No edit summary |
|||
Line 14: | Line 14: | ||
==[[tarjama|Tarjama]] da [[tafsirin]] aya ta 1-3== | ==[[tarjama|Tarjama]] da [[tafsirin]] aya ta 1-3== | ||
# Na rantse da zamani. | # ''Na rantse da zamani.'' <> I swear by the Time, [1] | ||
# Lalle mutum yana cikin [[asara]]. | # ''Lalle mutum yana cikin [[asara]].'' <> man is in a state of loss indeed, [2] | ||
# Sai dai waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna waiyya da haƙuri. | # ''Sai dai waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na gari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna waiyya da haƙuri.'' <> except those who believed and did righteous deeds, and advised each other for truth, and advised each other for patience. [3] | ||
===Tafsiri=== | ===Tafsiri=== | ||
Line 23: | Line 23: | ||
Sai Allah ya togace wasu bayinsa daga aukawa cikin wannan asara, su ne kuwa waɗanda suka siffantu da siffofi huɗu: | Sai Allah ya togace wasu bayinsa daga aukawa cikin wannan asara, su ne kuwa waɗanda suka siffantu da siffofi huɗu: | ||
# Imani da Allah duk abin da ya umarci bawa ya yi imani da shi, wanda hakan ba zai yiwu ba sai da ilimin sanin Allah. | # Imani da Allah duk abin da ya umarci bawa ya yi imani da shi, wanda hakan ba zai yiwu ba sai da ilimin sanin Allah. | ||
# Aiki na ƙwarai, wannan kuwa ya ƙunshi duk ayyukan alheri na sarari da na ɓoye; masu alaƙa da haƙƙoƙin Allah, da masu alaƙa da haƙƙoƙin bayinsa, na wajibai ko na mustahabbai. | |||
# Yi wa juna wasiyya da gaskiya, wadda ita ce kwaɗaitar da juna a kan yin imani da yin aiki na gari. | |||
# Yi wa juna wasiyya a kan haƙuri wajen bin Allah da barin saɓa masa, da haƙuri da ƙaddararsa marar daɗi. | |||
Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka: | |||
# Allah yana rantsuwa da duk abin da ya ga dama a cikin halittarsa. Bai halatta Musulmi ya yi rantsuwa da komai ba sai da Allah. | |||
# Nuna muhimmancin lokaci wanda a cikinsa mumini yake ribatar zamansa na duniya wajen neman yardar Allah. | |||
# Imani da Allah da aikata kyawawan ayyuka su ne suke sanya bawa ya samar wa kansa kamala. | |||
# Yi wa juna wasiyya da bin gaskiya da yin haƙuri, da su ne kuma mumini yake samar wa ɗan'uwansa kamala. | |||
# Aiwatar da waɗannan al'amura huɗu ne suke kuɓutar da bawa daga faɗawa cikin asara ta duniya da ta lahira, suke kuma sanya shi ya ci ribar rayuwarsa ta duniya. | |||
# Kira zuwa ga gaskiya yana buƙatar juriya da haƙuri. Hakanan riƙo da gaskiya yana buƙatar juriya da haƙuri. | |||
[[Category:Quran/103]] | [[Category:Quran/103]] | ||
[[Category:RijiyarLemo]] | [[Category:RijiyarLemo]] |