No edit summary |
|||
Line 205: | Line 205: | ||
# Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku ci riba ninki-ba-ninkin, kuma ku ji tsoron Allah don ku rabauta. --[[Quran/3/130]] | # Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku ci riba ninki-ba-ninkin, kuma ku ji tsoron Allah don ku rabauta. --[[Quran/3/130]] | ||
# Kuma ku tsoraci wuta wadda aka riga aka yi tanadinta domin kafirai. | # Kuma ku tsoraci wuta wadda aka riga aka yi tanadinta domin kafirai. | ||
# Kuma ku bi Allah da Manzo don a ji qan ku (a ranar tashin alqiyama). Tafsiri: | # Kuma ku bi Allah da Manzo don a ji qan ku (a ranar tashin alqiyama). | ||
Tafsiri: | |||
Bayan Allah ya bayyana cewa, ya taimaka wa muminai yayin da suke raunana, kuma ya taimake su ne saboda taqawarsu da bin umarninsa. Haka kuma lokacin da suka sami matsala a yakin Uhudu saboda saba wa umarnin Manzon Allah da suka yi, sai kuma a nan Allah ya tsawace su da su guji tsananin kwadayin tara dukiya, musamman ta hanyar cin dukiyar riba ninkin-ba-ninkin, wanda yana daga manyan laifukan da suka yadu a wannan lokacin. | |||
Sannan kuma ya nuna musu hanyar samun taqawa, wadda ita ce tafarkin samun duk wata nasara. Taqawa da ma ita ce aikata umarnin Allah da guje wa haninsa. Don haka a karshen wadannan ayoyi, Allah ya ja hankalin muminai da su ji tsoron Allah, don su sami rabauta duniya da lahira, kuma su tsoraci wuta, ta hanyar sanya shamaki tsakaninsu da ita, wadda an shirya ta ne musamman domin kafirai, wadanda suka bijire wa imani da Allah da abin da ya saukar wa Annabinsa. Ya umarci muminai da su yi wa Allah da'a da Manzonsa, domin da haka ne za su sami rahama duniya da lahira. | |||
Daga wadannan... | |||
# Kaurace wa cin riba yana daga cikin imani. | |||
# Taqawa ita take sa bawa ya guje wa aikata abin da ya saba aikatawa wanda Allah ba ya so. | |||
# Bawa yana sa ran samun rahamar Allah ne yayin da ya yi biyayya ga Allah da Manzonsa. | |||
# Dalilin ambaton 'ninkin-ba-ninkin' a lamarin riba, saboda abin da yake faruwa ke nan a lokacin da ayar take sauka. Domin mutum a lokacin yakan ba wa wani bashi amma da kari, shi kuma sai ya biya shi a lokacin da suka kayyade a tsakaninsu. Idan lokacin biya ya yi ba shi da abin da zai biya, sai mai kudin ya kara masa lokaci, tare da kara masa wani kudin na riba a kan na da, da haka, da haka har ribar ta ninnika uwar kudin. Shi ne ya sa Allah ya yi bayanin abin da yake faruwa, ba wai ana nufin riba ba za ta zama haramun ba sai ta zama ninkin-ba-ninkin, kamar yadda wasu suke da'awa. Riba haramun ce komai karancinta, kamar yadda Allah ya bayyana a Suratul Baqara, aya ta 287 [[Quran/2/287]]. | |||
# Bayanin an riga an halicci wutar Jahannama, tana nan an tanade ta domin kafirai masu dawwama a cikinta har abada. Amma Musulmai masu sabon Allah, su za su shige ta ne a yi musu azaba gwargwadon laifuffukansu, sannan a fitar da su daga cikinta. | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |