Toggle menu
24.1K
670
183
158.5K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 125: Line 125:
Sannan Allah ya bayyana wani abu da ya wajaba muminai su yi hattara da shi dangane da [[sha'anin]] kafirai da [[munafukai]]; wannan abu kuwa shi ne saboda tsananin kiyayya da hassadar da ke cikin zukatansu ga muminai, ba za su taba jin suna son su a zukatansu ba. Su muminai kam suna nuna suna kaunar su su kuma kafitai ba sa son su, ba sa kuma kaunar su; tsakaninsu da su kiyayya ce kawai. Kamar yadda muminai suka yi imani da duk littattafan da Allah ya saukar wa annabawa, amma su kafirai na Yahudu da Nasara sun ki yin imani da abin da aka saukar ga Annabi SAW, bayan kuma sun jirkita nasu littattafan. To duk wanda irin wannan ne halinsa; to kamata ya yi a ki miyagun halayensu na munafirci, duk sa'adda za su hadu da muminai sai su rika nuna musu sun yi imani, amma kuma da zarar sun ware, sun kadaita da junansu, sai su rika cizon 'yan yatsunansu, saboda tsananin bakin ciki da haushin muminai, domin suna ganin irin [[hadin kan]] muminai da kaunar da ke tsakaninsu. Sai Allah ya umarci Annabinsa ya gaya musu: "Sai dai ku mutu da bakin cikinku" domin Allah ya yi alkawarin sai ya cika wannan ni'imar tasa, ya daukaka addininsa ko ba sa so, sai dai [[bakin ciki]] ya kashe su. Allah kuma yana sane da bin da yake boye a cikin kirazan bayinsa, don haka zai yi wa kowa sakayya a kan abin da ya aikata.  

Sannan Allah ya bayyana abin da yake kara tsananin [[gabar]] kafiran ga muminai, watau duk lokacin da wani abin [[farin ciki]] ya sami muminai, sai su rika jin haushi, suna damuwa;   
Sannan Allah ya bayyana abin da yake kara tsananin [[gabar]] kafiran ga muminai, watau duk lokacin da wani abin [[farin ciki]] ya sami muminai, sai su rika jin haushi, suna damuwa; yayin da kuma wani abin bakin ciki ya same su, sai su rika murna, suna jin dadi. Sai Allah ya koyar da muminai abin da zai taimaka musu wajen jure irin wannan hali na kafirai, watau su zama masu hakuri, kuma masu taqwa, domin idan har sun rungumi wadannan siffofi guda biyu, to babu wani makirci da zai cutar da su. Allah yana kewaye da saninsa game da abin da wadannan kafiran da munafukan suke yi, kuma zai saka musu a kan hakan.  

'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' 
# Nisantar miyagun [[abokan shawara]] yana daga cikin imani, shi ya sa aka fuskantar da wannan maganar ga muminai.
# A nan an nuna ba kowa ne ya kamata ya zama abokin shawara ba. Idan an jarrabi mutum da mu'amala da makiya; to ya kamata mu'amalarsa ta kasance sama-sama, kada ya saki jiki ya rika buda masa sirrinsa, ko da kuwa zai rantse masa cewa yana son sa.
# Fadar Allah Ta'ala: "Sun so duk wani abu da zai kuntata muku..."

[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]