No edit summary |
No edit summary |
||
Line 150: | Line 150: | ||
Tafsiri: | Tafsiri: | ||
Bayan Allah SWT | Bayan Allah SWT ya bayyana cewa hakuri da taqawa su ne makamin da mumini zai tsare kansa da shi daga cutarwar maƙiyansa,sai kuma a wadannan ayoyi Allah ya fito da bayanin abubuwan da kan sabbaba rashin samun nasara a kan maƙiya. | ||
Allah yana tunatar da Annabinsa Muhammadu SAW lokacin da ya fito daga gidansa domin haduwa da kafiran Makka a ranar yakin Uhudu, lokacin da yake shirya rundunar muminai domin fita yaki, yana sanya kowa a muhallin da ya dace da shi. Domin Allah yana jin komai, yana jin shawarar da Annabi SAW ya yi da sahabbansa a kan wurin da ya kamata a yi wannan yaki. Kuma Allah shi ne masani dangane da ra'ayin da ya fi dacewa daga cikin ra'ayoyin da aka kawo a lokacin. Kuma yana sane da irin mugun nufin da kafirai da munafukai suka boye a zukatansu, har ma da abin da daukacin halittunsa suka boye a zukatansu. | |||
Allah yana tunatar da Annabi SAW lokacin da wasu kungiyoyi biyu daga cikin muminai, suka yi nufin su janye daga wannan yaki, su ne kabilun Banu Salima da na Banu Harisa, sai dai kuma Allah ya kafe dugadugansu. Allah ya sanar wa Annabi SAW cewa, gare shi shi kadai ya wajaba muminai su dogara. | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |