No edit summary |
No edit summary |
||
Line 310: | Line 310: | ||
# Wanda duk zai dogara da dabararsa da karfinsa wajen neman biyan bukatarsa, to zai gamu da cikas da kaskanci, amma wanda zai rika addu'a da komawa ga Allah, yana neman taimakonsa, to wannan shi ne mai samun biyan bukatarsa. | # Wanda duk zai dogara da dabararsa da karfinsa wajen neman biyan bukatarsa, to zai gamu da cikas da kaskanci, amma wanda zai rika addu'a da komawa ga Allah, yana neman taimakonsa, to wannan shi ne mai samun biyan bukatarsa. | ||
# Gabatar da tuba da neman gafara a lokacin addu'a yayin da wani bala'i ya sauka. Domin duk wani bala'i da zai auku a duniya, to yana aukuwa ne saboda zunubban dan'adam, don haka ba abin da zai yaye shi, sai tuba da neman gafara. | # Gabatar da tuba da neman gafara a lokacin addu'a yayin da wani bala'i ya sauka. Domin duk wani bala'i da zai auku a duniya, to yana aukuwa ne saboda zunubban dan'adam, don haka ba abin da zai yaye shi, sai tuba da neman gafara. | ||
== Tarjama Da Tafsirin ayoyin 149-155 na Surar Ali Imran == | |||
# 149) Ya ku wadanda suka yi imani, idan har kuka yi biyayya ga wadanda suka kafirta, to za su mayar da ku baya a kan dugaduganku, sai ku juya kuna hasararru. --[[Quran/3/149]] | |||
# A'a, Allah Shi ne Majibincin lamarinku; kuma Shi ne Fiyayyen masu taimako. --[[Quran/3/150]] | |||
# Da sannu za Mu jefa tsoro a cikin zukatan wadanda suka kafirta saboda abin da suka yi an sanya wa Allah kishiya, abin da bai saukar da hujja a kai ba; kuma makomarsu ita ce wuta. Kuma tir da makomar azzalumai (idan ta zama wuta). --[[Quran/3/151]] | |||
# Kuma tabbas hakika Allah Ya cika muku alkawarinsa yayin da izininsa; har zuwa lokacin da kuka yi rauni, kuma kuka yi jayayya a cikin umarnin (Manzo), kuma daga karshe kuka saba bayan (Allah) Ya nuna muku irin abin da kuke so. Cikinku akwai wadanda suke nufin duniya, kuma cikinku akwai wadanda suke nufin lahira. Sannan sai Ya kautar da ku kuka bar su don ya jarrabe ku; kuma tabbas hakika Allah Ya yi muku afuwa. Kuma Allah Ma'abocin falala ne ga muminai. --[[Quran/3/152]] | |||
# Ka tuna lokacin da kuke gudowa ba kwa waiwaye ma ku ga wanda yake baya da ku, kuma Manzo yana can bayanku yana ta kiran ku, sai (Allah) Ya saka muku da damuwa bisa damuwa domin kar ku yi bakin ciki bisa abin da ya kubuce muku, da abin da ya same ku. Allah kuma Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne. --[[Quran/3/153]] | |||
# Sannan bayan damuwa sai (Allah) Ya saukar muku da kwanciyar hankali har gyangyadi yana daukar wasu daga cikinku; amma wani sashin kuma tasu ta ishe su, suna yi wa Allah zato wanda ba na gaskiya ba, zato irin na jahiliyya; suna cewa: "Anya kuwa muna da ta cewa cikin wannan lamari?" Ka ce: "Lalle al'amari gaba daya na Allah ne." Suna boyewa a cikin rayukansu abin da ba sa bayyana maka shi; suna cewa: "In da al'amarin a hannunmu yake ai da ba a kashe mu a nan ba." Ka ce: "Ko da kun kasance kuna cikin gidajenku, tabbas da wadanda aka rubuta za su mutu sun fito da kansu, sun zo inda nan ne za su kwanta (dama)." Kuma Allah (Ya kaddara haka) don Ya jarraba abin da yake cikin qirazanku, kuma don Ya tace abin da yake cikin zukatanku. Kuma Allah Masanin abin da yake cikin zukata ne. --[[Quran/3/154]] | |||
# Lalle wadanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka hadu, Shaidan ne ya so ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas hakika Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai hakuri. --[[Quran/3/155]] | |||
Tafsiri: | |||
