Line 554: | Line 554: | ||
# Kuma ku tuna lokacin da Muka yi wa Musa wa'adin (ganawa da shi) na kwana arba'in, sannan ku kuma kuka kama bautar ɗan maraƙi a bayansa, alhalin kuna masu zaluntar kawunanku. --[[Quran/2/51]] | # Kuma ku tuna lokacin da Muka yi wa Musa wa'adin (ganawa da shi) na kwana arba'in, sannan ku kuma kuka kama bautar ɗan maraƙi a bayansa, alhalin kuna masu zaluntar kawunanku. --[[Quran/2/51]] | ||
# Sannan sai Muka yi muku afuwa bayan haka, la'alla ko kwa yi godiya. --[[Quran/2/52]] | # Sannan sai Muka yi muku afuwa bayan haka, la'alla ko kwa yi godiya. --[[Quran/2/52]] | ||
# Kuma ku tuna lokacin da Muka ba wa Musa Littafin (Attaura) da abin da yake rarrabewa (tsakanin gaskiya da ƙarya) ko kwa shiriya. --[[Quran/2/53]] | |||
# Kuma ku tuna lokacin da Musa ya cewa mutanensa: "Ya ku mutanena, lalle ku kun mayar da ɗan maraƙi abin bauta, don haka ku tuba zuwa ga Mahaliccinku, kuma ku kashe kawunanku; wannan shi ne ya fi alheri a gare ku a wajen Mahaliccinku. Lalle shi Mai yawan karɓar tuba ne, Mai yawan jin ƙai." --[[Quran/2/54]] | |||
Tafsiri: | |||
Sannan kuma Allah ya sake tuna musu lokacin da Annabi Musa AS ya je ganawa da shi ta tsawon kwana arba'in, su kuma Banu Isra'ila bayan tafiyarsa suka riƙa bauta wa ɗan maraƙi, suka zalunci kansu ta hanyar ɗaukar hakkin Allah na bauta su sanya wa ɗan maraƙi. Daga baya da suka tuba sai Allah ya yafe musu ko wataƙila sa yi godiya. | |||
Allah ya faɗi yadda tubar tasu za ta kasance yayin da Annabi Musa AS ya kirawo su ya shaida musu cewa, sun fa zalunci kansu ta hanyar bautar ɗan maraƙi. Don haka dole ne su tuba; tubar kuwa ita ce, wadanda ba su yi bautar ba daga cikinsu su kashe wadanda suka yi, domin ta haka ne kadai Allah zai yafe musu laifinsu, don kasancewarsa mai karbar tuba mai jin kai. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Banu Isra'ila ba su da wani uzuri na aikata shirka. Sai dai kawai sun yi amfani da tafiyar Annabi Musa AS wajen ganawa da Allah, sai suka shiga aikata kafirci da barna a bayan kasa. | |||
# Rashin samuwar wani malami a cikin jama'a yakan haddasa bayyanar shirka da bidi'a a tsakaninsu. | |||
# Bayanin cewa bautar wanin Allah SWT babban zalunci ne. | |||
# Bayanin yalwar hakurin Allah SWT, kuma Allah yana gafarta shirka ga wanda ya tuba. | |||
# Hukunci mai tsanani da Allah (SWT) ya yi wa Banu Isra'ila yayin da ya umarce su da su kashe kawunansu kafin ya karbi tubansu. | |||
# Allah SWT ya ba wa Banu Isra'ila Littafin Attaura bayan ya kubutar da su daga Fir'auna da jama'arsa. Babbar hikimar yin haka shi ne domin su kafa al'umma mai bin shari'ar Allah, su zamanto suna da wani saƙo da za su rayu a kansa su kuma yi aiki da shi. | |||
# Kyakkyawan abu ne ƙwarai ga mai kira zuwa ga Allah SWT ya riƙa amfani da salo na laluna da lallashi don jan hankulan mutane su saurari maganarsa su karbi gaskiya daga gare shi. | |||
# Wajabcin tuba zuwa ga Allah SWT nan take bayan aikata laifi. | |||
# Allah SWT yana karbar tuban bayinsa komai girman laifinsu idan har sun tuba sun bar shi. | |||
# Tuna wa wanda ya yi wa Allah SWT laifi ni'imomin da ya yi masa don ya ƙara fahimtar munin laifinsa na yi wa Allah butulci. | |||
== Baqara 55-57 == | |||
# Kuma | # Kuma | ||
pg66 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |