Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 250: Line 250:
# Nuni a kan cewa abin da ya faru ga masu ƙaryatawa na farko, irinsa zai iya faruwa ga masu karyatawa na yau da na gobe. Don haka al'umma su kwantar da hankulansu a kan duk wani zalunci da yake faruwa gare su, kuma su yi [[taka-tsan-tsan]] kada su shigar da kansu cikin masu karyatawa, sai uƙubar da ta same su su ma ta haɗa da su. Don haka a nan akwai lallashi, da kuma jan kunne.
# Nuni a kan cewa abin da ya faru ga masu ƙaryatawa na farko, irinsa zai iya faruwa ga masu karyatawa na yau da na gobe. Don haka al'umma su kwantar da hankulansu a kan duk wani zalunci da yake faruwa gare su, kuma su yi [[taka-tsan-tsan]] kada su shigar da kansu cikin masu karyatawa, sai uƙubar da ta same su su ma ta haɗa da su. Don haka a nan akwai lallashi, da kuma jan kunne.
# Allah yana kwantar da hankalin Musulmi cewa, gwagwarmaya tsakanin gaskiya da karya wani dadadden abu ne a tarihin kafuwar duniya, kuma koyaushe masu gaskiya ne suke samun galaba a kan makaryata ta hanyar taqwa da hakuri.
# Allah yana kwantar da hankalin Musulmi cewa, gwagwarmaya tsakanin gaskiya da karya wani dadadden abu ne a tarihin kafuwar duniya, kuma koyaushe masu gaskiya ne suke samun galaba a kan makaryata ta hanyar taqwa da hakuri.
# Ana yin tafiya ne a bayan kasa don wata kyakkyawar manufa a shari'ance.  
# Ana yin tafiya ne a bayan kasa don wata kyakkyawar manufa a shari'ance. Amma idan tafiye-tafien mutum ba  da wata kyakkyawar manufa ba ne, to wannan wahalar da kai ne kawai da barnar dukiya wadda shari'a ta hana.
 
# Alkur'ani littafi ne da ya zo da shiriya ga mumini da kafiri.
# Alkur'ani ya tattara bayanai a kan kowane abu kuma ga kowa da kowa, babu abin da Allah bai aje tushen bayaninsa a Alkur'ani ba, hakanan babu wanda bayanin Alkur'ani bai shafe shi ba.
# Babu masu amfanuwa da Alkur'ani sai masu taqwa. Don haka taqwa ita ce musabbabin samun shiriyar Allah, da kuma wa'azantuwa da Alkur'ani.
# Wanda duk bai wa'azantu da Alkur'ani ba, to ya tuhumi kansa.
# Duk sa'adda taqwar mutum ta kara, to shiriyarsa da wa'azantuwarsa da Alkur'ani ma za su karu.
# Imani yana kara sanya wa zuciya karfi da karin dogaro ga Allah a cikinta.
# Ya kamata mumini a kullum ya kasance mai karfin hali da rashin karayar zuci, domin duk sa'adda mutum ya karaya, ya yi rauni, to zai yi asarar alheri mai yawa. Da zarar ya tashi tsaye da karfinsa, to zai cim ma samun duk alhairin da yake nema da izinin Allah, domin ba wanda ya san gobe sai Allah.
# Duk sa'adda imanin al'umma ya karu, to daukakarta ma za ta karu, don haka bawa yana samun daukaka ne a wurin Allah, gwargwadon imaninsa.
# Allah swt yakan hada bawansa da nau'in jarraba iri-iri don ya gwada imaninsa.
# Allah swt ya sanya rayuwar duniya ta zama mai jujjuyawa ga dan'adam daga dadi zuwa wuya, daga wuya zuwa dadi ko daga sharri zuwa alheri ko daga alheri zuwa sharri, domin kada mutum ya nutsu a kan cewa kullum zai yi ta zama ne a yanayin jin dadi, wanda hakan yana iya mantar da shi ranar lahira. Kuma da a ce Allah ya aje duniya a yanayin azaba koyaushe, to da dan'adam ya jikkata.
# A cikin wadannan ayoyi, Allah ya lallashi zukatan muminai a kan matsalar da ta same su a yakin Uhudu sai ya bayyana musu wasu hikimomin da suka sa ya yi hakan, kamar haka: 1) Ita duniya Allah yana bayar da ita ga mumini da kafiri, saboda da man ita gida ne mai karewa, sabanin lahira, ita Allah ba ya bayar da ita sai ga mumini kadai. 2) Allah yana jarrabar bayinsa ya sa kafirai su yi galaba a kansu don tantance tsakanin mumini na gaskiya da wanda ba na gaskiya ba. 3) Da a ce koyaushe Musulmi su ne masu cin nasara a kan kafirai, to da sai mutane su rika shiga Musulunci ba don suna so ba, sai don suna tsoro. 4) Allah yakan dora kafirai a kan Musulmi, a wasu lokuta su kashe su, domin ya zabi shahidai a cikinsu. 5) Don Allah ya tsarkake muminai daga zunubbansu. 6) Don Allah ya halaka kafirai da azabarsa yayin da kafircinsu da zaluncinsu suka tsananta.
# Fadar Allah swt cewa: "Allah ba ya son azzalumai." yana nuna cewa, shahidai ba sa yin zalunci ta hanyar saba wa Allah da Manzonsa cikin ayyukansu. Don haka wanda ya mutu ta hanyar zaluntar wasu ba zai taba zama shahidi ba a wurin Allah, don Allah ba ya son azzalumai.
# Duk sa'adda aka siffanta wata daula da siffar zalunci, to ba za ta yi karbo ba, Allah zai kawar da ita komai dadewa.
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]