Line 87: | Line 87: | ||
# Adalcin Allah. Bayan ya soki kungiyar Ma'abota Littafi masu kafirce wa Allah, da kashe annabawa ba da wani hakki ba. To don kada wani ya zaci duka haka halayensu suke, sai Allah ya bayyana cewa, a cikinsu akwai na kirki, masu halaye da yake so. To haka ya wajaba a rika yin adalci, ko da kuwa da wanda ake sabani da shi ne. | # Adalcin Allah. Bayan ya soki kungiyar Ma'abota Littafi masu kafirce wa Allah, da kashe annabawa ba da wani hakki ba. To don kada wani ya zaci duka haka halayensu suke, sai Allah ya bayyana cewa, a cikinsu akwai na kirki, masu halaye da yake so. To haka ya wajaba a rika yin adalci, ko da kuwa da wanda ake sabani da shi ne. | ||
# Muhimmancin yawan karatun Alkur'ani cikin dare. Kuma sallar nafila ta dare ta fi ta rana saboda mai salla a lokacin ya fi tara hankalinsa wuri guda, domin babu wani abu da zai dauki hankalinsa kamar da rana, kuma akwai kauce wa riya a cikinta, da sauran wasu abubuwa masu rushe ayyuka, ko su nakasa su. | # Muhimmancin yawan karatun Alkur'ani cikin dare. Kuma sallar nafila ta dare ta fi ta rana saboda mai salla a lokacin ya fi tara hankalinsa wuri guda, domin babu wani abu da zai dauki hankalinsa kamar da rana, kuma akwai kauce wa riya a cikinta, da sauran wasu abubuwa masu rushe ayyuka, ko su nakasa su. | ||
# | #Muhimmancin umarni da kyakkyawan aiki, da hani da mummuna. Saboda muminai bayan sun inganta kansu da imani, kuma suna kokarin inganta wasu ta hanyar umartar su da kyawawan ayyuka, da kuma hana su munana, wannan kuwa shi ne matukar kamala. | ||
#An gabatar da ambaton karatun Alkur'ani a kan imani da Allah da ranar lahira, domin bai yiwuwa mutum ya yi imani da abu, sai bayan ya san shi, don haka idan sun karanta ayoyin Allah, sai su san mene ne ranar lahira, sannan su yi imani da ita. | |||
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 116-117 == | |||
# Lalle wadanda suka kafirta, dukiyoyinsu da 'ya'yansu ba za su wadatar da su komai ba a wurin Allah; kuma wadannan su ne ma'abota wuta; suna masu dawwama a cikinta. --Quran/3/116 | |||
# Misalin abin da suke ciyarwa a wannan rayuwa ta duniya kamar misalin iska ce mai tsananin sanyi, sai ta auka kan shukar wadansu mutanen da suka zalunci kawunansu, sai ta lalata ta. Kuma Allah bai zalunce su ba, sai dai kawunansu suke zalunta. --Quran/3/117 | |||
Bayan da Allah ya ambaci siffofin wadanda suka yi imani daga cikin kafirai, sai kuma a wadancan ayoyi Allah ya bayyana siffofin kafirai da azabar da ya tanada musu a ranar Alkiyama, domin a gane bambancin da ke tsakanin mumini da kafiri. Allah ya bayyana cewa yawan dukiya da 'ya'ya da kafirai suke takama da shi a duniya, a wurin Allah ba zai wadatar da su komai ba, domin ba zai kare su daga azabar Allah ba; za a jefa su wutar Jahannama ne, su dawwama a cikinta har abada. | |||
Kuma dukiyar da kafirai suke ta batarwa a nan duniya, da nufin yakar gaskiya da masu kira zuwa gareta, za su kashe ta ne a banza, domin ba za su taba cin nasara ba. | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |