Toggle menu
24.1K
669
183
158.4K
HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Toggle preferences menu
Toggle personal menu
Not logged in
Your IP address will be publicly visible if you make any edits.

Quran/3/Rijayar Lemo Tafsir2: Difference between revisions

From HausaDictionary.com | Hausa English Translations
Line 398: Line 398:
A wadannan ayoyi Allah swt yana fada wa Annabinsa cewa, saboda rahamar da Allah ya yi masa ne, ya sa ya zama mai saukin kai ga sahabbansa, mai tausasa musu mu'amala, don haka duk suka tattaru a wurinsa, suna bin umarninsa. Da abin a ce shi mai mummunan hali ne, mai kakkausar zuciya, to da duk sun watse sun bar shi.
A wadannan ayoyi Allah swt yana fada wa Annabinsa cewa, saboda rahamar da Allah ya yi masa ne, ya sa ya zama mai saukin kai ga sahabbansa, mai tausasa musu mu'amala, don haka duk suka tattaru a wurinsa, suna bin umarninsa. Da abin a ce shi mai mummunan hali ne, mai kakkausar zuciya, to da duk sun watse sun bar shi.


An karbo daga Aɗa'u dan Yasar ya ce: "Na gamu da Abdullahi da Amru dan Asi, sai na ce masa: "Fada mini siffar Annabi SAW da take cikin littafin Attaura." Sai ya ce: "Kwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alqur'ani, inda Allah yake cewa: "Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargadi, kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona, na sa maka suna 'Mai dogaro', ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa ya yi gafara.  
An karbo daga Aɗa'u dan Yasar ya ce: "Na gamu da Abdullahi da Amru dan Asi, sai na ce masa: "Fada mini siffar Annabi SAW da take cikin littafin Attaura." Sai ya ce: "Kwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alqur'ani, inda Allah yake cewa: "Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin mai shaida, kuma mai albishir mai gargadi, kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona, na sa maka suna 'Mai dogaro', ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa ya yi gafara. Kuma Allah ba zai karbi rayuwarsa ba, har sai bayan ya tsaida addini da shi, har mutane su furta Kalmar Shahada, wadda ita za ta bude idanun da suka makance da kunnuwan da suka kurumce da zukatan da suka toshe." [Bukhari #2124].  


‘Ata’ ibn Yasar reported: I met Abdullah ibn Amr, may Allah be pleased with him, and I said, “Tell me about the description of the Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, in the Torah.” Abdullah said, “By Allah, he is described in the Torah with some of what is mentioned in the Quran: O Prophet, We have sent you as a witness, a bringer of glad tidings, and to give warning, (33:45) and to guard over the illiterate, for you are My servant and My messenger. I have called you a trustworthy man, who is neither rude nor loud in the markets, nor does he return evil with evil, rather he pardons and forgives. Allah Almighty will not take him back until he has made straight the religion which was crooked, that they will say there is no God but Allah, through which eyes are made to see, ears are made to hear, and neglectful hearts are awakened.” [[https://www.abuaminaelias.com/dailyhadithonline/2012/10/15/prophet-described-tawrat-torah/ Source]: Ṣaḥīḥ al-Bukhārī 2125].
{| class="wikitable"
|+
|1
|‘Ata’ ibn Yasar reported: I met Abdullah ibn Amr, may Allah be pleased with him, and I said,
|An karbo daga Aɗa'u dan Yasar ya ce: "Na gamu da Abdullahi da Amru dan Asi, sai na ce masa:
|-
|2
|“Tell me about the description of the Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, in the Torah.”
|"Fada mini [[siffar]] Annabi SAW da take cikin littafin Attaura."
|-
|3
|Abdullah said, “By Allah, he is [[described]] in the Torah with some of what is mentioned in the Quran:
|Sai ya ce: "Kwarai an siffanta shi a Littafin Attaura da wasu siffofinsa da suke cikin Alqur'ani, inda Allah yake cewa:
|-
|4
|O Prophet, We have sent you as a [[witness]], a bringer of glad tidings, and to give warning, (33:45)
|"Ya kai wannan Annabi, lalle mun aiko ka a matsayin [[mai shaida]], kuma mai [[albishir]] mai gargadi,
|-
|5
|and to guard over the illiterate, for you are My servant and My messenger.
|kuma mai tsaron Ummiyyai, watau Larabawan da ba sa rubutu da karatu. Kai bawana ne, kuma Manzona,
|-
|6
|I have called you a trustworthy man, who is neither rude nor loud in the markets, nor does he return evil with evil, rather he pardons and forgives.
|na sa maka suna 'Mai dogaro', ba mai mugun hali ba ko mai kaushin zuciya ko mai yawan hayaniya a kasuwanni ba, ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai ya yi afuwa ya yi gafara.
|-
|7
|Allah Almighty will not take him back until he has made straight the religion which was crooked, that they will say there is no God but Allah, through which eyes are made to see, ears are made to hear, and neglectful hearts are awakened.”
|Kuma Allah ba zai karbi rayuwarsa ba, har sai bayan ya tsaida addini da shi, har mutane su furta Kalmar Shahada, wadda ita za ta bude idanun da suka makance da kunnuwan da suka kurumce da zukatan da suka toshe."
|}
Sannan Allah swt ya umarce shi da ya yi afuwa a kan kurakuransu da gajiyawarsu, kuma ya nema musu gafarar Allah, ya kuma nemi shawararsu cikin abubuwan da kan taso masu bukatar sai an yi shawara. Bayan shawara kuma, duk abin da ya ga shi ne ya fi maslaha, to ya ci gaba da zartar da shi, ya dogara ga Allah, Allah yana son masu dogara da shi.


Sai kuma Allah swt ya bayyana wa muminai cewa, idan har ya qaddara musu samun wata nasara, to babu wanda ya isa ya karya su ko ya ci galaba a kansu; idan kuwa ya yi watsi da su, ya kyale su, to  har abada babu mai iya taimakon su, don haka lalle muminai su dogara da Allah shi kadai.


pg458
Sannan Allah ya fadakar da cewa, ba ya daga cikin halayen annabawa su saci dukiyar ganima, domin Allah ya tsare su daga cin amana ko wani mugun hali, don haka bai dace a tuhume su da wani abu irin wannan ba.
 
Yawancin makaranta sun karanta ayar kamar haka: An yugal - watau suka yi rufu'a a kan (yu), suka kuma yi fataha a kan ayn. Ma'ana "Bai kamata ba a ha'inci wani annabi...".
 
Sai kuma ya ambaci sakamakon wanda ya saci dukiyar ganima da cewa, zai zo dauke da kayanta a ranar gobe qiyama a gadon bayansa, sannan kowane rai za a yi masa sakayya a kan aikinsa, kuma babu wanda za a zalunta komai.
 
An karbo daga Mu'azu dan Jabal rA ya ce: "Manzon Allah SAW ya aike ni, bayan na kama hanya na tafi, sai kuma ya aika a kirawo ni. Da na dawo sai ya ce: "Ko ka san don me na aika a kirawo ka? Kada ka kuskura ka dauki wani abu na ganima ba tare da izini na ba, domin yin haka satar dukiyar ganima ce wanda duk ya saci dukiyar ganima, to zai zo da abin da ya sata ranar alqiyama. Don haka ne na kirawo ka, sai ka tafi wurin aikinka." [Bukhari #200].
 
From Mu’az bin Jabal, he said: “The Messenger of Allah (saw) sent me to Yemen. As I traveled he sent someone after me to call me back so I returned. He said: ‘Do you know why I sent for you? Don’t acquire anything without my permission as it is illicit (Ghulul), and whoever acquired illicitly will bear what he acquired on the Day of Judgement. For this I called you. So proceed with your work’” ([https://systemofislam.com/article/funds-of-the-khilafah-state/12-illicit-money-from-the-rulers-or-civil-servants-money-acquired-illegitimately-and-fines source]: narrated by Tirmidhi).
 
An karbo daga Umar dan Khattab rA ya ce: "Ranar yakin Khaibara, wasu sahabbai sun zo suna lissafa wa Manzon Allah SAW cewa, wane ya yi shahada, wane ma ya yi shahada, har suka zo kan wani mutum, sai suka ce, wane ma ya yi shahada." Sai Manzon Allah SAW ya ce: "A'a, ba haka ba ne, ni na gan shi a wutar Jahannama saboda wani mayafi da ya sata daga dukiyar ganima." Sannan Manzon Allah ya ce: "Ya kai dan Khattab, tafi ka yi shela a cikin mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai muminai kadai." Ya ce: "Sai na fita na shelanta wa mutane cewa, babu mai shiga Aljanna sai mumini kadai." [Muslim #114]
 
It is narrated on the authority of 'Umar b. Khattab that when it was the day of Khaibar a party of Companions of the Apostle (ﷺ) came there and said:
 
So and so is a [[martyr]], till they happened to pass by a man and said: So and so is a martyr. Upon this the Messenger of Allah remarked: Nay, not so verily I have seen him in the Fire for the garment or cloak that he had stolen from the booty, Then the Messenger of Allah (ﷺ) said: Umar son of Khattab, go and announce to the people that none but the believers shall enter Paradise. He ('Umar b. Khattab) narrated: I went out and proclaimed: Verily none but the believers would enter Paradise. [[https://sunnah.com/muslim:114 Source]: Sahih Muslim 114]
 
'''Daga wadannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:'''
# Kwadaitarwa a kan kyawawan halaye da tausasawa wajen mu'amala, domin yin haka ne yake kawo [[hadin kai]] na al'umma, ya haifar da soyayyar juna; rashinsa kuma shi ne yake haifar da rarrabuwar kai da qiyayyar juna.
# Kyawawan halayen shugaba na addini sukan sa mutane su gane addinin, su karbe shi, yayin da miyagun halayensa kan iya sa mutane su nisanci addinin, su tsane shi.
# Neman shawara ibada ce da mai yin ta zai sami kusanci ga Allah.
# A cikin neman shawara, akwai hikimomi da yawa, daga cikinsu akwai:
## Hana shugaba yin mulkin kama-karya.
## Koya wa mutane yadda za su gudanar da al'amuransu, su sami gogewa a kai.
#Haramun ne
 
 
pg462
[[Category:Quran/3]]
[[Category:Quran/3]]