Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 243: Line 243:
A wadannan ayoyi Allah yana lallashin zukatan Musulmi ne bayan abin da ya faru gare su a yakin Uhudu, na kashe da dama daga cikinsu da kafirai suka yi. Allah yana bayyana masu cewa, su zagaya a bayan kasa don su ga yadda sunnonin Allah suka faru ga al'ummomin da suka gabace su, su ga yadda Allah ya yi wa kafiran ga daukacin mutane, yana fayyace musu gaskiya, yana kuma nuna musu hanyar barna don su guje ta, sannan yana shiryar da masu taqwa zuwa mikakkiyar hanya, yana gargadin su da nisantar hanyoyin bata.
A wadannan ayoyi Allah yana lallashin zukatan Musulmi ne bayan abin da ya faru gare su a yakin Uhudu, na kashe da dama daga cikinsu da kafirai suka yi. Allah yana bayyana masu cewa, su zagaya a bayan kasa don su ga yadda sunnonin Allah suka faru ga al'ummomin da suka gabace su, su ga yadda Allah ya yi wa kafiran ga daukacin mutane, yana fayyace musu gaskiya, yana kuma nuna musu hanyar barna don su guje ta, sannan yana shiryar da masu taqwa zuwa mikakkiyar hanya, yana gargadin su da nisantar hanyoyin bata.


Allah kuma ya umarci Musulmi da kada su yi rauni domin abin da ya same su a yakin [[Uhudu]]; su ne ko yaushe suke a sama, kuma masu rinjaye matukar suna rike da imaninsu.
Allah kuma ya umarci Musulmi da kada su yi rauni domin abin da ya same su a yakin [[Uhudu]]; su ne ko yaushe suke a sama, kuma masu rinjaye matukar suna rike da imaninsu. Idan suna ganin an kashe musu [['yan'uwa]] a yakin Uhudu ko an yi wa wasu raununnika, to su tuna su ma kafiran irin haka ya faru gare su, an kashe wasu da dama daga cikinsu, an raunana wasu a yakin Uhudu da yakin Badar. Don haka kada su ci gaba da wannan damuwar da suke ciki, su sani wannan sunna ce ta Allah, haka yake jujjuya kwanaki a tsakanin mutane, yau ku yi nasara, gobe kuma makiyanku su yi nasara a kanku. To amma hikimar Allah a irin wannan aiki nasa ita ce don ya rarrabe tsakanin muminai na gaskiya da wadanda suke na jabu, kuma Allah ya nufi wasu muminai da yin shahada, watau wadanda za a kashe don daukaka addininsa. Allah ba ya son azzalumai, wadanda su ne kafirai da munafukai faɗararru wadanda suka zalunci kawunansu. Kuma yana daga hikimar Allah a wannan aiki nasa, ya tsarkake muminai daga zunubbansu a dalilin abin da ya same su na kisa da raunatarwa, domin idan ya zamanto koyaushe su suke ta samun nasara, to sai ji-ji-da-kai ya shiga zukatansu, sai kuma su sami raunin imani, wanda kuma shi ne zai jawo musu fushin Allah da azabarsa. Sannan kuma Allah ya yi alkawarin sai ya halakar da kafirai saboda dagawarsu da zurfafawa cikin zalunci da kafirci, wanda shi zai sa Allah ya kawar da su daga bayan ƙasa gaba dayansu.
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
 
# Kwadaitarwa a kan yin izinai da wa'azi daga abubuwan da suka faru ga al'ummomin da suka gabata.
# Nuni a kan cewa abin da ya faru ga masu ƙaryatawa na farko, irinsa zai iya faruwa ga masu karyatawa na yau da na gobe. Don haka al'umma su kwantar da hankulansu a kan duk wani zalunci da yake faruwa gare su, kuma su yi [[taka-tsan-tsan]] kada su shigar da kansu cikin masu karyatawa, sai uƙubar da ta same su su ma ta haɗa da su. Don haka a nan akwai lallashi, da kuma jan kunne.
# Allah yana kwantar da hankalin Musulmi cewa, gwagwarmaya tsakanin gaskiya da karya wani dadadden abu ne a tarihin kafuwar duniya, kuma koyaushe masu gaskiya ne suke samun galaba a kan makaryata ta hanyar taqwa da hakuri.
# Ana yin tafiya ne a bayan kasa don wata kyakkyawar manufa a shari'ance.  


[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]