Line 521: | Line 521: | ||
Tafsiri: | Tafsiri: | ||
Daga nan har zuwa aya ta 61 Allah ya bayyana irin ni'imomi daban-daban da ya yi ta yi wa Banu Isra'ila, | Daga nan har zuwa aya ta 61 Allah ya bayyana irin ni'imomi daban-daban da ya yi ta yi wa Banu Isra'ila, amma maimakon su yi masa godiya ta hanyar biyayya ga Manzonsa Annabi Musa AS sai suka rika nuna butulci da kangare wa umarnin Allah da kin biyayya da girmamawa ga Annabi Musa AS. Allah ya kirawo su yana tuna musu irin ni'imominsa ga iyayensu wanda ko la'alla yin hakan zai sa musu godiyar Allah da shiga cikin addinin gaskiya na Musulunci, ya kuma tuna musu yadda ya fifita su a kan sauran al'ummomi na zamaninsu ta hanyar aiko musu da manzanni daga cikinsu da saukar musu da littattafai, sannan ya tsoratar da su azabar lahira, ranar da kowa ta kansa yake, babu wani wanda zai iya magance wa dan uwansa wata matsala a wannan rana, ko ya fanshi dan'uwansa kafiri ta hanyar ceto shi daga azabar Allah. | ||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Wajibi ne ga Banu Isra'ila su gode wa ni'imar da Allah SWT ya yi musu. Yana daga cikin godiyar Allah SWT su bi Annabinsa Muhammadu SAW da ya aiko musu. | |||
# Fifita Banu Isra'ila a kan sauran mutane fifiko ne da ya shafi zamaninsu kadai, saboda yawancinsu a wancan lokacin suna da ilimi da imani da kuma ayyuka nagari. | |||
# Bayanin tsananin ranar alqiyama wanda a cikinsa duk wata dangantaka ba za ta amafani kowa ba wajen ta kare shi masa azabar Allah ko ya samu sassauci, sabanin rayuwar duniya. | |||
# Kafirai ba za su sami ceto ko fansa ko taimako ba a ranar alqiyama. | |||
Baqara 49-50 | |||
# Kuma ku tuna lokacin da Muka kubutar da ku daga jama'ar Fir'auna wadanda suke dandana muku mummunar azaba, suna yanka 'ya'yanku maza, kuma suna kyale 'ya'yanku mata. A cikin wannan lamari akwai babbar jarraba daga Ubangijinku. --[[Quran/2/49]] | |||
# Kuma ku tuna lokacin da Muka raba muku kogi, sai Muka kubutar da ku, kuma Muka nutsar da jama'ar Fir'auna, alhalin kuna kallo. --[[Quran/2/50]] | |||
Tafsiri: | |||
A nan kuma Allah ya tuna musu irin yadda Fir'auna shi da magoya bayansa suka rika gana wa iyayensu azaba ta hanyar yanka 'ya'yansa maza da kyale mata don su bautar da su a gidajensu, amma sai Allah ya kubutar da su daga wannan matsananciyar azaba. Wannan kuwa ba karamar ni'ima ce gare su ba, don haka ya zama wajibi a kansu su yi wa Allah godiya. | |||
Sai kuma Allah ya ambata musu wata ni'imar ta daban wadda ya yi musu lokacin da Fir'auna da rundunarsa suka biyo su don halakar da su. Bayan sun iso gabar kogi sai Allah ya umarci Annabi Musa AS da ya daki kogi da sandarsa, sai ko ta rabu gida biyu, suka ga hanya totar a gabansu suka bi suka ketare. Lokacin da Fir'auna ya iso shi da rundunarsa suka fara bi ta wannan hanyar sai Allah mayar da wannan kogi ta hade da su suka halaka gaba daya, mutanen Annabi Musa AS suna gani domin su huce haushin abin da ya faru gare su a baya. | |||
'''Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:''' | |||
# Babbar | |||
pg62 | |||
[[Category:Quran]] | [[Category:Quran]] | ||
[[Category:Quran/2]] | [[Category:Quran/2]] | ||
[[Category:Rijiyar Lemo]] | [[Category:Rijiyar Lemo]] |