Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
No edit summary
No edit summary
Line 292: Line 292:
# Babban abin da yake yin tasiri wajen samun kyakkyawa ko mummunan sakamako daga Allah, shi ne niyyar bawa, ba kawai abin da yake na zahirin aikinsa ba.
# Babban abin da yake yin tasiri wajen samun kyakkyawa ko mummunan sakamako daga Allah, shi ne niyyar bawa, ba kawai abin da yake na zahirin aikinsa ba.
# Tabbatar da cewa, Annabi mutum ne kamar sauran annabawa da Allah ya aiko. Ya rayu har ya isar da saqon da aka aiko shi da shi, kuma ya rasu ya koma ga Ubangijinsa; don haka ba ya nan a duniya kamar yadda wasu suke riyawa.
# Tabbatar da cewa, Annabi mutum ne kamar sauran annabawa da Allah ya aiko. Ya rayu har ya isar da saqon da aka aiko shi da shi, kuma ya rasu ya koma ga Ubangijinsa; don haka ba ya nan a duniya kamar yadda wasu suke riyawa.
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 146-148 na Surar Ali Imran ==
# 146) Kuma sau da yawa an sami wani annabi (daga cikin annabawa), mabiya masu yawa sun yi yaki tare da shi, amma ba su taba yin rauni ba saboda abin da ya same su a tafarkin Allah, kuma ba su taba yin ragwanci ba, kuma ba su taba mika wuya ba. Kuma Allah Yana son masu hakuri. --[[Quran/3/146]]
# Kuma ba su da wata magana sai fadar: "Ya Ubangiji, Ka gafarta mana zunubanmu da ketare iyakar da muka yi cikin lamurranmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutanen da suke kafirai. --[[Quran/3/147]]
# Sai Allah Ya ba su ladan duniya da kyakkyawan lada na lahira. Kuma Allah Yana son masu kyautawa. --[[Quran/3/148]]
Tafsiri:
Bayan Allah ya ba da labarin abin da ya faru ga muminai a ranar yakin Uhudu, sanda aka samu cikas a yakin, har wasu daga cikinsu suka gudu daga fagen daga, sai kuma Allah ya nuna musu cewa, hanyar mabiya annabawa iri daya ce, watau hakuri da juriya a wurin jihadi, saboda haka su ma bai dace da su gudu ba.
A kan wannan ne Allah yake ba da labarin cewa, sau da yawa wani annabi daga cikin annabawa yakan yi yaki tare da mabiyansa masu yawa, kuma wani rauni ya same su a yakin, amma hakan bai sa sun karaya sun rabu da addininsu ko sun watsar da jihadin daukaka kalmar Allah ba; jikinsu bai yi sanyi ba, zukatansu ba su yi rauni ba, himmarsu ba ta dakushe ba, ba su ba makiyansu kai bori ya hau ba. Don haka Allah yake son masu hakuri irin wadannan.
Bugu da kari, duk irin abin da ya sami wadannan jarumai a yake-yakensu, ba abin da suke furtawa da bakunansu sai kawai neman gafarar Allah a kan zunubbansu ko abin da suka ketare iyakar Ubangijinsu a cikin lamuransu. Suna kuma rokon sa ya ba su ikon jajircewa, ya kuma ba su nasara a kan makiyansu kafirai. A sakamakon haka, sai Allah ya yi musu kyakkyawar sakayya ta duniya, ya ba su nasara da ganima da daukaka, kuma ga kyakkyawan sakamako na lahira, suka cim ma yardar Allah da dawwama a gidan Aljanna. Allah kuwa yana son masu kyautatawa, don haka ne ya yi musu kyautayinsa a duniya da lahira.
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Yin koyi da magabata na gari daga cikin al'ummomin da suka gabace mu.
# Wanda duk ya yi hakuri a wajen biyayya ga Allah Ta'ala, bai nuna gazawa ba ko raki, to wannan Allah zai so shi.
# Wanda duk zai dogara da dabararsa da karfinsa wajen neman biyan bukatarsa, to zai gamu da cikas da kaskanci, amma wanda zai rika addu'a da komawa ga Allah, yana neman taimakonsa, to wannan shi ne mai samun biyan bukatarsa.
# Gabatar da tuba da neman gafara a lokacin addu'a yayin da wani bala'i ya sauka. Domin duk wani bala'i da zai auku a duniya, to yana aukuwa ne saboda zunubban dan'adam, don haka ba abin da zai yaye shi, sai tuba da neman gafara.
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]