More actions
No edit summary |
|||
Line 67: | Line 67: | ||
In-book reference: Book 4, Hadith 41 | In-book reference: Book 4, Hadith 41 | ||
HUKUNCIN KARATUN FATIHA A CIKIN SALLAH 3. | |||
@ Ba aya ba ce a fatiha, sa’annan kuma ba komai bace a cikin Surorin Kur’ani. | |||
Wannan it ace fahimtar Mazhabar Malikiyyah. | |||
Dalilin su itace kamar haka: | |||
• Hadisin Aisha (RA) ta ke cewa: “MANZON ALLAH SAW YA KASANCE YANA BUDE SALLAH DA KABBARA, DA KARANTA ALHAMDULILLAH RABBIL ALAMIN” | |||
Imam Muslim ya Ruwaito shi a Babin Sallah 1/357 Hadisi mai lamba 498. | |||
• Hadisin Anas (RA) yake cewa: “ NA YI SALLAH A BAYAN ANNABI SAW, DA ABUBAKAR DA UMAR DA USMAN, AMMA SUN KASANCE SUNA BUDE SALLAH DA ALHAMDULILLAH RABBIL ALAMIN”. | |||
Bukhari 2/188, Muslim 1/299, Abu Dauda a Hadisu mai lamba 782, Tirmizy a Hadisi mai lamba 246. | |||
A wata riwayar da Imam Muslim ya ruwaito daga Anas (RA) yace “SUN KASANCE (Wato Manzon Allah SAW, Abubakar, Umar, da Usman) BA SA AMBATON [BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM] A FARKON KARATO KO A KARSHEN SA”. | |||
• Daga cikin dalilan su na cewar Bismillah ba aya ba ce a fatiha, Hadisin Abu Hurairah (RA) yace: Na ji Manzon Allah SAW yana cewa: Allah Madaukakin Sarki yace: “NA RABA SALLAH TSAKANI NA DA BAWA NA GIDA BIYU, KUMA BAWA NA YANA DA ABUN DA YA TAMBAYA. | |||
IDAN BAWA YA CE: ALHAMDULILLAH RABBIL ALAMIN. | |||
SAI ALLAH SWA YACE : BAWA NA YA GODE MUN. | |||
IDAN BAWA YA CE: ARRAHMANIR RAHIM. | |||
SAI ALLAH SWA YACE: BAWA NA YA YABE NI………………” | |||
Sai su ka ce: Fadin Allah ‘NA RABA SALLAH” yana nufin Fatiha, ya sanya mata sunan Sallah, domin Sallah bata inganta sai da ita, da ace Basmalah aya ce a fatiha da an aambace ta a cikin wannan Hadisin na Kudsi. | |||
• Da ace Basmalah aya ce a fatiha da zai zama akwai Maimaicin [ARRAHMANIR RAHIM], sai ya zama Surar da zama kamar haka [بسم اللرحمن الرحيم, الحمد لله رب العالمين, الرحمن الرحيم] wannan sai ya zama kamar babu tsare na Balagha a kai. Kamar yadda suka fada. | |||
• Su ka ce rubuta ta a farkon surori anyi ne don tabarraki da ita (ma’ana don a bambance tsakanin sura da sura), rubuta ta a farkon surori ba yana nufin ita ma aya ce a kur’ani ba. | |||
Ibnul Arabi Almaliki yace: WANNAN ZAI NUNA MAKA CEWAR BA AYA BACE A KUR’ANI SABAODA SABANIN MUTANE AKAN TA, ALKUR’ANI KUMA BABU SABANI A CIKIN SA, BAYANAI SAHIHAI SUN NUNA [BASMALAH] BA AYA BA CE A FATIHA KO WANINTA, SAI DAI A CIKIN SURATUL NAMLI (Kamar yadda na bayyana hakan a baya). | |||
Ya ci gaba da cewa: LALLAI MAZHABAR MU [Malikiyyah] SUN RINJAYAR DA HAKA KO DA TA HANYAR HANKALI NE, WANNAN YASA TUN ZAMANIN MANZON ALLAH SAW, HAR ZUWA LOKACIN IMAM MALIK, A MASALLACIN ANNABI SAW DAKE MADINA, BABU WANI DA YA TABA KARANTA [بسم الرحمن الرحيم] A CIKIN SALLAH, SABODA KOYI DA SUNNAH…..” | |||
Don Karin bayani duba Tafsirin Qurdabi 1/93 da Ahkamul Kur’an na Ibnul Arabi 1/20. | |||
@ Aya ce a Fatiha da ko wace Surah. | |||
Wannan itace fahimtar Mazhabar Shafi’iyyah. | |||
KU BIYO NI SANNU A HANKALI INSHA ALLAHU. | |||
Muhammad Albani Misau | |||
16/2/2016. | |||
[[Category:Hadiths]] | [[Category:Hadiths]] | ||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/1]] | [[Category:Quran/1]] |