A wadannan ayoyi Allah yana gargadin muminai ne da kada su buye ma ta kafirai, domin yi musu biyayya zai iya jefa su cikin kafirci, su halaka duniya da lahira. Allah shi ne mai jibintar lamarin bayinsa, kuma shi ne mai ba da nasara; su kuma kafirai ba wata nasara ko taimako da za su iya ba muminai. | |||
Sannan Allah ya yi wa muminai albishir cewa, zai jefa tsoro a cikin zukatan kafirai, saboda shirkar da suke yi wa Allah ba tare da wata hujja ko wani dalili ba, a lahira kuma wutar Jahannama ce makomarsu, tir kuwa da wannan irin makoma ta azzalumai. | |||
Sai Allah ya cigaba da tunatar da sahabban Annabi SAW matsalar da aka samu a yakin Uhudu ta bangaren wasu daga cikinsu saboda saba wa umarnin Annabi SAW da suka yi, bayan da Allah SWT ya cika musu alkawarin da ya yi musu na ba su nasara a kan abokan gabarsu. Da farko Allah ya dora muminai a kan kafirai, har sun fara kashe su, sai kuma Musulmi suka fara ja da baya a sakamakon sabanin da ya barke tsakanin maharba hamsin da Annabi ya ajiye su a kan wani bangare na dutsen Uhudu, ya umarce su da kada su bar wannan wurin ko da kuwa sun ga alamun cin nasara tare da Musulmi. To amma sai suka saba wannan umarni yayin da suka ga Musulmi sun fara cin nasara a kan kafirai, suna bin su da sara da suka, sai kuma wasu suka tafi suna kwasar [[ganima]], suka bar wurin tsayuwarsu, amma wasu sun ci gaba da tsayuwa inda aka tsayar da su. Daga nan sai Allah ya juyar da lamarin muminai, galaba ta tabbata ga kafirai, suka juyo kan Musulmi da sara da suka ta gaba ta baya. | |||
Jabir dan Abdullahi rA ya ba mu labarin abin da ya faru a ranar Uhudu ya ce: "Mun hadu a filin yaki tare da mushrikai, Annabi SAW ya ajiye wasu maharba a kan wani dutse, ya shugabantar musu da wani sahabi ana kiran sa Abdullahi dan Jubai rA, ya kuma fada musu cewa: "Kada ku bar wurarenku ko da kuwa kun ga mu ne muka yi galaba a kansu ko kuma kun ga sun yi galaba a kanmu, to kada ku taho taimaka mana." Jabir ya ce: "Yayin da muka fara fafatawa da su, sai suka ranta a na kare, muka ga mata suna ta gudu suna hawan duwatsu, sun bude qwaurinsu ana ganin mundayensu. Da maharban nan na kan dutse suka ga haka, sai suka rika cewa: "Ganima! Ganima!!" Sai shugabansu Abdullahi ya ce musu: "Annabi SAW fa ya umarce mu da kada mu bar wurarenmu." Sai suka qi jin maganarsa, suka shiga kwasar ganima. Haka na faruwa, sai reshe ya juye da mujiya, mushirikai suka yiwo kansu, har suka kashe sahabbai saba'in. Daga nan Abu Sufyan ya leko yana cewa: "Muhammadu na cikinku? Dan Abu Quhafata yana cikinku? Dan Khaddab yana cikinku?" Duk Annabi SAW yana ce wa sahabbai: "Kada ku amsa masa." Sai Abu Sufyan ya ce: "Duk an kashe wadannan. Da a ce suna da rai, da sun amsa." Sai Umar ya kasa hakuri, ya ce: "Karya kake maqiyin Allah! Allah ya bar maka abin da zai ci gaba da tozarta ka." Sai Abu Sufyan ya ce: | |||
pg454 | |||
[[Category:Quran/3]] | [[Category:Quran/3]] |