurransu gare su mike tsaye domin ganin al’umma ta kubuta daga irin wannan baraza, domin kuwa alokacin da mutane suka kwanciyar hankali saboda rashin tsaro, to sun rasa wani babban bangare na rayuwarsu, domin kuwa babu wani abu da za su iya yi cikin kwanciyar hankali, kenan mafi yawan abubuwan da suke yi sai an tawaya a cikinsu saboda rashin tabbas kan rayuwarsu da lafiyarsu.
Duk da cewa Zulkarnain ba shi kadai ya gudanar da wannan aiki ba, sai da taimakon jama’a, wanda hakan ke nuni da cewa a koda yaushe ana bukatar hannun mutane wajen ci gaban lamarinsu da kyautatar rayuwarsu.
Masana tarihi sun tabbatar da cewa wannan katanga da Zulkarnain ya gina wa wadannan mutane har yanzu tana nan daram, kuma tana a tsakanin wasu tsaunuka ne biyu da suke Kafkaz. Dangane da shi kansa Zulkarnain an samu mabanbantan ra’ayoyi tsakanin masana tarihi, wasu suna cewa Almakduni ne, wanda a zamaninsa ya yi tafiye-tafiye zuwa yankuna na duniya, daga yammacinta zuwa gabacinta, kuma ya yi ta wayar da kan mutane a duk inda ya same su kan tafarkin tauhidi.
Yyin da kuma masana tarihin suke cewa Zulkarnain shi ne Kurush sarkin Hakhamnshiyawa da aka yi Iran dubban shekaru, wanda shi ma kissarsa ta yi kama da abin da aka fada kan Zulkarnain, da suka shafi tafie-tafiye zuwa yankunan gabaci da yammacin duniya, da taimakon mutane da kiransu zuwa ga tauhidi, kuma shi ne ake danganta babbar katangar yankin Kafkaz da shi, wadda kuma malaman tarihi sun tafi kan cewa ita ce katangar Zulkarnain.
Darussan da za a dauka anan su ne:
1 – Duk inda mutane suka bukaci taimako, to ya rataya kan mahukunta su saurare su kuma su taimaka musu gwargwadon iyawa.
2 – Bukatuwa zuwa tsaro tana kan gaba a kan akasarin bukatu na rayuwar zamantakewar jama’a.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 95-101 (Kashi Na 517) ===
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat kahfi, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun ayoyi na (95) da (96) a cikin surat Kahfi
قَالَ مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيْرٌ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجْعَلْ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ رَدْماً{95} آتُونِي زُبَرَ الْحَدِيدِ حَتَّى إِذَا سَاوَى بَيْنَ الصَّدَفَيْنِ قَالَ انفُخُوا حَتَّى إِذَا جَعَلَهُ نَاراً قَالَ آتُونِي أُفْرِغْ عَلَيْهِ قِطْراً{96}
95 - Ya ce: "Abin da Ubangijĩna Ya mallaka mini, a cikinsa yã fi zama alhẽri. Sai ku taimake ni da karfi, in sanya babbar katanga a tsakãninku da tsakãninsu."
96 - "Ku kãwo mini guntãyen bakin karfe". har a lõkacin da ya daidaita a tsakãnin duwãtsun biyu (ya sanya wutã a cikin karfen) ya ce: "Ku hũra (da zugãzugai)." Har a lõkacin da ya mayar da shi wutã, ya ce: "Ku kãwo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa."
A cikin shirin da ya gabata an yi bayani kan wasu mutane da Zulkarnain ya samu suna rayuwa a tsakanin wasu manyan tsaunuka biyu, wadanda suke fuskantar barazanar tsaro daga wasu muggan mutane azzalumai da suke cutar da su, sai suka nemi taimakon Zulkarnai kan ya gina musu wata katanga da za ta raba tsakaninsu wa wadannan jama’a masu shishigi, a kan za su ba shi ladar wannan aiki.
Sai Zulkarnain ya ce musu zai yi musu wannan aiki, amma su taimaka masa da karfafa daga cikinsu, su dauko masa karafa da zai yi wannan aiki da su, kuma suka yi aiki kamar yadda ya bukace su har ya kammala gina musu katangar karfe da ta kange su daga yajuju da majuju, sai ya ce musu abin da ya yi mani na falala ya fi abin da kuke son saka mini da shi na lada.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Waliyan Allah suna shiga gaba-gaba wajen taimakon mabukata da warware matsalolinsu gwargwadon ikon da Allah ya ba su.
2 – Haduwar mutane a kan aiki na jama’a domin ci gabansu ta fuskar rayuwarsu ta zamantakewa ko tsaro ko tattalin arziki, shi ne babban mabudin nasararsu.
3 – Ko da mutane suna da abin da za su biya kansu bukata na daga kudade ko kayan aiki, amma kuma ba su da sahihin jagoranci da zai nuna musu hanya, to za su wanzu cikin fangima ne, domin Zulkarnaini ya sami mutane da duka bin da suke bukata domin su kare kansu daga yajuju da majuju, amma babu wanda ya san yadda za a yi hakan a cikin sai da Zulkarnaini ya sa musu hannu.
Sai a saurari karatun ayoyi na (97) da (98) a cikin surat Kahfi
فَمَا اسْطَاعُوا أَن يَظْهَرُوهُ وَمَا اسْتَطَاعُوا لَهُ نَقْباً{97} قَالَ هَذَا رَحْمَةٌ مِّن رَّبِّي فَإِذَا جَاء وَعْدُ رَبِّي جَعَلَهُ دَكَّاء وَكَانَ وَعْدُ رَبِّي حَقّاً{98}
97 - Dõmin haka bã za su iya hawansa ba, kuma bã zã su iya huda shi ba.
98 - Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijĩna. Sai idan wa'adin Ubangijĩna ya zo, ya mayar da shi nikakke. Kuma wa'adin Ubangijĩna ya kasance tabbatacce."
Wannan ayar tana yin ishara da abubuwan muhimmai guda uku, na daya : katangar da Zulkarnain ya gina tana tsawo da gwabi, kuma ta ginu matukar ginuwa, ta yadda yajuju da majuju ba za su iya haurawa kanta ba ko huda ta.
Abu na biyu shi ne : Zulkarnain bai danganta wannan aiki da kansa ba ko mutanen da suka taimaka masa, ya danganta hakan da rahamar ubangiji ga mutanen wannan wuri domin tsaronsu da kuma zaman lafiyarsu.
Abu na uku shi ne : Ya isar musu da sako cewa akwai wata rana da za ta zo wato kiyama, wadda alkawalin ubangijin dukkanin talikai ce, idan wannan rana ta zo to komai na duniya zai rushe ita ma wannan katangar duk da kwarinta za ta rushe ta warwartse saboda tsananin girgizar da kasa za ta yi a wannan rana, kuma zuwan wannan babu tantama a cikinsa, domin kuwa Alkawalin ubangiji ne, kuma alkawalin ubangiji gaskiya ne.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Yin aiki tare da dikka da kuma kyautata shi na daga abin da aka sani a cikin sira ta waliyyan Allah, abin buga misali da shi kan hakan ita ce katangar Zulkarnain, wadda aka gina dubban shekaru, kuma tana ci gaba da wanzuwa har ranar tashin kiyama.
2 – Bayin Allah na gari a koda yaushe suna danganta duk wata fala da suka samu a rayuwarsu zuwa ga Allah, domin kuwa sun san cewa Allah shi ne mai kowa da komai.
3 – Duk nasarar da muka samu a cikin kowane irin lamari na duniya, to kada kuma mu manta da kiyama ranar da komai zai kare sai mulkin Allah.
Sai a saurari karatun ayoyi na (99) zuwa (101) a cikin surat Kahfi
وَتَرَكْنَا بَعْضَهُمْ يَوْمَئِذٍ يَمُوجُ فِي بَعْضٍ وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَجَمَعْنَاهُمْ جَمْعاً{99} وَعَرَضْنَا جَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ لِّلْكَافِرِينَ عَرْضاً{100} الَّذِينَ كَانَتْ أَعْيُنُهُمْ فِي غِطَاء عَن ذِكْرِي وَكَانُوا لَا يَسْتَطِيعُونَ سَمْعاً{101}
99 - Kuma Muka bar sãshensu a rãnar nan yanã garwaya a cikin sãshe, kuma aka bũsa a cikin kaho sai muka tãra su, tãrãwa.
100 - Kuma Muka gitta Jahannama, a rãnar nan ga kãfirai gittãwa.
101 - Wadanda idãnunsu suka kasance a cikin rufi daga tunãni, kuma sun kasance bã su iya saurãrãwa.
Idan muka kwatanta wannan aya da abin daka ambata acikin aya ta 96 a cikin surat Anbiya, za a iya fahimtar cewa a lokacin tashin kiyama ya zo katangar Zulkarnain za ta rushe, kuma yajuju da majuju za su sake afklawa kan mutane suna masu kai mummnan hari, tare da figita mutane da watsa su, za su kame wasu bangarori a kan doron kasa, daga karshe kuma mutane za su bar duniya baki daya bayan busa kaho, a lokacin busa kaho na biyu duk su hallara a wurin da za a yi tashin kiyama, a lokacin wadanda suka kafirce ma Allah a rayuwar duniya, suka yi sharholiya suka sheke aya, za su kuka su yi da sun sani a lokacin da Allah ya bijiro da wutar jahannama, domin su sun kasance suna kawar da kansu daga sakon Allah ba su su ma sauraren abin da ake gaya musu na daga ayoyin Allah, a ranar kiyama babu aiki balantana mutum ya yi istigfari, ko kuma ya yi wani aikin ibada domin ya samu lada.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – Daga cikin alamun karshen duniya, mutane za su rude su yi ta fangima, wasu masu mugunta kuma za su yi ta cutar da sauran raunana.
2 – Da dama daga ni’imomin duniya hanyoyi ne tuna Allah da gode masa, amma mafi yawan mutane ba su tuna Allah a lokacin da suke cikin ni’ima da walwala.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 102-106 (Kashi Na 518) ===
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat kahfi, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun aya ta (102) a cikin surat Kahfi
أَفَحَسِبَ الَّذِينَ كَفَرُوا أَن يَتَّخِذُوا عِبَادِي مِن دُونِي أَوْلِيَاء إِنَّا أَعْتَدْنَا جَهَنَّمَ لِلْكَافِرِينَ نُزُلاً{102}
Shin wadanda suka kãfirta sun yi zaton (daidai ne) su riki wadansu bãyĩna, majibinta baicina? Lalle ne, mun yi tattalin Jahannama ta zama liyãfa ga kãfirai.
Wannan ayar ci gaban bayin ayar da ta gabata ne a cikin shirin da ya wuce, dangane da mutanen da suka kafirce ma Allah kuma suka rike wasu a madadin Allah, wannan ayar tana cewa da irin wadannan mutane shin suna zaton za su riki wasu mutane ko wasu abubuwa na daban abin bauta koma bayan Allah ? alhali Allah madaukakin sarki shi ne mahalicci kuma ubangiji kowa da komai ? suna zaton cewa wani koma bayan Allah zai iya yaye matsalolinsu kuma saka su cikin sa’adar duniya ? Da wane irin hankali ne suke yin tunani har da za su yi watsi da Allah su kama wani abu na daban ? Hakika wadanda suka kafirce ma Allah suna da azabar jahannama a ranar kiyama, sakamakon kafircin da suka yi a duniya.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – kafirai ba su da wata hujja ta hankali da suka dogara da ita wajen kin bin Allah, suna bin san ransu ne wajen yin abin da suka ga dama a rayuwar duniya.
2 – Yin musun samuwar ubangiji ba shi kadanai kafirci ba, jibinta lamari ga wani wanda ba Allah ba kuma ba a kan tafarkinsa ba, nau’i ne na kafirci, domin kuwa Allah madaukakin sarki shi kadai ba hada shi da wani abu na daban a cikin bauta da jibinta lamari.
Sai a saurari karatun ayoyi na (103) da kuma (104) a cikin surat Kahfi
قُلْ هَلْ نُنَبِّئُكُمْ بِالْأَخْسَرِينَ أَعْمَالاً{103} الَّذِينَ ضَلَّ سَعْيُهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ يَحْسَبُونَ أَنَّهُمْ يُحْسِنُونَ صُنْعاً{104}
103 - Ka ce: "Kõ mu gaya muku game da wadanda suka fi hasãra ga ayyuka?"
104 - "Wadanda aikinsu ya bace a cikin rãyuwar dũniya, alhãli kuwa sunã zaton lalle ne sũ, sunã kyautatawa ga (abin da suke gani) aikin kwarai?"
Wadannan ayoyi masu albarka suna yin bayani ne dangane da mutanen da suke zaton cewa sun yi ayyuka na gari a rayuwarsu ta duniya, da hakan ya hada mutanen littafi da suka canja abubuwan da aka ambata a cikin littafansu suka shiga bin shirme da surkulle, ko kuma musulmi da suka karkace bin sahihin tafarkin ma’aiki, sakamakon bin wasu abubuwa da ba su cikin addini.
Daga cikin abubuwa masu hadari da suke fuskantar mutum har da zaton cewa ayyukansa masu kyau ne a duniya, amma ranar kiyama idan an duba ayyukansa sai a ga mummunan aiki, domin kuwa tabbas akwai abin yake yi a cikin ayyukan nasa da ya yi hannun riga da koyarwar addinin Allah, hakan kuma zai nisantar da shi daga samun rahamar ubangiji a lahira.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Yawan aiki ba shi ne ke tseratar da mutum ba, muhimmin lamai dai shi ne mutum ya yi aiki yana tsarkake niyya ga Allah, kuma yayi kokarin sanin sahihin tafarki domin yin abin yake daidai.
2 – Kada mutum ya gina zatonsa a kan cewa duk abin da yake yi daidai ne, amma ya yi iyakacin kokarinsa domin yin abin da yake daidai bisa hujja, domin kada ya zo ranar kiyama ya ga akasin abin da yake zato dangane da ayyukansa.
Sai a saurari karatun ayoyi na (105) da kuma (106) a cikin surat Kahfi
أُولَئِكَ الَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ رَبِّهِمْ وَلِقَائِهِ فَحَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فَلَا نُقِيمُ لَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَزْناً{105} ذَلِكَ جَزَاؤُهُمْ جَهَنَّمُ بِمَا كَفَرُوا وَاتَّخَذُوا آيَاتِي وَرُسُلِي هُزُواً{106}
105 - Wadancan ne wadanda suka kãfirta da ãyõyin Ubangijinsu, da kuma haduwa da shi, sai ayyukansu suka bãci. Sabõda haka bã zã mu tsayar musu da mizani ba a rãnar kiyãma.
106 - Wancan ne sakamakonsu Jahannama sabõda kãfircinsu, kuma suka riki ãyõyina da manzannina abin izgili.
Wadannan ayoyi masu albarka ci gaban bayani ne kan mutanen da suke yin aiki kuma suke zaton cewa a lahira su ne masu rabo, alhali abin da suka aikata ya yi hannun riga da abin da Allah ya umurce su. Duk kuwa da cewa ayar tana kiran irin wadannan mutane da wadanda suka kafirce ma ayoyin ubangijinsu, duk kuwa da cewa su suna ganin cewa suna kan sahihin tafarki, amma saboda wani abu da suka yi wanda Allah bai yarda da shi ba, ya kira su da wadanda suka kafirce ma ayoyinsa kuma suka kafirce da kiyama, koda kuwa a baki suna furta cewa sun yi iamani da kiyama, amma saboda abubuwan da suka aikata na sabo da suka nisantar da su daga rahmar Allah, dukkanin ayyukansu da suke ganin za su amfanar da su a lahira sun baci, saboda haka ba su rabo daga baiwar da Allah zai yi wa bayinsa na gari a wannan rana, maimakon haka ma sakamonsu wutar jannama ne, saboda abin da suka aikata da kuma yin watsi da ayoyin Allah da sakonnin da manzanninsa suka zo musu da su.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Kada ya zama ayyuka na zahiri su ne kawai ma’auni wajen gane hakika, domin kuwa sau dayawa aiki zai zama zahirinsa mai kyau ne amma badininsa sabanin haka, kamar ganga ce mai zakin sauti idan an kada ta, amma idan aka duba cikinta ba za a samu komai ba.
2 – kafirce ma ubangiji da yin izgili da ayoyinsa da manzanninsa, kan yi sanadiyar bacewar ayyuka na alkhairi baki daya, hakan kan jawo ma mutum mummunan karshe a lokacin da zai bar gidan duniya, Allah ya kare mu.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
=== Suratul Kahfi, Aya Ta 107-110 (Kashi Na 519) ===
Jama'a masu saurare Asslamu alaikum barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannuka mai sanda, inda muke yin dubi a cikin ayoyin kur'ani mai tsarki, tare da yin bayani gwargawdon iko kan abin da suke koyar da mu, tare da yi mana hannunka mai sanda a cikin lamurran rayuwa. Har yanzu muna cikin surat kahfi, sai a biyo mu sannu a hankali a cikin shirin.
Sai a saurari karatun ayoyi na (107) da (108) a cikin surat Kahfi
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَانَتْ لَهُمْ جَنَّاتُ الْفِرْدَوْسِ نُزُلاً{107} خَالِدِينَ فِيهَا لَا يَبْغُونَ عَنْهَا حِوَلاً{108}
107 - Lalle ne, wadanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyuka na gari, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyãfa a gare su.
108 - Suna madawwama a cikinta, bã su nẽman makarkata daga barinta.
A cikin shirin da ya gabata an ambaci makomar wadanda suka kafirce ma Allah a rayuwar duniya da kuma abin da za su iske a lahira na daga azabar Allah, sakamakon karyata ayoyin Allah da bin son ransu a cikin rayuwar duniya. Wadannan ayoyi masu albarka kuwa suna yin bayani ne dangane da makomar muminai da suka yi ayyuka na gari suka tsakake zukatansu tare da yin komai domin Allah, irin wadannan bayin Allah aljanna ce masafkinsu a ranar kiyama, a nan za su ci gaba da zama har abada a cikin ni’imar ubangiji suna masu farin ciki da jin dadi, duk kuwa da cewa sun yi hakuri a duniya wajen bin Allah da kiyaye dokokinsa, amma Allah zai yi sakamako da ya fi dukkanin ayyukan da suka yi a duniya, domin kuwa aikin mutum ba zai iya kai ga samun aljannar Allah ba sai da rahama daga ubangiji.
Bisa ruwayoyi da suka zo daga manzon allah (SAW) aljanna mataki-mataki ce, wata ta dara wata daraja, amma mafi daukakar daraja daga cikinsu ita ce aljannar Firdausi.
Darussan da za a dauka a nan su ne :
1 – Domin samun dacewa da aljannar ubangiji a ranakiya dole sai da imani da kuma aiki na gari, domin dukkaninsu abubuwa ne da ba su rabuwa da juna, a lokacin da mutum ya zo da imani amma babu aiki, ba lissafa shi a cikin bayin Allah da wadannan ayoyi suke yin bayani a kansu, haka nan kuma idan ya zo da aiki komai kyawonsa amma babu imani, shi ma ba ya daga cikin bayin Allah da suka sharuddan shiga aljanna.
2 – Saboda girman aljanna da fadinta da kuma yawan ni’iomin da ke cikinta, ‘yan aljanna ba su bukatar wani wuri na daban da ba aljanna ba, domin kuwa na ni’ima da jin dadi da mutum bai taba sani ba yana nan ciki.
Sai a saurari karatun aya ta (109) a cikin surat Kahfi
قُل لَّوْ كَانَ الْبَحْرُ مِدَاداً لِّكَلِمَاتِ رَبِّي لَنَفِدَ الْبَحْرُ قَبْلَ أَن تَنفَدَ كَلِمَاتُ رَبِّي وَلَوْ جِئْنَا بِمِثْلِهِ مَدَداً{109}
109 - Ka ce: "Dã tẽku ya kasance tawada ga (rubũtun)kalmõmin Ubangijina, lalle ne dã tẽkun ya kãre a gabãnin kalmõmin Ubangijĩna su kãre, kuma kõda mun jẽ da misãlinsa dõmin kari."
Wannan aya ta biyun karshe a cikin surat kahf tana yin ishara ne da dukkanin sakamako na abin da aka fada ne a cikin wannan sura mai albarka na daga ayoyin Allah, kama daga batun ashabul kahf, abin da ya gudana tsakanin annabi Musa da kuma Khidr, da kuma kissar Zulkarnain, saboda haka ne ayoyin karshe na surat Kahf suka zo da siga ta umurni ga manzon Allah da ya fada wa dukkanin talikai, inda aka yi amfani da kalmar Kul, wato ka fada, domin tabbatar da cewa dukkanin abin da aka ambata a cikin wannan sura ba fadar ma’aiki ba ce, fadar Allah madaukakin sarki ce, cewa ya fada ma talikai cewa da a ce dukkanin tekun da ke duniya zai zama tawadar rubutu da za a rubuta kalmomin Allah da shi, to tekun ya kare ba tare da an kammala rubuta kalmomin Allah ba, ko da kiuwa za a yi ta kawo wasu tekunan makamantansa a matsayin tawada to da za su ta karewa, ba tare da kalmomin Allah sun kare ba.
Ma’anar kalmomin Allah a nan lamari ne da ya fita daga duk wani ilimi da dan adam yake da shi, domin dan ba zai iya sanin dukkanin kalmomin Allah ba, amma zai iya sanin wasu daga ciki, da hakan ya hada da dukkanin abin da yake cikin duniya baki daya na daga cikin kalmomin Allah, haka nan kuma akwai abubuwan da suke ba cikin wannan duniya ba wanda Allah ne kawai ya bar ma kansa sani dangane da su, sammai da kassai dukkaninsu suna cikin kalmomin Allah, littafan da annabawa suka zo da su suna cikin kalmomin Allah, duk wani abu da Allah ya halitta to kalmar Allah ce, wannan ne ya sanya aka kira annabi Isa (AS) da kalmar Allah a cikin kur’ani mai tsarki, domin shi yana daga cikin mu’ujizozi na Allah a tsakanin ‘yan adam.
Darussan da za a iya dauka a nan su ne :
1 – Dukkanin abubuwan da Allah ya halitta a cikin duniya wadan da mutum ya sani da ma wadanda bai sani ba, da ma wasu abubuwan da ba a cikin duniya suke ba duk kalmomin Allah ne.
2 – A duk lokacin da mutum yake yin nisa cikin ilimi tare da gano abubuwa da bai sani ba, a lokacin yake kara fahimtar cewa lallai bai san komai daga boyayyen ilimin Allah ba.
Sai a saurari karatun aya ta (110) a cikin surat Kahf
قُلْ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يُوحَى إِلَيَّ أَنَّمَا إِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ فَمَن كَانَ يَرْجُو لِقَاء رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلاً صَالِحاً وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَداً{110}
110 - Ka ce: "Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku abun bauta guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haduwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na kwarai. Kuma kada ya hada kõwa ga bauta wa Ubangijinsa."
A cikin wannan aya ta karshe a cikin surat Kahf, an umurci manzon Allah (SAW) da ya sheda ma mutane cewa ; shi mutum ne kamarsu, shi ba mala’ika ba ne ko wata halitta ta daban, amma kuma banbanci a tsakaninsa da sauran mutane shi ne, shi Allah ya zabe shi a matsayin ma’aikinsa, yana yi masa wahayi da abin da zai shiryar da mutane da shi, ya fitar da su daga duhun bata da shirka da surkulle, ya kai su zuwa ga hasken imani da shiriya, zuwa ga bautar Allah ubangiji da kadaita shi, kuma ya sheda ma mutane sharadin samun rahamar ubangiji da gafararsa a ranar da za a hadu da shi, sharadin hakan kuwa shi yin aiki na gari, da kuma nisantar hada bautar Allah da wani abu na daban wato shirka.
A cikin wannan aya an karfafa batun tauhidi da kuma nisantar shirka, ta yadda muminai za su zama cikin fadaka domin kada su fada cikin hadarin hada bautar Allah da wani abu na daban, ko da kuwa boyayyar shirka ce da aka yi bayani kanta a cikin shirye-shiryen da suka gabata.
Darussan da za aiya dauka a nan su ne :
1 – Kada mutum ya taba daukar kansa fiye da matsayin da Allah ya ajiye shi, domin manzon Allah da kansa ya kira kansa a matsayin mutum kamar kowa, bai kira kansa wani abu fiye da mutum dan adam ba, wannan ita ce kamala, domin kuwa mutum zai iya zama abin koyi ga sauran mutane, ba mala’iku ko sauran halittun Allah ba.
2 – Fatar samun aljannar ubangiji ba tare da aiki na gari ba hakan ba ya da ma’ana, a koda yaushe fatar mutum na damfara ne da kokarinsa.
Da wannan ne muka kawo karshen shirin namu na wannan lokaci, sai idan Allah ya kai mu a shiri na gaba za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin wannan lokacin, a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin, nake yi muku fatan alkhairi, sai saduwa ta gaba, wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.