Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 273: Line 273:
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 142-145 na Surar Ali Imran ==
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 142-145 na Surar Ali Imran ==
# 142) Yanzu kuma tsammanin za ku shiga Aljanna ne alhalin Allah bai bayyanar da masu yin jihadi daga cikinku ba, kuma bai bayyanar da masu hakuri ba. --[[Quran/3/142]]
# 142) Yanzu kuma tsammanin za ku shiga Aljanna ne alhalin Allah bai bayyanar da masu yin jihadi daga cikinku ba, kuma bai bayyanar da masu hakuri ba. --[[Quran/3/142]]
# Kuma hakika kun kasance a da can kuna ta burin mutuwa tun kafin ku gamu da ita, to hakika a yau ga ta kun gan ta alhali kuna kallo da ido. --[[Quran/3/143]]
# Kuma Muhammadu ba wani ne ba face Manzo kawai wanda hakika manzanni sun shude gabaninsa. Shin yanzu idan ya mutu ko aka kashe shi, sai ku juya baya a kan dugaduganku? Duk kuwa wanda ya juya baya a kan dugadugansa to ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma da sannu Allah zai saka wa masu godiya. --[[Quran/3/144]]
# Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne qayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za mu ba shi ita, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za mu ba shi ita. Kuma da sannu za mu saka ma masu godiya.
Tafsiri:
A nan Allah yana nuna kuskuren muminai masu zaton cewa za su shiga Aljanna don kawai sun yi imani, ba tare da Allah ya jarrabe su ya tantance masu jihadi dominsa da kuma masu hakuri.
Allah kuma ya tuna musu cewa, sun kasance a baya suna fatan haduwarsu da abokan gabarsu, suna mararin su yi mutuwar shahada; to ga shi a ranar Uhudu sun ga mutuwar da idanunsu, kuma sun kasa jurewa su yi hakuri, har su kai ga samun abin da suke fatan su samu.
Sannan Allah ya ci gaba da bayanin cewa, Annabi SAW ba mai dawwama ne a duniya ba; shi ma kamar sauran annabawa yake; wasu daga cikinsu mutuwa suka yi, wasu kuma kashe su aka yi. To yanzu idan shi ma ajalinsa ya qare ta hanyar mutuwa ko kisa, shi ke nan sai su yi ridda su bar addininsu? To wanda duk ya yi ridda ya bar addinin Allah, to ba zai cutar da Allah da komai ba, kuma Allah zai saka wa masu godiya daga cikin bayinsa.
Allah kuma ya bayyana cewa, babu wani rai a duniya da zai mutu sai da izinin Allah, wato idan ajalinsa ya yi. Sannan Allah ya bayyana cewa, yana ba wa kowa sakamakon aikinsa daidai da niyyarsa; wanda ya yi aikinsa don neman duniya, to sai Allah ya ba shi wani abu daga cikinta; wanda kuma ya yi aikinsa don neman ladan lahira, shi ma sai Allah ya ba shi wani abu daga cikinta kuma zai saka wa masu godiya.


[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]