Line 392: | Line 392: | ||
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 159-161 na Surar Ali Imran == | == Tarjama Da Tafsirin ayoyin 159-161 na Surar Ali Imran == | ||
# 159) To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu'amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi. --[[Quran/3/159]] | # 159) To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu'amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi. --[[Quran/3/159]] | ||
# Idan Allah Ya ba ku nasara, to ba wanda ya isa ya rinjaye ku, amma idan Ya taɓar da ku, to wane ne ya isa ya taimake ku in ba shi ba? Kuma muminai wajibi ne su dogara ga Allah Shi kadai. --[[Quran/3/160]] | |||
# Kuma bai dace ba ga wani annabi ya yi ha'inci. Duk wanda ya yi ha'inci kuwa zai zo da abin da ya ha'inta ranar tashin alqiyama. Sannan kowane rai a cika masa (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su (halitta) ba za a zalunce su ba. --[[Quran/3/161]] | |||
Tafsiri: | |||
A wadannan ayoyi Allah swt yana fada wa Annabinsa cewa, saboda rahamar da Allah ya yi masa ne, ya sa ya zama mai saukin kai ga sahabbansa, mai tausasa musu mu'amala, don haka duk suka tattaru a wurinsa, suna bin umarninsa. Da abin a ce shi mai mummunan hali ne, mai kakkausar zuciya, to da duk sun watse sun bar shi. | |||
An karbo daga Aɗa'u dan Yasar ya ce: "Na gamu da Abdullahi da Amru dan Asi, sai na ce masa: "Fada mini siffar Annabi SAW da take cikin littafin Attaura." Sai ya ce: "Kwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alqur'ani, inda Allah yake cewa: "Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargadi, kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona, na sa maka suna 'Mai dogaro', ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa ya yi gafara. | |||
pg458 | pg458 | ||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |