Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 108: Line 108:
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 118-120 ==
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 118-120 ==


# Ya ku  --Quran/3/118
# Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku riki abokanan shawara wadanda ba a cikinku suke ba, ba za su sassauta muku mugunta ba, sun yi burin duk abin da zai kuntata muku, hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu; amma abin da zukatansu suke boyewa ya fi girma. Hakika Mun bayyana muku ayoyi; in kun kasance kuna hankalta. --Quran/3/118
# Sai ga shi ku dinnan kuna son su, su kuwa ba sa son ku, kuma ku kuna yin imani da Littattafai gaba dayansu, kuma idan sun gamu da ku, sai su ce: "Mun yi imani." Idan kuma sun kebanta, sai su rika cizon 'yan yatsu a kanku saboda bakin ciki. Ka ce: "Sai dai ku mutu da bakin cikinku." Lalle Allah Masanin abin da yake cikin kiraza ne. --Quran/3/119
# Idan wani kyakkyawan abu ya same ku sai ya bakanta musu rai, amma idan wani mummunan abu ya same ku, sai su rika farin ciki da shi; amma idan kuka yi hakuri, kuma kuka yi takawa, makircinsu ba zai cutar da ku komai ba. Lalle Allah Yana kewaye da sanin abin da kuke aikatawa. --Quran/3/120
Tafsiri:
 
Bayan Allah SWT ya gama bayani a kan halayen muminai da na kafirai, sai kuma a wadannan ayoyi yake gargadin muminai da kada suna nuna musu asirinsu, su bar 'yan'uwansu muminai domin wadannan kadiran bai kamata a amince musu ba; duk sa'adda suka sami wata dama ta cutar da muminai; to sai sun yi amfani da ita. Kullum kuma suna jiran su ga muminai sun fada cikin wata wahala su kuma su samu abin yi musu dariya. Saboda tsananin kiyayyarsu ga muminai, har ta kai ba za su iya boye kiyayyar a zuciyarsu ba, sai su rika subutar baki suna fito da ita a fili, duk da haka kuma kiyayyar da ke cikin zukatansu ta fi girma fiye da wadda bakunansu suka furta har muminai suka ji. Allah ya bayyana ayoyinsa ga muminai a fili, kuma bayanin zai amfane su har idan sun saurare shi, sun kuma fahimce shi.
 
An karbo daga Abu Sa'id Alkhudiri (rA) ya ce,
 
Annabi SAW ya ce: "Babu wani annabi da Allah ya taba aiko shi, ko wani halifa da Allah ya ba shi halifanci, face yana da kashi biyu na masu ba shi shawara; kashin farko suna umartar sa da kyakkyawan aiki, suna kwadaitar da shi a kai; kashi na biyu kuwa suna umatarsa da sharri, kuma suna kwadaitar da shi a kan aikata shi. To tsararre shi ne wanda Allah ya tsare. [Bukhari #7198]
 
Narrated Abu Sa`id Al-Khudri:
 
The Prophet (ﷺ) said, "Allah never sends a prophet or gives the Caliphate to a Caliph but that he (the prophet or the Caliph) has two groups of advisors: A group advising him to do good and exhorts him to do it, and the other group advising him to do evil and exhorts him to do it. But the protected person (against such evil advisors) is the one protected by Allah.' " https://sunnah.com/bukhari:7198
 


[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]